Uncategorized

Kamanni Complete Hausa Novel

 

A hankali suke fitowa daga mall din tana rik’e da hannunsa tana motsi da lips dinta tana bashi labari yayinda yake sauraronta yana murmushi, dafe kai yayi yace,

“Gosh… Rumana jirani a mota, I will be right back…”.

Rumana tace, “Alright, Yaa Rafeeq”.

Rafeeq ya juya ya koma cikin mall din yayinda Rumana ta soma tafiya a hankali, tana da matuk’ar kyau, brown skin, tall, slim, gorgeous and breathtaking, tana sanye da gown tayi rolling veil….

************

Ahmad yace, “Imran ka ragewa kanka damuwa in sha Aallah za’a samu Jidda a cikin koshin lafiya…”.

Imran yace, “Ahmad dole ne ka ganni a cikin damuwa, kwanaki biyu kenan babu Jidda babu labarinta, a koda yaushe Ammi a cikin kuka take, Abbi ma daurewa kawai yake amma yana cikin matuk’ar tashin hankali… Babu wanda hankalinsa yake kwance a cikin family din nan…”.

Imran ya tsaya cak daga maganar da yake a sanadin hango Rumana da yayi jingine da mota, yace,

“What… Jidda…”.

Ahmad ya kalli inda take yace,

“Wallahi ita ce…”.

Imran ya k’arasa inda take da gudunsa tareda hugging dinta yana mai sakin ajiyar zuciya yace,

“Jidda you are back… Alhamdulilahi…”.

Rumana ta tureshi tana kallonshi cike da mamaki tace,

“How dare you…”.

Imran yace, “Jidda…”.

Rumana tace, “Pardon… Did you know me…”.

Imran ya kama hannunta yace,

“Jidda am your brother… Imran… Ki zo muje gida, tun bayan b’acewarki family dinmu suke cikin tashin hankali…”.

Rumana ta dafe kai tana kallonshi da mamaki tace,

“Pardon… My name is not Jidda my name is Rumana… And ban sanka ba…”.

Imran ya daka mata tsawa,

“Jidda!…”.

Wannan ne ya janyo hankalin mutane zuwa wurinsu, mutane suka taru a kansu, Rumana tace,

“Ban sanshi ba yazo yana kirana Jidda this and that…”.

Imran yace, “Karya take, k’anwata ce yau kwana biyu kenan rabonta da gida an nemeta an rasa…”.

Wani dattijo yace, “Ba sai ka rantse ba, duk wanda ya ganka ya ganta zai tabbata jininka ce…”.

Wani saurayi yace, “Hakane… Tabbas…”.

Rumana tace, “I tell you ban sanshi ba…”.

Ahmad yace, “Don Allah ku taimaka mamu, wallahi k’anwarshi ce…”.

Rumana ta dafe kai ganin babu wanda ya fahimceta a cikin mutane, Imran ya zaro wayarshi yana nunawa mutanen hotuna, Rumana ta dafe kai ganin babu wanda ya fahimceta tace,

“Let go, muje… Wadanda zaka kaini wurinsu zasu saka ka maidoni ne tunda na tabbata sunana Rumana not Jidda kuma ban sanka ba…”.

Imran ya rik’e mata hannu ta fizge, yayi gaba tabi bayanshi, Ahmad yana biye dasu, Imran ya bude mata backseat ta shiga yayinda shi da Ahmad suke zauna a frontseat, tana ji Imran yana kiran waya yana sanar da cewa yaga Jidda, cikin ranta tace,

“Whatever…”.

A bakin wani katon get sukayi horn mai guard ya wangame get, mansion ne babba amma Rumana kallon akurkin kaji take mashi compare tun inda ta fito….

Ahmad yace, “Hajiyarmu ta kira…”.

Imran yace, “Send my regard…”.

Ahmad yace, “Sure… Jidda sai na shigo…”.

Rumana ta tab’e baki tace,

“Wacce Jidda… Sunana Rumana, zaku mayar dani inda kuka daukoni ne…”.

Imran ya fito tareda bude mata backseat ta fito tana k’arewa compound din gidan kallo, Imran yace,

“Muje…”.

Rumana tace, “Ai dole zan je ko don aita ta kare su saka ka mayar dani inda ka daukoni…”.

Yayi gaba tabi bayanshi, saida suka shiga parlor sannan tsoro ya kamata ta soma nadamar biyoshi da tayi, what if aka ki mayar da ita, what if shiri ne aka yi domin kid*napping dinta, yanzu haka Yaa Rafeeq yana can yana nemanta, taja tayi turus yayinda tsoro ya kamata, Imran yace,

“Ammi… Abbi… Na samo Jidda… Ina ta kira baku picking…”.

Abbi da Ammi sukayi appearing da saurinsu yayinda wata cute yarinya er kimanin shekaru shidda ce ta rugo tayi hugging dinta tace,

“Adda Jidda Ina kikaje ne Ammi tana ta kuka…”.

Rumana ta ture yarinyar tace,

“Ke ni sunana Rumana, am not Jidda… Hajiya da Alhaji ku saka d’anku ya mayar dani inda ya daukoni, tun a can nike fad’a mashi I’m not Jidda, my name is Rumana amma yaki ji, Yaa Rafeeq yana can yana jirana, ku saka ya mayar dani inda ya dauko…”.

Ammi ta karaso da sauri tareda kamata tana hawaye tace,

“Itace… Jidda ce…”.

Rumana tace, “You are mistaken, I’m not Jidda…”.

Ammi tace, “Jidda mi kike cewa haka, I’m your mother… Where have you been?”.

Rumana ta durkushe tareda fasa k’ara saying,

“I’m not Jidda… Sunana Rumana…”.

Imran yace, “Abbi ka kira doctor…”.

Ganin da gaske suke ta soma ihu da duk karfinta tana fasa duk abun da yazo gabanta….

“Na boni sunyi kidn*apping dina… Yaa Rafeeq kazo ka ceceni…”.

Saida doctor yazo yayi mata allurar bacci sannan tayi lamo bacci yayi awon gaba da ita….

*********

 Jidda ce takure a daki mai duhu daga ganinta ta wahala a tsoroce take, wani abun mamaki shine kamarta daya sak da Rumana kamar carbon copy haka suke, wani katon gardi ne ya shigo tareda daka mata tsawa, saida ta firgigita tayi baya da sauri, yace,

“Ance ki bada numbar danginki kinki, idan kika ji wuya da kanki zaki bada…”.

Ya dungure mata takeaway ya juya ya fice tareda dannawa dakin key, da sauri ta bude takeaway din ta rarumi abincin tana turawa da saurinta daga gani ba karamar yunwa takeji ba, saboda sauri har kwarewa takeyi, can ta dafe jiki tana b’ata fuska, ta soma kwarara amai….

wannan littafin na kudi ne duk wacce take so naira dari ukku ne 300, VIP 700, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

For those of you asking yadda zasu biya kudin, zaku biya ne ta hanyar tura hoton Katin MTN via WhatsApp 09169472057, ko kuma VTU/Transfer ta 09169472057, sai kuyi screenshot ku tura via WhatsApp 09169472057

WRITTEN BY:      HAFSAT HISHAM

NOVEL NAME:   KAMANNI

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         66KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      1- SEPTEMBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦300 KO 700

Proceed To Download Kamanni Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button