Zakuna Biyar Page 35 By Princess Teema
DEATH OR LIFR (DOL)🔥Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya ɗan yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin ɗakinsu Arya ɗin. A tsakiyar ɗakin ya tsaya, ya zuba mata idanu, tana zaune saman electric mattress ɗinsu, ta sanya bluetooth a kunne, dik iskar dake tashi bata da labari.Angelina dake zaune gefenta ne ta taɓata game da cewa. “Ke”. Ɗago kanta yi daidai lokacin da take cewa. “Kai ma muryanka na da daɗi ai causin…….”. Gagara karisa maganar ta yi a lokacin da idanunta suka sauƙa a kan angry face ɗin Noor. Da sauri ta zabura ta miƙe tsaye, wani irin mugun kallo ya dallah mata wanda bai san ya yi ba, in a harsh way ya ce. “Da waye kike waya?”…… Da sauri ta cire bluetooth na kunnenta, hannunta na ɗan kerma, dan gabaɗaya yadda ya ɗaure faska ya razanata, murya na ɗan rawa ta ce. “Wani….. Wan…. Wani brother ɗina ne”.Wani kallo da ya wurga mata ne yasa ta haɗiyi yawu gwad…… “Ashe kina da brother kenan?”. A faɗa…… Kallonsu Angelina da Manassa suke yi, while Manassa na ta faman rikita hankalin Vash dake cikin tantansu, ta gama ce mashi wai ta gani a in da yake ana ruwan sama, kuma zata kawo mashi ziyara daren yau, dik ta rikita bawan ALLAH, wlh ya yarda aljana ce. “No, he’s my Aunty’s son, tare muka yi school, mother ɗinsa sister ɗin dad ne…….”. Hannun da ya ɗaga mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Cikin fushi ya ce. “Kuma kike cewa he have a sweet voice ko?”..Tsuru-tsuru ta yi da idanu, dan bata zaci ya ji ba, kuma wlh ita ba da wata manufa ta faɗa ba, kawai guy ɗin ya ce mata your voice is so sweet shi ne ita ma ta ce naka ma da daɗi, kun gane irin wannan abin ai? Wai ka ɗan mayarwa mutum magana mai daɗi, ashe sarkin kishi kuma lover boy ɗinmu ya jita. Jama’a watau family ɗin Noor duniya ne, lovers ne, ga kishin balai da iya shagwaɓa.Kai ya ɗan jinjina. “Your voice is so sweet”. Ya maimaita yana ɗan jinjina kai……. Zata yi magana daga cikin wayar guy ɗin ya ce. “Vanisha are you okey?”.Ta ɗan zazzare idanu a kan face ɗin Noor kafin ta ce. “Nothing Yosif”….. “I hear like kina magana da wani, who’s he?”……… Ƙara zazzaro idanunta a kan Noor ta yi. Daidai lokacin su Angelina suka mimmiƙe tsaye suna kallonsu. Wani irin kallo Noor yai mata like ki bashi amsar da waye kike magana!.Ɗan tattauna lips ɗinta ta fara yi. “Yosif bye”. Tana faɗa ya katse kiran. Muryarta na ɗan rawa ta ce. “My Romeo…….”. Bai jira jin me zata ce ba, waje ya nufa cikin fushi.Da gudu ta rufa mashi baya, a tsakiyar wajen tantin nasu ta tare gabansa, kamar zata yi kuka ta ce. “Please my Romoe, isn’t what you’re thinking……”.In a harsh way ya ce. “How do you know that I’m thinking something? Or you’re hiding something for me right?!”…… Kai ta fara girgiza mashi, kawai tasan yadda ya fita nan ne zai yi tinanin ko soyayya take yi da wani, shiyasa ta ce isn’t what he’s thinking, amma ya sake fassarata ta wani sigar.Raɓawa gefenta ya yi zai wuce, a lokacin ruwan saman ta fara karfi sosai. Da gudu ta juya, ta ruga ta faɗa bayansa, ta ƙanƙame shi tightly, hakan yasa dikkan sojojin dake kallonsu suka yi ƙasa da kai dan girmanawa a garesa. Tsalle ta yi ta haye bayansa, ta saƙalo wuyansa. Aikuwa cikin fushi ya dawo da ita ta gabansa, da karfi ya yakiceta daga jikinsa, ido cikin ido ya kalleta, ga ruwa na zuba a kansu, a fusace ya ce. “Kada ki sake taɓani, ina baki wannan umarni ne ba amatsayin masoyinki ba, sai a matsayin oganki!!”. Yana gama faɗin hakan ya saketa tare da tureta gefe, ya wuce ya nufi bakin ruwa. Abinku da bata taɓa faɗa da shi ba, durkushewa ƙasa a wajen ta yi, kuka ta fara yi, ALLAH sarki bata san komai ba sai soyayyansa, slowly ta kifa kanta a ƙasa, wani irin kuka ne ya kubce mata. Da gudu Angelina da Manassa suka yo waje. Angelina ce ta watsa da gudu ta yi kanta, a cikin ruwan ta je ta rungumota tana bata hakuri.Takaici tamkar Arya dake tsaye a bakin tantin ta rufesu da duka, sun zubar mata da mutunci a cewarta, siririn tsaki ta ja tare da komawa ciki abinta. Daidai lokacin Unays ya fito, ganin Angelina a cikin ruwa ne yasa ya yi gaggawar shiga ciki shi ma, ya isa daidai lokacin da Angelina ta ɗago V, sai dai V na ta famar langwaɓewa tana a barta a cikin ruwan ita kam. Sai hakan ya zamana kamar ta fi karfin Anglina ta gagara ɗagata.Ganin hakan yasa Unays ya ce. “Let me help you, bari in kai maki ita ɗaki”. Ya faɗa yana matsowa zai ɗauketa wai irin shi zai taimakawa Angelina ko zai zamu ya sace zuciyarta, taƙi kulashi ne, yana ta neman dama……. Matsawa baya Angelina ta yi tana faɗin thanks………. Hannu yasa zai cicciɓi V, sai kuma ya tsaya cak, da sauri ya ja da baya daga kusa da ita kallonsa a kan Noor dake nufosu tamkar wani zaki, shi da Leo duns bubbuɗe kamar zakuna, ya nufo wajen yana dallahwa Unays ɗin wani irin mugun kallo mai kama da ka taɓata kaga yadda zan yi da rayuwarka.”Ki ɗauketa kawai”. Unays ya faɗa yana ƙara ja da baya game da mai da kallonsa a kan Angelina ɗin. Ta yi mamakin jin ya fasa taimaka mata, ita kanta V mai kukar ta yi mamaki. Slowly ta ɗago kai karaf suka yi 4 eyes da Noor. Ƙara ɗaure fuska tamau ya yi, ya ɗauke kallonsa daga kanta, ya zo ya wucesu tare da Leo.Angelina ta gane karatun, watau Noor ne ya hana Unays ɗaukar V, ya ALLAH kaga wata soyayya da kishi ga fushi a gefe, kai Noor akwai rigima wlh, ya dai yi fushi, amma ba zai bari wani ya kusantota ba…….. Sai dai ita V ɗin bata gane ba, ta zaci ya daina sonta kenan, shiyasa take ta faman kuka.Arya kuwa tana komawa ciki ta hau aikinta na duba drone da suka tasa a wannan daji, ta share su V, a cewarta basu da hankali sam-sam.Tantin Leo suka shiga shi da Noor, a saman electric mattress ɗin Leo suka zauna, Noor ya yi ƙasa da kai tamkar mai tinanin wani abu, kallo ɗaya Leo yai mashi ya ɗauke kai tare da faɗin. “What are you thinking?”……. Nisawa ya ɗan yi. “My Jeliet, na wuceta tana kuka, zuciyana tamkar ba zai iya ɗauka ba”. Wani kallo Leo ya wurga mashi like baka da aikin yi, daga nan yai shiru bai yi magana ba. A daidai lokacin Arya ya faɗo ɗakin bakinta ɗauke da excuse, sai da ta faki idanun Leo ta dallah mashi harara kafin ta ƙame ta sara mashi. Noor ya ganta sarai, a cikin ransa ya ce. “Ban san me yake tsakaninsu ba, kullum sai Arya ta harari brother ɗina, anya ba son shi take yi ba?”.Shi kuwa Leo yana zaune shiru bai motsa ba bare ya ɗago ya kalleta, a dake ta ce. “Sir, there’s something you should come and see!”. Kai kawai ya ɗan jinjina ba tare da ya ɗago ba. Juyawa ta yi ta fita, amma kafin nan sai da ta dallah mashi mugun harara.Tana fita ya miƙe tsaye, kayan jikinsa ya fara ragewa, shi kuwa Noor ya gyara ya kwanta cike da tinanin V a ransa. Pjs jade color kalar idanunsa Leo ya sanya a jikinsa, ya tara kitson kansa ya ɗaure da kyau kafin ya sanya winter coat a saman pj’s ɗin, sannan ya sanya beanie, beanie wata hular sanyi ce irin mai laushi sosai ɗin nan. Bayan ya kammala ya fita ya nufi room nasu Arya. A lokacin Angelina ta yi ta maza ga ɗauki V sun shige cikin tantin nasu.Zaune ya isko Arya gaban laptop ɗinta tana duba dajin da kyau. Jin kamshin perfume ɗinsa yasa ta ɗago kai, zuba mashi idanu ta ɗan yi, while shi kuma yana kallon gaban screen na laptop ɗinta.Gently ya taƙo ya ƙariso, dik ɗakin natsuwa tsit suka yi, Manassa da Angelina suka zubawa Leo idanu, V na kife saman mattress ɗin har yanzu tana kuka. Hakiƙa Manassa ta ce Leo yana yi mata yanayi da Vash, musamman idan zai yi magana, sai ka zaci Vash ne yake motsa baki yake magana a wajen, dimple ɗinsu iri ɗaya, sharpe na eyes ɗinsu iri ɗaya, dan dai idanun Leo jade ne, kuma kamar sleeping eyes haka suke, na Vash kuma a waje suke gulu-gulu, amma shape ɗin ɗaya.Saitin in da Arya take ya tsaya, slowly ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, zubawa dajin idanu ya yi for 2 mins, sai kuma ya ce. “Wannan ai hayaki ne?”. Ɗagowa da kallonta a kansa ta yi, sai taga ba ita yake kallo ba, shiru ya ɗan sake yi, can kuma ya kai hannunsa saman mouse ɗinta, ya ɗan yi ƙoƙarin yin gaba da drone ɗin, amma sai abin ya ci tura, ya yi iya yinsa abin yaki yiwa.Slowly ya dawo da kallonsa a kan, while ta tsaye ƙashin wuyan nan nasa da ya fito sosai da kallo, kunga ya sunkuyo kanta ne, so tana iya kallon wuyansa sosai. Ganin ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta wani irin rass gabanta ya faɗi, gagara kallon cikin idanunsa ta yi, cikin zafa ta yi ƙasa da idanunta. “Meyasa drone ɗin yaki yin gaba?”. Ya faɗa in a cool way. Sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta saita natsuwarta kafin ta ce. “Nima ban san meyasa ba, amma na fi tinanin akwai gagarumin abin da dake bayan dogayen bishiyun da hayakin ke fitowa daga wajen ne”. Tana magana muryanta na ɗan rawa, dan gabaɗaya ganinsa a dab ita ya rikitata, har take jin kamar numfashinta zai ɗauke.Daidai lokacin Zaynish ya shigo hannunsa rike da bindigarsa, yana sanye da army waterproof jacket, ya yi kyau matuƙa, a kusa da Leo ya ƙariso ya tsaya, zuba mashi idanu su Angelina suka yi, a dake ya sarawa Leo kafin ya rage tsawonsa, ta ɗan sunkuyo yana kallon wajen.A daidai lokacin Noor ma ya shigo, dan jin Leo shiru. Yana shigowa V ta miƙe zaune tana kallonsa, shi kuwa tamkar bai san da zamanta a wajen ba, a ɗayan gefen Leo ya tsaya, ya zamana Arya da Leo suna Tsakiya. Zubawa hayakin wajen idanu suka yi. Hayaki ke bakinkirin yake tashi a tsakiyar dokar daji, gaba daji baya daji, waje mak sunkuru da cikowar itatuwa, waje ne da ba zaka taɓa yarda halittar ɗan adam tana rayuwa a wajen ba, akwai alamar ban tsoro a wajen, ga wasu manyan tsaunuka da koguna a wajen.Noor ne ya ce. “Idan muka yi duba da tsuntsayen dake shawagi a sararin samaniyar kewayen hakan na nufin akwai tabkeken reku a wajen! Idan kuwa haka ne lallai ba shakka wannan teku dake kusa damu ta ratsa ta wajen”..Jinjina kai Leo ya yi alamar haka ne, in a cool way sosai ya ce. “Idan kuwa akwai taku a wajen to tabbas akwai wutar lantarki a waje, dik yadda aka yi akwai igiyoyin wuta sosai a wajen wanda su ne suka haka drone ɗin nan wucewa, lallai muna buƙatar sanin menene a wajen cikin gaggawa, dan ga dikkan alamu gagarumin abu ne a wajen”……. Jinjina kai Zaynish da Noor suka yi, su kuwa matan gabansu ne ya yi mummunar faɗuwa jin batun da mazan ke tattaunawa.Zaynish ya ce. “Idan muka yi duba da hayakin dake tashi ba hayaki ne na yau da kullum ba, lallai wannan hayaki gagarumin abu ne ake ƙonawa, ku yi duba da yadda yake tashi sama, a maimakon ya yi sama gabaɗaya, sai yana watsewa a cikin dajin, alamar abin da ake ƙonawa yana ɗauke da guba”.Kai suna jinjina alamar haka, ba shakka a zancen Zaynish….. Jama’a ku tafawa renon AZURE, sun san aiki!.Leo ne ya ce. “Zaynish, Noor, ku kira Vash ina da magana daku a ɗaki”…… Da okey sir suka amsa, dawo da kallonsa a kan Arya ya yi. “Keep watching the place, komai ƙanƙantar motsi ki sanar dani”. Yana kai karshe ya miƙe daga kanta, cikin zafa ya nufi waje.Bayansa ta bi da kallo, bata iya zare idanunta ba har sai da Zaynish ya zo wucewa, sannan ta ɗauke kai. Sunkuyowa kanta Noor ya yi, cikin zola ya ce. “Brother ɗina yai maki kyau ne?”. Ɗago da kallonta a kansa ta yi, zata mashi tsiwa sai taga yai mata mugun kwarjini, haɗiye maganarya ta yi, ta ɗan yi ƙasa da ido. Ɗagowa yai zai nufi waje raunatacciyar muryar V ta katse shi da cewa. “My Romeo”. Ai ƙara ɗaure fuska ya yi, ya fice da sauri ba tare da ya kalli in da take ba.Yana fita V ta fashe da sabon kuka tare da kwantowa jikin Angelina tana ɗan shessheƙa, yau Romeo ya yi fushi mai zafi da ita. Ita kuwa Arya ta cigaba da kallon aikinta, Manassa da Angelina suka zauna yin gulmar Leo da Zaynish, ba su yi gulmar Noor ba saboda kada V ta sauke haushi a kansu. A yayin da a waje kuma ruwan sama na zuba tamkar da bakin kwarya, while sojojinsu guda 34 ciff suka tsaye cikin ruwan kewaye da tantunansu dan bada tsaro, sun sanya army waterproof jacket. To mu leƙa sashen jigon labarinmu, mu ɗan duba su sister Maya sai mu sake dawowa, watakila kafin mu dawo sun gano wani motsi, su kuma lovers Romeo and Juliet kila zasu shirya. ————————-🔥WS-HOSPITAL.🔥Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!…. Bayan sun kammala hiran, sai suka tashi, suka shiga baiwa jariran madara wanda nurses suke haɗa masu suna ajiyewa kowani baby a jikin bed ɗinsa. Suna baiwa yaran suna murmushi suna cigaba da baiwa junansu shawarin yadda zasu kara sace zuciyoyin 3D.A ɗayan ɓangaren kuma, 3D tsaye a cikin SECTION E, a ɗakin Drugs factory ɗinsu. Dr James tsaye gaban wasu injuna, yana sanye da kayan ƙariya, yau nose mask dake face ɗinsu irin manyan nan ne masu ɗauke da oxygen, hakan zai sanya ba zasu shaƙi numfashin Drugs factory ɗin ba, wannan oxygen ya wadatar da su. Dr Kamal ne ya ɗauko wannan jini dake bokiti, wanda suka sanya a freezer ta daskarar masu da shi, tin ɗazun dama suka ajiyesa a waje mai ɗumi, ya narke, a cikin wani tangameme faranti mai zurfi ya zuba jinin, wani karfe dake tsakiyar farantin ya fara jujjuyawa yana kwaɓa jinin, engine ne wajen.Almost 10 mins, wannan inji yana juya jinin jaririn, sai Dr James ya ɗauko wani ainahin sinadari a cikin kwalba wanda ake cewa collagen peptides ya zuba a cikin jinin jaririn. Collagen peptides sinadari ne dake ƙarfafa fata, hana wrinkles, da inganta laushin fata.Ya barshi kamar 10 mins injin na mixing ɗinsa, sannan ya sake ɗauko ainahin sinadarin retinoic acid ya zuba a ciki, manyan kwalabe ne sosai fa yake ɗaukowa, sinadarin retinoic acid yana sabunta fatar jiki, rage wrinkles, da hana tsufa.Bayan ya zuba injin ta yi mixing like 10 mins sai ya sake ɗauko, hyaluronic acid shi ma ya zuba a ciki. Hyaluronic acid ainadarin ne dake hana bushewar fata, yana sa fata ta yi taushi da ƙyalli tamkar glass, bayan ya zuba dakamar 10 mins shima sai ya sake ɗauko kwalbar nicotinamide mononucleotide ya zuba a ciki.nicotinamide mononucleotide sinadari ne dake sabunta kwayoyin halitta, watau cells da kuma kashe alamun tsufa. After 10 mins inji na mixing, suka haɗe da juna da jinin jaririn, sai ya sake ɗauko resveratrol ya zuba a ciki. resveratrol ana samun shi ne a cikin inabi, yana da tasiri wajen hana tsufa da kuma kare fata daga lalacewa, yana da matuƙar amfani a aikin 3D. Baya ga shi sai ya ɗauko coenzyme ya sake juyewa a ciki. coenzyme yana da matukar amfani wajen inganta kuzari a cikin jiki da kuma hana lalacewar fata, bayan shi ya ɗauko kwalbar epidermal growth factor ya zuba a ciki. Epidermal growth factor sinadarin ne dake sabunta fata a gaggauce cikin ƙanƙanin lokaci ya warkar da raunuka da dik wani tabo, ki koma tamkar ƴar tsana, babu tabo ko kaɗan a jikinki.Ya sake ɗauko stem cells watau ƙwayoyin halitta na asali ya zuba a ciki, in jin dai tana nan kunne tana mixing komai ta haɗesu su zame abu guda.stem cells yana sabunta fata da gyaran jiki gabaɗaya, daga shi sai ya ɗauko alpha lipoic acid ya sake zubawa, tsabar yadda injin ke mixing har wani hayaki-hayaki ne yake tashi daga cikin farantin, ga sinadaran da ake ta daddalawa a ciki. To alpha lipoic acid shi ma sinadarin ne dake rage kumburin fata da hana tsufa. Daga shi sai ya ɗauko babbansu kuma na ƙarshensu watau glutathione ya zuba. Wannan sinadarin yana sa fata tayi haske sosai, yana cire wrinkles, komai yawan tamu-tamun tsufarki zai yi fata-fata da shi ya mai da skin ɗinki very smooth tamkar yarinyar ƴar 13 years, yana da karfi sosai, a take yake cire tamu-tamun, sannan ya fi sauran dik sabonta fata da hana shi tsufa sosai.Yauwa kafin mu wuce gaba, dama na ce maku zan yi maku bayanin kan sinadaran dake cikin jinin jariri dan ku samu ƙarin ilmi kuma ku fahimta da kyau, dan haka kafin mu ce zuwa gaba ku ji me 3D zasu aikata, bari in baku wannan bayani.A jinin jariri akwai sinadarin hematopoietic stem cells kamar da na faɗa a haba, to hematopoietic stem cells sinadarai ne dake samar da sabbin ƙwayoyin jini red & white blood cells. Ana amfani da su wajen warkar da cututtuka kamar ciwon sankara, sannan suna wanke tsoffin jini. Na biyu a baya na ce a jinin jariri akwai sinadarin mesenchymal stem cells su kuma waɗannan ƙwayoyin halitta suna taimakawa wajen sabunta fata, ƙashi, da sauran sassan jiki, dik tsufarka zaka zama sabon matashi mai ji da karfi da lafiya tamkar ɗan yaro under age.Na uku a jinin jariri akwai erythropoietin, shi kuma sinadarin da ke taimakawa wajen samar da jan jini red blood cells, kun san jan jini daban yake, masu shi daban suke, da lafiya da karfi.Na huɗu akwai fetal hemoglobin. Wannan nau’in haemoglobin ne da ke cikin jinin jariri, wanda ke da ƙarfin ɗaukar iskar oxygen fiye da na manya, idan ka yi amfani da maganin 3D hmmmm, karfi da lafiya kam a dai yi shiru kawai. Na biyar akwai alpha fetoprotein, wannan sinadari ne da ake samu a cikin jinin jariri, wanda ke sabonta garkuwar jiki, idan kin tsufa garkuwar jikinki ta raunata ta yadda kowani cuta zai iya yi maki shigar farad ɗaya, to wannan sinadari na sabonta garkuwar jiki, ki zama tamkar yara.Na shidda akwai Interleukins & growth factors, waɗannan sinadarai ne dake ƙarfafa garkuwar jiki da kuma sabunta ƙwayoyin halitta. To su ne a jinin ɗan jariri wanda sai sun razana jaririn suke samo jikinsa ya sakarwa jininsa waɗan nan sinadaran ta yadda in sun marƙaɗa shi sun matso jinin zai zo ɗauke da sinadaran!.To mu cigaba da bibiyar 3D yau mu ga abin da ya turewa buzu naɗi, amma kafin nan ina da tambaya! Mun gama jin na jini, to shi kuma ɓargon ƙashin fa? Me suke yi dashi? A gaskiya shi fitina da balainsa ya fi na jini, a hankali zamu iso garesa, zaku ji komai, haɗarinsa yawa ne da shi, shiyasa na ware mashi lokaci na musamman.Bayan kamar 30 mins da kammala zuba sinadaran injin na mixing Dr Mark ya tsayar da injin, komai ya haɗe sosai. Dr Kamal ya ɗauko color ɗin da suke buƙata, white suka sanyawa haɗin, take da injin ya sake mixing komai ya zama fari tas tamkar farin fenti, ba zaku taɓa cewa akwai jini a ciki ba, Dr James ya ɗauko fm, sinadarin dake kashe ƙarnin jini da dik warin wasu sinadaran, ya zuba a ciki, suka ɗauko wani powder mai kamshin inabi da sauran kayan itatuwa suka zuba a ciki.Injin ya sake mixing sosai kafin su sake kash injin. Sannan suka danna wani madanni, gabaɗaya farantin ya yi sama, ya juye maganin cikin wani abu tamkar ball, daga nan suka kunna wasu injuna dake gaba guda biyu kafin su kunna makunnin wannan ball ɗin. Nan take ball ɗin ya fara motsawa yana sama ya ɗan yi ƙasa.Matsawa kaɗan suna yi izuwa karshen injinan suka tsaya, a wajen akwai wani katon baff a bakin karshen injunan. Sun rungumo hannayensu a saman kirji, idan suna aiki ba’a magana, babu wanda ya ce da wani ƙala, kowannensu yana lissafin kan yadda zasu ƙara inganta aikin nasu ne.After 30 mins da tsayuwarsu a wajen sai ga bakin injin ya buɗe, you can’t believe what i saw my people. Ya ALLAH, a jere drugs suka fara zubowa a cikin wannan baff ɗin, yadda kuka ga ake arranging magunguna a cikin saches ɗinsu, haka waɗan nan magunguna suka fito daga cikin injin, ko kasheki za’ayi idan ba’a gabanki aka haɗa wannan magani ba ba zaki taɓa cewa akwai jini da waɗan nan sinadaran a ciki ba, pure magunguna ne a ciki farare ƙal….. Kin taɓa jin maganin hana tsufa? mai da tsohuwa yarinya.To waɗan nan magunguna ba komai bane face magungunan mai da tsohuwa yarinya, maganin gyaran jiki, skin ɗinki ya zama irin na waɗan can na kwana, maganin glowing, lightning, glass skin da sauransu, zai sabonta maki halitta cikin ƙanƙanin lokaci. Shiyasa basa karɓar sperm da eggs na munana sai kyawawan mutane, dan dik wanda ya sha maganin ya zama yaro, ya kuma yi kyau sosai, shiyasa dik nurses dake cikin wannan asibitin suke da mugun kyau, dan sperm and eggs na kyawawan gaske ake ɗaukowa! Fatan yanzu kun gane dalilin da yasa dole sai na kyawawa!.To ina matan littafin nan masu shan maganin gyaran jiki? Masu shan maganin ƙarin haske, su skin care manya! To koma dai me ga abin da kike sha nan, mu munga komai, munga dik abin da 3D suke haɗawa, dan haka mu bamu a wannan layin na su glowing, ko ya kuka ce mutanen kirki?….. Watau ni kaina ina kiɗimewa idan na tina abin da suke haɗawa da wannan ɓargon ƙashin jariran fa, mun dai ji na jini, ko ya na ɓargo da kuma shi kansa garin ƙashin da tsoƙa ɗika yake? Yanzu shikenan jarirai guda biyar ɗin nan sun tafi har abada? Haka zasu cigaba da salwantar da rayuwan jarirai? Suna niƙasu tamkar masara! Tamkar ba rai bane da su? Wannan wace iriyar balai ce, rai fa, su ɗauka su saka cikin inji ya niƙa ya fitar masu da jini daban, garin tsoka da ƙashi daban, ɓargon cikin ƙashi daban, rai fa, ran ma na jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, la haula wala ƙuwata illah billah, allahumma ajirni fi musibatin, wannan musifa ina zamu tsaya da ita? Ba dole jama’a su dinga ganin tashin hankali da musifu ba, ace ƴan ɗan adam akewa wannan ɗibar albarka, ya ALLAH.Bayan magungunan sun gama zuba ne 3D dikka suka ɗebo ruwa a boket duka zuba cikin farantin da ya haɗa maganin da farko, sannan suka kunnasa, farantin ya yi sama, ruwan ya zuba cikin ball, daga nan suka sake tsayawa a gefe. After 30 mins sai ga magunguna da basu kai ka farko ba sun fara fitowa, watau marasa karfi sosai aka yi yanzu da ɗaurayar inji. Waɗan nan marasa karfi sosai ɗin sai kun sha sosai yake biyan buƙata, kuma shi ne mai arha daidai talakawa!. A baff daban marasa karfin suka zuba, dan da na farko ya gama fitowa sun janye baff ɗin gefe, sai suka sanya wani.Bayan komai ya gama fita sai suka haɗa karfi suka cicciɓi baff ɗin magani mai karfin suka fito dashi wajen ɗakin, suka koma suka ɗauko mara karfin suna fito da shi waje. (Ni na rasa ma wani irin suna zan baiwa wannan ɗaki saboda musifar dake cikinsa, kai ya ALLAH. To bari dai mu bashi sunan ɗakin niƙa jariran, tin da babban abin da suke yi a ciki kenan.A wajen ɗakin niƙa jariran suka dire baff dikka biyu ɗin, magunguan yana dayawa, ga baff ɗin da girma, sai da suka yi da gaske suka iya ɗauka. Suna ajiyewa Dr Mark ya kira guards madaka karti su uku suka zo suka ɗauki baff ɗin, amma kafin su ƙirasu sai da suka rufe kofar ɗakin niƙa jariran da matakan tsaronsu na wutar lantarki, babu wani mahaluki da yake shiga masu wannan ɗaki, su kaɗai suke shiga, saboda su kaɗai suka san ɓarnar da suke yi a ciki. Bayan guards ɗin suka bi izuwa wani katafaren ɗaki mai girman gaske, kwalayen magunguna ne cike a cikin ɗakin, a nan guards ɗin suka sauƙe baff ɗin dikka biyu, akwai ma’aikata mutum 10 a ciki, aikinsu kawai shi ne shirya magungunan a cikin kwalaye ƙanana kafin a shiryasu cikin manyan cartons.Saman haɗaɗɗun chairs da aka tanada masu suka zauna, suka zuba idanu suna kallon yadda ma’aikatan nan ke aiki da jikinsu wajen ganin sun shirya komai yadda yakamata a kan lokaci. Suna sanya magunguna marasa karfi a kwali daban, mai launin white and ratsin ash, su muma magunguna masu karfi kwalinsu farine tas.Sai around 10 na dare 3D suka je suka yi wanka, suka shirya cikin shiga iri ɗaya, white pj’s, basu ko ci abinci ba suka dawo ɗakin aiki. A lokacin ma’aikatan sun shirya cartons 20 na masu karfi, 10 na marasa karfi, kowani carton kuma yana ɗaukar kwali ƙanana na maganin guda 25. Umarni Dr James ya baiwa guards uku da su fitar masu da cartons 30 ɗin dikka da aka shirya waje. Cikin ƙanƙanin lokacin suka fitar da shi suka ajiye a tsakiyar SECTION E ɗin, sannan suka koma bakin aikinsu. Wayansa Dr James ya ɗauka, password na tsaron lantarki dake jikin wani kofa dake fuskantarsu ya cire. Yana cire password ɗin shocking na wajen ya mutu, tangameme kofar karfen dake wajen ya wangale kansa.Da kansu 3D suka fara jidan kwalayen drugs ɗin suna shigarwa cikin wannan ɗakin. Cikin ƙasa da 10 mins suka kammala, a lokacin 12 na dare ya yi. Bayan sun kammala shigar da komai kaf, sai suka rufe kansu a cikin ɗakin, suna rufewa lantarkin wajen ta kawo, shocking ya dawo, dik wanda yakuskura ya zo jikin kofar bushewa zai yi, dan wasu irin mahaukatan shocking ne a wajen. Wuta na kawowa ɗakin naga wani haɗaɗɗen katafaren ɗaki ne, ga sofa set, AC, TV, tamkar office na wani hamshaƙin muƙamin gwamnati, komai na cikin ɗaki fari ne tas, an zuba maƙudan kuɗaɗɗe ba karya, ya ALLAH. Dr Kamal and Dr Mark ne suka wuce suka yi zamansu a saman sofas ɗin.Shi kuwa Dr James wayarsa ya shiga latsawa kamar na 5 mins, sai ga pop dake ɗakin ta gefen hagu ya fara motsawa, jim kaɗan wajen ya buɗe tamkar kofa, sai ga tsani an juro da shi ciki. Miƙewa su Dr Mark suka yi, suka fara jidan kwalayen drugs ɗin suna haura tsanin, kowannensu kwali bibbiyu yake ɗauka su haye tsanin. Suna hayewa hudawa suka yi cikin wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa, tamkar store ne, empty yake, a nan suke shirya magungunan. A cikin ɗakin wani babban likita dake sanya cikin kayan aikinsa ne a tsaye, ya rungume hannayensa a kirji yana kallonsu suna shigo da drugs ɗin. Wannan likitan shi ya zuro masu tsanin, shi Dr James ya turawa saƙon sun iso, shi ne ya buɗe wajen ya sako masu tsani dan su haura.Wai kun san tsadar magungunan kuwa? To ko shugaban ƙasa ba na kowani ƙasa ne yake iya jurar sayen maganin dik bayan wata ɗaya yana sha ba, suna da tsada, dan kwali ɗaya ƙarami mai ɗauke da drugs ƴaƴa kwara 6 kawai ya kai 1M, in dai kana son mai da kanka yaro matashi kuwa dole ka dinga sha dik tsadarsa. Amma ai kunga sun yi marasa karfi sosai watau ɗaurayar inji, waɗan nan basu da tsada sosai, carton ɗaya baya wuce 100k, kunga a karton kuma kwali 25 ne a ciki, zai kama kowani kwali 4k kenan, kunga shi da sauƙi a kan masu karfi. Marasa karfin ne ƴan iyayi yaran malan Shehu suke kashe kansu da wahalar sai sun saya su gyara jiki, ayi glowing da lightning, ayi ta zuba kuɗi, ba’a ci ba a tsaya dole sai an gyara skin, bayan ga kayan gyara da Manzon ALLAH ya faɗa, wanda littafan musulunci suka koyar, dik bai maku ba. Idan baki san kayan gyaran da Manzon ALLAH ya faɗa, littafan musulunci suka koyar ba In Sha ALLAH a karshen littafin nan na yi alkawarin zan rubuta!.My people you can’t believe what I saw there. Bayan sun kammala shirya drugs ɗin, Dr Kamal and Dr Mark suka tsaya tattaunawa da wannan babban likita dake tsayen, shi kuma Dr James ya nufi kofar da zata fidda shi daga ɗakin. Ya ilahi, yana buɗe kofar kun san me a wajen?. Katafaren asibiti ne na al’umma a tsakiyar birnin Avaris, babban asibitin gwamnatin na ƙasar ne! In baku fahimta bari in maku gwari-gwari. Kenan WS-HOSPITAL a tsakiyar al’umma take ba tare da kowa ya sani ba, sai dai tana underground ne, nasan dayawanku suna tinanin a dokar daji WS-HOSPITAL take, aikuwa gata a tsakiyar gari, a garin ma a babban birnin Eldoria, kasar da aka haifi daddynsu Lion, bugu da ƙari ƙarƙashin asibitin gwamnatin ƙasar, dik wannan haɗuwa da tsayuwar WS-HOSPITAL a ƙarƙashin ƙasa yake. Jama’a WS sun zarce yacce kuke tinani, manyan kai ne da kamasu abu ne dake kamar wuya, ai tin da kuma ji Lion da kansa ya ce kamasu abu ne mai balain wahala, daga nan zaku game ba ƙananan kai bane, sun zarce tinaninku, ku duba yadda suka shinfiɗa gini a ƙarƙashin ƙasa tamkar ba za’a mutu ba fisabilillahi, suke baiwa ƙarƙashin ƙasa wutar lantarki kusan gabaɗaya na birnin Avaris, shiyasa a ƙasar ake wahalar rashin wuta, to ashe ga in da wutar take tafiya, ba’a iya ɗauke wuta a WS-HOSPITAL ko na second ɗaya, saboda abubuwan da suke sanyawa a freezers irinsu sperm, eggs, blood da sauransu.Dole wuta lantarki tai yawa a wajen, ga nan jama’ar Avaris kullum cikin ƙorafin babu wuta, da an kawo da an ɗauke, kuma Avaris tana daga cikin ƙasashen da ta fi tsaranta karfin wutar lantarki, suna da uranium, amma ace kullum suna kukan rashin wuta, ashe da in da ake kai wutan a bar jama’a a gantale. Har fa hanyar yadda motoci zasu iya shiga underground ɗin a wannan gini an shinfiɗata, sai dai motocin in zasu shiga sai sun yi tafiya mai nisa zuwa cikin daji, a can aka yi wani waje da aka haɗa, aka yi shinfiɗaɗiyar titi har cikin WS-HOSPITAL, ta nan Dr Mark yake fito da motar jarirai idan an saya a wani waje, hmmmm babu wanda zai taɓa expecting akwai hanyar zuwa ga 3D palace a cikin wannan asibiti ta gwamnati…… Hmmmmm, shiyasa a wannan asibitin ba ko’ina ake barin mutane su shiga ba, wannan ma iya abin da kuka gani yanzu ne, ainahin labarin yana book 2 jama’a, ALLAH yasa kanmu ya iya ɗaukar wasu abubuwa, kai ya ALLAH ƙazantar dake duniyar nan, ALLAH ne kaɗai zai iya maganin komai! Ni dai yanzu addu’a ta ɗaya, ALLAH ka bamu cikawa da kalmar shahada da ni da mutanena na kirki, In Sha ALLAH wlh mutuwar shahada zamu yi my people!. Amma ku daga ganin iya hospital na World system kun san ba mutane ne da zasu kamu ta sauƙi ba, basu fito ba sai da suka shirya, kai akwai abubuwa idan muka natsa cikin labarin nan, baku ha komai ba.Cikin asibitin Dr James ya shiga, kewaye ya fara yi yana duba yadda ɗakunan da majinyata suke yake, babu abin da zaku ɗaga a asibitin nan ku kirasa mai kyau sosai, komai a gurɓace a lalace da yake government hospital ne, amma ku duba irin aljannar duniyar da suka shinfiɗa a ƙarƙashin ƙasa dan biyar buƙatar kansu kawai, ya ALLAH gwamnatin Avarsi ku ji tsoron ALLAH, ita duniya dai wuni muka zo yi, kowa zai koma ga ALLAH, tabbas zaku tsaya ne a gaban ALLAH da abubuwan da kuka shuka a duniya, ku tuba tin kuna da sauran lokaci.Ya jima yana kewaye cikin asibitin nan, wani sashe ma idan ya shiga yawu yake tofarwa saboda lalacewar asibitin, daga karshe ya koma wannan private room ɗin, suka koma cikin WS-HOSPITAL ɗinsu, dan abin da ya kawosu kawowa kenan maganin, daga wannan asibitin kuma za’a fitar da magungunar ne zuwa ƙasashen ketare, manyan dattawan alhazawa da masu mulki ake sayarwa magungunan.Can na tina lokacin da su oooo suke cewa basu son bakaken fata, wai fararen fata suke so, su jikinsu baya tsufa, bakaken fatanmu su yi ta tada hankalinsu suna damuwa a kan su suna tsufa! Su yi ta sha’awar jikinsu ooo, wai yana da kyau basa tsufa, my sister zauna yadda ALLAH ya ajiyeki shi ne ya fi maki alkhairi, baki san me yake behind rashin tsufar nan ba! MAGANIN MAI DA TSOHUWA YARINYA! MAGANIN HANA TSUFA! HMMMMMMM. Saura mu ji me suke yi da ɓargon ƙashin da kuma shi kansa garin ƙashi da tsokar jariran kuma!.Kai tsaye SECTION D suka wuce, Dr Mark ya koma room ɗinsa ya kwanta tin da shi babu ruwansa da love.To mu ɗan koma baya kaɗan a kan su Zinta kafin mu cigaba. Bayan sun kammala baiwa babys ɗin nan madara mai ɗumi, zama suka yi a gefen gado, sister Zinta ta buga uban tagumi tamkar mai tinanin wani abin. Taɓata sister Maya ta yi tare da cewa. “Tinanin me kike yi?”.Nisawa ta ɗan yi. “Darling nike tinani, sister ina jin tamkar bashi da lafiya, anya ba zan fita in je in duba shi ba kuwa? Zan binciko shi a gidan nan, nasan wani ɗakin suka kaisa”…….. Shiru sis Maya ta yi, sai kuma da yake soyayyar ƙanin nasu ya rufe masu idanu sai ta ce. “Mu je mu duba shi, na tabbata yana kusa da mu”. Kai sister Zinta ta jinjina, sai kuma ta ce. “Sister kina ganin da gaske alluran magani suka yi mashi?”. …. Kai tsaye Maya ta girgiza kai alamar a’a kafin ta amsa da. “Wlh ba magani bane, cuta ce, baki ga yanayin kalar ruwan ba? Kin lura akwai chemicals da muka haɗa a cikin cutar da yake ikirarin maganin ne?”. Jinjina kai sister Zinta ta yi. “Tabbas cuta ce, amma koma menene zan ɗaukosa, zan gwadasa, in dai cuta ce tabbas zan yi mashi magani, ai mu muka haɗa chemicals ɗin, dik kuma mun san makarin chemicals ɗin”. Kai sister Maya ta jinjina. “Ko ni nasan makarin dikka chemicals da muka haɗa, kuma zan iya haɗa mashi magani”….. Shiru sister Zinta ta ɗan yi, can ta ce. “Kina tinanin meyasa 3D zasu saka mashi cuta? Baki tinanin kamar wani mugun abu ake shiryawa? Meyasa muke haɗa waɗan nan chemicals ɗin? Me suke yi da su da kullum sai su je SECTION C sun ɗeba? Me kike tinanin ake yi da su?”.Abinku da jinin daddy Haiza’an, shiru Maya ta ɗan yi, can ta ce. “Ina tunanin cuta suke kirkira, to anma ina suke kai cutar? Me suke yi da shi?”……. Sister Zinta ta ce. “Kina ganin bai kamata ace mun san me suke yi ba?”. Kai ta jinjina. “Yakamata ace mun sani, to amma ina suke kai dikka waɗan nan abubuwa? Baki ganin shi ma yakamata mu sani?”.Jama’a na faɗa zan sake faɗa, dan jiya na samu tambayoyi a kan abin da na faɗa na sake faɗa! Dik nurses dake wannan asibitin kyankyasarsu suka yi, basu ɗaukar ma’aikata daga waje, su suka kyankyashi kayansu, suka renesu, suka basu ilimi ta ɓangaren da suke son su sani, a cikin 3D ɗin nan kowanne da abin da ya fi kwarewa, Dr Mark yana da ilimi kan sanin chemicals fiye da yadda kuke tinani, shi ya karantar da su Dr Maya, Dr Kamal yana da sani ɓangaren kafiya sosai, shi yakarantar da sauran nurses dake aikin lafiya, waɗan da ke duba yaran da ake cire eggs ɗinsu, su yi treating babys idan basu da lafiya, Dr James ubansu kenan, yana da ilimi da baiwar sani a dikka ɓangarorin, dan haka basu ɗaukar ma’aikata daga waje, babu wanda yake shigowa wannan asibitin face abin da suke fitarwa, komai da kuke gani a nan asibitin aka kirkiresa, basa amfani da abubuwan waje face kayan abinci da ruwan roba sa ake shigo masu da shi. Haka zalika bayan 3D babu nurses da suke fita bare su je su yi aiki a waje a wani asibitin, ko sperm da suke saye 3D suke fita su ɗauko shi, dan haka take note! Basa ɗaukar wasu ma’aikatan daga waje, kuma nasu ma’aikatan ma basa fita waje su yi aiki a wani asibitin.”Gaskiya yakamata mu sani, zuciyata ta fara rawa, ina jin kamar akwai wani abin da ya saɓa”. Sister Maya ta faɗa. Sister Zinta zata yi magana suka lura sauran nurses ɗin su suke kallo, da sauri suka ja baki suka yi shiru. Sister Maya ta ɗauko wani baby, yana barcinsa, amma saboda tsabar son yara ba zata barshi ya huta ba, ta kwanta tare da kwantar da shi a saman cikinta, tana shafa bayansa, tana jin tamkar ta mai da shi cikin cikinta saboda so, a haka barci ya saceta.Ita kuma sister Zinta shiru ta yi, ta buga tagumi tana tinanin maganganun da suka yi, lallai dole akwai in da suke kai waɗan nan abubuwa, kuma tana zargin cuta ce, idan kuwa cuta ce lallai zuwa yanzu darling baya raye, dan kuwa in har waɗan can mugayen chemicals ɗin da suka haɗa dikka aka juye cikin wannan aiki to ba shakka wannan cutar ƙare dangi yakamata a sanya mata suna.Haka kawai ta ji zuciyarta na raya mata lallai ta fara bincike, lallai ta nemo maganin wannan cuta, tana jin zata iya, kuma tabbas zata iya, dan kuwa in baku manta ba su suka haɗa kaso 60 na kwayar cutar, in kuwa ta ce zata yi bincike ta ɗauki chemicals da zasu karya waɗan can tsab zata iya haɗa magungunar, ko bata yi komai complete ba za’a samu kaso 85 cikin ɗari. A haka ta dinga wannan tinani har sister Maya ta farka daga barci around 8 na dare, ganinta zaune shiru yasa ta ce. “Sister, yadda na barki baki motsa ba? Lafiya dai ko?”……. Kai ta girgiza alamar ba lafiya ba, idanunta take suka kawo ruwa taf, murya a raunace ta ce. “Sister dole akwai wani abin da yakamata mu sani a kan darling, ina son ganinsa, yau ba zan yi barci ba, zan jira oga ya zo sai ya kaini wajensa”.Jinjina kai Maya ta yi, tana saɓa wannan baby a shoulder ɗinta, ta amsa da ita ma ba zata yi barci ba, zata jira 3D. Haka suka kasance, suka dinga hidima da babys ɗin har yaran suka yi barci, sannan ne suka zauna zaman hira, ko abinci basu ci ba, da suka ji yunwa suka ɗauko crispy chicken ɗinsu, suka cinyesa su biyu basu tsanwa kowa ba. Haka suka kasance har karfe 12, da yake sister Zinta tasha barcin rana yau, ita kuma sister Maya ta sha na mangrib, sai yazama basa jin barci sam, da karfin hali irin nasu sai da suka jira around 1 na dare, sun fara fidda rai da zuwan 3D, unexpected suka ji an turo glass door ɗinsu. 3D sun yi mamaki ganin wutar ɗakin a kunne, da suka shigo kuma sai suka yi mamakin ganin matan nasu idanunsu biyu, su kuwa suna ganinsu suka ɗan miƙe tsaye, amma basu razana irin razanar da suke yi a baya idan sun gansu ba, bare ma sister Zinta da ita yanzu gabaɗaya ta ji tsoron Dr James ya fara fita a zuciyarta tin da ya cire kayansa gabaɗaya a gabanta, ya yi wasa da jikinta, tin daga wannan lokaci take jin tamkar ita da shi abu ɗaya ne, and ta fara fahimtar yana sonta sosai, dan haka ba zai yi mata komai ba ko da ta yi mashi laifi. A gabanta Dr James ya tsaya, cikin sanyin murya ya ce. “Me kike yi baki yi barci ba?”……. Murmushin dole ta ƙaƙalo kafin ta ce. “Waiting for you my oga”. Har cikin ransa ya ji wani irin daɗi, hannunsa ya ware mata tafukansa game da miƙa mata, ɗaura nata kyawawan hannun a kai ta yi, tana ɗan shagwaɓe fuska ta ce. “Ba zaka ɗaukeni kamar ɗazun ba?”………. Ya ALLAH, wani irin madarar daɗin da ya ji ba, baisan lokacin da ya jawota jikinsa ba, ya rungumeta yana ɗan shafa bayanta.”Muje side ɗinmu ko?”. Ya faɗa can ƙasa……. Ɗan shagwaɓe fuska ta yi kafin ta ce. “Ka kaini in ga darling ɗin please”…… Kai ya jinjina mata alamar to, sannan ya rage tsawonsa, cak ya ɗauketa suka fito waje. Bai zame da ita ko’ina ba sai side ɗinsu. A saman katafaren bed ɗinsa ya direta, zai sauƙa ƙasa ta yi saurin riƙo hannunsa. “Baka nuna mun darling ɗin ba”. Tana narai-narai da fararen idanun nata ta faɗa. Ɗan riko shoulder ɗinta ya yi. “One minute”……. Ya faɗa tare da saketa, ya wuce ya nufi wajen laptop ɗinsa, ɗaukota ya yi, a kusa da ita ya zauna tare da kunna laptop ɗin. Tana kallon dik abin da yake yi, bai yi zaton tana naɗar komai a kanta ba.Wani folder da aka rubuta new project ya shiga, nan ya yi mata playing video ɗin darling a cikin kwalba, a yadda ya ɗauke shi video yaron yana kwance shiru tamkar mai tinanin wani abin. Kura mashi ido ta yi, sai ta hau murmushi, rashin sani ya fi dare duhu, da tasan balain da yaron nan yake a ciki da bata yi murmushi ba, amma tana murmushi, ta matsa kusa da laptop ɗin sosai, dama ta yi wa desktop computer farin sani, dan a cikinsa aka koyar da su ilimin sanin chemicals, dan haka laptop bai bata mamaki ba.Video ɗin ta kare ta sake dawo da shi baya, tana ta murmushi, a tinaninta darling yana cikin farinciki ne, ya sha madara ya ƙoshi ne ya yi shiru. Dr James ya ɗan rungumota yana faɗin. “Babynku yana nan lafiya, muna wani gwaji ne, amma zai dawo gareku”…….. Da yake bata ga zahiri ba, a video ne sai ta yarda darling yana nan lafiya, ta dinga murna, har da rungume Dr James, cikin shagwaɓa ta ce. “Sir ina son nunawa Maya darling ɗinta”. Yana shafa kanta izuwa bayanta ya ce. “Zan sanya Dr Kamal ya nuna mata, ba sai kin je ba”. Ya faɗa tare da jawo laptop ɗin kusa, ko kaɗan bai yi tinanin ta yi wani tinani a kansu ba tare har ya ce ba zai yi wani abin a gabanta ba, a kan idanunta ya turawa Dr Kamal video ɗin ta email, ya ce mashi ya nunawa Maya.Daga haka ya kashe laptop ɗin, ya ɗaura saman side sofa dake kusan da bed ɗin. Dik yadda ya yi a laptop ɗin ta naɗi komai. Jawota jikinsa da kyau ya yi, in a romantic way ya fara sarrafata, yana juyata son ransa. Cikin ƙanƙanin lokacin ya rabata da kayan jikinta, ya cire nasa shi ma, ya dinga wasanni da ita, sai da ya tabbatar da ya gama kiɗimata da salonsa, sannan ya saita penis ɗin, ya shigeta, dan yau ya yi alkawarin mayar da ita matarsa da gasken kuwa.Sosai ta ji zafi, ta fara ƙoƙarin turesa tana mashi magiyan ya kyaleta, amma bai kyaleta ɗin ba, sai da ya mai da ita mace, ta yi kuka har ta godewa ALLAH, ta dinga dukansa tana turesa, amma ina, bai raga mata ba……. Sai da ya gama bidirinsa, sannan ya kwanta tare da jawota jikinsa, ya hau rarrashi yana bata baki, ya dinga lallaɓata har ya samu barci ya ɗauketa. Lokaci guda wani irin zazzafar sonta ne ya ƙara shigarsa, ya zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu, yana jin tamkar ya ƙara shigarta, dan wani sabon sha’awarta yake ƙara taso mashi. Duba time ya yi a wayarsa, karfe 3:30 na dare, dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, sannan ya sauko ƙasan bed ɗin. Message yai typing wa su Dr Kamal, sannan ya shige cikin toilet. After 30 mins ya fito, a gurguje ya shirya, gaban bed ɗinta ya dawo, sumbatar cheek ɗinta ya yi kafin ya jawo bargo ya lulluɓeta, a gaggauce ya nufi waje dan lokaci na neman ƙure masu.Yana fitowa parlo ya isko su Dr Kamal a tsaye, suna haɗa idanu Dr Kamal ya ce. “Jammy kar dai ka aikata abin da ka faɗa? Naga face ɗinka sai wani kyalli yake yi”. Hararansa Dr James ya yi, shi kaɗai yasan irin tsananin farincikin da yake ciki, ya ALLAH, yau ya mori daɗinsa.Gaba ya wuce ba tare da ya yi masu magana ba, da sauri suka rufa mashi baya. Kai tsaye SECTION D suka nufa, suna zuwa ba ɓata lokacin suka sake ɗaukan jarirai guda biyar suka fita da su izuwa ɗakin niƙa jarirai, biyu daga cikin babys ɗin sai feket-feket suke yi alamar suna son yin kuka, sun farka, ɗayan sai buɗe baki yake yi, alamar yana jin yunwa, yana son ya yi kuka a bashi madara, da alama sarkin ci ne.Dr James na rike da babys biyu, Dr Kamal na rike da ɗaya, Dr Mark na rike da biyu, to na hannun Dr James ne suke ta faman ƙoƙarin fara kuka, ga alamar suna jin yunwa sosai, sai zuro harshe waje ɗayan yake yi.Basu diresu a ko’ina ba sai saman wannan gado na lantarki. Kunna lantarki Dr James ya yi, take yaran suka fara wani irin girgiza kamar yadda waɗan can na baya suka yi. Wannan baby mai zuro harshe waje yana son cin abincin nan gwanin ban tausayi, ya ƙara zuro harshen nasa waje, jikinsa na wani irin kakkarwa sosai, dadashinsa na garuwa da juna, yatsunsa na wani irin kerma, sun zazzare idanuwansu waje gwanin ban tausayi.Haka wannan shocking ya dinga jansu na ɗan lokaci, sannan Dr James ya kashe bayan ya tabbatar jikinsu ya saki waɗan nan sinadarai da ake so. Ya danna gadon tai sama da su, wannan jariri dake jin yunwa ne ya fashe da kuka a lokacin da shocking ɗin ta tsaya, kuka sosai yake yi, jininsa na ɓari sosai, harshensa ya zazzago waje. Yana wannan kuka suka tura shi cikin wannan ball ɗin. Kara fashewa da kuka mai tsanani ya yi, da alama ball ɗin cikinsa akwai zafi matuƙa. Ko gezau 3D basu yi ba, tamkar ba rai suke gani a cikin mawuyacin halin nan ba. Ya rabb, suna jiyo kukan jariri mai jin yunwar nan a lokacin da suka sanyasu cikin injin nan, yana shiga da suka kunna injin ihu ɗaya ya yi, daga nan ji kake ɗiff ya ɗauke wuta, injin ya murɗe mashi wuya kenan. Ya ilahil alamina, wace iriyar musifa ce wannan, ya ji da yunwar ne ko kuwa da azaban nan? Ya ALLAH ka sakawa waɗan nan jariran, dik masu sayar da mahaifa da sperm ɗinsu ALLAH ka walaƙanta rayuwansu!.Haka suka ɗauki bokitaye suka tari jini, garin ƙashi da tsoƙa, ɓargon ƙashi, suka ɗauka zuwa freezers room ɗinsu, suka shiryasu ciki, sannan suka koma side ɗinsu dan su je su yi wanka su yi shirin fitowa aiki, a lokacin 5 na asuba ta yi!.My people a wannan ɗauki ɗaiɗai da sukewa jariran kowani dare suna niƙasu kuna tinanin one day one time su sister Zinta ba zasu farga bane? Yanzu saura babys 45, watau shiyasa kenan yaran basa taɓa wuce 3 months a asibitin, watau irin ɗauki ɗaiɗai ɗin nan ake masu kenan!.Bayan ya yi wanka ya shirya, sai ya tada sister Zinta, da sabon kuka ta tashi mashi, rarrashinta ya dinga yi, da kyar ya samu ta yi shiru, a sanyayye ya ce. “Sorry my wife, zan je office, zan dawo by 1 in duba ki, yau ina da aiki sosai, amma ke yau na hutar dake aiki, ki kwanta a nan ki huta, za’a kawo maki dik abin da kike so”. Cikin muryan kuka ta ce. “Ni ka turo mun sister Maya, ita kaɗai nike son gani”…. Nisawa ya ɗan yi, ya sunbaci goshinta kafin ya ce. “Yanzu zan turota, amma ki mun murmushi”…… Din da tana cikin ciwo hakan bai hanata murmurawa kaɗan ba, kara sumbatar goshinta ya yi tare da miƙewa, yai mata sallama ya fito.Tsaye ya isko Dr Kamal da Maya a tsakiyar parlon, yana faɗa mata ta je ta yi wanka ta fita wajen aiki, sai dare zai sake zuwa ya ɗauketa, shi kuma Dr Mark da ba ruwansa da soyayya tini ya yi gaba abinsa.A dake Dr James ya ce. “Maya ki je sama ɗakina sister ɗinki na kiranki”. Daga haka bai sake magana ba, ya sauƙo ya nufi waje. Jawota jikinsa Dr Kamal ya yi, ya rungumeta tare da bata sumbata a goshi. Ya saketa yana mata bye-bye. Sama ta haye tana mashi bye-bye ita ma, sai murmushi take yi. Sai da ya ga hayewarta sannan ya wuce ya bi bayan Dr James suka nufi cikin hospital ɗin. ————————–CRYSTAL PALACE.🔥Abba khaiza’an’s House.A yau Abba ya shirya sadaki na alfarma, da misalin karfe 8 na dare, ya shirya cikin shiga ta alfarma, ya sanya thobe and bisht, ya naɗa rawani tamkar wani balarabe, amma haskensa kowa ya gani yasan ba balarabe bane. Kai tsaye ya tasa Faryan da Harleen a gaba, dan dole ya ce su rakasa ya je ya kai wannan sadaki, yana son jibi jumma a ɗaura wannan aure, ba fa fashi ko za’a mutu. Kai Abba namu na amana.Ga Abba ga grandpa, me kuke tinani a kan wannan kai sadaki?
