Gargadar So Chapter 71 By M Shakur
Gidansu tayi, tana kaiwa unguwansu babu kowa a kofar gidan amman kunya yahanata fita, ga idanunta sunyi jazir, takai almost 10min a motan sannan ta kalli fuskanta a mirror lips nata sunyi pink yirr, idanunta sunyi ja, tadai daure kafin su Baba suzo waje tabude motan tafito tashiga gida tana tafiya awaware tanadan dingishi, tana shiga compound nasu mutane, su Miemie suka fara rungumeta ga jama’a agidan ana bude akwaitinta da bamata san an kawoba, ga yan anguwa ana ganinta aka fara ayiriri Ammi data ganta fitowanta daga dakin Aminu kenan ta taho wajenta da sauri tace “amarya ba lafiya sannu an sallamoki muje kihuta” Ammi ta kamata suka wuce daki, Ammi tabita da kallo ahankali tace “ya jikin? Shiya kawoki”? Gyadama Ammi kai tayi tana sauke kai ba bakin magana tai zuru zuru, Ammi da hartaga shedan ruwan gashinta ta saman hijabi tace “kinsha asibiti bari nakai miki ruwa bayi kiyi wanka ko sannu zakici abinci akawo miki?” Girgizama Ammi kai tayi da kyar tace “wanka zanyi nai bacci” gyadamata kai Ammi tayi tace “akwai ruwan zafi bari nahada na kai miki” Ammi tafice ruwa mai zafin gaske takai mata abayi da botiki daya daban na sirki sannan tadawo ganin Hawwa tayi harta cire kaya tadaura zani tasa another hijabi daban, Ammi tabi dakin da kallo tace “ina kayan da kika cire na bada awanke”? Dasauri tace “uhmm ahh suna cikin akwati na ki barshi zan wanke” Ammi tace “toh muje” kamata tayi daurewa tayi tabi Ammi har bayi ta kaita Ammi tai murmushi kadan kawai ta dawo tadan gyaramata gadon ta kakkabe taje tadawo da ita daki kuma tafita, Hawwa tacire hijabinta ahankali tadauki ribbon ta kulle gashinta dayake sharkap tadauki dankwali na atampa ta kulle kan kar agane da ruwa, dogon riga har kasa na abaya tasa ta kwanta sai bacci.Khaleel yadinga kiranta rannan taki dauka tama maida wayan silent mode, rannan bacci tayi da daddare mai kyau har gari yawaye ko farkawa batayiba batasan me Khaleel yayi ba but dai kaman ta zubar da abinda ke damunta da daddare.Da sassafe yau Wednesday aka fara shirye shirye henna day, still tayi using hot water zafin yaragu sosai tasoma dainaji, an aiko da bridal dresses nata jiya da daddare, tayi wanka kenan tana cikin saka HKG atampan dasu Hafsa suka fito mata dashi daga akwatinta na henna party Aminu ya shigo yace “Ya Hawwa Khaleel na waje yakawo miki Noor” faduwa gabanta yayi sosai dan kallonshi tayi sai kuma tace “okay” kanninta ko wanne yashiga makale dariya shikuma Aminu da gulma yace “suna miki dariya Ya Hawwa” kallonsu tayi aiko suka bushe da dariya Hafsa tace “ayiriri amarya” hararansu tayi tadauki gyale maroon tayafa kan atampan wlh tayi kyau tana tafiya ahankali sai kanshi take tayi waje, a zaure taga Khaleel da Noor da katon box na kayanta, tana ganin Hawwa tai wani ihu tai tsalle Hawwa ta dauketa tana murmushi Noor tace “My FAA” haderai Khaleel yayi yace “careful Noor stop rough handling my wife kaman yanda kikemin batada karfi kaman ni, besides she’s sick” dan hararanshi Hawwa tayi batare data kalleshi ba tana kallon Noor tace “don’t mind him your FAA have power” kankameta Noor tayi saikuma ta mata kiss a kumata tace “I love you soo much FAA, you look super duper beautiful right Dad”? Khaleel na kallon Hawwa kaman zai hadiyeta yana tuna abinda yafaru jiya tsakaninsu yace “right princess, she’s beautiful external and internal” sauketa Hawwa tayi da sauri tazo wajen takai hannu zata karbi akwatin Noor sabida su koma ciki kafin yafara iskanci wannan daya fara maganan banza gaban yarinya kawai Khaleel yajawota zuwa jikinshi and just give her a tight hug daidai Baba da Aminu na shigowa zauren hakama kanninta su Hafsa kawai suka fasa ihu. “Wuyuuuuuuhuuuu” Baba yawani kume murmushi akunyace Hawwa ta fizge kanta kaman zata nutse akasa ganin Baba da kanninta sunga yanda yake rungumeta, Baba yama su Hafsa dakuwa yace “kunci gidanku me kuke haka”? Noor sai washe baki take tana kallon Dadynta da Hawwa, Hawwa tai sauri zataja jakan wlh Khaleel yakasa daurewa dudda gasu Baba kaman wanda Hawwa tama magana yakama hannunta yace “karki tafiiiiiii” awani shagwabe sai kawai su Hafsa sukahau “ayiriririiiii” Baba yadan kwashe da dariyan manya kadan yadaga sanda zai rapka musu suka kwasa aguje sukai cikin gida Baba yace “Noor muje na kaiki dakin Mamanki tunda Babanki na magana da ita” dasauri Noor tabi Baba hakan yasa Hawwa tajuyo cikeda masifa still taki kallon idanunshi tace “mehaka kakemin gaban mutane”? Kaman zaiyi kuka yace “I’ve missed you, baki daukan wayana, baki magana dani why? Mena miki wai”? Akufule Hawwa tace “I don’t accept you, I don’t accept wannan auren, ban sonka nagaya maka” shiru yayi yana kallonta yakasa magana, kawai Hawwa ta fizge hannunta da jakan tawuce cikin gida abinta, nan fa aka fara henne party ga komi Juzzyfabevent event takawo, hatta su zubo da bottle water, kunun aya, popcorn amsaka sticker sunan Hawwa da Khaleel so lovely, matan ta iya decoration da kowa yashigo mamaki yake compound din gidan Baba Juzzyfabevent ta komar haka, she sabi the job. Ana playing waka compound na Baba da girma so set up yayi kyau professional masu henna da aka kawo suka fara mata ana rawa, Noor na rawa dasu Miemie, Hawwa sai kallon Noor take tana kama da Khaleel tanada kyau kaman shi, dasauri ta girgiza kai tana gayama kanta me ruwanta da kyawunsa, duk wnada keson lalle zama kawai yake amai, Hawwa kawai bin kowa da kallo take especially yan uwanta barinma Ammi da Baba, Ammi stood as her Mom, komi ita keyi, ita ake tambaya, yan unguwan na Maman Amarya kawo gishiri, kawo omo, abada this and that duk haka suke kiran Ammi, Baba na farin ciki bini bini yashigo yaduba zanen da akema Hawwa yatafi yakara dawowa yace amata mai kyau, yasake dawowa yace azana sunan Ibrahima atafin hannunta, har aka faramai dariya, Hawwa kawai taji kuka na taso mata, she wish aure ne da mutumin arziki wanda yasan darajan mace, all this prep, farin cikin da Baba keyi, dasu Ammi da yan uwanta Allah yasa tamayi 1month bai saketa ba.

