Uncategorized

Macijine Shi Page 47-48 Hausa Novel

 

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 47/48

_________________Kai tsaye part ɗin nanny Adeeb ya nufa da fattu,suna zuwa kuwa nanny ta gyara ko ina sai ƙamshi ke tashi,dakin fattu suka shiga ,ya zaunar da ita abakin gado.kallonta yayi na ɗan wani lokaci yana tunanin wannan ƙamshin na jikinta yayi yawa ,kuma zai iya sanyata mura ma,dan shi kansa ƙamshin ya buwaye shi.

Ahankali ya buɗe bakinsa yana  mai faɗin ” nanny ahaɗa mata ruwa tayi wanka saita sake wannan kayan” ya faɗa yana kallon nanny dake kusa da fattu tana faɗin” ke ƴar nan !wannan ƙamshin fa?tunda kuka dosa part ɗin nan nake jin ƙamshin,turaren magajin faɗa,ashe ajikinki yake”cewar nanny Tana mai kallon fattu,kafin ta dawo da kallonta kan Adeeb tana mai cewa” ai dole ma tayi wanka dan wannan turaren yayi yawa ajikinta,kasan shi kuma turare shu’umin abune,yanzu zai saka cikin wani hali,barin ma wannan turare naka mai sanyi ƙamshi, ga yara irin su Rashad birjik afada” nanny ta faɗa tana mai kama hannun fattu suka nufi toilet.

Shiru Adeeb yayi yana kallon ƙofar da suka shiga,lallai dole ma ya hana fattu sanya turare dan maganar nanny gaskiya ce,shi kansa cikin wani irin shauƙi yake jinsa,hakanan tunda ya shaƙi ƙamshin ajikin fattu.

Tashi yayi cikin nutsuwa ya fice daga ɗakin. 

Dakin ammi ya nufa lokacin tana zaune gaban wani ƙaton akwati mai ruwan gwal ,sai sheƙi yake da ɗaukar ido,ba komai bane cikin akwatin sai sarƙoƙinta na gwal kala -kala.

Wata yar ƙaramar akwatin ce ahannunta tana mai kallon sarkar fattu data adana aciki.

Murmushi tayi tare da faɗin”nayi alƙawarin keda haɗuwa da  ahalinki saidai alahira,zanyi ƙoƙarin toshe duk wata hanya da zata sadaki dasu,domin cike burina” ammi ta faɗa cikin zuciyarta tana mai murmushi da ƙarewa kyakyakywar sarƙar kallo.

Kamar daga sama ta tsinkayo sallar Adeeb .dan haka cikin azama ta maida sarƙar cikin dan akwatin tare da rufe babban ta maida shi ajiyarsa.

Zama Adeeb yayi kusa da ita ,ba tare da yaga abinda tayi ba.cikin zafin zuciya yake magana da harshen larabci” ammi zan ɗauki mataki mai tsanani akan Rashad da mahaifiyarsa ,Dan kuwa sun ƙetare iyakarsu” Adeeb ya faɗa yana huci cikin ɓaci rai.

Wani daɗine ya mamaye zuciyar ammi ,amma a zahiri da sauri ta kamo hannun Adeeb tana mai marairaice fuska tace ” haba habeebee ,me yayi zafi ?me sukayi maka?Indai akan wannan maganar ce ,to kabar komai ahannuna zanyi wa tubkar hanci,bazai kara zuwa gurin ta ba”Ammi ta faɗa tana mai shafa bayan hannun Adeeb ɗin.

Girgiza kai yayi cike da jin tsanar Rashad da Amma,kafin yace ” ba wannan maganar bace,ammi Rashad ya ɗauke sarƙar da zata zama makamin da zai sada yarinyar da mahifanta,kuma nasan wannan tabbas shirin Amma ne, Ammi na rasa me kika tsarewa matar nan ta Tsaneki da ahalinki baki ɗaya,kullum burinta ta ganmu cikin tashin hankali ,why Ammi ?” Adeeb ya faɗa cikin mugun damuwa da tausayin Ammin nashi.

Sosai Ammi ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ,kafin ta fara magana” habeebee nima bansani ba ,duk yadda nake ƙaunarta da iyalinta,amma sam bata gani tun kana yaro take ƙoƙarin saita ga bayanka ,amma Allah bai bata Sa’a ba, kai dai karvi gaba da haƙuri, sannan kabi komai cikin lumana.kuma awannan karon na goyi bayan ka ɗauki mataki akansu har sai sun bayyana sarƙar nan” Ammi ta faɗa cikin ƙarfafa gwuiwa ga Adeeb . Jinjina kai yayi cike da gamsu da shawarar ammin nashi.sun jima suna tattaunawa akan al’amarin ,ba abinda ammi ke yi sai tunzura Adeeb cikin cikima da basira.

Download>>> Kufan Wuta Hausa Novel By Safiya Huguma

Amma kuwa tana zaune abakin dagon Rashad,yayin da take shafa masa maganin zafi aciwonsa bayan yayi wanka da ruwan dumi.sosai take jin zafin abinda Adeeb yayiwa Rashad,kalli yadda yaji masa ciwo kamar wani marar gata?lallai saita ɗauki mataki,dan bazata yarda da wannan cin mutuncin ba.

Kallon Rashad tayi wanda yake ɗan runtse ido idan ta shafa masa maganin

 zafin.

“Haƙiƙa Adeeb yana wuri gona da iri masarautar nan,kaima fa ɗane ba bawa ba,dan me zaiyi maka irin wannan dukan?saikace ya sami yaronsa, haƙiƙa bazan amince ba ,dole mai martaba ya shiga maganar nan,kuma wllh nayi alƙawarin sainaga bayan Ammi ,dan kuwa ita ke daure masa….yake abinda yaga dama.haka kawai an maidamu kamar wasu matasa iko agida,bazai yiwuba ,sam bazan laminci wannan abun ba” Amma ta kai ƙarshen zancen ta cikin fushi sosai da bacin rai.

Kallonta Rashad yayi shima cikin ɓaci rai,yana mai faɗin “amma kibar wannan maganar atsakanin mu ,kar ki bari mai martaba yaji,dan kuwa da kaina zan ɗauki mataki,wllh saina yi masa abinda sai yayi dana sanin aikata min wannan abun akan wata bare,ke dai kawai ki zubamin ido” Rashad ya faɗa yana mai kitsa abubuwa cikin ransa.

Wannan kenan.

Baƙi sun fara zuwa ta ko ina ,manyan sarakai da yan siyasa na ƙasar Misra, ko ina acikin gidan jama’ane keta kaiwa da kawowa,dan kuwa yau ne za’a gudanar da ƙayatacciyar walimar murnar dawowar prince Adeeb gida,daga ɓangaren Amma baƙi sunzo sosai,matan sarakuna na ƙasashe da dama,da matan manyan masu kudi da yan siyasa.dan haka hadimai sai kaiwa da kawowa suke dan kula da  baki.

Yayin da bangaren Ammi kuwa ,ba magana ,dan kuwa itace uwar taro ,mai gayya mai aiki kenan,sosai ta tara manyan matan sarakuna dana yan siyasa ,da matan manyan attajiran larabawa,kai harda na ƙasashen Afrika .

Ammi taci uwar kwalliya cikin kaya na alfarma ,tayi ado da gwala-gwalai sai ƙamari take bugawa tana cikin matan data gayyata suna ta hira kafin a fara gudanar da taro.

Busar sarewace ta karfe fadar ,alamun da ke nuna wasu baƙin sarakan sun sami hallara,murmushi Ammi tayi dan kuwa ta gane busar ko ta wace ƙasace, ba kowa bace bace ƴar uwarta gimbiya Zulaihat ,wacce ke auren Sarkin gana.dan haka cikin farin ciki ta mike tare da cewa matan tana zuwa.kafin ta fice zuwa farfajiyar da aka ware musamman dan tarbar baƙin ta ,gurine ƙayatacce wanda yasha ado ,aka wadatashi da komai na jin dadi.

Tana tafe haɗimanta na biye da ita ,murmushine ɗauke akan fuskarta wanda ya ƙara ƙasa ta fuskar tata.

Wata farar mace ce kyakyakywar gaske ta fito daga cikin lafiyayyar motar da aka bude,masha Allah matar ta ko ina ta hadu ,fuskarta ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa,idanunta na kan Ammi rungume juna sukayi cikin farin ciki,ammi keyiwa matar Barka da zuwa.

Wasu kyawawan yara ne su biyu suka fito daga ɗaya gefen,da ala’ma yaran tagwayene duba da yadda suke tsananin kama da juna.yaran zasu kai shekara goma ,saidai yanayin jin dadi da hutu,yasa zaka yi tunanin sun wuce hakan,suna sanye da kaya iri ɗaya ,cikin shiga ta ya’yan sarakai.

Gurinsu ammi suna nufo cike da murna suka rungume Ammi,ita cikin jin daɗi ta rungumesu tare da sunbatar  gishinsu,tana mai faɗin,” yazeed and zayyad  my children” ammi ta faɗa tana shafa kansu.

Part ɗin ammi suka nufa gaba ɗayansu,cike da murna.

Adeeb ne zaune bakin gado yayin da tareeƙ ke gefensa ,yana tashi shiryawa,shi dama Adeeb baida aboki ,tareeƙ kaɗai ne abokinsa kuma yaronsa,dashi yake ko wace irin shawara ,dan haka ya zuma suna zaune suna shiryawa,dan Adeeb baya barin kowa ya shigo masa part ɗinsa, shi fa akan dole yake abubuwan masarauta, dan sam sarauta bata burgeshi, yafi son kasuwancinsa.

Kallon tareeƙ yayi yana mai faɗin,”tareeƙ nufa na gaji da wannan shirin Please ya isa haka” ya faɗa yana ɗan kwaɓe fuska cikin salon shagwaba.

Murmushi tareeƙ yayi yana mai ɗaurawa Adeeb wani agogon azurfa ahannunsa kafin yace ” yallaɓai yaufa dole kayi haƙuri ,dan kuwa saikayi shiga irin ta yarima sosai ” tareeƙ ya faɗa yana ɗan danne dariyarsa ganin yadda Adeeb ya wani marairaice kamar zaiyi kuka.harararsa Adeeb yayi yana mai faɗin” dariya ma zakayimin ko?ai kaima mugune nasani ,shiyasa kake ta lodamin kaya haka kamar wani dan dako”

Dariya sosai tareeƙ ya sanya yana mai faɗin” yallabai kasan fa yau sauka gaji da ganin yan mata ,dan zasu yi ta kawo maka hari ne,Suda iyayensu,dan haka dole kayi adon da zaka rikitasu” tare ya faɗa yana kallon yanayin Adeeb ɗin.

Haɗe rai Adeeb yayi yana mai gwabe baki yace ” aikuwa zasu wahalar da kansu ne kawai,dan duk ba wacce zata burgeni acikinsu” ya faɗa yana mai mikewa tare da gyara kwalar rigarsa.

Murmushi tareeƙ yayi kafin yace “amma yallaɓai yau idan Madam ta ganka zaiyi wahala ta gane ka ,dan kuwa kayi matuƙar kyau Masha Allah,yau lafiya ayarimanka sai” tareeƙ ya faɗa yana mikawa Adeeb wani takobi ,wanda ke matukar gyalli da ɗaukar ido.

Murmushi ne yakub cewa adeeb,jin tareeƙ ya ambaci Madam,kallon kansa ya karayi cikin madubi,masha Allah,ko aljanu ya kalli Adeeb to tabbas dole saiya yaba kyau da Allah yayiwa adeeb.

Karanta Littafin>>> Matar Hariji Page 41-50 Hot Romantic Hausa Novel

” Kasan bata da lafiya ma,kuma bazata je gurin taron nan ba,zata zauna tare da nanny ,acikin gida,dan haka muyi sauri muje In dubawa sai mu wuce ” Adeeb ya faɗa yana mai rataya takobin.

Murmushi tareeƙ yayi yana mai jin dadi cikin zuciyarsa,tabbas hasashensa yana neman zama gaskiya,dan kuwa ya kula Adeeb ya faɗa kogin SOYAYYA ,wanda hakan yayi masa daɗi,fattu itace daidai da Adeeb.” Yallaɓai kayi kama da mai son zuwa ganin budurwarsa fa” tareeƙ ya faɗa yana ɗan sosa kansa.

Ƙeyarsa adeeb ya ɗan buga kafin yace ” ka manta dai ba budurwa ba ,mata zakace ,kuma kasan hakkin ta ne induba lafiyarta ,kafin na sawwaƙe mata,iya muje” Adeeb ya faɗa yana mai kamo hannun tareeƙ.

Murmushi tareeƙ yayi yana mai cewa ” zaka dawo hanya ma yallaɓai” ya faɗa cikin zuciyarsa.

Suna fitowa kuwa hadiman da suke ƙofar part ɗin suka ɗauka kirari da bushe bushe irin na larabawa,runtse ido Adeeb yayi cike da damuwa,dan shikam wannan bushe bushe baya so ,dan dai ba yadda zaiyine.

Cikin takun izza da isa yake takawa ,tareeƙ yan gefensa sai hadiman dake binsa baya suna busa.

Kai tsaye ya wuce part ɗin ammi,da gudu su zayyad suka taho suka rungume ,Adeeb cike da murna ,dan kuwa sun saba dashi sosai.dagsu yayi daya bayan ɗaya yana dariya ,

Download>>> Bakar Inuwa By Billy Abdull

Gimbiya suhaimat ma cike da murmushi take kallon Adeeb,yaron yana burgeni sosai,yana da nutsuwa ga don yara,har ƙasa ya durƙusa ya gaida gimbiya suhaimat,da amminsa, sosai ammi ke yaba kyan da Adeeb ɗin yayi,wani lambu ta ɗauko na na zinare ta sanya masa hannunsa ,tare da   wani turare mai kanshi daɗi.

Murmushi yayi tare da mata godiya sosai,kafin ya ɗan juyo yana kallon gimbiya suhaimat,haka kawai yaji gabansa ya fadi sosai ,wani tunanine ya ɗarsu cikin zuciyarsa ,saidai da sauri ya kawar da batun daga ransa,ya yayi waje .yana gab da ficewa saiga gimbiya Zulaihat ta shigo part ɗin ,taci uban ado kamar wacce zata gasar sarautar kyau.

Kallo daya Adeeb yayi mata ya kauda kansa tare da haɗe fuska.

Ita kuwa neman gigicewa tayi da yadda taga Adeeb yayi kyau,cikin hanzari ta tari gabansa tare da kamo hannunsa tana mai jin kamar ta rungume shi.

Wani shegen kallo da Adeeb ya watsa mata ,bata san lokacin datayi saurin sakin hannunsa ba ,” kayi kyau my prince”ta faɗa tana wani narkar da fuska cike da tsantsar ƙaunar Adeeb ɗin.

Harara ya watsa mata tare da tsaki kafin ya bar gurin cikin sauri.

Kai tsaye part ɗin nanny suka shige ,tana  zaune afalo ,gefen ta kuma ,wani ɗan karamin akwatine mai kyau da ɗaukar ido.

Zama sukayi shida tareeƙ suka sata atsakiya, gaida ta sukayi,ta amsa cikin farin ciki tana mai shafa kan Adeeb,akwatin nan ta buɗe tare da ɗauko wani zobe mai kyau sosai ta zira masa ayatsansa na dama.

Murmushi yayi tare da sumbatar zoben kafin yace ” tana ina ” ya faɗa cikin salonsa yana ɗan yamutse fuska.

“Tana ciki magajin faɗa ” nanny ta faɗa .

Tashi yayi cikin nutsuwa ya nufi dakin da fattu ke zaune…..

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Novel

Masu karatu ina barar addu’ar ku,iftila’in rusau ne ya faru agarinmu,wllh gidaje sai rushewa suke,,dan Allah ku samu cikin addu’a bayin Allah suna cikin damuwa sosai ,shiyasa kukajini shiru kwana biyu,abin ya taɓa har anguwar da mahaifiyata take 

Muna buƙatar addu’ar ku.

Na gode

Mrs babi ce💘💘

Back to top button