Harijin Sarki Page 37 Romantic Hausa Novel
Daren ya rufe Fes da wani irin duhu mai nauyin tsoro da natsuwar da ba a saba gani ba. Rana bata haska gaba ɗaya ba tun daga safe kamar sararin samaniya na shirya wani abu, wani abu da ba kasafai yake faruwa ba.Ameer yana tsaye a cikin dakin tsafinsa, idonsa ja, jikin sa kuwa duk ya zamo kamar wuta. Hasken ƙonanniyar kyandir na walƙiya kan gwarzayen da suka cika bango; wasu an ɗaure da igiyar zare, wasu kuma an binne su cikin yashi mai alamar jini.Yana magana da murya mai kauri, “Na kirawo ku, ku halarci wannan daren. Na yi alkawari ban tsaya a gaban wannan wuta don jin daɗi ba, sai na ga ƙarshen wannan jariri da ya kawo mini cikas.”Sai iska ta hura cikin ɗakin, wutar kyandir ɗaya ta mutu, sannan wata murya mai nisa kamar daga ƙasan ruwa ta amsa “Ameer… ƙaddara ba a canza ta da tsafi… me kake ƙoƙarin yi?”Ya fashe da dariya, yana dukan ƙasa da sanda mai ɗauke da ƙwanƙolin zinariya.“Ni ba ɗan ƙaddara bane! Ni sarkin ikon duhu ne! Idan haske ya fito, zan murɗe shi da hannuna!”Cikin ɗan lokaci, guguwa ta mamaye sararin Fes. Mutanen gari suka fara rufe kofofinsu, suna kiran sunan Allah. Cikin masarauta kuwa, Sultan da Samha suna tsaye a saman benen su, suna kallon sararin da ke canjawa zuwa ja kamar jinin mutum.Samha ta rungume Rayyan a kirjinta, tana karanta Ayatul Kursiyyu cikin hawaye.“Allahumma inni a’uzu bika min sharri ma khalaq…”Rayyan, wanda yanzu ya kai shekara ɗaya da rabi, ya ɗago idanunsa — a tsakiyar su akwai haske mai sanyi, kamar tauraro da aka ajiye cikin ruwa.A lokacin da Ameer ya ɗaga sandar tsafi don aika ƙarshen sihirinsa zuwa masarauta, hasken Rayyan ya tashi bai fito daga rana ba, bai fito daga ƙasa ba, amma daga zuciyar yaron nan.Wutar da Ameer ya kunna ta koma kanta, kyandirai suka buga ƙasa suka watse, jikin sa ya fara ƙonewa amma bai fadi ba. Muryarsa ta rikice cikin ihu“Ba zai yiwu ba! Ni Ameer ɗan ƙasashen duhu, ba zan mutu da haske ba!”Sai murya ta fito daga iska ba ta ɗan adam ba, ba ta aljani ba, murya ce mai sanyi da karfi, mai kama da hucin ruwan teku “Kowane duhu yana da ƙarshe Kuma kowane haske yana da farkonsa.”Wata kyalli ta haskaka sararin sama gaba ɗaya. Ameer ya ɗaga hannunsa da ƙarfi don kare idanunsa, amma hasken ya cije shi gaba ɗaya, kamar gawayin da ya bushe ya faɗi Ƙasa matacce cikin ƙasƙanci da taɓewa, Ƙasa ta karɓi jikinsa ba tare da hayaƙi ko ƙura ba.Samha ta rusuna, tana kuka da murna a lokaci guda, ta rungumi Rayyan da ƙarfi, tana cewa“Allah Ka kare min wannan haske, Ka sa ya zama hujja ba jaraba ba” Sultan ya durƙusa kusa da ita, idonsa cike da hawaye.“Duniya ta huta daga duhu… amma kin san kuwa Samha, wannan yaron… ba ƙaramin ɓangare bane na ƙaddara” Samha ta juyo, ta ce a hankali “Na sani, kuma zan koya masa cewa ikon Allah ya fi duk wani ikon tsafi… har abada”Wannan daren, sarautar Morocco ta koma cikin nutsuwa, amma iska ta ɗauki ƙamshin turaren tsafi alamar cewa ba a gama ba, sai dai an fara sabon zaman haske. ✨***** ***** *****Shekaru uku sun shuɗe tun ranar da duniya ta ga ƙarshen Ameer. Amma duk wanda ya rayu a Morocco har yanzu yana tuna daren nan daren da iska ta yi ja kamar jini, daren da rana ta ɓace kuma haske ya fito daga jariri Masarauta ta sake fasali gaba ɗaya.Tsakanin fada da jama’a, ana jin natsuwa ta musamman. Mutane suna faɗin cewa Rayyan shi ne albarkar da Allah ya aiko musu don ya kawar da duhu. Samha Ta koya masa addu’a tun yana shekara biyu. Yanzu, yana da shekara huɗu, idan ya yi barci, sai iska ta tsaya na ɗan lokaci kamar tana sauraron numfashinsaA kowace rana da safe, Samha kan tashi da shi zuwa ƙananan lambunan da ke bayan masarauta, inda take koya masa kalmomin Allah, takance masa“Ka sani Rayyan, duk wanda ya dogara ga Allah, shi ne hasken duniya. Amma kada ka taɓa alfahari da abin da baka ƙirƙira ba” Yaron zai murmusa cikin halin da ke sa zuciya ta lafa, yana tambayar ta da muryar sa mai sanyi“Ummu, idan Allah ne haske, to me yasa wasu suke cikin duhu?”Za ta shafi kansa tace“Saboda sun rufe idanunsu da son zuciya Idan ka so gaskiya, duhu ba zai taba riskarka ba.”Sultan kuwa, ya zama mutum mai sanyi sosai Wanda a da ke cike da izza, yanzu ya cika da tawali’u. Bayan mutuwar Ameer, ya rufe dakin tsafi gaba ɗaya, ya gina masallaci a wurin, Amma har yanzu yana jin nauyin tambayoyi da ba ya samun amsarsu musamman game da ɗansa Rayyan.Sau da yawa sai ya zauna kusa da shi yana kallo, yana faɗin a ransa:“Shin wannan yaron zai zama sarki ne ko Ruhaniya ce kawai yake cikin jikinsa?”Akwai rana ɗaya da ta canza komai, Rayyan yana wasa a cikin fadar da rana ke haskawa, sai wata tsuntsuwa ta faɗo daga sama ta kife a ƙasa, jikinta na rawa. Ma’aikata suka firgita, amma Rayyan ya matsa kusa, ya ɗaga tsuntsuwar cikin hannunsa ƙarami, sannan ya rufe idanunsa.A gaban kowa, tsuntsuwar ta fara motsi… sai ta tashi ta nufi sama ta ɓace cikin sararin haske.Kowa ya durƙusa, wasu suka fadi saboda mamaki, Samha ta ɗauke shi ta rungume, tana cewa da murya mai tausayi “Ka kiyaye sirrinka, ɗana… ba kowa ne zai fahimta ba”Sultan ya tsaya daga nesa, idonsa na cike da mamaki ba na tsoro ba, amma na natsuwar sanin cewa haske ya dawo da gaskiya cikin sarautarsa.Daga wannan rana, aka fara kiransa a cikin masarauta da suna“Rayyan al-Nur” (Haske mai rai)



