Mallama Juwariyya

Alamomin Aljani Na Zahiri Da Kuma Yadda Za’a Maganceshi Da Izinin Allah.

ALAMOMIN ALJANI NA ZAHIRI

Wainnan dama wasu suna daga cikin Alamomin da Aljani zai iya nuna kansa amma sai wanda ya san su ne zai fahimtar da ke. Aljani mugu shine wanda baya bayyana kansa balle a masa magani, wanda zai fadar da ke ya tashi, ai ya nuna a masa magani kenan tun da an san da shi, mugun kuwa baya tashi sai dai ya rinka azabtar da ke ta fanni iri iri. Aljani ya kan sa mutum ya rinka jin wainnan dama wainda basu ba saboda kowa akwai irin nasa Alamomin, gasu kamar haka:

Karanta>>> Addu’ar Yaye Baƙin Ciki, Kunci Da Kuma Damuwa Daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. 

1.Yawan ciwon kai mai tsanani da jiri.

2.Ciwon Mara, baya da kuma kwankwaso.

3.Jin motsi a gabanki kamar tana, ko kiji motsi a cikinki yana zuwa bangare bangare.

4.Jin abu kamar kiyashi na bin jikinki, ko kamar tsutsa, haka nan zaki rinka jin motsi a kanki kamar wani abu na tafiya.

Karanta>>> Ladubban Karbar Addu’a Guda 25 Daga Malam Aminu Daurawa

5.Jin wani abu mai dan nauyi ya kwanta a wani bangaren jikinki, wani lokacin ya tashi daga wannan wurin ya koma wani wurin.

6.Jin zafi ko sanyi a tafin kafarki, ko kiji wannan wurin yayi dumi kamar an sa wuta, can kuma sai ya matsa ya koma wani wurin.

7.Jin wani abu kamar yana hadiye ki.

8.Rashin son kitso ko wani abu da zai taba kanki, zubewar gashi dss.

9.Rashin barci da daddare.

10.Yawan faduwar gaba da tsorata da abu qanqani.

Karanta>>> Kana So A Amsa Maka Addu’arka Lokacin Kunci 

11.Rashin son mutane da gudun mutane, da tsoron mutane in ta shiga wurin da akwai mutane da yawa kamar kasuwa, da rashin son magana da mutane.

12.Yawan fushi da tsiya, kiji kowa ma haushi yake baki haka nan kiji kin tsani mutane.

13.Qin aure, da rashin son maza, mace taji bata son namiji yace yana sonta, ko yace zai turo gidan su, wata ma gaba daya zata ga babu mai kulata, babu mai cewa yana son ta. Ko kuma idan wani ya fito neman auren sai zancen ya lalace saurayin yace ya fasa, in shi kuma yake so sai taji ita kuma bata son shi.

14.Zaki rinka ji kamar ana miki magana, ana cewa ki aikata wani mugun abu, ko idan kina kallon wuqa sai kiji kamar ana cewa ki coka ma wane, ya zamana dai ba a rabaki da mugun tunani.

15.Yawan jin zafin jiki, kasala da kuma ciwo na rashin dalili, wato ba a rabaki da zazzabi jikinki yayi zafi, kuma ko kin sha magani baya bari.

Karanta>>> Addu’ar Kariya Daga Sharrin Sihiri, Mayu Da Kuma Kambun Baka

16.Yawan son kade kade da raye raye, wato aljani zai rinka saki yin wasu abubuwan da da can ba halinki bane, lokaci daya sai aga kin canza kin tashi daga mutumiyar kirkin da aka sanki.

17.Yawan kallon madubi da yawaita kallon jikinki tsirara a madubi.

18.Son dare, ya zama kin fi son dare akan rana, haka nan da son zama a cikin duhu.

19.Jin kamar ana kiran sunanki ko firgita yayin da kike ke kadai a wuri, koma ki rinka ji kamar ana biyoki in kina tafiya, ko kamar wani abu na bin qafarki.

20.Yawaita kuka na rashin dalili ko rashin kuka, wasu sun ce yana daga cikin alamun aljani.

Karanta>>> Addu’ar Neman Tsari Daga Sharrin Aljani Ko Wanne Iri Ne Da Izinin Allah

21.Qin karatun Qur’ani, da kasa karanta Qur’ani koma daukansa, kiji rabin kanki na miki ciwo ko wani bangare na kanki kamar zai tsage saboda tsananin ciwo, ko kuma jin bacci da kasala, kiji kamar an cire miki karfin jikinki, kuma kiyi ta hamma kina jin bacci. Ko kuma ana fara karanta Qur’ani gabanki yayi mugun fadi, kuma ki rinka ji a ranki baki so, ko kiji kamar ana tsira miki allura a kunni.

22.Jin kamar ana tsira miki allura a jikinki, duk da wasu sun ce alamun sihiri ne to amma aljani ma yana sawa kiji kina zaune an tsikara miki abu kamar allura har sai kin yi zunbur kin tashi.

23.Rashin jin dadin saduwa da tsanar miji yayin da ya nuna alamar yana son saduwa da ita, ko kuma koda yayi zata ji ita bata ji komai ba, wato dai an dauke mata sha’awa. Da kuma jin zafi yayin jima’i.

24.Aljani zai iya sanyawa mace mugun infection ta yi ta fama yaqi warkewa.

25.Jin kamar kin aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba, wato kamar kina bacci kamar kina farke.

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

26.Ganin inuwa kamar na wani, ko kiji an danneki baki numfashi, sai kin yi addu’a sannan a tashi kanki.

27.Yanke jiki ki fadi baki san in da kanki yake ba har aljani yayi magana, ko ki fadi ba tare da yayi magana ba, amma dai kin san baki san abun da ya faru ba.

28.Jin kamar an daura miki dutse a zuciyar ki, wato ki ji nauyi a ranki, ko kiji an matse miki numfashin ki, ko in kin kwanta ki kasa numfashi da kyau.

29.Samun ciwukan da da can baki da su, aljani yana sawa mutum ciwo a jikinsa wanda likita zai duba ya gani wata rana kuma ace ba a gani ba, sai ka ga mace tana ta yawon neman magani bata san aljani bane ke wahalar da ita.

30.Yawan waswasi musamman a ibada. Da rashin son yi ibadan na gaba daya.

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

31.Rikitar miki da al’ada, yanzu zaki ganki ba jini ya dauke, sai kin yi tsarki kinyi sallah sai kawai ki sake ganin jini haka zai ta miki wasa.

32.Hana haihuwa, aljani yakan hana mace haihuwa, ko kuma in ta tashi haihuwa sai an tsaya a kanta saboda zasu azabtar da ita.

33.Zama da datti da qazanta, aljani ya kan hana mutum tsafta da zama cikinsa idan yana jikinsa, musamman idan aljanin arne ne.

34.Sumbatu da firgici a cikin baccin ki, za a ga kina maganganu marasa kan gado koma kiyi ta firgita kina ajiyar zuciya kuma duk bacci kike.

35.Lalacewar jiki ko ciwo a wani sassa da aljani ke zama.

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

Wainnan dama wasunsu da yawa suna daga cikin alamar akwai aljani a tare dake. In kuma namiji ne shima zai iya experiencing problems dinnan ba wai dole sai mace ba. Kamar rashin son aure, rashin sha’awa gaba daya, mafarkin suna soyayya da wata mace har sun yi aure duk a mafarki, da tsanar matar sa haka nan ya ji ya tsani matar sa. Allay Ya tsare daga sharrin su.

 

SHAWARWARI GA MASU JINNU

Duk wanda yake fuskantar matsalolin na jinnu akwai abubuwan da ya kamata ya fahimta kuma ya kiyaye.

1.Mafiya yawan mutane basa ganin tasirin magani ne saboda a zuciyar su suna kokwanto, duk kuma abin da kake kokwantonsa to abu mai wuya ne ka ga tasirin sa. Idan Annabi ya ce wannan addu’ar zata kare mutum daga dukkan wani abun cutar wa daga safe zuwa yamma, ko daga dare zuwa wayewar gari to kiyi Imani 100% cewa Allah zai baki kariya. Annabi shine mai gaskiya abin gasgatawa da ya ce Habbatus sauda tana maganin dukkan cuta ban da mutuwa to sai kiyi imani cewa idan ina amfani da ita zaki warke daga dukkan cuta. Sai ki ga cikin yardan Allah kin nemi matsalarki wata rana ki ga bashi.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

2. Hakuri da gujewa gaggawa, idan an baki addu’a ko magani kada ki ďauka yanzu yanzu ko gobe ne zaki warke a’a, ki yi ta addu’a kina magani a kwana a tashi za ki nemi matsalarki ki rasa, domin Allah yana amsa addu’a mutuqar bawa bai yi gaggawa ba. Zaka ga mace tayi shekara tana abu, ta samu saukin wasu abun amma bata warke duka ba sai ta ce ita ta gaji da wahala wannan maganin baya mata komai sai ta dai na.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

3. Kiyaye dukkan abin da akace ki kiyaye da aikata dukkan abun da aka ce ki aikata da kuma jajircewa, kada ki fara amfani da magani ko ki fara yin addu’a ki ji sauki bayan kwana biyu ki watsar da komai ki koma rayuwar ki ta da, idan baki wasa ba in ya tashi dawo miki sai yayi har da gayya, domin aljani in shi kadai ya shige ki in ya ji dadin wuri sai yayi ta miki gayyan wasu.

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

4. Kiyaye neman magani ta hanyar zuwa wurin malamin duba ko boka, hakika haramun ne wannan, kada kije wurin wani mai aiki da aljanu kice ya rabaki da naki, in bai rabaki ba ya qara miki wasu. Kuma abun da za su yi shine wai sulhu, aljani ya fadi me za’a masa sai a masa ya bar jikinki. Zai iya yi kamar ya tafi, in aure ya hanaki to zaki ga kin samu kin yi amma yana nan bai tafi ba, iyaka ya dai na azabtar dake ne saboda ki aminta da boka da kuma aikinsa, kin gane hikimar da suka yi amfani da ita? Ana nan kuma wata rana komai zai dawo sabo, sai ki sake rugawa wurin boka sai ya ce ai wannan asiri aka miki ba waccen matsalar bace, a haka zasu yi ta dulmiyar dake. Boka ba zai iya baki tsari ba Allah ne mai tsarewa, asaran kudin ki kawai kike yi kina sake jawo ma kanki masifa. Don haka shine your eyes sister.

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

5. Abu na gaba shine yaqi da zuciyar ki, ‘yar’uwa suna yaqin kine kema kina yaqar su da ayoyi, addu’oi da ingatattun magungunan Manzon Allah. Kada idan suna nuna basa so ki biye ki dai na, a’a kiyi yaqi, idan kin yi amfani da wannan kin sha baqar wuya gobe ma haka zaki sake yi ba fashi. A haka haka tun kina yi kina shan wuya har wata rana zaki wayi gari baki jin komai har kiyi ki gama.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

6. Kokarin tsananta addu’a da roqo. Idan an miki ruqya aljani zai iya ya gama ihunsa ya jigata ya gudu, wani dan gatan ma ana kawo ki gaban mai ruqya zai fice, ayi karatun a gama duk bashi ma abin sa, bayan kun gama kuma sai ya dawo, haka nan in magani ne, zai yi nesa dake ya qi shigowa jikinki ko ya fita a jikinki in mazauni jikinki ne, saboda maganinki na azabtar da shi, to amma yana nan yana jiran ran da zaki dai na, sai ki ga komai ya dawo miki sabo, sai kuma a sake komawa wurin mai ruqya? Amma in ke ce kullum kike addu’an ki babu fashi fa bayan an cire? Har abada shi da ke, saboda ba zai taba samun daman shigowa ba don kullum cikin kariyan Allah kike. Ki zama mai ruqyan kanki.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

7. Shawarar qarshe ita ce koyon adduoi, musamman na safiya da maraice, babban sakaci ne ace babu wasu addu’oi da kika iya a kanki wanda ko baki duba littafi ba zaki karanta don neman kariya ba, duk addu’ar da aka baki aka ce na kariya ne daga shaidanu haddace shi ya kamata kiyi. Duk lokacin da kika ji alamar aljani zai shigo jikinki ko kika ji wani iri fara addu’oi kada ki dai na har sai kin dai na ji. Ba wai kawai ki zauna komai sai kin duba paper ba yanda in baki tare da paper shikenan zaki zauna ba addu’a saboda baki iya ko daya ba.

Ina roqon Allah ya kare mu daga sharrin shaidanu.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Haqiqa duk wanda ya kasance yana wayen gari har ya yammatu, babu wata addu’a na kariya daga sharrin mutum da Aljan.To lallai yana cikin hatsari mai girma. Domin duniya yanzu ya zama abun da ya zama. Kuma addu’a makamin mumini ce. In har ana yi ba a san adadin abun da Allah ke kare mutum daga shi ba.

‘Daya daga cikin manyan malamai Shaikh Waleed Basyouni sun dauki lokaci suna yiwa wani dan’uwa da aljani ya shige shi Ruqya. Cikin ikon Allah Aljanin ya fita jikinsa. Sai sheikh din da shi da wanda jinnun ya kama da wani, suna tafiya. Kawai sai Sheikh Waleed ya ji wani irin qara, kamar an zabga ma wani bulala da qarfin gaske. Sai wanda Aljanin ya buge yayi tsalle kamar an tunkuďa shi gaba, saboda qarfin wannan dukan. Sai Sheikh din ya je wurin sa da sauri ya bude bayansa. Kawai sai ga shaidan bulala radau a bayansa sanadiyyar wannan qara. Wanda sai da sheikh din yayi hour ashirin da hudu da mutumin ya tabbatar lallai duka ne. Sai malamin ya fahimci cewa lallai wannan Aljanin yayi mutuqar hasala saboda an fitar da shi. Sai malamin ya cigaba da masa Ruqya, sai ya tambaye su in sune suka masa wannan dukan. Sai yace eh shi ne, ya ce me yasa? Sai jinnun ya fadi cikin fushi da qara, cewa ya tsani mutumin kuma ransa ya ‘baci. Sai ya ce to me yasa ni da abokina da muke tare baka buge mu ba? Sai ya ce yayi burin, kuma ya so yin hakan, amma sun karanta wata addu’a yasa ya kasa. Wanda wannan addu’ar ita ce:

بِسْمِ اللهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ.

Bismillaahil-lazi laa yadhurru ma’as-mihi shay’un fil-‘ardi wa laa fis-samaa’i wa Huwas-Samee ‘ul- ‘Aleem. [Abu Dawud 4/323, At-Tirmidhi 5/465, Ibn Majah 2/332].

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Safe da yamma ake karanta ta kullum sau uku. Musamman maza masu fita kullum, baku san da wa kuke hada-hada ba. Sannan ko sabon gida mutum yayi, ya je tsakiyar gidan ya karanta wannan addu’ar sau 7 da qarfi. To ko da akwai jinnu zasu tattare yanasu-yanasu su fita. In basu tafi ba kuma, to ba zasu taba cutar da wani ba da yardan Allah. Sannan a koya ma yara har su iya kullum kafin su tafi makaranta su yi. Haka in yamma ta yi. Sannan kun san akwai kambun baka, da evil eye, mayu, yan secret cult dss. Don haka ga azkar mai sauki yan’uwa, in ma za ayi printing ne a yi, ko a rubuta kullum a karanta:

عوذ بالله السميع العليم من الشيطان الرجيم من همزه و نفخه و نفثه.

1.“Au’zubillahis Salimi’ul-Aleem, minash shaydanir rajim, min hamzihi wa nafkhihi wa nafthih”. X1

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

2.Fatiha x1

بِسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ ۝ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِيْنَ ﴿٢﴾ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيْمِ ﴿٣﴾ مَـٰلِكِ يَوْ مِ ٱلدِّيْنِ ﴿٤﴾ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِيْنُ ﴿٥﴾ ٱهْدِنَا ٱلصِّرَ‌ٰطَ ٱلْمُسْتَقِيْمَ ﴿٦﴾ صِرَ‌ٰطَ ٱلَّذِيْنَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّيْنَ ﴿٧﴾

3.Ayatul Kursiyyu x1

بِسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ ۝ ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلْحَىُّ ٱلْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُۥ سِنَةٌۭ وَلَا نَوْمٌۭ ۚ لَّهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَ‌ٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۗ مَن ذَا ٱلَّذِى يَشْفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذْنِهِۦ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَىْءٍۢ مِّنْ عِلْمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ ٱلسَّمَـٰوَ‌ٰتِ وَٱلْأَرْضَ ۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْعَظِيمُ ۝

Karanta>>> Tasirin Da Tazargade Ke Yi Ga Lafiyar Mata

4.Amanar-Rasulu x1

آمَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّ بِّهِ ۦ وَٱلْمُؤْمِنُونَ ۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِاللَّهِ وَمَلٓئِكَتِهِ ۦ وَكُتُبِهِ ۦ وَرُسُلِهِ ۦ ، لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ ۦ ۚ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ ٱلْمَصِيْرُ ﴿٢٨٥﴾ ‏لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۚ لَهاَ مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا ٱكْتَسَبَتْ ۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَآ إِن نَّسِينَآ أَوْ أَخْطَأْ نَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَآ إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ و عَلَى ٱلَّذِيْنَ مِن قَبْلِنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَا قَةَ لَنَا بِهِ ۦ ۖ وَٱعْفُ عَنَّا وَٱغْفِرْ لَنَا وَٱرْحَمْنَآ ۚ أَنْتَ مَوْلَىٰنَا فَٱنْصُرْنَا عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْكٰفِرِيْنَ ﴿٢٨٦﴾

5.Suratul Ikhlas X3

بِسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ ۝ قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ ۝ اللَّهُ الصَّمَدُ ۝ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ ۝ وَلَمْ يَكُن لَّهُ ۥكُفُوًا أَحَدٌ ۝

Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba

6.Suratul Falaq 3x

بِسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ۝ قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ ۝ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ ۝ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ ۝ وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ ۝ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ.

7.Suratul Nas 3x

بِسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ۝ قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ۝ مَلِكِ النَّاسِ ۝ إِلَـٰهِ النَّاسِ ۝ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ ۝ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ ۝ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ.

بِسْمِ اللهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ.

8.Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma’as-mihi shay’un fil-‘ardhi wa laa fis-samaa’i wa Huwas-Samee ‘ul- ‘Aleem. X3

حَسْبِيَ اللَّهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ.

Karanta>>> Gyaran Nono: Gare Ku Yan Mata Masu Kananan Nonuwa Ga Yadda Zaku Yi.

9. Hasbiyallaahu laa ‘ilaaha ‘illaa huwa ‘alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Adheem. X7

أعوذ بكلمات الله التآمّة، من كل شيطان و هاَمّة، و من كل عين لاَمّة.

10.“A’ozu bikalimatillahi taam’mah, min kulli shaytani wa haa’mah, wa min kulli aynin laa’mah”.X1

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ.

11.Aa’uzu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaqa. X3.

لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matar Aure Kashi Na Daya

12.Laa ‘ilaaha ‘illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa Huwa ‘alaa kulli shay’in Qadeer. X10.

لا اله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين.

13.La’ilaha illah anta subhaka innee kuntu minaz zalimen. X7

بِسْمِ اللهِ X3

أَعُوْذُ بِعِزَّةِ اللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ سبع مرات.

14.Bismillahi sau uku, Auzu bi’izzatillahi wa qudratihi min sharri maa ajidu wa uhaziru 7x. Wannan Addu’ar yawanci sai in mutum bashi da lafiya ne yake karantawa, amma believe me tana rugurguza jinnu. In fact addu’a ce mai mutuqar qarfi.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matar Aure Kashi Na Uku

Wadannan sune addu’a na tsari, marasa tsayi ga qarfin gaske. Cikin qanqanin lokaci mutum zai haddace in yana yi kullum. Kuma nan da nan ka karanta ka tafi in da zaka. Haka nan ka yi printing ka bawa iyali ta yi ta koyawa yara har su haddace. Kuskure ne zama babu addu’oin tsari.

Sannan asamu ruwa me yawa akaranta wannan ayoyin rukya aciki sukoma Sune Ruwan Sha Koda yaushe.

Karanta>>> Dalillai 4 Da Suke Sawa Nonon Mace Zuwa Ba Tare Da Ta Tsufa Ba.

AYOYIN RUQYA
***************

1. A’uziyyah da Basmalah.

2. Fatiha.

3. Suratul baqarah – ayah ta 1 zuwa ta 5.

4. Suratul baqarah ayah ta 163 da 164.

5. Suratul- Baqarah ayah ta 255 zuwa 258,

6. Suratul Baqarah ayah ta 285 har zuwa Qarshen surah.

Karanta>>> Abubuwan Da Ma’aurata Za Su Sha Don Samun Dauwamammiyar Ni’ima

7. Suratu Aali Imraan -ayah ta 18 da 19.

8. Sutatul A’araf- ayah ta 54 zuwa 56.

9. Suratul Mumineen ayah ta 115- har zuwa qarshen Surar.

10. Suratus Saaffat – ayoyi goma na farkonta.

11. Suratul AhKaf – ayah ta 29 zuwa ta 32.

12. Suratur Rahman – ayah ta 33 zuwa ta 36.

Karanta>>> Yadda Garin kurkum da na Citta suke Maganin kusan cututtuka 20

13. Suratul Hashri ayah ta 21 zuwa karshen surar.

14. Suratul-Jinni ayoyi 9 na farkonta.

15. Suratul-Ikhlaas

16. Suratul Falaq.

17. Suratun Naas.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

Wadannan ayoyin suna da tasiri sosai akan Aljanu. Tana konasu sosai. Imma ta fizgosu su bayyana, imma kuma ta koresu su gudu..

Amma da sharadin kasancewar mai karatun ya zamto mai kyakyawan Quduri azuciyarsa. Sannan ya siffantu da siffofi na kamala ta zahiri, da kuma kyawawan halaye daidai gwargwado..

Ya Allah ka ba marassa lafiyanmu lafiya. Mu kuma masu lafiyar ka Qara mana lafiya da zama lafiya.

Sannan Kuma aje Islamic chemist Asiyo wannan abubuwan. Ku tabbatar dashine Aka baku.

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Nonuwanki Lokacin Da Kike Shayarwa 

✓ Zuma mai kyau

✓ Kwayoyin habbatus sauda

✓ Man zaafaran

✓ Jan miski

✓ Bukhurul damirul jinnu

✓ Shayin shedanu

✓ Sazab

✓ Man zaitun

Dukkansu za’a same su a Islamic chemist.

Back to top button