Hausa novels

Halysaah Page 200 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 200…Hadiyah na zaune ita kadai a bedroom din khaleesat the next day da yamma, tun safe ta shiga dakin Mami ta gaisheta da Aunty Farida dake tare da Mamin kuma ko da wasa bata yarda sun hada ido da Mami ba a dakin, a haka tayi just 5 minute cikin dakin sannan ta tashi ta fita ta dawo dakin Khaleesat, shi ne bata sake komawa ba har zuwa yanxu da yamma, Mai martaba kuwa tun sannu da zuwan da ta fita tayi masa a downstairs jiya shi ma tare suka je da Khaleesat, shi ne bata sake komawa ta gaishesa ba yau, Khaleesat ta bude kofar dakin ta shigo da leda a hannunta, suna hada ido da Hadiyah ta fara murmushi ta karasa har gefen gadon ta zauna ta ajiye ledan hannunta tana kallon Hadiyah still smiling, Hadiyah tace “Meye kike kallona haka? Har kin gama girkin?” Khaleesat tace “Ba dai kin ki sakkowa mu yi ba, to har na gama, Mai martaba sai da yace me yasa babu ma’aikata a gidan, kilan yanxu za a kawo masu aiki” a hankali Hadiyah tace “The work is too much in this House, kuma bai kamata kina aiki ba a matsayin ki….” Khaleesat na murmushi tace “Wai ke me yasa baza ki saki ranki bane tun safe kina ta zaune a nan kamar wata mara gaskiya, kin koma gun su Mami ne?” Kai kawai Hadiyah ta girgiza mata, kamar bazata ce komai ba, sai kuma cikin sanyin murya tace “Mai martaba na parlon sa a downstairs ne? Har yanxu fa ban je na gaishesa ba, don Allah ki rakani mu je” Khaleesat tace “Ai sun ma fita da su Ya Jawwad basa gidan” Hadiyah tace “Tun safe suka fita?” Khaleesat couldn’t stop smiling, ta girgiza mata kai tace “A’a, daxu da rana suka fita….” Hadiyah tace “Hope you are not angry ban sakko na taya ki girki ba” Khaleesat tayi dariya tace “Haushin me zan ji, ai ga wani aikin nan na kawo maki….” Tana fadin haka ta matsar da ledan hannunta kusa da Hadiyah tace “Shan su ma kadai aiki ne, ba sai kin taya ni girki ba” Hadiyah tace “Meye wannan” Khaleesat tace “Dubawa zaki yi ai” Hadiyah ta bude ledan tana kallon abinda ke ciki, wani kallo tayi ma Khaleesat tace “Meye haka kuma?” Dariya sosai Khaleesat ke yi har da Kyakyatawa, Hadiyah ta hade rai tana ta kallonta, sai da wayar Khaleesat dake hannunta ya fara ringing sannan ta hadiye dariyarta ta kalli wayar don ganin me kiranta, Hadiyah ma kallon wayar take don saving din number tayi da Mi Vida, Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne, after some seconds ta shagwabe murya tace “Na gama mana, ka zata abincin bai yi dadi bane, in kayi order ya za ayi da wannan da na dafa din?” A hankali tace “Ohk tohm sai kun dawo” Daga haka ta katse wayar, Hadiyah dake kallonta tace “Cewa yayi za ayi order din abinci?” Khaleesat tace “Wai yana ganin kamar girkin zai min yawa, bai san har na gama ba” Hadiyah tace “Tuntuni basu ce za ayi order ba sai bayan da kika gama girkin” Khaleesat na murmushi tace “Ni dai ba wannan ne damuwata ba, kin ga damuwata nan…..” Ta fadi haka tana nuna ma Hadiyah ledan gabanta, Hadiyah tace “Wai inyi me da wannan abubuwan?” Khaleesat tace “Abinda ake yi da su mana, za su maki amfani” Hadiyah ta dinga kallon Khaleesat, Khaleesat sai gintse dariyarta take, amma sai da dariyar ta kubuce mata ta mike ta bar kusa da Hadiyah tayi dariyarta me isar ta sannan da kyar tace “Toh wallahi matsayina daya dake yau in gaya maki a gidan nan” Tana fadin haka ta fice daga dakin still laughing, Hadiyah was lost, ta dinga kallon kofar dakin babu ko kiftawa trying to understand what Khaleesat meant by her words, dai dai nan Aunty Farida ta shigo dakin da sallama, Hadiyah ta kasa amsa mata har sai da ta karaso cikin dakin ta zauna tana kallonta tace “Hadiyah” Hadiyah ta sauke ido da kyar tace “Ina yini Aunty” Aunty faridah tace “Lafiya lau” Ledan gaban Hadiyah take kallo tace “Ledan meye wannan?” Da sauri Hadiyah tace “Wallahi Halysaah ce ta zo ta ajiye yanxu, ban san ko na meye ba….” Aunty Farida ta dau ledan ta ajiye kan bedside drawer tana kallon Hadiyah da ta kasa kallonta, Calmly Aunty Faridah tace “Za mu koma Nigeria gobe da ke in sha Allah, get ready” Hadiyah ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace “To Aunty” Aunty Faridah ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, Hadiyah ta bi ta da kallo babu ko kiftawa, a ranta kuwa she is still shock at why Khaleesat will bring such package to her, har tana cewa matsayinsu daya yanxu, hawaye taji sun fara taruwa idonta cause she is not a child and she is not dumb, mikewa tayi ta dau package din ta tafi ta bude gun kayan Khaleesat ta dungurar a nan sannan ta koma ta zauna, ba a dau lokaci ba sai ga Khaleesat ta dawo dakin da fruits, da mamaki ta karasa kusa da Hadiyah tace “Ina package din da na ajiye a nan?” Hadiyah kamar bazata ce komai ba amma ganin kallon da Khaleesat take mata yasa tace “Aunty Faridah ta dauka, don ni ban san me yasa za ki ajiye min kayan mata ba ni ba miji ba, in yi meye da su??” Hadiyah na fadin hakan ta mike ta fara hada kayanta tana cewa “Aunty Faridah said we are leaving for Nigeria early tomorrow morning” Khaleesat tace “Nigeria kuma?” Hadiyah bata tanka ta ba, hakan yasa ta juya ta fita daga dakin ta sauka downstairs ta dau wayarta ta fara kiran Ajay, wayar na fara ringing ya daga, ta zauna gefen kujera a hankali tace “Kasan mene, wai fa tare za a koma Nigeria da Hadiyah” Ajay yace “Says who?” Tace “Haka Hadiyah ta gaya min yanxu, wai Aunty Farida tace ta hada kayanta” Calmly Ajay yace “We are almost home dear, idan na dawo za mu yi magana” Alamar dai bai son magana saboda suna tare da Sarki, Khaleesat ta mike bayan ya katse wayar ta wuce kitchen, abinci ta dauka ta kai ma su Mami Upstairs, Mami na kallonta bayan ta shiga dakin tace “Sannu da aiki Halysaah, girkin gidan nan ai yayi maki yawa ke kadai, amma an ma yi employing ma’aikata za su fara aiki daga gobe idan Allah ya kai mu” Khaleesat dai murmushi kawai take, sai kuma ta kalli Aunty farida dake kallonta tace “Aunty wai gobe za ku koma in ji Hadiyah?” Aunty Farida tace “Amma sai mun dawo Los Angeles don anjima za mu tafi can in sha Allah” Mami ta kalli Aunty Farida tace “Flight din magrib za ku bi kenan, Karfe nawa za ayi taron da sarki zai je?” Aunty Farida tace “Goma na safe ne, amma before 2pm muna garin nan in sha Allah” Mami tace “Allah ya kai mu lafiya, nima gobe da safe zan tafi Canada” Aunty Farida tace “Baza mu same ki ba gobe kenan idan mun dawo Mami” Mami na murmushi tace “Ina ga daga can Canada din ma zan tafi Nigeria nima, kuma kwana uku kawai zan yi a can” Mikewa Khaleesat tayi ta fita daga dakin. Ajay da Jay suna tsaye har sarki ya shiga parlor tare da fadawansa biyu, Jay zai shiga parlon Ajay ya fixgosa yana kallonsa daga sama har kasa yace “You’ve got no choice than to be respecting me from henceforth Man, ta yaya zaka riga waliyin ka shiga gida, it’s not done that way, aure fa nayi maka….” Yana fadin haka ya shiga parlon walking majestically Jay ya bi sa da wani kallo, can kawai yayi murmushi ya bi bayansa ya shiga parlon… Mai martaba na zaune downstairs Mami ta sauko ta karaso cikin parlon ta zauna kasa tayi masa barka da dawowa da ladabi sannan ta gaishesa, ya amsa yace “Amma kin daga tafiyar taki zuwa Canada har mu dawo LA ko Fulani?” Mami ta ɗan yi murmushi tace “Ai ko har na siya ticket amma zan yi rescheduling kawai ranka shi dade” Mai martaba yace “Ohk, an daura auren daxu, did you speak to ur daughter about it?” Mami tayi murmushi tace “A’a ban mata magana ba kam, ina ce zaka yi mata maganar da kanka ranka shi dade” Mai martaba yace “Ok I will do that when I am back tomorrow, don yanxu za mu tafi Airport ne” Mami tace “Ko kuma tunda tare za ku koma Nigeria da ita kawai ina ga a bari idan mun koma gida gaba daya sai a sanar mata ranka shi dade, nima ba dadewa zan yi a Canada ba in sha Allah” Mai martaba yace “Ba laifi Fulani, Allah Ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri’a dayyaba” Mami tace “Ameen ranka shi dade” Karfe bakwai saura Ajay da Jay suka tafi yi ma Mai martaba da Aunty Farida rakiya zuwa airport za su tafi LA. Khaleesat na bude wajen kayanta taga inda Hadiyah ta ajiye mata kayan matan da ta bata, dariya ta fara yi ta ciro su, wato ta ajiye mata su a wardrobe ta karata da su, Khaleesat ta fita daga dakin ta tafi dakin da Hadiyah ta makale tun daxu, kwance ta sameta tayi nisa tunanin da take a dakin, Khaleesat ta zauna gefenta tace “Dama cikin kayana kika ajiye wannan ledan Hadiyah” Hadiyah taki ce mata komai, Khaleesat tace “Kawai fa na cleansing din Mara ne ba wai wani abu ba, Mami ce ta taho min da su, ai ni bana wani shan kayan mata, ko sanda Ya Junaid bai nan fa tana bani” Hadiyah ta taɓe baki bata dai kulata ba, Khaleesat tace “Plss be serious mana Hadiyah” Hadiyah tace “Ni nace maki ina bukata ne wai?” Khaleesat tace “Allah idan baki sha ba bazan ji dadi ba, kenan baki yarda da ni ba, it’s not what you are thinking fa” Hadiyah ta mike zaune tana kallonta tace “Don Allah ki gaya min what’s going on a gidan nan Halysaah kar ki boye min komai plss” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta tallabi kuncinta tace “Ya Junaid ne ya gaya min za a maida auren ku da Ya Jawwad, shi yasa ma za a koma Nigeria tare da ke, don a can za a maida auren” Hadiyah ta sauke idonta jin abinda Khaleesat tace, lokaci daya ta yarda da maganar ta, a hankali tace “But me yasa baza aji nawa view din ba, to ni dai idan mun koma zan ce a’a ni bana so a maida auren, since he still haven’t said anything to me, sai girman kai yake min, ta yaya za a maida aure bayan yaki ya min magana har yanxu?” Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciyar tace “Kuma haka ne, yanxu ga shawara da zan baki idan kun koma Nigeria kawai ki ce lallai sai ya fara maki magana ya fadi intention dinsa na son a maida maku aure, if not it will look like kawai anyi forcing dinsa an maida maku auren ne” Hadiyah tayi shiru tana kallonta, Khaleesat tace “Is that okay by you?” Hadiyah ta gyada mata kai tace “Hakan yayi” Khaleesat tace “Don haka pls ki kwantar da hankalin ki, bana son ina ganin ki a haka, bari in kawo maki abinci ki ci” Hadiyah dai bata ce komai ba, Khaleesat ta mike ta fita daga dakin, sai da ta shiga dakinta ta dau package din maganin mata da Mami ta kawo mata sannan ta sauka downstairs tana murmushi. Abinci ta kai ma Hadiyah har Bedroom da kuma maganin da ta zuba a cup uku, it didn’t take her long to convince Hadiyah ta sha magungunan, ita ma kuma ta sha su a gaban Hadiyah kawai don ta tabbatar mata ai kawai na cleansing din mara ne kamar yanda tace mata, duk portion din da ta ba Hadiyah ita ma haka ta sha, na karshen ne Hadiyah taki sha, Khaleesat ta hade rai tace “To ki sha rabi ki rage min rabi, kema kinsan bazan wani dau maganin mata in sha ba ni da nake gudun Ya Junaid, da gaske na gyara ne magungunan ba na mata ba” Hadiyah tace “To gyaran me?” Khaleesat tayi keeping serious face tace “Gyaran jiki mana” Hadiyah tace “Na fa san magunguna Halysaah kar ki wani rena min hankali” Khaleesat tace “Ai ban ce baki sani ba, a bar batun wasa yanda nake tsoron lamarin nan kema kin san bazan sha maganin mata ba ana zaune qlau, ina ce kece kika yi noticing I am running every night” Hadiyah bata sake cewa komai ba ta dau last cup din ta sha rabi ta bar ma Khaleesat sauran, abincin ma kadan ta ci, Khaleesat ta mike ta fita da tray din tana ɗan murmushi ta sauka downstairs. Da daddare Khaleesat na bedroom dinta ta fito wanka ta gama shirin bacci ta daure gashinta da ta gyara, ta zuba turare a hannunta kenan Ajay yayi knocking kofar dakin sannan ya bude gently, don duk zatonsa Hadiyah na ciki, Khaleesat ta gama shafa oil turaren a jikinta ta juya tana kallonsa a hankali tace “Kun ci abincin?” shi ma yana kallonta daga sama har kasa don kayan baccin jikinta sun mata bala’in kyau, sannan it’s transparent yana hango every part of her beautiful body, har da pant din da ta saka, unlike sanda ya dawo ya ganta duk ta rame yanxu kam duk ta cicciko shape dinta ya dawo, ya jingina jikin kofar dakin kamar me jin bacci yace “Wani turare ne wannan kika saka wife?” Ta ɗan yi murmushi tana nuna masa gaban madubi tace “Gasu nan, Mami ce ta siyo min” Ya karasa cikin dakin yana kallon turaren, ya jawota jikinsa yana shafa cikinta murya can kasa yace “They are soo good Slushie, a ina ake siyar da su?” Duk da yanda jikinta ya fara mutuwa hakan bai hanata noke masa ba kamar zata yi kuka cikin sanyin murya tace “Ni dai ka tafi kar Hadiyah ta shigo” A hankali yace “Where is she?” Ganin inda yake saka hannunsa, tayi saurin cewa “Tana dakin dake kusa da wannan wallahi, nasan zata iya shigowa fa” Juyo da ita yayi ya waro ido yace “Waow” Ta kasa kallonsa saboda kunya, ta dinga boye fuskarta a jikinsa, lokaci daya shi ma duk jikinsa ya mutu, a hankali yace “Je ki ce mata i want to speak to her” Khaleesat ta kamo hannunsa don kar ya kara taɓata tace “Kilan fa a Nigeria ake son gaya mata an maida aurensu da ya Jawwad” Yace “Ke dai shiga ki kira min ita” Tace “Tohm” Dukawa tayi zata dau hijab dinta ya dinga kallon bayanta kamar zai hadiyeta, har ta saka hijab din sannan ta fita daga dakin ya bi bayanta walking slowly, Hadiyah har ta gama shirin bacci Khaleesat ta sameta a dakin bayan tayi knocking ta bude mata kofar, Khaleesat tace “Meye na locking kofar? A ina kika samu key” Hadiyah tace “Nothing, plss ya sunan turaren nan naki, it’s soo nice wallahi i love it” Khaleesat na murmushi tace “Kema ai naki ya min kamshi gashi dakin duk ya dauka da kamshi” Hadiyah tace “Ni dai ki gaya min sunan turaren, kin ji wani dadin kamshin da yake yi kuwa” Khaleesat na murmushi tace “Don’t worry zan nuna maki sai in dibar maki” Hadiyah tace “A’a ni dai ki gaya min inda kika siya kawai kika san ko zan siya ne” Khaleesat tace “Zaki siyan ne ma nan ba da dadewa ba, ko kuma in siya maki da kaina” Hadiyah ta mata wani kallo, Khaleesat tayi er dariya ta kai hannunta hancin Hadiyah cause her hand was still oily, Hadiyah ta lumshe ido saboda kamshi, Khaleesat ta shafa mata sauran turaren a jikinta, Hadiyah tace “A’a ni ban sa ki ba, sunan turaren kawai zaki gaya min” Khaleesat tace “Ya Junaid yace zaku yi magana da shi, yana waje yana jiran ki” Sosai Hadiyah ta ji gabanta ya fadi, tayi shiru tana kallon Khaleesat a zuciyarta tana tunanin maganar me Ajay zai mata, Khaleesat ta dauko mata hijab dinta da ta gani a dakin tace “Ki saka mu je don Allah, he is waiting for you” Hadiyah ta saka hijab din jiki ba kwari ta bi bayan Khaleesat suka fita, Ajay na tsaye corridor yana jiran fitowar su, Hadiyah ta karasa har inda yake tace “Yaya ga ni” Yace “Mu je” Yana fadin haka ya fara tafiya taga he is walking toward hanyar dakin Jay, Khaleesat was trying her best not to laugh har da keeping serious face, Hadiyah ta kalleta da mamaki tayi kasa da murya tace “Why?” Khaleesat ma na magana a hankali tace “Duk bazai wuce maganar maida auren ku bane mana, ke dai ki bi sa iyaka zama zaki yi ki ji abinda za a ce, kuma idan Ya jawwad yaki cewa komai still kinga kina da babban reason na cewa a’a idan aka koma Nigeria” juyowa Ajay yayi ganin Hadiyah bata bin sa yace “Kee, Ina wasa da ke ne?” Sunkuyar da kanta tayi ta fara bin sa” Khaleesat ta juya ta koma dakinta don kar dariya ya kubuce mata, haka Hadiyah ta bi bayan Ajay duk mood dinta ya sauya har suka isa dakin Jawwad, Ajay na bude kofar ya kalleta yace “Shiga…” Ta sunkuyar da kanta ta shiga cikin dakin, sannan shi ma ya shiga, Jay dake danna laptop dinsa ya daga kai yana kallon su, he look surprise seeing them shi ma, Hadiyah bata yarda ta hada ido da shi ba kuma taki zama a dakin har sai dai Ajay yayi mata magana sannan ta zauna, Ajay ya zauna yana kallonta, kai tsaye yace “Madam, an maida auren ku da Jawwad, so duk wani past mistakes din da kika yi a baya sai kiyi avoiding dinsu by all means, duk da cewar naga kin yi hankali kin nutsu yanxu, so a matsayina na yayanki na kawo ki dakin mijin ki yanxu, Allah ya baku zaman lafiya….” Tsabar shock Hadiyah kallon Ajay ta dinga yi babu ko kiftawa, kuma ko kwakkwaran motsi ta kasa, she just realized fooling dinta kawai Khaleesat take yi tun daxu, Ajay ya kalli Jay yace “Kai kuma na riga na gama maganata da kai tun daxu…” Yana kai wa nan ya mike yace “Allah ya tashe mu lafiya” Hadiyah ta mike tana kallonsa kamar zata yi kuka amma ta rasa abun cewa, Ajay ya hade rai yace “Kee, koma ki zauna Malama” Ta sauke idonta a hankali sannan ta koma ta zauna kan kujera tana jin zuciyarta na bugawa, Ajay ya nufi kofa, Jay na ganin haka ya mike ya jira har Ajay ya fita sannan ya nufi kofa, tashi Hadiyah tayi da nufin guduwa ta bi bayan Ajay, amma kamar Jay yasan next move dinta yayi saurin kulle kofar yayi locking, sannan ya juya yana kallonta, kuka ta fara yi tace “Ni ka bude min in fita” Tana ganin ya nufeta ta tafi can karshen gadon dakin ta makale ta marairaice amma ta kasa cewa komai.

Back to top button