Uncategorized

Maciji Ne Page 85-86 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 85/86

_______________Ƙarar faɗuwar abu da  sukaji,itace tayi sanadiyyar juyowarsu gaba ɗaya,ba komai bane ya fadi face tanfatsestiyar wayar queen suhaimat,Wanda shigowar su kenan ita da mijinta,dan tuni tareeƙ yayi musu iso zuwa dakin ammi,kuma gaba daya kalaman ammi akunnensu suka sauka,

Cikin rawar jiki  queen suhaimat ta ƙaraso cikin dakin,zuciyarta kamar ta kamar ta tsaga  ƙirjinta tafito, dan yadda take bugawa da ƙarfi,zaka iya juyo sautin bugun nata.

Gaban ammi tazo ta durgushe tana kallonta baki buɗe,kafin tace “uktee me kike cewa?me kunne na keji kina faɗa?Please kada kisa zuciyata ta buga,akan abinda kunne na yaji”queen suhaimat ta fada cikin rawar murya tana kamo hannun Ammi.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Cikin azaba ammi take kallon suhaimat,tana jin wani irin bakin ciki da ɓacin rai,yanzu shikenan, suhaimat tayi galaba akanta?shikenan suhaimat zata san wacece yarta,kuma ta ganta araye? Ina idan hakan ta faru shikenan ta zama marar nasara arayuwarta.dan haka cike sa tsana ta fizge hannunta daga cikin na Queen suhaimat,kafin ta yunkura da gyar ta tashi zaune,jingina tayi da jikin bango tana maida numfashi kafin ta fara magana”tabbas abinda kunnenki yaji suhaimat,to haka yake,nice nan narabaki da ƴarki,tun tana karama,Ni nasanya baiwarki ta satomin ita,kuma nasa aka jefar da ita acan wata ƙasar,ta yadda har abada bazaki ganta ba,domin ajeji nasa aka yardata, wanda nasan,ba wani mahaluki da zai ganta agurin,kuma ko namun dawa basu cinyeta ba,yunwa zata kasheta, sannan na kashe baiwarki da hannuna dan rufuwar asirina”ammi ta faɗa cike da rashin imani tana wani zazzaro kunburarrun idanunta.

Da baya Queen suhaimat ta koma ta zauna dabass.kunnenta yana amsa kuwwar maganar ammi,ko amafarki bata taba tsammanin jin wanan bayanin daga bakin ammi ba,she can’t believe ace ƴar uwarta ita ce  silar batan yarta,amma me tayiwa ammi haka da zafi?me ta tsare mata da har take burin ganin bayanta?

Cikin muryar kuka queen suhaimat tace”uktee,me nayi miki?wane laifin na aikata agareki, da har na cancanci wannan aika aikar agareki?nifa yar uwarkice ta jini,amma kika zabi ki cutar da Ni da abinda nafiso fiye da duniyata”

Cikin zafin rai ammi tace “saboda bana kaunar ki,bana sonki,na Tsaneki,ban taba sonki matsayin yar uwa ba,domin kedin mai nasarace,akan komai, ke kekiyin nasara akaina,an fifita sonki akaina,bayan haka kikazo kika auri mutumin da na ƙwallafa rai akansa,wanda nake fatan aura,amma aka aura mikishi,Ni kuma aka aura min wanda bashine cikin raina ba.suhaimat na Tsaneki,kuma nayi alƙawarin ganin bayanki, keda zuri’arki,dan kuwa ko su zayyad Allah ne ya tseratar dasu daga kaidina, da tuni na hallakasu sun bar duniyar nan”ammi ta fada tana jan numfashi da gyar,tsabar yadda take jin jiki.

Kuka sosai queen suhaimat keyi,tana jin wani irin ciwo da radadi cikin zuciyarta,yanzu yar uwar ta itace ta cutar da rayuwarta haka?wannan wane irin son zuciya ne,

Cikin kuka ta kalli ammi,yadda take fidda numfashi da gyar,ga ƙafarta ta dama sai jini take.

Tace “amma me yasa baki sanar dani kina son habib ba? Wllh Dana bar miki shi kin aura ,meyasa kika yi haka yar uwata?ina yata take ?ina kika kaita?na rokeki ki sanar dani inda kika kaita,zan tafi  neman ta, koda zan rasa raina akan hanyata  ta zuwa neman ta ne,hakan shine kadai zai sanya Ni farin ciki”queen suhaimat ta fada cikin matsanancin kuka,

Shi kuwa Sultan Habib tsabar kaduwa ya kasa koda matsawa daga inda yake,kallon ammi kawai yake yana jin kamar yaje ya shaketa ta mutu tabar duniyar ma kowa ya huta.

Ahankali Adeeb ya riko hannun fattu,wacce take bin iyayen nata da kallo,tun shigowar su,wani irin shauƙi da farin ciki ke dibarta, ji take ko ahalin yanzu ta koma ga mahaliccinta,tabbas tayi nasara tunda har ta ga iyayenta,wayyo Allah baffa ko kana ina ?dagaka wannan ranar  da kake burin zuwanta.

Da sauri ta kalli Adeeb hawaye na zuba cikin idanunta,lumshe ido yayi tare da girgiza kai alamun kar tayi kuka,sannan ya sanya hannu yana share mata hawayen idonta,kafin yayi mata nuni da taje gurin queen suhaimat.kallonsa tayi gabanta na tsananta faduwa,amma ya jinjina mata kai tare da sakin murmushin da zai kwantar mata da hankali.

Download>>> Auren Fansa Complete Document

AHankali ta fara takawa,cikin hikima da fargaba,kasancewar ba wata cikakkiyar lafiya gareta ba, hakan ya kara bata damar tafiya ahankali,kallo su amma da nanny suka bita dashi,cike da tausayawa,saidai nanny tana son gano kamar wani abu ya faru da fattu,duba da yadda take takawa ahankali,kuma tana ɗan dingisawa.amma tunani da sanin da wa fattun ke tare  dashi,yasa ta kawar da tunanin da takeyi,ta dauki hakan amatsayin fargaba ce kawai.

Queen suhaimat na kuka gaban,ammi tana faɗin “na roƙeki,ki sanar dani inda kika kaimin yata dan Allah “kawai saiji tayi andafa kafaɗunta .

Da sauri ta juyo tare da kamo hannun wanda ya dafata,

Fattu ta gani tsaye kusa da ita tana hawaye.

Kallon fattu tayi cikin kuka itama tace”dan Allah ƴata ko kinsan in da zan hadu da gudan jinina?wallahi  itace rayuwata,bani da wani abinso sama da ita,ki taimaka min idan kina da masaniya akan ƴata”ta kai karshen zancen ta tana Dora goshinta cikin rafin hannun fattu.

Kuka fattu keyi sosai ,ganin yadda mahaifiyarta ke tsananin kaunarta,amma saboda zalunci aka rabata da ita,yanzu gashi suna tsaye tare da juna amma bata san ko wacece agabanta ba.

Ahankali Adeeb ya taka zuwa garesu,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya ɗauko wannan sarƙar,domin tana tare da shi dama.

Kallonsa kowa keyi,harda queen suhaimat,ta bayan fattu ya tsaya tare da daura mata sarƙar nan.nan da nan sarƙar ta dauki walwali da haske ,tuni tambarin hoton zuciya mai dauke da harafin s&h ya bayyana jikin sarƙa.

Cikin kasalalliyar murya ammi tace “a’a Adeeb , a’a karka daura mata sarkar nan, nayi alƙawarin suhaimat harta mutu bazata ga yarta ba,me yasa ka je kasato min sarkarnan?ashe kaine ka ɗauke sarƙar Adeeb,ka cuceni,kai amanata wayyo ni ammi na shiga uku komai ya kare”Ammi ta fada cikin yanayi na fitar hankali,wanda zamu iya cewa kwakwalwarta ta tabu.

Wani shegen kallon tsana Adeeb ya jefo ammi dashi,kafin yace”kaicona rayuwarki ammi,kin cuci kanki,kuma tun yanzu kin fara ganin sakayyar Ubangiji akanki,Allah ya isa tsaninmu dake”

Adeeb ya fadi hakan cikin zafin rai da kumar zuciya.

Download>>>  Saran Boye Complete Document

Tareeƙ ne ya matso ahankali yana mai bubbuga bayan Adeeb,alamun rarrashi.

 

Cikin tsantsar ruɗu da wani irin farin ciki queen suhaimat ke bin sarƙar da ido,kafin ta kamo sarƙar tana kalla, da sauri ta fizgi sarƙar dake wuyanta,ta kara da sarka wuyan fattu,sak!!irinsu ɗaya komai da komai,

Hakan na nuna cewar fattu itace yarta?fattu itace gudan jininta wacce ta dauki tsawon shekaru tana nema?ya salam yanzu dama soyayyar da takeji azuciyarta ta fattu,tana da nasaba da kasantuwar fattu diyarta ta cikinta?wani irin kuka ne mai tsananin karfi ya kwacewa queen suhaimat,Tana mai kamo fuskar fattu,tana girgiza kai,cikin wata irin  murya mai fidda amo tace “FATIMA ZARA, da gaske kece ?kece zarana diyata abin sona?”queen suhaimat ta fada cikin yanayi na rudewa.

Cikin kuka sosai fattu ta jinjina kai tana kallon mahaifiyarta,da wata irin kalar soyayya mai narkar da zuciya.

Kankameta queen suhaimat tayi tare da kara sakin wani irin kuka mai rikitar da mai sauraro,tana faɗin”Alhamdullah ya Allah,Nagode maka ubangiji,  kaine mai juya farin ciki ya koma bakin ciki,bakin ciki ya koma farin ciki,yau kukana ya ƙare ka nuna min yata farin cikina abin sona,ya Allah ka kara karemin yata karka ba azzalumai dama akanta,Fatima zata diyata,abin sona “irin kalaman da queen suhaimat keyi kenan,tana ƙanƙame fattu,kamar za’a kwace mata ita,wanda saida ta sanya kowa kuka agurin,

Cikin sassarfa Sultan Habib ya ƙaraso gurin tare da rungumesu gaba ɗaya shima yana kuka.

Duk mai imani idan yaga wannan bayin Allah ,dole ya tausaya musu,dan kuka suke bilhakki da gaskiya.fattu har neman shiɗewa take tsabar kuka.

Su sukuwa sai sum batar fattu suke tare da godewa Allah,daya bayyana musu ita cikin aminci.

Kusan minti biyar suna cikin wannan yanayi  kafin abie yayi gyaran murya cike da alhini,yana jin zuciyarsa nayi masa zafi sosai,yace “Alhmdllh ba Abinda zamucewa Allah sai godiya,yanzu kam komai yazo ƙarshe,azzamar matar nan zata girbi abinda ta shuka,tsawon shekaru.dan haka akwai bukatar kowa yaje ya hutawa zuciya da jikinsa.Rashad kuyi hakuri,akan abubuwan da nayi ta nuna muka abaya kaida mahaifiyarka,sam hakan ba yin kaina bane,sharrin wanann makirar ne”abie ya faɗa yana nuna Ammi,wacce take kwance sharaf kamar gawa.

Girgiza kai Rashad yayi kafin yace “abie nima ka yafemin,domin nayi ta sanya ka cikin damuwa da tashin hankali,kuma duk sharrin ammi ne azzaluma”ya fada yana hararar gurin da ammi ke kwance sharkaf.

Matsowa gareshi Adeeb yayi tare da shafa kansa yace “Allah ya baka lafiya lilna, sannan ya kara tsaremi daga sharrin masu hali irin na ammi” da Amin suka amsa gaba dayansu.

Ko kallon inda ammi take Adeeb baisonyi,dan sosai yakejin haushin kansa ,na kasa fahimtar gaskiya da yayi tun dadewa,har ammi tayi wannan gagarumar nasara akansa.

Abie  ne ya sanya wasu dakaru suka shigo dan fitar da ammi daga dakin,yace su kaita can kurkuku mafi tsanani da duhu su ƙullewa aciki.kafin ayanke mata hukunci.

Haka suka kinkimi ammi batama san inda kanta yake ba sukayi waje da ita.

 Juyawa sukayi gaba ɗaya,Suna shirin barin dakin sukaji kamar motsi cikin dakin da aka kulle Zulaihat,dan haka cikin azama tareeƙ da Adeeb suka nufi ƙofar,da gyar suka balle kofar,dan sun rasa makullin.

Aikuwa suna budewa suka hangi Zulaihat kwance  abakin ƙofar  adaddaure,  gaba ɗaya jikinta jini kaca -kaca.cikin azama suka fara kunceta,ta galabaita sosai kuma har lokacin kanta na zubda jini,

Da gyar ta buɗe idonta ta kalli Adeeb tace “my prince,karkaci abincin nan akwai guba aciki, kuma tare suka hada baki zasu kasheka”ta karasa da gyar,jini na zuba daga bakinta.

Abie ne ya ƙaraso gurin da sauri yana faɗin”Zulaihat Meya sameki haka?waye yayi miki wannan abun,kuma ammi ita da wa suka hada bakin”abie ya faɗa yana jin bugun zuciyarsa na kara tsananta,dan baisan kuma wa Zulaihat zata ce ba.

“Cikin mawuyacin hali,Zulaihat tace”Abba…..na,abba na ne,tare suke kulla komai shida ammi,karku barshi”tana faɗin haka idanunta suka kakkafe  jikinta ya saki.

Cikin wani irin bugawar zuciya abie yace “w…a….z…..

Sai kuma ya kasa karasawa kawai ya zube agun asume.

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

Hmmmmm masu karatu wannan wace irin rayuwace ?wacce amana tayi karanci?dan uwa shine zai cutar da dan uwansa.

Allah kasa nufi karfin zuciyarmu ammen.

Mu hade next page.

Mrs babi ce 💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment 

More typing.

Back to top button