Uncategorized

Macijine Shi Page 41-42 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 41/42

_______________Adeeb yana barin gurin saiga rashy ya ƙaraso,zama yayi kusa da mahaifiyar tasa tare da sumbatar hannunta,

Kansa ta shafa tana faɗin “,magajin faɗa prince Rashad Muhammad ashraf”ta faɗa cike da jin dadin sunan.

Download>>> Bakar Inuwa By Billy Abdull

Turo baki Rashad yayi tare da kallon ammi yace ” ammi ta yaya zan zamo magajin fadar?bayan kinƙi yin wani abu akan wannan al’amari,ki dubafa,Adeeb ya dawo gida,kuma cikin ƙoshin lafiya yake,kina tunanin abie zai bar Adeeb ne,sannan Ni ya ɗorani akan karagar?

Shiru ammi tayi tana kallon Rashad har ya kai ƙarshe azancensa,kafin tayi wani murmushi kana tace ” Rashad kenan,kasan dai Adeeb yana jin maganata,sannan baya tsallake umarnina, yanzu akwai Abinda nake tunani akan yarinyar can ,daya zo da ita. Ina son tabbatar da wani abu ne game yarinyar ,wannan sarƙa ta wuyanta tabbas nasan iyalan dake da irin sarƙa,kuma sun rasa yarinyar su tsawon shekaru,

Amma idan har na tabbatar da zargina akanta,to zanyi iyakar ƙoƙarina na ganin bata haɗu da ahalin nata ba,dan haduwarsu da ahalin babban koma bayane agareni. Masanin ido kawai ,zakaga abinda zanyi akan wannan al’amarin.

Murmushi Rashad yayi tare da jin wani sanyi cikin ransa,dan yasan tabbas mahaifiyar tasu zatayi ƙoƙarin akan wannan al’amarin.

“Amma ammi Zulaihat fa?kinsan yadda take ƙaunar Adeeb ,kada ta bamu matsala”cewar Rashad kenan yana gutsirar dabino .

“Barni da zulaihat,bana jinta ko kaɗan ,yarinyar da ba wani hankali ta cika ba,itama bazan bari ta auri Adeeb ɗin ba ,lokaci kawai nake jira in maidata can gida”ammi ta faɗa cike da murmushi akan fuskarta.

Sun jima suna tattauna ita da Rashad agurin ,kafin suka koma cikin gida.

Fattu kuwa suna shiga toilet nanny ta hada mata ruwan wanka mai zafi,tace tayi wanka maza.

Bayan tayi wankan ne ,nanny ta bata wannan pant din tasa ajikinta ,sannan suka fito,har zuwa lokacin kuka fattu keyi,har yanzu jinin bai daina zubowa ba,yanzu idan jinta ya kare ya zatayi?mutuwa fa zatayi kenan.

Nanny sai rarrashinta take akan taci farfesun nan tasaha magani amma taki,kuma har lokacin marar ta ciwo take mata.

Suna cikin haka saiga Adeeb ya shigo ɗakin,tana ganinsa jikinta ya ƙaru.tun kafin ya zauna ta fara magana.

” Hamma na shiga uku har yanzu jini na zuba yake ,tsoro nake karya kare In mutu,dan Allah Hamma ka taimaka min” fattu ta faɗa tana mai miƙa masa hannu cikin kuka sosai.

Karanta Littafin>>> Matar Hariji Page 31-40 Hausa Novel

Da ɗan sauri Adeeb ya ƙaraso kusa da ita ya zauna,kallonta yake cike da tausayi,kafin ya riƙe hannunta wanda take miƙa masa yana ɗan murzawa kana yace” kina so ya daina zubowa ” ya faɗa cikin sanyin muryarsa.

Da sauri fattu ta jinjina kai tana hawaye.

” To kiyi shiru,ki daina kuka, sannan ki nutsu kici abinci Kisha magani,zakiga ya daina zubowa” Adeeb ya faɗa yana mai share mata hawaye wasu na zubowa.

“Hamma da gaske idan na daina kukan zai daina zubowa Ni tsoro nakeji kar jinina ya ƙare” ta faɗa cikin muryar kuka tana mai shagwabe fuska.

Jinjina mata kai yayi yace ” sosai ma kuwa,kuma jininki bazai ƙare a idan kika daina kuka” 

Ahankali fattu ta sanya bayan hannunta ta share hawayen,tana mai kallon Hammana nata.

Farfesun ya karba ahannun nanny ya fara ɗiba da cokali yana bata abakin,haka take cin farfesun kamar magani,kusan lokaci shida tayi tace ta koshi.

Bai takura mata ba,ya ajiye flate ɗin ,magungunan ya bare tare da miƙa mata.yamutse fuska tayi tana mai turo baki,alamun bata so.

Kallonta Adeeb yayi kafin yace ” ok baki son abun ya tsaya kenan?” 

” Ina so Hamma amma Ni bana son wannan abun aradu” ta fada cike da shagwaba, kafeta yayi  da idanunsa masu matuƙar haske da ɗaukar hankali,wani irin yakeji idan tana masa shagwabar nan,nan take zaiji jikinsa yayi week, kasala ta lullubeshi ,gara yayi ya bata maganin nan kar ayi abin kunya gaban nanny.

Hannunsa yaji fattu ta kama cikin nata tattausan hannu ,wani yuummmmm!! Yaji gaba ɗaya jikinsa ya ɗauka ,ahankali ya lumshe idanunsa yana mai sauke ajiyar zuciya.

” Hamma zansha to  kabani”fattu ta faɗa tana mai ƙara damke hannun Adeeb cikin nata.

Ƙara damke idanunsa yayi tamau yana mai fidda wani sauti da ɗan sauri,kusan minti biyu idanunsa na runtse ,kafin ya budesu,har sun sauya kala daga fari tas zuwa ɗan jaa kadan.

Ahankali ya zare hannunsa daga cikin nata,jikinsa sam ba kwari,maganin ya mika mata ,buɗe baki tayi ya saka mata maganin sannan ya bata ruwa.da gyar ta hadiye maganin tana ƙoƙarin yin amai.

Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungume ta tsam-tsam ,yana ɗan shafa bayanta slowly.

Lumshe idanu fattu tayi tana mai  shaƙar daddaɗan kamshi jikin Adeeb,lokaci guda kuma taji ciwon marar ta na raguwa sosai.

Shima Adeeb idanu arufe yake shafa bayan fattu,yana mai jin wani yanayi atattare dashi ,dadinsa ma nanny ta bar ɗakin tuni.dan haka gyara zama yayi ,tare da jingina bayansa jikin gado.sosai yake jin dadin yanayin da suke ciki ahalin yanzu,gaba daya yanayinsa ya sauya.sosai yake jin kansa cikin hali na buƙatuwa,wanda har wani hucin iska yake fesarwa daga bakinsa.

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 11-20 Hot Romantic Hausa Novel

Ahankali ya dago kan fattu tare da ƙura mata idanu,itama kallonsa take ,dan wani iri takeji ajikinta,bata san me takeji ba,amma kawai tana so hammanta yayi ta shafa mata bayanta. 

Ahankali Adeeb ya kira sunanta” Hulwa”can cikin makoshinsa,kallonsa take jin ya kira sunan Hulwa kuma yana kallonta.

Bai damu da kallon da take masa ba yaci gaba da magana ” me kike buƙata yanzu?ina ne yake miki ciwo” ya faɗa kamar mai yi mata  rada asaitin kunnen ta.

Da sauri ta ƙanƙame dantsen hannusa tana mai lumshe idanunta,dan wani irin abu dataji yana mata yawo cikin jikinta,lokacin da sautin muryarsa tare da iskar bakinsa suka doki kunne ta.

“Hammmma” ta furta ahankali cikin jan sunan.

Kallonta yake tare da karantar yanayin da take ciki,ko shakka babu yasan tana jin makamancin abinda yake ji ajikinsa,saidai shikam baida niyyar cutar da fattu,ko kaɗan dole yake nesanta kanshi daga gareta ,dan gudun faruwar wani abu.

Ahankali ya ƙara maimaita mata tambayar ,saidai wannan karon bai kai bakinsa saitin kunnenta ba.

“Hannunsa fattu ta kamo tare da ɗorawa asaitin mararta” marar Tata kuwa tayi zafi sosai ,kallon fuskarta Adeeb yayi wacce har yanzu idanunta ke rufe, 

“Nan ke miki ciwo” Adeeb ya faɗa ahankali muryarsa na dan rawa.

Jinjina kai fattu tayi ba tare da ta buɗe idanunta ba.

Ahankali ya kwantar da ita akan gadon,sannan ya ɗan daga doguwar rigar dake jikinta,nan take santala -santalan farare cinyoyinta suka bayyana,kallo Adeeb yabo cinyar Tata dashi,yana mai ambaton sunan Allah cikin ransa.

Ahankali yake ɗan shafa marar Tata tare da dan dannawa kadan kadan ,kamar yana mata tausa , shiru fattu tayi tana jin wani irin sanyi da daɗi na ratsa dukkan sassan jikinta,sosai take jin dadin abinda Hamma ka mata,dan kuwa tuni ta nemi ciwon mararta ta rasa,sai wani nishi take ahankali tana mai riƙe zanin gadon .kwantowa Adeeb yayi tare da ƙurawa lips ɗin ta idanu,buɗe ido fattu tayi tana mai kallon fuskarsa,

Kusan minti biyu suna kallon juna,kafin Adeeb yaji bazai iya ɗaurewa ba kawai ya hada bakinsu guri ɗaya ya fara kissing ɗin fattu.

Kusan mintina biyar zuwa bakwai suka ɗauka cikin wannan halin,gaba daya Adeeb ya fice daga hayyacinsa ,Banda nishinsa ba abinda kake juyowa aɗakin,yayinda fattu kuwa tayi lakwas tana amsar sakonsa, da alama dai itama tana karbar sakon yadda ya kamata.

Kamar wanda aka tsikara,Adeeb yayi saurin zare bakinsa tare da mikewa yayi hanyar fita daga dakin yana tangadi kamar ɗan giya.

Fattu ma saurin juya bayanta tayi tare da runtse idanunta,wani irin abu takeji yana yawo ajikinta ,kuma bataso hamma ya daina mata wannan abun ba sam.

Adeeb yana fitowa daga dakin fattu sukayi kiciɓis da Rashad shikuma yana shigowa babban falon,

Baki sake tashar ke kallon Adeeb ,ganin yanayin da yake ciki,kar dai ace Adeeb zagayawa yake gurin yarinyar nan fa? Dan kallo daya Zakayiwa Adeeb kasan yana cikin hali na buƙatuwa.

Kodai dama kafuwarta ce bamu sani ba ?yace taimakonsa tayi shima yake son taimakonta?(Dan ba Wanda yasan meye alaƙar dake tsakanin fattu da Adeeb ,hatta mai martaba ,sam Adeeb bai fada masa ba.

Shikuwa Adeeb ko kallon inda Rashad take baiyiba ,yayi ficewarsa daga ɗakin,Dan shikadai yasan meke damunsa.

Kai tsaye Rashad ya nufi dakin da fattu ke ciki,tana kwance  har lokacin bata ko motsaba, kallonta yake cike da tsantsar sha’awar ta ,abun tayi ta ko ina kalli hips ɗin ta kamar zai fasa rigar nan,ahankali ya Rashad ya ƙarasa bakin gadon yana mai karewa fattu kallo ,wani irin kashe ido yake yana mai jin kamar ya ruƙunkumeta ajikinsa,hmmmmm Allah ya kamu gobe ,ko kaɗan bazan saurarawa babyn nan ba,Rashad ya faɗa yana mai miƙa hannu da nufin taba abinda ke taimake masa idanu ajikinta.

” Kai- kai ɗan nan menene haka?me zakayi mata ajikin nata ?zo maza ka fice” nanny ta faɗa tana nuna masa hanyar waje.

Dan sosa kai Rashad yayi yana mai hararar nanny kafin ya fice daga dakin yana faɗin “wllh tsohuwar nan ta fiye samun guri,duk wannan banzan ne ya bata dama ,amma zanyi maganinta  ne.ya faɗa yana mai ficewa daga ɗakin.

Ammi kuwa waya ta dauka tare da kiran wata number,bugu biyu aka daga ,murmushi ammi tayi tana faɗin ” ƙawatafatan dai kina hanya ,zakizo gurin taron namu ?”

Ta can daya bangaren bansan me akacewa ammi ba ,na dai ji tace “hmmmmm ke dai ki bari kawai saikinzo dan akwai gagarumar matsala sosai” 

Shiru ta ɗanyi kaɗan kafin tace ” shikenan Allah ya kawoki lafiya  dole mu san abinyi” ta faɗa cike da daure fuska.

Ajiye wayar tayi tare da yin shiru ,da’alama tayi zurfi cikin tunanin mafita.

Adeeb kuwa yana shiga part dinsa ya zube akan kujera,ko takalmin bai iya cire wa ba ,kwanciya yayi rub da ciki akan kujerar ,idanunsa alumshe ya dafe mararsa da hannun damarsa ,fuskarsa ayamutse. Sai huci yake sauƙewa.

Wayarsa ce take ta faman ringing ,Amma ya kasa ɗagawa,haka tayi ta ƙara harta tsinke.

Dole ya ɗauki mataki ,dan gaskiya yana cikin matsala ,idan haka taci gaba da kasancewa to zai shiga damuwa matuka.

Ajiyar zuciya sauke arako na ba adadi,yana mai kara damke mararsa,ba abinda yake ji dagani sai fattu kwance kan ƙirjinsa,yayinda yanayinsa ke kara yin nisa.

“Washhhh ” ya furta ahankali yana mai dantse lips ɗinsa na ƙasa.

Nan da nan jikinsa ya kama rawa zazzaɓi mai zafi ya rufeshi ruff..

Muje zuwa masu karatu.

Anty mammy  ce

Karanta Littafin>>> Macijine Shi Page 39-40 Hausa Novel

 Mrs babi💘💘

Share and comment 

Fisabilillah.

Back to top button