Macijine Shi Page 57-58 Hausa Novel
Na mammy kabeer
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 57/58
________________Gimbiya suhaimat ta gama tsara cewa data huta zataje part ɗin Adeeb dan ganin yarinyar nan,
Saidai shigarta part ɗin ammi da yanayin da taga ammin yasa ta saurin,ƙarasawa cikin dakin ,cikin damuwa take faɗin”ukktee meke damunki? Yana ganki akwance?gimbiya suhaimat ta faɗa tana kamo hannun ammi ,wanda ba’a daura mata ruwa ajikinsa ba.
Ahankali ammi wacce tayi nisa cikin tunani ta buɗe idonta tana kallon gimbiya suhaimat,kafin ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido ta buɗe” ke dai bari suhaimat,yau naga abinda ban taba gani ba arayuwata,nan ta bata labarin abinda ya faru,saidai ta boye mata asalin labarin fattu,sai cewa tayi wata baiwa ce Rashad ɗin yayiwa fyade,dan ita atunanninta Rashad yayiwa fattu fyaɗen.
Download>>> Yar Harka Complete Novel Document
Sosai gimbiya suhaimat ta tausayawa yarinyar,sannan tayi Allah wadai da halin Rashad,zuciyarta na tsananin bugawa ,har cikin ranta take jin tausayin yarinya.kuma tayi alwashin ,saitaje taga yarinyar nan kafin ta bar ƙasar.
Rashad kuwa kai tsaye aka wuce dashi,lafiyayyen asibitin dake masarautar,emergency akayi dashi,cikin gaggawa likitoci suka duƙufa akansa dan ceto rayuwarsa.
Dan da dama cikin likitocin , sunyi tunanin hatsari ya samu mai muni.
Karon farko ruwa suka fara ɗauka masa,kafin suka fara bincikarsa,karayama kusan biyar ce ajikinsa, bayan munanan raunuka dake jikin sa,sannan since kansa ya bugu ,dole sai sunyi bincike akwakwalwarsa, dan tabbatar da lafiyarta.
Amma kuka take sosai cike da tarin damuwa da baƙin ciki ,meyasa Rashad zaiyi mata haka?me yasa gaba ɗaya halayyar Rashad ta sauya ne?da ɗan ta mai hankaline da nutsuwa ,sannan yana bin maganarta,amma daga baya ya fandare ya zama gagararre,yanzu ga irin abinda ya jama kansa.karaya har biyar ajikin mutum.Nan dai taci kukanta ta ƙoshi,tana zaune gefen ɗan ta.
Nanny ma ta farfaɗo ,hankalinta amatukar tashe ,tana zaune hawaye na zuba cikin idanunta,yayin da tareeƙ ke rarrashinta cikin kwantar da murya.
“Kayya tareeƙ abinnan na magajin faɗa,ya isheni yaron nan tun yana ƙuruciya yake haɗuwa da tuggun maƙiya,har zuwa girmansa,yaushe ne zai sami salama shima,kadufa wai Adeeb ne ya zama wannan ƙaton macijin,wanda idan awani gurin ka ganshi,sai inda ƙarfi ka ya ƙare wajen ceto rayuwarka.
Yanzu idan haka ta faru dashi awani gurin yunkurin kasheshi fa zasu yi”nanny ta ƙarasa cikin kuka tana fyace majina.
Hannunta tareeƙ ya kara damƙewa cikin nashi,kafin yace ” wai ummeee yaushe zasu sanar da gaskiyar da muka jima da sanine?yaushe zamu taimakawa yallaɓai mu haska masa hanya danya gane irin haɗari dake bibiyarsa arayuwa?na gaji da boye gaskiya ummeee kiyi wani abu”tareeƙ ya faɗa cikin damuwa.
“Tareeƙ baka san masarautar ya take ba,idan baka iya kama ɓarawoba ,to shi zai kama ka,dole mubi komai asannu,akwai lokacin bayyana gaskiya kaji?kayi hakuri”nanny ta faɗa tana mai shafa kan ɗan nata.
Yanzu ya jikin ɗiyata yake ?shikenan yanzu yaron nan ya lalata nata rayuwa?ya karbi budurcinta awulaƙance sannan tana cikin al’ada ?kai ban taba ganin fajiri irin Rashad ba,Allah ya saka miki ɗiyata”nanny ta faɗa cikin kuka sosai,tana tausayawa fattu.
Tareeƙ ma runtse ido yayi zuciyarsa na masa zafi,dan kuwa yasan ahalin yanzu Adeeb yana can cikin bakin ciki da damuwa,saidai shikam yana ganin kamar Rashad ɗin bai sami damar yiwa fattu fyaɗen ba suka karaso, yana kuma fatan Allah yasa hasashensa yazama gaskiya.
Download>>> Budurwar Mijina Complete Novel Document
Akan gado Adeeb ya shimfida fattu,wacce ke kwance kamar gawa,bata ko motsi,gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska,jikinta ko ina raunine ,dan kuwa ba ƙaramin azaba Rashad ya gana mata ba,lips ɗin ta sun bushe idanunta ya kumbura sosai.
Runtse ido Adeeb yayi lokacin da idanunsa suka sauka kan wuyanta zuwa ƙirjinta ,fasassun kwalabe duk sun soketa, zama yayi abakin gadon,cikin wata irin karaya da zafin zuciya.ji yake kamar yaje ya kama Rashad yayi gutsin-gutsin dashi,
Hannunta ya kama na dama ,ya riƙe cikin nashi,gam-gam .jikinsa sai rawa yake ,yama kasa aikata komai akanta.wai hulwarsace kwance agabansa kamar gawa.
“Why Rashad ?why ?duk matan dake cikin fadar nan sai matata?me yasa zaka aikata haka agareni?Adeeb ya faɗa afili yana mai kaiwa bango naushi, ji yake kamar zuciyarsa zata kama da wuta.
Da sauri ya mike tare da ɗauko first aid box ɗinsa, dan Adeeb cikakken likitane akan fannin lafiya yayi karatunsa .
Farar vest ɗin fattu data yage kaɗan daga sama ya kama,wacce ta rine da jini, ya cire mata ahankali,nan da nan albarkatun ƙirjinta suka bayyana,cikin faduwar gaba Adeeb ya kawar da kansa ga barin kallonsu,zuciyarsa na ci gaba da bugawa. haka ma ya zare wannan dogon wando dake jikinta ya ajiye gefe,ya rage daga ita sai pant Wanda shima gaba ɗaya yayi stairs saboda yadda jini ya ɓalle mata ,tsabar yadda ta shiga ruɗu da razani.
Hannun Adeeb karkarwa yake ya kasa aikata komai,dan haka cikin sauri ya janyo ƙaton bargonsa ya lulluɓe fattu dashi,iya saman ƙirjinta zuwa kanta ya bari abuɗe.
Sosai ya tausayawa fattu lokacin da yake cire mata kwalaben nan,dan kuwa taji ciwo da yawa,ko yaya ya taba gurin da kwalbar take saita zabura kamar zata farfaɗo.
Haka dai ya gama cire mata kwalaben nan,tas yayi mata dressing ɗin duk inda ya kamata, ya sami ruwan zafi da towel ya goge mata jikinta .sai dai kuma ba wani kayan da pant da kuma pad ɗin dazai canja mata.
Dan haka rigarsa ya ɗauko fara ƙal ,doguwar ya zura mata, kafin ya dauko mata kayanta,dan kuwa yana tunanin ta dawo nan part ɗinsa da zama kenan. Ƙarin Ruwa ya sanya mata ,kafin ya nufi ƙofa, kai tsaye ya kulle ƙofar ya fita zuciyarsa kamar wuta haka yake jinsa,ya nufi part ɗin nanny.
“Tareeƙ na roƙeka kada kace zaka sanar da magajin faɗa komai ahalin yanzu,dan kuwa bamu da kwararan hujjoji akan hakan ,ka bari nan da lokaci kankanin shida kansa zai gano komai,zamu nuna masa hanya ta yadda zai fahimci abubuwa da dama” nanny ta faɗa tana rike da hannun tareeeƙ.
Umme wllh zuciyata zafi take,Aduk lokacin dana ga yallaɓai cikin wani halin,yana zagaye da maƙiya ,amma bai sani ba,shi yana zaune dasu zuciya ɗaya ….
“Su waye maƙiyan nawa?sannan wace gaskiyar ce ake boyemin?”
Suka tsinkayo Muryar Adeeb yana faɗin haka cikin sautin da ba wasa acikinsa.
Da sauri suka juyo gaba ɗayansu, dan basu tsammanci ganin Adeeb ɗin awannan lokacin ba.
“Magajin faɗa yaushe ka shigo?ya jikin naka?ina ɗiyata take ?”nanny ta faɗa cikin inda-inda da son n kawar da zancen.
Ƙura mata ido Adeeb yayi cike da tuhuma ,gaba ɗaya ta daburce.da alama akwai abunda take boyewa ita da tareeƙ .kallonsa ya dawo dashi kan tareeƙ wanda kansa ke ƙasa ,shi yaji dadin jinsu da Adeeb yayi,fatansa ɗaya ayi komai yau akare.
“Tareeƙ, what wrong me kuke ɓoyemin? Dama akwai Abinda zaka iya boyemin tareeƙ ?na dauke tamkar kanina da muka fito ciki daya,why tareeƙ?” Adeeb ya faɗa yana kallon tareeƙ.
Kallon nanny tareeƙ yayi,yana jin ba dadi cikin ransa,dama yasan watarana hakan zata iya faruwa,shi baiga amfanin biye boyen ba , amma suna haɗa ido da nanny tayi saurin girgiza masa kai,alamun karya ce komai.
Download>>> Attajiri Ko Almajiri Complete Novel Document
“Tareeeƙ,am tolking to you me kuke hidden mini?kada kusa na fara zarginku fa,Please nanny,bayan ammina da abie, ku kadaine mutanen dana yarda dasu arayuwata,ku kaɗai ne waɗanda nake ganin bazasu taba cutar dani ba,karki karyamin zuciya nanny, Please me kuke ɓoyemin?” Adeeb ya faɗa cikin wata kalar murya mai cike da tsoron kar ace nanny da tareeƙ suma suna daga cikin maƙiyansa .
“Ka kwantar da hankalinka magajin faɗa,wllh har abada bazamu taba cutar da rayuwarka ba,saidai mu bata kariya, amma kasani akwai mutanen da kake kallo matsayin maƙiyanka,saidai sam,ba haka abin yake ba. azahiri kake ganinsu matsayin maƙiya,amma abaɗini sune masoyanka na haƙika.
Su kuma wadanda kake kallo matsayin masoya,suke son ganin bayanka, sune waɗanda suke cin dunduniyarka,Adeeb ka kula kazamo mai lura da mutanen da kake tare dasu ” nanny ta faɗa tana mai riƙe da hannun Adeeb,fuskarta ɗauke da damuwa.
Kallonta kawai Adeeb keyi,tunda ta fara maganarta ,me take nufi kenan?su waye ya yarda dasu ,kuma suke cin dunduniyarsa?
Sannan suwaye yake wa kallon maƙiya ,alhalin sune masoyansa na asali?kallon nanny yayi cike da tarin tambayoyi zuciyarsa na harbawa da gudu.
“Nanny ban fahimceki ba,me kike nufi da kalamanki? Please kiyimin bayanin da zan gane”Adeeb ya faɗa yana kallon nanny,idanunsa sun kada sunyi jajur dasu.
Ajiyar zuciya nanny ta sauƙe mai ƙarfin gaske,sannan tace magajin faɗa ,idan baka manta ba,shekaru kusan sha takwas mijina da kuma gimbiya nazli sunyi haɗari suka mutu,sanadiyyar wuta data kama motar da suke ciki,harda yaranta mata su biyu,nanny ta faɗa tana kallon Adeeb,
Runtse ido Adeeb yayi da mugun ƙarfi,har abada bazai taba mantawa da wannan baƙar rana ba ,ranar data zamo mafi muni arayuwarsa.
Bude idonsa yayi wanda suka cika da kwalla yana kallon nanny kafin cikin rawar murya yace ” tabbas nanny bazan taɓa mantawa da wannan rana ba,domin itace rana mafi muni arayuwata” ya faɗa yana mai lumshe idanunsa hawaye suka ziraro sharrrt.
“To kasani wannan haɗarin ba afkuwa yayi ba ,shiryashi akayi” nanny ta faɗa tana mai kallon Adeeb ,
Azabure Adeeb ya bude idanunsa,da suka gama zama jajur dasu,kallon nanny yake cikin kiɗima da ruɗewa” nanny kamar ya ban gane ba,me kike nufi da shiryashi akayi?waye ya shirya?kuma meye dalilin shiryawa?”Adeeb ya faɗa aruɗe.
Kamo hannunsa nanny tayi ta zaunar dashi akan kujera dan kuwa gaba ɗaya jikin sa rawa yake.
“Tareeƙ maza jeka kulle mana ƙofar nan”nanny ta faɗa cikin damuwa.
Ahankali tareeƙ ya nufi ƙofar tare da kullewa, yana jin sanyi aransa,koba komai yau zasu sauke nauyin da yayi musu bake bake acikin zuciya.
” Nanny kiyi saurin sanar dani, domin zuciyata gab,take da tarwatsewa,dan kaɗuwa” Adeeb ya faɗa cikin tsantsar zaƙuwa .
Ajiyar zuciya nanny tayi kafin tace ” ina son ka saurari maganata da kunnen basira ,sannan kayi min kyakykyawan fahimta,kasani bazan taɓa cutar da kaiba, kuma duk abinda nayi nayine don tsiratar da rayuwarka” nanny ta faɗa hannunta riƙe dana Adeeb.
“Please nanny go street to the point kina kara sani cikin wasi-wasi” Adeeb ya faɗa cikin muryar damuwa ,jikinsa na rawa ,ba abinda yake son ji sai wanda ya shirya wanann haɗarin.
Mikewa nanny tayi tare da zuwa jikin window ta tsaya ,kallon Adeeb take tare da karantar yanayinsa, kamar yadda shima yake kallonta cike da ƙosawa.
Ahankali ta buɗe baki tace”ba kowa bane ya shirya wannan hadarin face ……….
Download>>> Dr. Bobby Complete Novel Document
Wayyo masu karatu cajina ya kare ,amma karku damu mu tara anjima,
Nice dai anty mammynku.
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.