Novel Document

Nakasa Ba Kasawa Bace Book 2

Nakasa ba kasawa bace Book 2 By Aisha Aliyu Garkuwa

Description/Story:

Nakasa Ba Kasawa Bace Book 2! Written By Aisha Aliyu Garkuwa 

 

Description Of Nakasa Ba Kasawa Bace Book 2

Cikin tsananin tsoro da mamaki. Maryam ta rumtse idanunta da azaban k’arfi tare da cewa.

“Innalillahi waInna’ilaihirajiun. Zaleeha kashe kanki zakiyi baki da hankali ne?.”

Sai kuma duk falon ya ricab’e sabida. Ihun da Zahira keyi tanayi tana tsalle da burburwa tare da cewa.

“Shike nan ai an huta.”

Aunty Lubna kuwa da Ziyada ruggume juna sukayi tare da rumtse ida nunsu,

Ganin yadda Zaleeha tasa knife d’in ta yanke wuyan hannunta tare da kurma ihu mai gigitarwa, tuni jini yaketa tsiyanyowa yana zubowa har k’asa.

Cikin wani irin tsoro da al’ajabi da firgici ya Ahmad yayi sauri ya k’arasa gabanta, tare da sa hannu ya fizge knife d’in data saitashi kan jijiyar mak’ogoronta.

Ihun Mama da Yayarta Ruda da Zahira ya cika gidan gaba d’aya.

Mamy da Aunty Lubna da Ziyada ma kukan sukeyi mai cike da tsoron ganin Zaleeha zata aikata kisan kai.

Ga kuma ihun da itama Zaleehan takeyi tanayi tana tsalle tana.

“Wallahi zan kashe kaina! gwara in mutu kowa ya huta! In yaso in na mutu a raba gawata biyu a kai musu dukansu biyu kowa a bashi tsagi d’aya.”

Ya Ahmad kuwa hannunta data yanke yaketa kamowa dan ganin yadda jini ke zuba alamun ta yanke sosai.

Baba Malam kuwa tun sanda yaga ta yanke kanta, ya juya ya bar wurin yana tafe jiri na fizgarshi sabida tsananin tashin hankali da b’acin rai.

A gabanshi a gidan shi ƴarshi ke kirari da tutiyar kashe kanta, a kan mijin da itace tace ya turo iyayenshi.

Gaba d’aya idanunshi basa gani, sabida wani fitinennen duhu daya mishi k’awanya kan kwayar idanunshi, babu abinda yakeyi sai sunan Allah yake ambato,

Wai yau shi Malam Bashir Sulaiman Dukku shine za’ayi kisan kai a cikin gidanshi, kuma yarsa ce ta cikinsa, lallai fulani sunyi gsky da sukace, (Te’ud’o laddefu and’i dayan sabere) kowa ya auri daji tofa yasan tabbas wata rana zai haifi Saura/lampo.

Jiki na rawa ya zauna dirsham a bakin gadonshi tare dasa hannu duka biyu ya tallabe kanshi kana yaci gaba da zancen zuci.

“Eh tabbas yau dai yaga zahiri, ashe ba banzaba Fulani keda k’abilanci a fagen neman aure da bada aure, yau gashi yaga illa da kuma dafin gwamutsa zuriya, sabida ai dai kowa ya sani abinda d’iyarshi Zaleeha take inkarin zata aikata koma yace ta aikata kafurcine wanda addinin musulunci yayi tir dashi, kisan kai ko kashe kai al’adace ko d’abi’ace ta kafurai marasssa imani da tawakkali wanda basuyi imani da Allah da manzonsa ba, bare suyi imani da k’addara mai kyau ko akasin haka.”

Wani irin fitinennen kukane mai cushe zuciya da numfashi ya kwabcewa dottijon nan mai cikar haiba da kamala, mik’ewa yayi cikin tsananin kuka ya d’auki yar karamar jaka,

Qur’an da wasu littafan ya saka a ciki, sannan yasa ATM nashi da carbinshi kana ya d’auki car key d’inshi.

A hankali ya nufi cikin gidan inda yake jiyo ife-ifen na k’ara tsananta,

Dib-dib-dib haka zuciyarshi ke bugawa da tsananin k’arfi da firgita Kardai ta kashe kan nata ne?.

Yana isa ya samesu gaba d’aya suna tsaye a tsakar gidan, sai Zaleeha daketa kwaso akwatunan da yan uwan Abdussalam suka kawo tana ta watsosu tsakar gida,

gaba d’aya tayi kaca-kaca da komai ta birkice ta zama kamar mai shafar al’janu.

Ya Ahmad ne keta kamota tana zillewa duk ta birkice gashin kanta yayi biji-biji ya hargize ta zama kamar zarerriya

Wani k’aton akwati ta jawo wanda wlhi ko maza zai sunyi da gaske zasu jawoshi sai gashi ta figoshi ta turoshi waje,

Ahmad ne yayi sauri tareta cikin gigita da kid’ima ya kamo hannunta dake zubda jinin tare da cewa.

“Wallahi al’janine a jikinta, sune suke sata yin komai.”

Da sauri ya sake hannunta ya kalli Ziyada data ruga a guje ta nufi mahaifin nasu,

tana zuwa ta durk’usa gaban Baba malam hannu duka biyu ta d’ago cikin tashin hankali ta saki kuka mai sauti tare da cewa.

“Dan Allah Baba Malam kayi hak’uri, kada ka tafi, in ka tafi ka barmu ya zamuyi, dan Allah Babana kayi hak’uri, wlhi gwara ka kori ita Zaleeha tunda bazatayi maka biyayya ba.”

sai kuma ta kifa kanta bisa rumfar sawunshi cikin neman al’farma.

Hakama Maryam da gudu tazo gabashi ta durk’ushe murya na rawa cewa.

“Wayyo Allah na wayyo Ya Ahmad ka bar Zaleeha kaga zata kashe mana mahaifinmu da bak’in ciki.”

Sai kuma ta matso gab dashi cikin tsananin kuka take magiya.

Tuni Ahmad ya mance da Zaleeha bare matsalarta yazo tsakiyar k’annenshi suka durk’usa gaban Mahaifin nasu suna kuka mai tada hankali.

Zaleeha kuwa sam bata cikin nitsuwarta bare tasan illar abinda take aikatawa asirin da uwarta tayi mata ya shafe nitsuwarta burinta kawai ta firgita kowa a fasa batun aurar da ita.

Ido Baba Malam ya rumtse ganin Mamy ta motso gareshi cikin kuka take cewa.

“Kada laifin mutun d’aya ya shafemu baki d’ayanmu, idan ka tafi ya zanyi da rayuwata? ina zan shiga? Me ya rage min da zaman gidannan? Dama d’ana kwaya d’aya tak Allah ya bani, shi kuma ba’a gidan yakeba, dan k’ashin Kanka ne da aurenka nake zaune a gidan nan, ni banyi maka laifiba Maryam batayi makaba hakama Ziyada da Habu da Zakiriyya to meyasa zakayi nesa damu akan laifin da bamu aikata ba?.”

Ta k’arishe mgnar tare da durkushewa gefenshi kana ta kamo hannunshi murya na rawa tace.

“Duk in da zakaje sai ka tafi damu, in kuma laifinsu ya shafemu ne, wlhi kana fita nima zan bar gidan nan.”

Kalamam Mamy sunyi matuk’ar k’ara gigita su Maryam kawai sai suka saki sabon kuka.

Mama kuwa da Ruda da Zaleeha ihu sukeyi wai bak’in ciki ya haukata Zaleeha.

Daga bakin Gate Habu ke jiyo ihu da hargitsin dake cikin gidan nasu,

Ko parking bai gama dai-dai tawa ba ya fito cikin motar, a guje ya nufi cikin gidan nasu gaba d’aya jikinshi kerma yakeyi.

Wani irin tsayuwa yayi tare da zaro idanunshi baki d’aya, kuka da magiyar dasu Maryam keyi ya ganar dashi abinda ke faruwa.

Wani irin tafasa da harzuk’a zuciyarsa keyi, juyowa yayi tamkar zautacce,

Zaleeha da ta Kikimo wani akwatin ne ta harboshi, dai gaban Habu, kana ta juya tayi hanyar shiga parlour da niyar kwaso wani.

Wani irin razanannen k’ara ta saki jin wani irin azabebben naushi da Ya Habun nata ya d’irka mata a tsakiyar gadon bayanta har saida tayi tangal-tangal zata fad’i k’asa,

bata gama gigitar naushinba taji yasa k’afarshi ya tareta daga fad’uwar da zatayi ya naushi k’irjinta wanda saida ta bada sautin hak.

Bata ida tsayuwarba tayiji yasa k’afarshi ya tad’eta ta yi k’asa, ji kake gib ta bugi k’ofar parlour tayi gaba ta dawo baya,

sai kuma ya zaro belt d’in k’ugunshi ya juya kan belt d’in dai-dai inda k’arfen yake ya fara tsula mata tamkar Allah ya aikoshi.

Ihu da karaji ta sake tare da fara mirginawa tamkar macijiya tana.

“Wayyo Ya Ahmad ya Habu zai kasheni! Wayyo goshina ya fashe! Wayyo k’uguna ya karye, wayyo Allah na na mutu na lalace”.

Shi kuwa binta yakeyi a baya yana had’a mata naushi da gula da zana tare da magana cikin haki dake nuna tsantsar tafasar da zuciyarsa keyi.

“Shegiyar yarinya. tsinenniya mara amfani a doron duniya, kiyi ihu da kyau ki fad’a da k’arfi kasheki zanyi, tun kafin ki kashe mana mahaifinmu, kasheki zanyi koda ma rage mugun iri, shegiya mai zuciyar arnan kan duwatsu. Shegiya mai gadon bak’ar zuciya.”

Ina Ahmad, Maryam, Mamy, Ziyada su bata Zaleeha sikeyi ba bare su ceceta daga bugun gardi da Ya Habu keyi mata.

Ganin alamun habu zai kasheta ne yasa Mama tayi tsalle tare da shiga tsakaninsu, da k’arfi ta ingiza Habu baya tare da cewa.

“Dan ubanka kai farar zuciyarce da kai? Nace kai ɗin farar zuciyar ce da kai? da kake cewa tayi gadon bak’ar zuciyar a ina ta gado kenan?.”

Kan Zaleeha ya kumayi sunkuyowa yayi yasa hannu ya damk’o wuyanta tare da shak’ewa da k’arfi kana ya kalli Mama tare da cewa.

“Eh nima bak’ar zuciya gareni kuma, data kashe mana uba gwara na kasheta, bak’ar zuciyar kuwa a ina zamu gada banda wurin bak’ak’en arnan iyayenkin can dake bautar gumaka.”

Aunty Lubna ce tayi k’arfin halin kamo hannun Habu da niyar cotar rayuwar Zaleeha daketa kakarin mutuwa tuni idanunta sunyi zuru-zuru a woje, sai kuma ya jiyo muryar Baba Malam na cewa.

“Abubakar ka dawo haiya cinka, kisan Kai ya sab’awa addinin musulunci.”

jin haka yayi matuk’ar sace mishi zuciya hakan yasa ya hankad’e Zaleeha, kana yazo ya durk’usa gaban mahaifin nasu cikin rauni yace.

“Dan Allah da al’farman manzon rahma Baba Malam kayi hak’urki ka gafarcemu ka rufa mana asiri kada kayi nesa damu.”

Ita kuwa Zaleeha wani irin azabebben tari takeyi tun sanda Habu ya sake mata wuya tarin takeyi tare da kuka,

Aunty Lubna ce ta ruggumeta sukaci gaba da kuka a haka,

Ruda kuwa tunda Habu yazo ta silale ta bar gidan dan tsoron yaron take.

Ita kuwa Mama akwatuntan su Abdussalam d’in ta fara tattarewa tana maidasu parlournta.

Shi kuwa Baba Malam kanshi ya jujjuya tare da rab’awa gefen su da nufin zai fita, ganin hakane yasa fargabansu ya ninku sama da sau d’ari, Maryam ce ta kife kanta a k’asa cikin kuka tace.

“Kaito na! Kaiton rayuwata da bani da damar share hawayen mahaifina, Yau da ace bani da aure wallahi da na sharewa maka hawayenka baba malam Kodako Saifuddeen kurmane makahone gurgune kuturune wallahi matuk’ar zakayi farin ciki tabbas da zan zauna dashi.

Inama ana rabuwa biyu wallahi da na kasu biyu.”

Ziyada ma kukan takeyi tare da kamo hannun Baba Malam cikin rauni tace.

“Baba kada ka tafi ka barmu, in yana sona ni zan zauna dashi.”

Gaba d’aya sun rud’e da kuka hatta habun kuka yakeyi bare kuma Maryam da Ahmad masu rauni…

Nakasa ba kasawa bace Book 2 txt

 

File Name   Nakasa Ba Kasawa Bace 2… Hausa Novel Doc.
Title  Nakasa Ba Kasawa Bace Book 2
Author    Aisha Aliyu Garkuwa 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/08/2024
File Size    1.2MB
Format Size    TXT
Book Price    500
Phone No   09097853276
Download Nakasa Ba Kasawa Bace Book 2 By Aisha Aliyu Garkuwa 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button