Hausa novels

Halysaah Page 12 By Khaleesat Haydar

Washegari da safe Khaleesat ta gama duk abinda zata yi a gida ta shirya ta tafi makaranta, tana zaune favourite spot dinsu ita da Safiyyah bayan sun fito daga aji, Safiyyah na facing dinta tace “Tsakaninki da Allah ina kika je jiya da yamma da naje gidan baki nan? Ni dai nasan babu inda kike zuwa a garin nan, ba kuma frnds gare ki ba, So where did u go?” Khaleesat da idonta ke kan jotting da tayi a aji tace “To ke meye na zuwa da yamma likis, i was expecting you around 5pm not 7pm” Safiyyah ta amshi takardan hannunta tace “Ina maki tambaya kina min tambaya, ko akwai abinda kika fara boye min ne Khaleesat?” Tagumi tayi tana kallon Khaleesat din da tuhuma, sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta, dariya ta bata amma bata yi ba, kamar dai bazata ce mata komai ba sai kuma ta bude baki tace “Mun fita zuwa restaurant ne da Housemate dina” Safiyyah ta buda baki tana kallonta with surprise, can tace “Waw, really? Housemate dinki fa kika ce?” Sai kuma tayi dariya tana gyara zama idanuwanta kamar za su fito tace “Anya Khalee babu magana a kasa kuwa? Restaurant fa kika ce? How did he convince you har kika bi sa zuwa restaurant?” Khaleesat ta tabe baki tace “Toh meye kuma a kasa? Daga dai ya kai ni restaurant mu ci abinci? Kinsan yaushe rabon da inci abincin kirki a gidan?” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “He notice i haven’t been eating shi ne yasa har ya kai ni restaurant” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Ai kece da dora ma kanki abinda Allah bai dora maki ba kawata, akan Abdul din da naga yayi updating status da jersey jiya alamar har ya koma Nigeria ya ci gaba da harkokin gabansa ke kina nan kina neman kashe kanki, wallahi in zaki ajiye lamarin gayen nan a gefe da zai fi maki alkhairi a rayuwarki, very very heartless guy with no conscience, dubi tsabar zuciyarsa ta dutse ne ya gwammace ya kara siyan ticket yayi juyawarsa ya koma Nigeria, Allah ma yasa yayi maki ya jiki zuwan da yayi” Khaleesat dai tayi shiru tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta daga kafada tace “Ga dai Housemate din nan naki duka duka yaushe har ma ku ka san juna? Amma ya gane kina cikin damuwa har da kai ki restaurant for dinner, to this is how a caring and understanding Boyfriend and a Gentleman should be” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace “Ni babban damuwata kar ya sake dawowa kasar ban sani ba Sophie, ce masa nayi Housemate dina frnd din Nancy ne fa, kinsan bai san Nancy bata gidan ba ai har yanzu, to kar ya sake dawowa unexpectedly ya gansa” Safiyyah tace “Abinda zai faru kawai kiransa zaki yi ta yi har sanda ya ga daman daga kiranki, ki basa hakuri ki samu ku shirya, in har ku ka shirya duk wani movement dinsa zaki dinga sani, yanzun ma ai don baku communicating ne all this while shi yasa kawai ya taho kamar an jefosa, banda haka ai duk sanda zai zo yana gaya maki” Khaleesat tace “Haka ne, amma kin san irin zuciyarsa wallahi zan iya kiransa sau goma ma bazai daga ba, ko na masa magana ta WhatsApp bazai yi reply ba” a sanyaye ta kare maganar, Safiyya tace “Bari in kirasa ta wayana yana picking zan ce ya kirani, daga nan in ya kira sai in baki wayar ku yi settling dispute din karyan ku” Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, amma tasan hakan kadai shi ne way out, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara kiran Abdul, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa sai gashi ya daga, sallama tayi masa ta gaishesa tace “Pls in ba damuwa ka kirani” Katse kiran yayi sai gashi ya kira tayi picking sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amshi wayar gabanta na faduwa ta kai kunne, Safiyyah ta tashi ta bar ta a wajen ta koma wani waje ta zauna, a hankali Khaleesat tace “Don Allah kayi hakuri ka saurareni…” Shiru yayi da yaji muryarta, nan da nan hawaye ya cika idonta muryarta na rawa tace “Pls kayi hakuri da abinda ya faru, i promise you hakan bazai sake faruwa ba” Yace “Dama akwai abinda ya faru ne?” Tayi shiru bata ce komai ba, yace “I am asking you, akwai abinda ya faru ne dama?” Ta sunkuyar da kanta tace “Don Allah kayi hakuri, i am truly sorry plss” Yace “Look i am super busy now, idan kin shirya gaya min abinda ya faru kike ban hakuri sai ki kirani ta layin ki anjima” Cikin sanyin murya tace “Toh Nagode” Katse wayar yayi, ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta kyabe baki ta dawo kusa da ita ta zauna tace “Ya ku ka yi da shi?” Khaleesat ta ja tsaki tana tattara reading material dinta tace “An gaya masa banda ina tsoron kar ya dawo without notice ni zan sake magana da shi ta waya ne” Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat tana tunanin yaushe bakinta ya fara budewa haka akan Abdul ne wai, Dariya Safiyya tayi tace “Shi Abdul din naki Khalee?” Khaleesat ta ki bata amsa, har ranta ita fa yanzu tana jin bazata iya ci gaba da tolerating abubuwan Abdul ba, ita kanta bata san daga inda wannan liver din yake zuwa mata ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru but she is not tolerating anymore. Wajen karfe biyu ta koma gida, bayan tayi wanka tayi sallah ta sauya kayanta ta kwanta, sai bayan da tayi la’asar ta shiga kitchen ta jingina da cabinet tana tunanin abinda zata girka, tuwo taji take son ci, kawai daga karshe tayi deciding tayi tuwon since tana da duk ingredients din girka tuwon, kan kace me ta gama girka tuwo da miyar kuka with enough obstacles a ciki, ta gama goge gogen kitchen din sannan ta fito parlor wajen karfe biyar, dai dai shigowar Housemate dinta gidan, ita dai tana tsaye kusa da kitchen, ya juya ya kalleta bayan ya kulle kofar parlon yace “Good evening Halysaah” Tace “Good evening” Yace “What are you cooking with such a nice Aroma” Tace “Tuwo ne” Ya karaso cikin parlon yace “Really, it’s been long na ci tuwo fa” Tana kallonsa tace “In kawo maka?” Ya dan buda ido yace “Ok thank you” Juyawa tayi ta koma kitchen din, ya zauna saman kujera hoping ba da yawa zata saka masa ba, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo parlon da plate dauke da tuwo with a diff bowl of soup, tun da ta duka ta ajiye abincin yake kallon bowl din miyan babu ko kiftawa, can dai ya daga kai ya kalleta yace “Wani miya ne wannan Halysaah?” Ta koma gefe tace “Miyar kuka ce” Lkci daya yayi yaƙe yana shafa kansa yace “Wow, but bana cin irin miyan, i thought vegetable soup ne, baki yi stew ba?” Ta wani kallesa, a takaice tace “Babu, kuma kayi tasting miyan ne kafin kace baka cin irin sa?” Ya jingina da kujera ya sauke ajiyar zuciya yace “Na ma ci abinci few minutes ago fa” Dukawa tayi ta dau bowl din ta mika masa miyan tace “Taste it first before concluding” Ya dan kalleta yana murmushin dole yace “Ok, where is the spoon?” Tace “Shi ba a cin sa da cokali ai, da hannu zaka sha” Yayi shiru sai kuma yace “Then bari in wanke hannu” Yana fadin haka ya mike, ta koma gefe don basa hanya sannan ta bi sa da kallo har ya tafi bandakin dake parlorn ya wanke hannu sai gashi ya dawo, bayan ya zauna ta mika masa miyan tana kallonsa, shi dai bai yarda ya hada ido da ita ba, tun da ya kai finger ya lasa miyan ya kai baki ya kasa dago kai, ita dai kallonsa kawai take bata ko kiftawa, can dai yana murmushi da kyar ya dago yace “It’s sooo nice amma na ci abinci wallahi Halysaah” Duk da dariyar da ya bata ta dake tace “To ai tunda ka sa na zuba sai ka ci ko kadan ne cause i am not throwing it away” Bata jira cewarsa ba ta juye masa miyan a kan tuwon dake plate ta dau plate din ta mika masa tana kallonsa, he was totally speechless and confuse at the same time, tana kallonsa da kyau tace “Karba” Ya kai hannu a hankali ya amsa plate din tuwon, in ya debi tuwon sai ya dangwala miyar kamar yana tsoronsa sannan ya kai baki, sosai ya bata dariya amma fa bata yi ba, instead sai murmushi take, sau uku yana diban tuwon yana ci kuma har sannan yaki yarda su hada ido da ita, kana ganinsa kasan da kyar yake cin abincin, his facial expression says it all, wayarsa ne ya fara vibrate, ya ajiye tuwon da sauri ya fiddo wayar yana kallon screen, sai kuma ya kalleta yace “This is an urgent call Halysaah bari in shiga daki in daga” Kasa basa amsa tayi don kar ma tayi dariyar da take dannewa, ya mike ya nufi dakinsa da sauri don ko jiran jin abinda zata ce bai yi ba, tana ji ya sa ma kofar dakin makulli bayan ya shiga, sai a sannan ta zauna gefen kujera ta rike kanta tana dariya, after some minutes ta mike ta dau plate din tuwon still smiling ta wuce dakinta. Khaleesat na Voice call ta WhatsApp da Ummanta wajen karfe tara da rabi na dare taji Housemate dinta na knocking kofar dakinta, bayan tace ma Ummanta tana zuwa ta ajiye wayar sannan ta sauka daga kan gado ta saka hijab ta tafi ta bude kofar, yana jingine jikin bangon opposite din dakinta idonsa a kulle, yana jin bude kofa ya bude idon da sauri, kana ganinsa kasan daga bacci ya tashi, tun da ya shige daki daxu yace ana kiran wayarsa bata sake ganinsa ba sai yanzu, yace “Zan tafi sai da safe Halysaah, but pls ki dan kulle kofar i can’t find my key” Ita dai bata ce komai ba tana kallonsa, he look so sleepy, ya ciro wayarsa dake ta vibrate a aljihu, tsaki yayi after picking yace “Kai dalla ina hanya” Daga haka ya mayar da wayar aljihu ya sake yi mata sai da safe ya juya ya fara tafiya, ta bi sa da kallo har ya isa parlor, jingina taga yayi ta bayan kujera ya rungume hannunsa ya rufe ido, Khaleesat ta sauke idonta sannan ta fito daga dakinta tana tafiya a hankali ta tafi parlon, bude ido yayi da sauri jin tafiya, sai kawai ya nufi kofar fita daga parlon, tace “Since u can’t control ur self a ko ina ka samu bacci kake, be it standing, sitting, driving and even walking, then why not sleep over?” Ya dan kalleta jin abinda tace, nan da nan kuwa yaji baccin ya bar idonsa gaba daya, yana mata kallon mamaki at the same time yana sosa kai yace “Yaushe kika ga nake yin duk wannan da kika lissafa Housemate?” Ita dai ta rungume hannu tana kallonsa bata ce komai ba, ya dauke kai yace “I was only meditating ba wai bacci nake ba, in dai kika ga na rufe ido to i am meditating” Yana fadin haka ya nufi kofa ya bude yace “Good night, kar ki manta ki kulle kofar” Daga haka ya fita ya tura mata door din, ɗan murmushi tayi tana tafiya a hankali ta isa kusa da window ta dan bude curtain din tana lekansa, parking space taga ya nufa ya bude motarsa ya shiga, she is just hoping yana shiga bazai fara wani baccin ba a cikin motar, after few seconds taga ya fara reverse, ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa har ya bar Garage din ya dau hanya, sake curtain din tayi slowly, ta dan tsaya for few minutes sai kuma ta tafi daki ta dauko key dinta ta kulle kofar ta wuce dakinta, sake kiran Ummanta tayi ta WhatsApp, bayan Umma ta daga Khaleesat tace “Ko kin fara bacci ne Umma?” Umma tace “Aa idona biyu ina jiran ki, Abdul ya maki wata magana ne?” Khaleesat tayi shiru jin abinda Umma tace, ta girgiza kai tace “A’a bai ce min komai ba, me ya faru Umma?” Umma tace “Daxu Hasiya Matar Malam Saleh ta zo gidan nan” Sosai Khaleesat taji gabanta ya fadi, Malam Saleh aminin mahaifinta ne, yawanci abubuwa da yawa a bakin matarsa Ummanta ke ji tunda ba gaya mata baban nasu ke yi ba, abu da yawa ma sai dai taji a duniya ba dai a bakinsa ba, Khaleesat tayi karfin halin cewa “Me tace Umma?” Umma tace “Wai ko an tsaida maganarku da Abdul, haka dai tace min” Khaleesat was short of words, lokaci daya jikinta yayi sanyi, sosai maganar ta zo mata a bazata, she could feel her self tearing up, hankalinta yayi mugun tashi cikin lkci kadan, Umma tace “To ina jira dai in ga ko Malam din zai yi min magana, in ba ayi hankali ba kuma in ji a bakin matansa tun da su zai gaya masu ai, kuma kin ce Abdul din bai ce maki komai ba har yanzu ko?” Khaleesat ta goge hawayen da ya gangaro idonta, tana gyada kai da kyar kamar Umma na ganinta amma ta kasa cewa komai, Umma tace “Khaleesah?” Da kyar Khaleesat ta bude baki ta amsa don bata son Ummanta tasan kuka take, Umma tace “Naji kinyi shiru ne” Khaleesat ta dake tace “Ba komai Umma, ina duba wani karatu ne a takarda” Umma tace “To shikenan, kiyi karatun ki ma yi magana washegari ko?” A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayar hannunta ta kwantar da kanta saman pillow hawaye na sauka idonta, bata san menene ya sa all of a sudden taji she can’t marry Abdul ba unlike before da har cikin ranta tasan bata da option dole ne aurenta da shi, tana kuma masa fatan ya canza wataran, yanzu kam bata jin haka a ranta, instead ji take bazata iya aurensa ba ma, Khaleesat bata yi wani baccin kirki ba daren ranan nan fargabanta daya kar ma yace a daura auren nan take, tasan in har suka ce ma iyayenta haka babu abinda zai hana a daura auren nan sai wani ikon Allah. Da safe Khaleesat ta tashi da ciwon kai sosai, kana ganinta kasan tana cikin damuwa ba kadan ba, haka dai ta shirya ta fita zuwa makaranta, warce take son tayi ma magana ta dan ji saukin abinda ke damunta sai bata shigo school ranan ba, wayarta ta ciro kawai tayi dialing number Abdul cause she can’t hold it anymore, kiran na shiga ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne a hankali ta gaishesa, amsawa yayi yace “Ya aka yi?” At first tayi shiru, sai kuma tace “Ba komai i only called to greet you” Yace “Which side of the bed did you wake up from today da kika kirani ki gaisheni?” Tayi masa shiru, yace “ke dai fadi abinda kike so Malama, foodstuffs din ki ne ya kare ko me?” Ta hade rai tace “Yaushe ka siya da har zai kare?” Yace “Bazai kare ba dama mana tunda baki wani cin abinci sai cookies da kayan kwadayi” Ta wani turo baki bata ce masa komai ba, after few seconds tace “Kawai naji a jikina ne kamar da wani abu dake shirin faruwa shi sa na kira ka” Yace “Wani abu kamar me fa?” She was mute bata basa amsar tambayarsa ba, yace “Anyway, ko ma me kika ji a jikin ki haka ne, zan shiga meeting yanzu sai anjima” Katse wayar yayi a nan take, ta dinga kallon screen din wayarta wani tsanarsa na yawo a zuciyarta, a baya duk abubuwan da yake mata bata taba jin tsanarsa ba sai dai haushinsa yanzu kuwa kawai ji tayi ta tsanesa, ta ja tsaki ta mayar da wayarta jaka tana jin wasu hawaye na cika idonta, rashin zuwan Safiyyah makaranta ya sa bata tsaya su gama karatun ranan ba ta kama hanyar gida kawai cike da damuwa, tana jiran Lyft din da tayi ordering sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tun daxu ta kirata bata daga ba sai yanzu ta biyo ta, Khaleesat ta daga ta kai kunne tana jin muryar Safiyyah tace “Baki da lafiya ne?” Da kyar Safiyyah tace “Tun jiya da daddare, na ma zata rasuwa zan yi kawata” Khaleesat ta ɗan bude ido tace “Me ya sameki?” Safiyyah tace “To ina ma na sani Khaleesat, Allah sa ba poison dina matar nan tayi ba don tun jiya sai yanzu nasan mutanen dake kaina” Khaleesat tace “Subhanallah, kina gida ne yanzu?” Safiyyah tace “Har da karin ruwa kuwa” Khaleesat tace “To bari in taho gidan yanzu” Khaleesat na maida wayarta jaka ta nufi gidansu Safiyyah, bayan tayi knocking kofar Surayya ta bude mata, Khaleesat ta sauke ido ta gaisheta, in ba kasa kunne sosai ba ma baza kasan Surayya ta amsa ba, Khaleesat taji muryar Mustapha na tambayar matar tasa wanene, ji tayi kamar ta juya ta fasa shiga cikin gidan, amma kasancewar a bude Surayya ta bar kofar yasa ta karasa ciki walking slowly, without looking at Mustapha dake parlor ta gaishesa, ya amsa yace “Ya karatun Khaleesat?” Khaleesat tace “Alhamdulillah, ya jikin Safiyyah?” Yace “Alhamdulillah, she is inside her room” Khaleesat ta juya ta nufi dakin Safiyyah, da gasken ruwa ta tarar ake kara mata don ta zata kawai tace mata haka ne don ta zo, Khaleesat ta zauna gefenta da damuwa tace “Sannu Sophie, ya jikin?” Safiyyah tace “Ba sauki Khaleesat, wallahi kilan abu matar nan ta saka min a abinci” Khaleesat tace “Don Allah ki dena cewa hka, kin ga yayanki ai bazai ji dadi ba in kina wnn magana” Safiyyah tace “Wallahi ita ce don lafiya na dawo gida jiya, ni na zata ma na rasu, sai da na farfado naga ba haka ba” Khaleesat tace “Allah dai ya baki lafiya, kin ci abinci?” Safiyyah tace “Ni bazan ci abincinta ba gaskiya tun daxu sai fruit kawai nake ta sha da lemon kwali” Khaleesat tace “Ko in je gida in maki girki? Me kike son ci?” Safiyyah tace “Ko tuwo da miyar kuka ne ki min in kina da ingredient, kawai shi naji nake so wallahi” Khaleesat tace “To ba damuwa, bari inyi sallah sai in tafi in maki girkin” A haka Khaleesat tayi sallahn azahar ta bar gidan bayan tayi ma Surayya da mijinta sallama, Mustapha ne ma ya tambayeta har zata tafi, Shine tace masa zata dawo anjima, Khaleesat na isa gida taga motar Housemate dinta a Garage, tana bude kofar ta shiga parlor ta gansa kwance kan 3 seater yana bacci, har ta kulle kofar bata ga ya bude ido ba, ta nufi dakinta ta shiga ciki ta canza kaya sannan ta fito ta shiga kitchen, tuwon ta dora har zata fara hada ingredient na miyar kukan sai kuma ta fasa taji gwara tayi vegetable soup kawai, ita kanta bata san menene yasa take son yin vegetable soup din ba duk da bata wani son cin miyar ganye she prefer slimy soup, sai da ta gama tuwon sannan tayi ordering lyft da zai kai ta nearest African store da zata iya siyan ingredients din miyan Vegetable.*Make ur payment before the end of free pages* _Halysaah is just 500 naira_ 07087865788 ✍🏻

Back to top button