Ruwan Zuma Page 38 Hausa Novel
(38) Sati d’aya da dawowar Haydar daga Abuja amma tsakaninsa da matarsa Laila babu jituwa sannan har lokacin dukkaninsu suna fushi da juna. Suna kwana su tashi basu ga juna ba domin daga shi har ita avoiding juna suke yi. Motarta da yake d’auka yaje aiki ya daina, kafin ma ta fito shi ya hau achaba ya tafi gurin aikinsa ba zai dawo ba kuwa sai gab da magriba, yana wanka kuwa zai k’ara fita sai k’arfe tara ko goma na dare zai dawo. Abun yana damun Laila bana wasa ba, wani lokacin idan ta zauna tayi tunani sai taga kamar laifinta ne data kasa sarrafashi yanda take so, ina wayonta, dabarunta da kuma shekarunta suke? Ko duk sun tafi a banza ne tunda ta kasa jawo Haydar? Wani lokacin kuma sai taga duk laifinsa ne daya kasa fahimtarta yake kuma son d’aura mata abunda bata yi niyya ba. It’s like baya tausaya mata bisa halin da take ciki shine yake son k’ara mata damuwa a kan damuwar da take ciki. Wannan dalilai nata ne yasa ta kasa fahimtar Haydar balle tayi k’ok’arin gyara rayuwar aurensu, a cewarta shi yake uzzura abun har ya kai ga haka. Da yammacin ranar bayan Laila ta dawo daga shago ta samu wata sabuwar mota a farfajiyar gidansu, kallon motar tayi sama da k’asa sannan ta shige sashenta tana tunanin na waye ne, ko dai abokin Haydar ne ya kawo masa ziyara? To waye kenan? Tunda tasan abokinsa d’aya ne Nasir kuma bashi da mota. Bayan magrib ta jiyo k’arar motar za’a fita da ita daga gidan, hakan yasa tayi saurin isa bakin window ta d’aga labulen kad’an tana lek’awa. Haydar ta gani zaune a mazaunin direba ya juya k’eya yana reverse zai fita. Motar Waye ya d’auko? Bata son ya fara jaye-jayen abokai har yana kar6ar aron motocinsu. Hankalinta bai kwanta da hakan ba kawai ta d’auki wayarta ta kunna Data tana jiran sakonni su gama shigowa ta duba Whatsapp status d’insa watakila ko ya saka hotonsa tare da mai motar, kai ko wani abu da zai sa ta gane motar waye ne. Status d’insa mai d’auke da hotuna guda uku ta shiga, a nan taci karo da rubutunsa da yake cewa Company d’insu ta bashi kyautar mota. Hoto na biyu shine motar data gani a gidan nasu, na k’arshe kuma shi da Alhaji Abdul ne a gaban motar dukkaninsu fuska ba yabo ba fallasa. Zuciyarta babu dad’i ta ajiye wayar a gefenta tana tunanin yaushe zasu daina wannan tsamin ita da Haydar. Har ga Allah ta gaji kuma tana buk’atar da old Haydar back, mutum mai sonta da gudun 6acin ranta, mutum mai sakata farin ciki da kuma kareta idan buk’atar hakan ta taso. Me yake shirin faruwa da zaman aurensu? Ya daina shiga sabgarta kwata-kwata wanda yanzu ko abincinta baya ci ita ma kuma sai ta daina yin abincin. Duk akan haihuwa suke wannan rigimar? Kenan haka zasu cigaba da zama tunda bata da niyyar haihuwa? Bayan ya dawo da k’arfe goma ta shiga shashensa ta sameshi yana kallo yana shan wasu fruits d’in daya dawo dasu, yana amsa sallamarta ya maida kanshi kan tv yaci gaba da kallon kamar bai ganta ba. Shiru suka yi na kusan seconds talatin sannan ta fara magana. “Ashe mota kayi shine baka fad’a mini ba?�? “Eh.�? Ya bata amsa a gajerce. Shiru tayi tana kallonsa tana jin wani sabon sonshi na k’ara shiga zuciyarta, yanda ya mayar da fuskarsa ta zama blank ya kuma d’auki hankalinsa kaf ya d’aura kan abunda yake kallo yana jefa grapes a bakinsa shi yafi tafiya da hankalinta. Ashe gaskiya ne da ake cewa abunda yake shareka kai kuma shi kake son hankalinsa. Ita da tazo da niyyar jin ba’asi sai ta 6ige da k’ara fad’awa sonshi kuma tana bin surar jikinshi da kallo dalilin k’in saka kaya da yayi sai gajeren wando. Kamar wanda baya son motsawa ya juyo da kanshi ya dubeta yaga shi take kallo, bai canja fuskarsa ba ya k’ara juyawa yaci gaba da kallon bayan ya k’ara jefa grape a bakinsa. “Ka gaji dani ko Haydar? May be yanzu ka fara regretting aurena ko?�? A bazata yaji furucinta wanda hakan yasa ya juyo ya dubeta fuskarsa d’auke da mamaki. Wannan reaction d’in data gani yasa taci gaba da maganarta domin ta jawo hankalinsa. “Ka d’aukeni tamkar ba mutum ba kuma tamkar ba matarka ba, it’s like zaman gaba kake yi dani.�? “What are you saying Laila? Me kuma ya kawo maganar gaba for God’s sake?�? “In ba gaba ba me zai sa ka daina magana dani? Abun farin ciki ne ya sameka amma ka kasa fad’a mini, shine ka iya d’aurawa a Whatsapp status d’inka duniya su gani alhali ni matarka dana fi kusanci da kai bani da masaniyar abunda ke faruwa a rayuwarka. Me ya jawo haka in ba gaba ba?�? “Ki daina nanata wannan kalmar bana son ji.�? “Karya nayi ne Haydar? Ka canja halayenka, ban yi tunanin hakan zai ta6a faruwa damu ba wallahi. Ina duk promises d’in daka mini akan cewa you’ll always be by my side no matter what? Ina maganarka na cewa my needs and wants are your priorities? Ina dad’in bakinka na cewa farin cikina shine naka? Ina suke? Ko duk k’arya ne? Ko dai nima ka mini dad’in bakin samari ne ka saye zuciyata da dad’ad’an kalamai wanda basu kai zuciyarka ba.�? “Kina fad’in hakan kamar nine na fara gudunki, stop being the innocent here Laila. You know damn well abunda ya shiga tsakaninmu. Ban fara gudunki ba sai da kika fara guduna, haka kuma ke kika fara tauye mini hak’k’ina sannan nima na gwada miki irin nawa. Kin k’i haihuwa dani me kike son in miki? Akwai tsanar daya kai wannan ne? Akwai abunda ya fishi bakin ciki ace matarka ta sunnah auren soyayya na gudun haihuwa da kai? Kin san me nake ji a zuciyata? No!! Baza ki ta6a sani ba saboda you are not in my shoe. So karki sake zuwa gurina kina playing kamar nine mai laifi bake ba, in baza ki haihu dani ba fine zan nemi wata hanyar Insha Allah.�? Yana gama fad’in hakan ya ture abunda yake ci gefe ya d’auki wayarsa ya fara dannawa ranshi a 6ace. “Wace hanya kenan?�? Ta tambayeshi. “Zaki gani.�? Ya mayar mata da amsa ba tare daya dubeta ba. “Aure zaka k’ara kenan?�? Sai da yayi d’an jimm kamar mai tunani sannan yace, “Who knows?�? Wannan amsa nashi yasa taji wani tuk’uk’in bak’in ciki a zuciyarta tamkar zai faso k’irjinta. Wai Haydar ne ke tunanin yi mata kishiya? Ita Laila? A k’uruciyarta ma ba’a mata kishiya ba sai data tsufa? “Tambayarka nayi ko ka gaji dani ne baka bani amsa ba.�? A very confused Haydar ya kalli Laila yana tuna maganarsu ta k’arshe ko ya danganci gajiya da juna, ko da ya gama tunani bai gani ba sai yayi shiru bai bata amsa ba. “Hakan na nufin da gaske ka gaji dani kenan? Abunda nake tsoro kenan tun daga farko amma ka kafe ka mini alk’awarin rainbows and sushine ba tare da kayi la’akari da cewa tsohuwa zaka aura ba yarinya ba. Yanzu daka aureni ka lura da abunda ka aura does not match to your expectations shine kake son guduna ko? I sacrifice a lot a kanka wanda har d’ana sai dana rasa ya shiga duniya saboda aurenka da nayi. It’s alright Haydar, duk hukuncin daka yanke daidai ne kuma ko yanzu ka rabu da ni zan d’auki hakan a cikin k’addara ta.�? Sake baki Haydar yayi yana kallon Laila cike da mamaki da kuma gaskata duk wanda yace mata na juya magana a cikin lokaci k’ank’ani. Me take tunani da wad’annan maganganun suka fito daga bakinta? Wa yayi maganar rabuwa da wani maganar expectations? Hawayen daya taru a idanunta ne ya sauk’o kan k’uncinta tayi saurin tashi ta fita daga falon Haydar ya bita da ido, domin ya kasa tunani balle har ya aikata komai. Ya kai minti biyar yana kallon k’ofar data fita sannan ya samu nitsuwa kad’an ya d’auki wayarsa ya danna kiran wani number ya shiga d’akinsa yana amsa sallamar wanda ya kira. Minti talatin da haka ya fito ya wuce sashen Laila ya sameta zaune a falo ta zubawa bango ido tana tunani, daga ganin idanunta kuwa ya gane tayi kuka bana wasa ba dalilin jan da suka yi. A kujeran da take zaune ya zauna ya dubeta da kyau yace, “Laila ban yi maganan rabuwa dake ba haka kuma ban miki alama ko na nuna miki baki kai ga abunda nake nema ba, hasalima sai dana dubi perfection d’inki da rayuwata sannan na fara jin sonki a raina da kuma son kasancewa tare dake. Aurenmu yazo a bazata kuma a k’urerren lokaci wanda shiyasa bamu samu zama muka yi hiran haihuwa dake ba, wannan dalili yasa yanzu muke samun matsala har kike tunanin rabuwa zanyi dake. Bana fatan rabuwa dake ko da kuwa ke kika nemi hakan, sai dai decision d’in da kika d’aukarwa rayuwar aurenmu is too harsh, haihuwa ba k’aramar magana bace a aure Laila. Nayi tunanin idan na nuna miki fushina zaki sauk’o kuma kiji tausayina ki bani abunda nake so, sai dai na lura hakan da nayi k’ara nesantani yayi dake ba tare da an samu abunda ake so ba. Amma har gobe ina fatan ki zauna ki dubi al’amarin nan Laila, ni d’aya mahaifiyata ta haifa ban san danginta ko na mahaifina ba. Ina son tara zuriya ina son gidana ya cika da ‘yayan da zan kirasu tsatsona tunda Ammi ta k’i fad’a mini asalina. Don Allah karki hanani hakan Laila, wallahi ina son haihuwa Ina son ganin ‘yayana.�? Yana fad’in hakan ya kamo hannunta cikin nashi yana kallon yanda idanunta ke tsiyayar hawaye wanda shima da zai samu sarari kukan zai yi ko zai ji sauk’i a zuciyarsa. “I know kinyi sacrificing a lot Laila, but bakya ganin kamar kin datse mini abu mai girma a rayuwata? Bakya ganin kamar abun ya mini yawa? Anya kuwa kin ta6a tunanin Allah zai kamaki da laifin k’in haihuwa ba tare da kwakkwaran dalili ba? Ko kina tunanin daidai kike yi?�? Dakatawa yayi yana kallonta tana share hawayen fuskarta ta k’i kallon inda yake, haka kuma ta k’i yin magana. “Har duniya ta nad’e babu macen da zan yiwa son da nake miki in kika d’auke mahaifiyata, ke na gani nake so kuma nake son tara zuriya. Shin ni kin mini adalci idan kika hanani haihuwa? Ki dubi al’amarin nan Laila.�? Ya k’arishe maganan yana jijjiga hannunta kamar mai son tura mata ra’ayinshi kwakwalwarta. Shiru tayi bata ce komai ba har na kusan minti d’aya, hakan yasa jikin Haydar yayi sanyi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana murza ‘yan yatsunta a hankali. Bai jima ba ya d’ago kanshi ba yabo ba fallasa yace, “Shikenan, idan hukuncin da kika yanke mana kenan fine, Allah ya bamu hak’urin zaman da juna.�? Ai da sauri Laila ta juyo tana kallonshi cikin tsananin mamaki tace, “Kana nufin ka yarda da hakan?�? Kwanciya yayi a jikin kujerar ya rufe idanunsa yace, “Ya kike so inyi to?�? “Ka yarda?�? “Eh, amma ba haka na so ba Laila. Kuma zan so ki canja kamar yanda nima na canja for you.�? “Haydar ba kyamar haihuwa da kai nake yi ba…..�? “Baki fahimceni ba nima kuma zai yi wuya in fahimceki. Mu bar maganar kawai. Allah ya kawo mana mafita ya kuma za6a mana abunda yafi alkhairi.�? Shiru tayi domin farin cikin data fara yi har ya kau dalilin ambaton mafitan da yayi. Kenan zai k’ara aure gaba? Tana son tambayarshi amma ita kanta she is not ready to hear his answer, bata ma son tunawa. Shiru suka k’ara yi a karo na ba adadi wanda har lokacin Haydar idanunshi a rufe suke amma bai yi bacci ba. Ita kuma tsura mishi ido tayi tana tunani had’e da tausayin wannan rayuwar tasu mai hard’e da sark’akiya da shafin drama kala daban-daban. Tana son kai hancinta jikinshi ta shak’i k’amshinsa da take so sosai, wanda dalilin hakan yasa har yau bata daina satar rigunansa tana d’aurawa kan pillownta ba. Tana son su koma yanda suke wato ya zama tudun dafawarta ko da kuwa ita ta kasa zama tashi. Tana son mijinta tana kuma son k’arisa rayuwarta dashi shiyasa ko da wasa bata son yin tunanin had’a soyayyarsa da wata. Tashi tayi tsaye tace, “Zan kwanta.�? “Sai da safe.�? Ya fad’i hakan yana bud’e idanunsa kana ya mik’e tsaye ya nufi hanyar sashensa. Kamar gunki Laila ta tsaya tana kallonshi har ya fita daga falon nata. Ba yace sun shirya ba? Jiki ba kwari ta rufe k’ofa kana ta shiga d’akinta ta kwanta bayan ta jawo rigarsa ta d’aura saman pillow. Ta kai minti arba’in tana juye-juye bacci ya kasa d’aukanta. Ganin ba sarki sai Allah yasa Laila ta tashi ta nufi sashen Haydar zuciyarta na bugu dalilin bata son koda wasa ya kawo a ransa cewa sha’awarsa take ji duk da cewa hakan ne ba karya bane. A kan katifarsa ta sameshi ya kwanta amma yana danne-danne a wayarsa. Yana jin k’arar k’ofa ya d’ago ido ya ganta tsaye a bakin k’ofa tana inda-inda ta kasa shigowa kuma ta kasa fita. Zuba mata ido yayi yaji dame tazo, ita kuma hakan yasa ta k’ara daburcewa kunya kamar ta nitse tace, “Kazo muje mu kwanta.�? “Nan yafi mini dad’i.�? Ya bata amsa yana ajiye wayar a gefensa. “Tunda kace komai ya wuce bai kamata mu cigaba da raba gurin kwanciya ba, ba haka muke ba.�? “A lot of things changed Laila, amma nan yafi mini dad’i shiyasa ban koma d’akinki ba.�? “To me kake nufi kenan?�? “Zan cigaba da kwana a nan, you can come if you want.�? K’unk’uni ta fara yi ta tako ta shigo d’akin, har ta kwanta a gefenshi bai gane me take cewa ba kuma bai damu ya sani ba tunda bata yi niyyar yaji ba. Murmusawa yayi a karon farko yana mamakin hali na mata, musamman na matarsa Laila. Wayarsa dake tsakaninsu ya k’ara d’aukowa yaci gaba da dannawa ba tare daya kulata ba. “Hasken wayarka ya hanani bacci.�? “A low yake fa.�? “A hakan dai.�? Bai k’ara cewa komai ba ya kashe wayar ya ajiyeta a k’asa kana ya gyara kwanciyarsa ya fara addu’an bacci, yana gamawa ya shafa a jikinshi ya shafa mata kana ya rufe idanunsa. Minti hud’u da haka Laila ta juyo tana kallon silhouette d’insa dalilin hasken farin watan daya mamaye d’akin. “Haydar.�? Ta kira sunanshi. “Na’am.�? “Har yanzu fushi kake yi dani?�? “Me kika gani?�? “Baka bani amsa ba.�? “No, bana fushi dake.�? “To me kake yi hakan kenan?�? “Me nayi?�? “Hakan.�? Shiru yayi bai k’ara cewa komai ba, jikinta ne yayi sanyi ainun har tana dana sanin biyoshi domin ba haka ya saba mata ba. A daa zai biye mata har yaji menene laifinsa, amma a yanzu baya son jan magana da ita. Wace irin illa ta yiwa rayuwarsu da soyayyarsu ne? Meyasa ya canja har haka? Zuciyarta ce ta fara bugawa data fara tunanin ko ya gaji da ita ne ya fara hango k’ananan ‘yan mata, ko dai ya daina sha’awarta ne saboda ita tsohuwa ce? A take wannan insecurity ya shiga zuciyarta ya samu guri ya zauna daram. Babu 6ata lokaci taji duniyar ya fita a kanta ta fara ganin kamar bata kai ba domin ta kasa jan ra’ayin d’a namiji kanta. Ita Laila yau namiji ke jawa aji? “Stop overthinking and bring your ass here.�? Fad’in Haydar yana d’aura hannunsa kan k’ugunta. “Huhhh?�? “Idan kina overthinking kina yawan had’iye yawu akai akai. I said COME.�? Yanda ya k’arfafa kiran yasa ta mirgana ta shiga jikinsa, kanta ta d’aura kan k’irjinsa tayi ajiyar zuciya bayan ta shak’i kamshinsa da take mura fi, shi kuma ya zagayeta da hannunsa yana d’aura ha6arsa a kanta. “Bazan cigaba da fushi dake ba saboda babu amfanin hakan tunda a daa nayi amma banga wani canji ba, but kema ba dole kiga komai da kike gani a baya ba saboda kin hanani abu mafi soyuwa a raina. Zan yi hak’uri inga yanda Allah ya tsara mini kema kuma kiyi hak’uri da yanda zamu yi rayuwa.�? Hawaye ne taji ya taru a idanunta ya sauk’a kan k’irjinsa amma shi bai nuna alamun yaji hakan ba. “Baka sona kamar daa ko?�? “Kiyi bacci, nima gobe ina da zuwa gurin aiki.�? Wannan kad’ai yasa ta gane amsarta ba tare data ji daga bakinsa ba, lallai ta musu illah bana wasa ba, kuma duk akan haihuwa. Bayan ya tafi sallah da asuba itama ta tashi ta nufi sashenta tana tunanin rayuwarsu, a daa ganinta kad’ai idan yayi sai sha’awarshi ta tashi amma jiya kwanciya tayi a jikinshi amma bai nuna komai ba tamkar namiji d’an uwansa ne ya rungumeshi. Ba dai ya daina marmarinta ba? Kenan hakan zai iya faruwa? Anya bata yi saurin cewa ba zai iya had’a soyayyarta da wata mace ba kuwa? A yanzu da take kwalli d’aya tak a gurinshi bata ishesa kallo ba, Ina ga kuma in yana da wata? Bayan tayi sallah gari ya fara haske ta tashi ta shiga kitchen ta d’aura musu breakfast, tana gamawa ta ajiye a kan dinning table kana ta shiga d’akinta tayi wanka. Kwalliya mai tsada ta yiwa fuskarta sannan ta nad’a laffayar da ta saka ranar aurensu, she wants him to remember that day da yake d’okinta yana jin sonta a ranshi. K’amshin humra kad’ai ke tashi a jikinta ta fito a Lailarta, wato Dawisu Sarkin ado. Sashensa ta nufa ta samu yayi wanka ya shirya yana tattara gadgets d’insa yana sakawa a jakar Laptop d’insa. Sallamar da tayi yasa ya d’ago ido yana amsawa, gaisheshi tayi kamar kullum amma wannan karon cikin jan aji irin ta matan da suka san kansu kana ta kad’a ido tace, “Na dafa maka abinci, a kawo maka nan ko zaka je can kaci?�? “Barshi zan ci a can d’in.�? Ya fad’i hakan yana zuge zip d’in jakar amma hankalinsa na kanta. A hankali ta tako ta kar6i jakar daga hannunsa kana ta juya ta fara tafiya yabi bayanta idanunsa na kan mazaunanta tana juyasu. A kan kujeran falonta ta ajiye masa jakar sannan ta isa dinning table ta fara bud’e kwanukan tana saka masa. Duk wannan abun da take yi hankalinsa na kanta yana battle tsakaninsa da zuciyarsa wacce ke raya masa abubuwa da dama har da hanasu fita aiki yau dukkansu. Tana gama saka mishi abincin ta ajiye a gabanshi tare da kofin tea kana ta koma falo tana duba cikin jakarta. “Baza kici abincin bane?�? Ya tambayeta yana kai loma bakinsa domin yayi kewar girkinta. “Ina azumi.�? Ta bashi amsa. A take fantasy d’inshi na zama a gida yayi canceling kanshi da kanshi saboda matar gidan na azumi. “Na me kike yi?�? “Wanda nasha a Ramadan.�? “Meyasa bazaki bari sai daga baya ba?�? Ya k’ara jeho mata tambaya domin da alama yau yana son yin magana da ita. Jakarta ta ajiye a gefe kana ta dubeshi da kyau tace, “Saboda bansan ranar mutuwata ba, zai fi dacewa in yi in gama. Kasan mu tsoffi an fi mana zaton mutuwa.�? Dariya yayi wanda yasa Laila ta k’ulu har tayi dana sanin kiran kanta tsohuwa, ita da take son ya yabeta amma ya nuna ya yarda da maganarta. “Laila kenan. In kina magana kamar wacce ta bawa saba’in baya. You are not old, hasalima kallon yarinya nake miki saboda duk hankalinku d’aya.�? “Me hakan yake nufi kenan?�? Wani gefe na zuciyarta kuma taji dad’in kallon yarinya da yake mata. “Babu, amma idan zaku jera da sa’o’inki baza ace shekarunku d’aya ba saboda kin fisu kyan jiki da fuskar yarinta.�? “Hmm.�? Kawai tace amma zuciyarta fari tass dalilin yabonta da yayi. Kenan har yanzu akwai d’igon sonta a zuciyarsa. Daga nan basu sake yin magana ba har ya gama cin abincin ya tashi suka fita, fatan alkhairi ta mishi da samun motarshi kana kowa ya shiga nashi suka fita daga gidan bayan sun yiwa juna sallama. Kafin Haydar ya isa gurin aiki aka kira wayarsa ya d’auka yana cewa, “Ya aka yi?�? “Yalla6ai yaronku na cikin wani mawuyancin hali dalilin sata da suka yiwa mai sayar musu da magani, Shi kuma ya musu dukan fitar hankali har muna zaton ya karya su.�? “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Shi da waye Sannan suna ina?�? “Shi da Banney, sannan an tarkatasu zuwa police station dalilin Ima ya kai k’ararsu bayan dukan daya musu.�? “Ka tsaya a gurin duk abunda ya faru in sani. Lokaci yayi da zai dawo gida ko ya k’i ko ya so.�? Yana fad’in hakan ya kashe wayarsa kana ya kira Mas’ud yace, “Kana ina ne?�? “Ina gida, wani abu ne? Ina Kalti?�? Ya tambaya jin yanayin Haydar kamar ba lafiya ba. “Lafiyanta kalau. Zan zo muyi magana ne kan kan abunda ya faru zuwana Abuja. Mas’ud na samu Abul.
Mum Fateey 👌




