Hausa novels

Fatalwar Delu Part 7

🤡 FATALWAR DELU 🤡

 

Part 7

 

Kingboy Isah 👑

 

Short story

 

 

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

 

 

Ba komai idona yayi arba da shi ba face wata kyakykyawar budurwa, ga ta dai doguwa fara a iya hasashena na kasa gano ainahin da mutanen wace kasa yarinyar take yanayi. Balarabiya ce ko yar india na tabbata wannan idan yar fulani ce ma to ubanta balarabene. Idan kuwa ba yar fulani ba sai dai ko shuwa arab. Bayan nayi zurfi a cikin tunanin nawa, banyi aune ba sai ji nayi ta ce, “Bawan Allah kana kashe mun ido da hasken fitila”. Ai bayan na janye fitilar daga haske fuskarta da nayi, da sauri na murza idanuna da hannu kana na runtse ido na girgiza kaina a zatona har yanzu a duniyar mafarki nake irin wanda na farka daga shi yanzu. Domin ko kadan banyi tsammanin wannan yarinya mai kama da larabawa zata iya magana da harshen hausa ba. “Yi hakuri”. “Na furta da sauri”. Sai ji nayi ta ce, “Bawan Allah ko mai shagon nan Bukar yana nan?”. Nayi saurin cewa, “Aa baya nan yau ba a nan ya kwana ba”. Na kalli agogon hannuna kusan karfe daya da rabi na dare, kana na juya gareta hade da cewa, “Lafiya dai ko kike nemansa, ko ya san da zuwanki ne?”.

 

 

Shiru ta yi na dan lokaci daga hasken fitilata da ya haska gefe, ina iya ganin fuskarta tabbas ta hade rai, “Aa bai sanni ba, da na ganka a kwance nayi zaton ko shine dama taimako na zo nema a wajensa”. Na ce, “Lafiya dai ko, wane irin taimako kike nema a wajensa cikin dare haka?”. Sai ji nayi ta ce, “Dama wajen biki mukaje ni da yan gidanmu wani gari shine suka taho suka barni a can ni kuma da dare yayi naji ba zan iya kwana a garin ba, sai na yanke shawarar tahowa gida. Amma da na zo nan garin sai naji ana ta bani tsoro tun dazun nake ganin abubuwa ban tsoro, ina tafi har abubuwa na ga suna giftawa ta gabana, wallahi tsoro nake ji kar labarin da ake cewa fatalwar Delu tana kashe mutane da tsakar dare a garin nan abun ya faru a kaina, shiyasa da na ganka a kwance na zata Bukar din ne na zo ya taimaka ya bani wajen kwana ko kuma ya rakani gida, tunda na ganshi a waje nasan baya tsoron Fatalwar da ake zance”. Nayi shiru ina nazarin maganganunta wanda daga karshe na fahimci rainin wayo ne kawai a cikinsu. In ba dan iskanci ba kinsan kina jin tsoro kuma ana kashe mutane a garin nan me yasa zaki ratso ta ciki.

 

 

Kai na daga ina kare mata kallo, sanye take da daguwar farar hijab, ni sai yanzu ma na lura da yarinyar nan akwai alamun zargi sosai a kanta. Tabbas idan ba aljana ko fatalwa bace, to yarinyar nan duk inda ta fito ba yar kasar nan bace, amma yanayin yadda hausarta ke fita ta dade a cikin hausawa ko kuma ma a nan aka haifeta. Na danyi murmushi irin na yake, kana na ce, “Ayya na tausaya miki, amma sai dai ina mai baki hakuri kinyi rashin sa’a ba Bukar din bane, Ni kuma bako ne a garin nan, bansan wani masauki ba da ya wuce wannan shagon, sannan ba zan iya baki ki shiga ki kwanta ba a matsayinki na mace. Amma zan iya rakaki garin naku idan babu nisa daga nan”. Daga jin haka na ga alamun fuskarta ta cika da farin ciki “Na gode sosai garin babu nesa ko kadan daga nan”. Tana fadin haka na ce “To shikenan bari na mayar da kayan nan daki”.

 

 

Na kwashi tabarma da filo na jefa daki, na daukko makulli na kule, nan take na ce ta shiga gaba sai in dinga binta a baya tunda ita ta san hanyar. A dai-dai wannan lokacin ni kaina bansan abinda nake shirin aikatawa, shirmene, ganganci ko kuma son nuna jarumta kawai, domin duk wani alamun zargi sun tabbata dake nuna cewa wannan yarinyar ba mutum bace, nasan dai ban taba gani ko jin wanda akace yaga fatalwa ko aljani ido da ido ba sai a labari, amma in da za’a barni zan tabbatar da cewa yau na gani, zuciya irin ta maza ni fa yarinyar nan ko aljana ce ta saye zuciyata wallahi, don kyawonta, tsayinta kai komai nata ma yayi man, watakil ma shiyasa na aminta da zan rakata ba tare da gardama ba, idan na ga gidansu kuma da gaske ba aljana bace mutum ce, dole na karbi lambar wayarta. Muna cikin tafiya na ce, “Baiwar Allah shin ke matar aure ce ko budurwa”. “Ni budurwa ce ba matar aure ba”. Ta bani amsa a takaice, na ce “Ni tun dazun muke ta jayayya da zuciyata ni da ita mun kasa bambance asalin yarenki, domin kyawonki ya shallake duk inda nake hange da hasashe, shin dan Allah balarabiya ce ko ko buzuwa?”.

 

 

Duk da kasancewar a bayanta nake, yanayin yadda naji tayi magana tabbas murmushi tayi, “To ka canka da kanka mana a ganinka ni wace kabilar ce”. “Balarabiya?”. Ta ce, “Aa”. Na ce “Buzurwa ko bafilata”. Nan ma dai amsar aa ce, Na ce, “To shuwa arab?”. Ta ce “Duk baka canka dai-dai ba”. Jin haka yasa na ce, “To ni dai na kure iya tunanina ban gano asalin kabilarki ba, kuma dai ban sani ba ko zaki taimaka ki fada min, idan so samu ne ma tare da sunanki, ni har da lambarki ma ina so”. Ji nayi ta ce, “Lambata kuma? Ai ni bani da waya, sannan me zakayi da lambata idan da ace ma ina da waya?”. Muna dai cigaba da tafiyar da bansan gidan ubanwa zamuje ba cikin dare, mun dai kutsa kai wata yar hanya da bansan ina take zuwa ba, saukinta daya akwai dan haske na farin wata kuma ina haska fitilata. “Eh to, da yake wani lokacin ina da zuciya da zafin rai, na dade ina neman maganin wannan halin nawa ban samu ba. Amma yau karon farko jin sassanyar muryar nan taki, yasa naji a jikina na samu maganin waraka daga cutar zafin rai, kinga da kina da waya duk lokacin da raina ya baci sai in kiraki, na tabbata ko sallama nayi kika amsa raina zaiyi sanyi”

Fatalwar Delu Part 7

 

Gani nayi ta tsaya cik ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya, kai ni kaina tsayawa nayi ina kallonta, domin na gaza gane dariyar kalar ta farin ciki ce in yayi yawa, ko kuwa ta wani dalili ne daban. Kai wannan dariyar ta fi kama da dariya irin ta shedanu kuma mugayen mutane, sam bai kamata a samu kyakyyawar budurwa kamar wannan tana irin wannan dariya ba, don ina kallonta harda rike ciki. Zuwa can da na lura dariyar ba mai karewa da wuri bace, na ce “Ke kuwa me ya baki dariya ne haka?”. Ba zato ba tsammani sai gani nayi ta tsaya cik da dariyar da take tamkar daukewar wutar nepa, ta kuma juyo tana kallona. Kamar zatayi magana sai kuma na ga ta nuna ni da yatsa ta sake barkewa da wata mahaukaciyar dariyar. Ni na tabbata yarinyar nan akwai abinda yake damunta, in ba haka ba miye abun dariya a cikin maganata. Ji nayi tana yunkurin yin magana amma dariyar ta hanata don haka na ce, “Kinga dan Allah yi hakuri ki sassauta dariyar nan, kinga yanzu dare ne har daga nesa za’a iya jiyowa”.

 

 

Kamar dai dazun sake katse dariyar tayi lokaci guda na ga fuskarta babu annuri, cikin dai muryarta mai sanyi naji ta ce, “Bayan mahaifiyata kaine mutum na farko da ka fara sakani dariyar farin ciki, musamman da naji ka yabeni irin yabon da nake muradin ji, naji ban gaji da jin zantukanka ba cigaba ina sauraronka”. Al’ajabi da mamaki ne ya cika zuciyata, au wai ita wannan yarinyar a haka nufinta dariyar farin ciki ne take? To ai kuwa idan da haka ake dariyar farin ciki da an rika tsorata mutane ba dalili, don kuwa dariyar nan tafi kama da ta mahaukaci sabon kamu. Ganin tayi tsaye tana kallona bata alamar juyawa balle inyi tunanin zamu cigaba da tafiya, yasa na ce “Shin an kusa zuwa gidan naku ne? Ai kamata yayi mu karasa kinga dare na kara yi ni kuma gobe ina da tafiya mai nisa ya kamata in kwanta da wuri”. “Babu inda zakaje”. Abinda naji ta fada kenan, da sauri na ce “Me kika ce?”. “Ba komai”. Ta fada a takaice. Bansan me take nufi da babu inda zanje ba, amma ganin tana neman barin maganar ya sa na biye mata na ce, “To shikenan muje gidan naku”.

 

 

Ta juya baya tana leke-leke bansan uban me take dubawa ba, kana ta juyo gareni ta ce, “Ai nan ma ya wadatar ka koma kawai”. Nan ma dai wani sabon mamaki ne ya sake kamani, domin na duba bayanta jeji ne babu alamar gari a kusa gashi kuma tana cewa in koma ya wadatar. Cikin rashin fahimta na ce, “Kamar ya in koma, kin daina jin tsoron ne yanzu ko me?”. Ta ce, “Kai dai tunda na ce ka koma to kawai ka koma, shine zabi mafi alkhairi a gareka”. Ni duk ban fahimci me take nufi da hakan ba, ni ba burina rakatan ba, burina dai shine in san gidansu watakil yadda ta kwanta min a rai ko bayan na koma gida ne sai in rika aiko Bukar yana kawo mata waya muna gaisawa. Don haka na kafe kan cewa lalai sai na rakata na ga gidansu, ita kuma ta kafe a kan lalai-lalai in koma nan ya isa.

 

 

Muna cikin jayayya ba zato ba tsamani kawai sai jin wani iska nayi mai karfi, kai tsaye na ga hijabin dake kan budurwar ya sauka zuwa wuyanta, nan take dogon gashin kanta ya mike tsaye ya fara motsi da kanshi tamkar macizai a saman kannata. Idanunta sukayi wani irin ja tamkar danjar mota. Duk kyan yarinyar nan sai ga ta ta koma tamkar dodanniya mai matukar abun tsoro, baya-baya na fara yi a tsorace da ganinta. Tabbas na tsorata matuka don wannan ne karo na farko da na taba ganin abu makamancin haka a rayuwata, ko da yake wani bari a zuciyata yana gaya min duk wannan mafarki ne ba gaske ba. Muryarta na tsinkayo tana fadin, “Na ce ka koma tun kafin in canza ra’ayina na yafema da nayi. Idan ka ce sai ka biyeni mamata da kanina da ka daka dazun ba zasu taba kyaleka ba sai sun kasheka, nima na yafe ma ne saboda kalaman ka sun burgeni”. A zuciya na ce, lalai yarinya ai ba sai kin kara nanata in koma ba da gudu ma zan koma kuwa, har na mike zan juya a guje sai kuma na tsaya na juya hade da cewa, “Tunda ke fatalwa ce ina da tabbacin kina da alaka da mafarkin da nayi dazun, da na ga wasu na kokarin kashe Bukar, kuma dazun da kika zo wajena naji kina tambayarsa, ina fatan ba wani mugun abu kuke kullawa a kansa ba”. Ji nayi ta kyalkyale da mahaukaciya dariya, sannan wata magana marar dadin saurare ta biyo baya, “Bukar dole ya mutu, dole ne ma sai na kasheshi sannan hankalina zai kwanta”…………..

Also read

Fatalwar Delu Part 1

 

Zan cigaba

Back to top button