Hausa novels

Sanyi Da Zafi Complete Novels Document

Description/Story:

Sanyi Da Zafi Complete Document Written By Maman Shakur 

 

Description

Anatse yayi sallama yashiga wani babban falon wanda suke kira da Shakallo dan sirri kadai kesa a shigo cikin falon, wani irin kirar samfarin gini akama dakin kaman wani museum, yanada fadi da kirma dakin ga wasu ado na gwalagwalai sai babban carpet daya lullube ko’ina a girman falon, sai filoli na tumtum dasuke jejjefe akan carpet din na kishingida anmai ado na sarauta a jikinsu.
Mutane biyar ne zaune a falon maza hutu sai mace tsohuwa guda daya, Mai Babban daki wacce take tsohuwa ta manyanta dan akalla zatai 76 da idanunta sukai jazur tana sanye da Alkaybba hannunta rikeda tissue dakuma charbi tanaja, sai Waziri, Wambai, Makama dakuma Sarkin dawaki, chan kuma saiga wasu Manyan dattawa maza guda biyu dake kama da Mai Babban daki sun shigo sun zauna suma, dan faduwa gabanshi yayi dan haduwan mutanen nan wanda bayan sarki sune masu fada aji a fadan nan kasan babban abune, karasowa yayi tsakiyan dakin sannan yasami waje yazauna yakalli Mai Babban daki yace “Gwaggo kene kika aika akirani”? Girgiza kai tayi kafin ahankali tasa tisssue saman fuskanta tashare hawayen tasss sannan tace “aminan mahaifinka sukasa akiraka amatsayinka na babban dan sarki Kabeer” dasauri yadagokai yakallesu sauran jama’an dakin dake kallonshi yace “tooh” anatse babban cikinsu Makama yace “kannenka duka sun iso? Dan karfe hudu zamukai Sarki makawancin sa” cikeda kamala dakuma natsuwa yace “Yarima Halilu, Ibrahima, dama suna nan, Munir yanzu yakirani jirginsu ya sauka a Abuja, shikuma Umaru yanzu haka jirginsu yatashi daga lagos din shikuma…..” yay dan shiru, atare dukansu yan dakin sukace “Yarima Riyad fa”? Adan hankali yasauke yar boyayyen ijiyan zuciya yace “nakirashi ba adaddi bana samunshi” salati mai Babban daki tasaki tace “bantaba ganin gantalallen yaro irin Riyad ba, yau yana Egypt, gobe yana Cyprus, jibi yana Oman gata yana zanzibar, citta yana China ko Iceland, ohh ni Shatu, chanake yau yana France ka gwada number shi ta chan kuwa Dan Buri? Idan baka da number kaje wajen Fulani ka amsa” cikin murya mai laushi Dan buri (Kabeer) yace “Gwaggo kema kinsan baitaba yin cikakken wata daya agari dayaba yabarta yatafi wata, kuma har ita mahaifiyarshi Fulanin batasan inda yayi ba dan nasameta itama tana kiranshi baya shiga, ni narasa mecece matsalan Riyad da ya gwammace yayta yawon duniya daya zauna akasarshi inda aka yankemai cibiya, ya girma baisan…….” Hannu sarkin Wambai yadagamai yace “ya isa” yadan sauke ijiyan zuciya yace “yanzu dai sabida shi bazamu jinkirta yima sarki abinda yakamata ba, nasan duk inda yake aduniyan nan zaiga news na rasuwan mahaifinshi dan haka zamu ganshi, yanzu tashi katafi” tashi yayi ahankali yamike yawuce yafita yanajan dan tsaki aranshi bayan yakai waje.
Cikeda bacin rai daya daga cikin jama’an dake falon yace “Gwaggo I’ve said this time without number to Mai Martaba he should call Riyad to order, duk cikin yaran Sarki babu gantalalle kaman Riyad, yaki zama ya koyi komi na al’addun mu, yanzu me za’a gayama jama’a akaga shine kawai bayanan” kowa na dakin binshi yake da kallo sai dayan dake kusada shi da ake kira da Usmanu yace “a’a Yaya Riyad yarone mai natsuwa dukanmu nan munsani sana’o’inshi ke kaishi kasashen nan kuma Mai Martaba shiya ya aminta da hakan ya bashi go ahead tunda yaga yaron nada passion for business, Riyad yaro ne mai matukar kyawun hali ga tausayi dukkan mu anan munsan da hakan” cikeda zuciya yace “kai ina magana harka isa kabani amsa Usmanu” cewan yayan da ake kira da Hambali, zasuhau gardama Mai Babban daki tace “shup! Hambali Usmanu kunsan dan uwanku ya rasu kuwa? Fada kuke kokarin yi sabida danshi?” Shiru duk sukayi basu kara magana ba…

Direct flat din mahaifiyarshi Dan Buri yayi wacce take uwargida, wani irin babban gidane da is as if daga inda yake zuwa side din zaije wani anguwa ne, kana ganin Masarautan kasan akwai kudi bana wasaba, dudda ga mata ana koke koke bai hanashi yawuce su yashiga cikin flat dinsu ba. Tana zaune tsakiyan mabiyanta tana kuka yamata alamu da idanu datazo yayi sama, mikewa matar da akalla zatai 48yrs tayi tana gyara lullubi tabishi idanunta sunyi jazur, dakinta yabude kofa yashiga dasauri itama tashigo yamaida kofan yarufe yana manna key, cikin rage murya irin ta munafukai kaman ba itace ke kuka afalo yanzun nan ba tace “ya akayi? Me suka cemaka” Dan murmushi yayi yace “har yanzu ba’a sami Riyad awayaba Mama, abin yamin dadi” dasauri ta dunkulle hannu tawani watsa a iska tace “da kyau Alhamdulillah! Nifa dama Riyad ne kadai matsalata Dan buri dan duka yaran sarki kafisu kudi, kafisu ilimi sannan kafisu connection, gaka kafito daga tsatso mai kyau tsatsona, kuma kai akafi sani afadan nan, Riyad shikadai ne zai nuna maka arziki dakuma kwalin karatu tunda yanada PHD yanzu, amman banda haka meyafika dashi yaron da ko mata baidashi anata gulma ma ana cewa ba lafiya gareshi ba yanda yaki yayi auren nan, kowani Bafade ko jama’an Babbanka za’a tambaya wasukafi so yazama Sarki kowa cha zaiyi kai kai akafi sani kaine jagoran gidan nan kuma dan sarki na fari kasha kuruminka kaman kazama sarki kagama, yanzu dai bari a bunne sarkin anjima dakaina zanje wajen Mai Babban daki anjima, banda Riyad Baffanku Hambali shine mayen kujeran kuma zanyi komi na kaudasu, yi maza wuce katafi waje sabida jama’a su ganka ashaidaka, duk wani kaninka ko kanwarka dazasu iso ka tsaya ka rungumesu kanuna musu soyayya, kazama kaine tsaye akan komi kana kula da komi kaji hakan zaisa kasake farin jini, yanzu tafi tafi ko me ake ciki kadinga fadamin kodako awayane kaji, Mai Martaba yariga ya garzaya saidai kuma mu hadu alahira Mulkin nan kuma tun kafin akaishi makwanci zan fara shige da fice saka akai, kaine d’ana dan fari kaine kuma magaji” Murmushi yamata sosai harda dan dariya yace “Mama kinyi ne arayuwa” da sauri ta shafa fuskanshi tace “kaga daina nuna farin ciki yi fuskan nan ne kaman kai kadai akama mutuwan nan agidan nan” gyadamata kai yayi yakoyi sakwa sakwa da fuska uwa zai fashe da kuka nan ko ranshi fess yawuce yafita daga dakin.

Komawa yayi waje inda dubbanin jama’a suka taru ga kannenshi su Halilu, Ibrahim, Shu’ibu duk sun iso da Iyalansu da akai cikin gida dasu Munir shine last person daya iso wajajen yana zuwa wajen da Babban wan nasu ke zaune yayi cikin jama’a tareda yayyinshi kafinma ya gaidasu yace “Dan Buri kasami Riyad?” Girgizamai kai yayi kaman salihin nan yace “no tunda kun iso yanzu za’a sallaci Baba bazamu jirashi ba kodama yana hanya ne sabida shi bazamu bari Baba ya kwana ba” Munir baice komiba yajuya yafito zuwa wani waje da ba mutane sosai yaciro wayanshi yashiga kiran Riyad danko jiya sunyi waya wuraren 1 nadare but numbershi baya shiga yanzu harzai maida wayan kunnenshi kaman wanda yatuna wani ba yashiga email nashi ya aikamai sako sannan yawuce yakoma ciki akai Alwala aka sallaci mai martaba aka bunneshi nan cikin fada.
Magana sai yawo yake kan duka yaran sarki sun sallaci mahaifinsu banda Yarima Riyad dan Sarki na biyar cikin yaran sarki maza guda shidda ran Dan Buri fess har wani kara haskakawa yake jin yanda rumors din ke flying.
Cikin gida Munir yashiga tareda yayyinsu zuwa babban falo da duka matayen Marigayiya Sarki ke ciki kowacce zaune sanye da hijabi idanunsu jazur ga yan uwa da abokan arziki duka aciki, wajen Fulani suka fara zuwa dukansu yaran anatse suka gaisheta amsa musu tayi suka wuce wajen Fulani 2 suka gaidata itama ta amsa su suka wuce wajen ta uku itama ta amsa ta hudun suna gaida aka dan zauna akai addu’a aka shafa sannan suka fice suka koma wajen maza dan karban manyan baki top politicians manyan kasa from across the world.

Sanyi Da Zafi Complete Document txt

File Name   Sanyi Da Zafi… Hausa Novel Doc.
Title   Sanyi Da Zafi Complete
Author    Maman Shakur 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    25/09/2024
File Size    200KB
Format Size    TXT
Book Price    500
Phone No  07012181461
Download Sanyi Da Zafi Complete Document By Maman Shakur 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button