Novel Document

Namijin Duniya Book 1 Hausa Novel

Tafiya sukeyi cikin nutsuwa suna hira su biyu Hauwa’u ta kalli Inteesar tare da cewa”Inteesar gaskiya ina ganin musamu wani gurin mu fake saboda naga hadari na niyyar tasowa ke sarkin mura”.
“toh yanzu a ina zamu fake anan gurin”.
“kinga wata rumfa can muje muɗan fake in ruwan ya ɗauke semu wuce gida”.
“toh”.
nan suka ƙarasa rumfar wani me shayi suka zauna zamansu keda wuya ruwan sama ya kece aka shiga ruwa kamar da bakin kwarya.

Andaɗe ana ruwan sannan ya ɗauke suka tashi suka cigaba da tafiya sunyi nisa sukaga wasu motoci ƙirar Land cruser baƙaƙe se ta tsakiyar data ƙasance roice-roice fara tas me baƙin tintac motar itace ta cikon ta bakwai wato dai ma’ana a tsakiya danno kai sukayi sunzo wuce daidai su Inteesar bazato sukaji ruwan taɓo da kwatami ya watsomusu a jikinsu sakamakon motar fallatsamusu da tayi cikin sauri da zafin zuciya Inteesar ta wawuri wani dutse dake kusa dasu ta jefi ɗaya daga cikin motar dutsen be tsaya akan kowacce motaba se a glass ɗin farar motar nan ta tsakiya tass kakejin ƙarar fashewar glass ɗin a razane Hauwah ta kalli Inteesar tare da kallon motocin tace”nashiga uku Inteesar kinsanko motar wa kika fasawa glass kuwa?”.
cikin masifa wadda ita kanta batasan tanada itaba tace”ko motar waye ina ruwana meyasa su masu kuɗi basusan darajar ɗan Adam ko cemusu akayi muba mutane bane ke bakiga abinda sukayimana ba ruwan kwatamifa suka fallatsamana kina kallo kuma ko niyyar tsayawa basu da ita amma ke saboda rashin kishin kai yasa ki cemun wai nasan motarwa na fasawa glass ina ruwana ko wayemana ai tare suke”.

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Jin ƙarar glass yasashi ɗagowa daga karatun daily thrust ɗin da yikeyi tare da zubawa gaban motar da yike ido wow na furta sakamakon ganin haɗaɗen matashin guy ɗin yagaji da haɗuwa komai nashi abun burgewane saurin fita drivern yayi bejimaba ya dawo cikin girmamawa yace”Oga wasu yarane kan amfallatsamusu ruwan taɓo shine ɗaya daga cikinsu tayi jifan amma gashi can su Muhd sun zagayeta”.
cikin muryarsa da kamar ammasa dole yace”buɗemun mota”.
“angama ranka shidaɗe”.
nan drivern ya buɗemasa a hankali ya zura ƙafarsa waje yafita cikin takun zaratan maza masuji da class yaƙarasa gurin wanda hakan yayi daidai da ɗaga hannun Muh’d ze wankawa Inteesar mari.
a ɗan daƙile NAMIJIN DUNIYA yace” Dakata Muh’d”.
yaƙarasa maganarsa tamkar wanda aka tilastawa
Wani ƙasƙantaccen kallo me cike da zallan ƙyama da wulaƙanci yake jifanta da shi Cikin lion voice ɗinsa yace” ke Waye Ubanki da me kike gadara da har zaki fasamin glass ɗin motana ubanki waye a ƙasarnan”.
Lokaci ɗaya Idanunta suka rine saboda tsananin ɓacin rai saboda dukda suke talakawa batason a wulaƙantamata iyaye a zuciye tace “Da Uban da kake gadara dashi nake gadara mutumce kamarka”.
Azuciye ya ɗaga hannunsa da niyyar yarfa Mata mari yaji an riƙe Murmushi ta saki me cike da takaici da ƙunan rai tace” daka mareni tabbas da ka aikata kuskure mafi muni atarihin Rayuwar ka idan har ka yadda wannan wulaƙantaccen hannunka ya taɓa tsaftacciyar fuskata ta”.
ta faɗa tare da yin wurgi da hannunsa Bata jira Jin abinda zeceba ta finciki Hannun Hauwa da jikinta keta rawa suka bar wajen.

Hannu yasa ya hargitsa tulin sumar dake kansa kana ya furzar da iska me zafi daga bakinsa wani irin tsuma jikinsa keyi yayinda jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu-ruɗu dasu tabbas tunda yake babu wani mahalukin daya taɓa muzantashi irin wannan bagidajiyar yarinyar tamkar ze tashi sama ya juya yashi ɗaya daga cikin motocin guard ɗinsa kafin yaƙarasa sun buɗemasa ƙofa shiga yayi tare da lumshe sexy eyes ɗinsa yayi da sukayi ja dasu tare da furta “senayi maganinki ko ƴar waye harni NAMIJIN DUNIYA za’ah samu wata dirty girl zata gaggayamun magana nayi alƙawari sekinyi regreting ɗin abunda kikayi “.
yana wannan zancen zucin har suka isa wani tanƙamemen building dogo kallo ɗaya zakayiwa haɗaɗɗen building ɗin ka fuskanci ma’aikatace saboda mutane daketa hada-hada a gurin suna gama parker motocin Muh’d yace”Oga mun iso”.
buɗe lumsassun idanunsa yayi da sukayi ja ya kalli handle ɗin ƙofa alamar a buɗemasa buɗemasa Muh’d cikin takun ƙasaita haɗe da jiji dakai ya fito ma’aikatan dake gurinne gabaki ɗayansu suka shiga gaidashi ba tare daya amsaba yashiga tafiya saboda tsananin ɓacin ran da yike ciki be zame ko inaba se gurin elavatorn da shikaɗai yike hawa ya danna yashiga ya rife a hawa na goma elavatorn ya tsaya tare da wangale ƙofar fita yayi tare da nufar wata haɗaɗɗiyar ƙofa yashiga nan take wani haɗaɗɗen guri ya bayyana se wata mata datasha atarch akanta yare-yare fuska tasha mai ga heavy make up data cika fuskarta dashi tana danna waya ta bayyana tana ganinshi ta ƙara gyarawa cikin ƙissa tace”Oga sannu da zuwa”.

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

be amsamataba hakan yasa tagane yau yana cikin ɓacin rai dan haka takama kanta tare buɗemasa ƙofa yashiga tanƙamemen office ɗinsa daya gaji da haɗuwa kallo ɗaya zakayiwa office ɗin kasancewa kuɗi sun zauna domin komai na more rayuwa akwaishi zama yayi sakatariyarsa daketa kwarkwasa tashiga zayyanemasa shadul ɗin ranar jingina yayi da kujerarsa tare da lumshe ido fita sakatariya Zeezee tayi bata jimaba se gata da wani haɗaɗɗen cup a hannunta taƙarasa gaban table ɗin da Namijin duniya ke zaune tace”sir your copee is ready”.
ba tare daya buɗe idoba yayimata da nuni data bashi miƙamasa tayi ta juya a hankali yashiga shan copee lokaci ɗaya yaji wata nutsuwa tazomasa ya aje cup ɗin tare da danna wayarsa yayi dialing wata number bugu ɗaya aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren wancan yace”Oga ɗiyar massenger ɗin Sir Ahmad ce”.
wani murmushin gefan baki Abdallah Namijin duniya yayi ba tare da yayi maganaba ya kashe wayar tare da tura text ya jingina da kujerarsa yana tinano irin abubuwan daya tanazarwa Inteesar.

Ɓangaren Inteesar ko suna barin gurin Hauwa’uh ta kalli Inteesar tace”nifa tsoro nikeji saboda nasan NAMIJIN DUNIYA baze taɓa barinkiba Inteesar meye danya watsamana ruwa”.
“gaskiya duniya ba gaskiya wato shi bakiga abinda yayimanaba saboda yanada kuɗi seni nawa kika gani ba wani tsoronsa da zanji ai mutum ne shina kamar kowa kodon kina sonsa shiyasa kike kareshi”.
“ba haka bane ƙawata kawaidai……”.
saurin dakatar da ita Inteesar tayi tare da cewa”dame kikeso naji da baƙincikin gidanmu koko dana irin wa’innan watsatstsun mutanen da basusan darajar ɗan Adam ba”.
“ya haƙuri ƙawata”.

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

suna wannan zancen suka iso gidansu shiga gida tayi itama ta shige gidansu.

Kamar kullum Inteesar nashiga gida ta tadda su Uwar Gwarama da maƙarrabanta a tsakar gida tanata zuzzubs tsumi a roba wanda ta zabga uban flavour a ciki seka ɗauka tsumin arziƙine bakinta ɗauke da sallama tashiga ba wanda ya amsamata Inteesar tayi gurin Innah Uwar Gwarama ta duƙa cikin ladabi tace”Innah sannu da hutawa”.
taɓe baki Uwar Gwarama tayi tare da cigaba da zuba tsuminta ba tare dataji haushiba ta miƙe tafara tafiya bazato taji su Ruƙayya da Bilki sun tintsire da dariya Bilki tace”dolema mutum ya rasa mashinshini tunda an riga angama badakai a waje”.
“kema dai banda abinki waye zeje ya auri ragowar ƙarti yanaji yana gani da kuɗinsa”.
“wallahi sede a ƙare abinsu waje ba’ah wannan hotel ba’ah wancan yawon karuwanci da sunan makaranta”.
wata matashiyar yarinya ce tafito me tsananin kama da Inteesar tace”badai yayata ke yawon karuwanciba sede waccan”.
ta nuna Uwar Gwarama dake zuzzuba tsumi nanfa Uwar Gwarama tashiga bala’i tana cewa”ƙarya akemata ai gaskiya suka faɗa inbanda ta tsaya yawon barikinta aida tini tasamu miji saboda kowa yasan metake aikatawa mijin aurema ya gagareta ba’ah taɓa zuwa nan gidan da koda sau ɗayane gurin Inteesar ba”.
“hakane Iyah muma nan gida zamu barta danba mesonta”.
suna cikin wannan maganar Abbansu ya shigo fashewa Uwar Gwarama tayi da kuka tashiga zayyanemasa ƙarya da gaskiya aiko yashiga jibgar Inteesar da Khadija seda yayi me isarshi sannan ya kyalesu.

AFTER ONE DAY

Sanye Abbah yike da Uniform ɗin masu shara sega wani me irin kayansa gaisawa sukayi yace”a’ah Ahmadu se yanzu kazo”.
“a’ah na daɗe da zuwa ina bayane yanzu gashi inji Oga tin ɗazu yabayar yace abaka inkazo”.
ansa Abbah yayi yana dubawa yaga takardar sallamace daga aikice sosai hankalinshi ya tashi yana ƙoƙarin tafiya office ɗin Ahmad Malam Ahmadu ya dakatar dashi tare da cewa”yace kar abarka ka shiga gurinsa”.
sosai hankalin Abbah yaƙara tashi a wannan ranar duk yadda yaso dayaga Ahmad abu ya faskara dole haka ya tafi gida.

Jiki ba kwari haka Abbah yashiga gida tare da zama kusa da Uwar Gwarama jiki a sanyaye kallonshi Uwar Gwarama tayi tare da cewa”lafiya kashigo hannu na dukan cinya Malam”.
“Ladidi an koreni a aiki”.
Khadijat dake zagayowa dake zagayowa daka backyard ɗin gidan ce wani farinciki duk ya lulluɓeta da murnarta ta shiga ɗakinsu tana ƴan waƙe-waƙenta ɗago kai Inteesar tayi daga karatun Alqur’anin da takeyi tare da cewa”meyafaru naga kina murna”.
“Abbah aka kora a gurin aikinsu”.
“shine kuma kike murna”.
“eyi ai gwarama da aka koresa daga aikin koba komai a dena banbantamu da ƴaƴan so shima yaji yadda mukeji a zuciyarmu na abinda yikemana kamar ba ƴaƴansa ba duk ya tsanemu ni wani lokacin har tinani nike anyako Abbah ne babanmu”.
“Khadija meyasa kike irin wannan ne koba komai ai mahaifinmune kidena irin wannan inkuma ba hakaba zamu ɓata”.
“yi haƙuri Aunty”.!!!!!!

 

Title Namijin Duniya
Book Type          Txt
Live On Aihausanovels
Released Date 16th April 2023
Author Real Eeasha
Uploader Mr. Aihausa
Phone No:          Nil
Group          

 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Danna Inda Aka Saka Download Here

 

 

Back to top button