Hausa novels

Fatalwar Delu Part 1

Fatalwar Delu Part 1

 

🤡 FATALWAR DELU 🤡

 

Part 1

 

Kingboy Isah 👑

 

Short story

 

 

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

 

 

🤗 Kunsan dai na tsoro ne ko? To muje zuwa.

 

 

Bayan na kai lomar karshe ta tuwon da muke ci, wanda ya sha yajin daddawa irin ta mutanen kauye na dubi abokina Bukar hade da kyalkyalewa da dariya, tukun na kada kai na ce, “Haba abokina wannan labari na ka ai ya fi kama da tatsuniya, shin wa ya fada maka fatalwa gaskiya ce? Ko ka taba ganinta da idanunka ne?”.

 

Ya dubeni da kyau fuskarsa babu alamun wasa kana ya ce, “Abokina wallahi gaskiya nake fada maka, a wannan gari namu akwai fatalwa da ta addabi mutane, kai a takaice ma kashe duk wanda ya shiga hannunta take yi. Naji ni ban taba ganinta ba, domin duk wanda ya ganta baya iya bada labarinta, don kuwa ba zai kai safe da rai ba.

 

Na kara kura masa idanu sosai, na fuskanci iya gaskiyarsa yake fada mini, amma sai na sake tuntsirewa da dariya. Wanda hakan ya sashi canza fuska, na dade ina dariya duk da na fahimci canjin fuskar a tare da shi. Daga bisani kuma na fara sude hannu ina yar dariya na ce, “Yi hakuri abokina mayar da kwanukan abincin nan gida, ni bacci nake ji wallahi na gaji da jin labarin fatalwar nan taka domin na kasa gaskata shi”. Yayi kwafa kana ya mike tsaye ya kwashi kwanukan abincin da kofin ruwa ya fita.

 

Bukar abokina ne da muka hadu can garin Inugu wajen neman kudi, yanzu ya dawo ganin gida garinsu, kasancewar mun shaku sosai yanzu da zan wuce gida garinmu, shine ya nemi in biyo ta garinsu mu gaisa. Da nayi niyar wucewa amma yanzu magariba tayi dan haka ya bukaci inyi hakuri in kwana, wai garin nasu babu kyau in dare yayi. Shine yake bani labarin wai wata Fatalwa Delu mai kashe mutane idan suka fito da dare a garin nasu. Ni dai ko kadan ban gaskata labarin da yake bani ba, don haka da fitarsa na haura saman katifarsa inda ya nuna min a matsayin makwancina, na kwanta hade da fiddo wayata na hau jin waka.

 

Misalin karfe tara ina sauraron waka ni kadai a dakin, a hankali na fara jin ana buga wani abu da karfi, gam! gam! gam! Daga bisani kuma na fara jin gudun mutane ya cika gari tamkar na dawaki, gaba daya garin ya dauki hayaniya. Nan da nan na mike tsaye na fito waje, kasancewar kauye ne, ko da na fito banga kowa ba da alamu masu gudun a dan nesa dani suke. Na juya zan shiga dakin kenan na jiyo gudun kato, ina waigawa na ga mutum ya rugo a guje inda nake, sai da ya matso kusa na kula ashe Bukar ne a sukwane tamkar wanda ya ga mutuwa.

 

Fatalwar Delu Part 1

 

“Kai gudun me kake lafiya?” Na fara tambayarsa, shi ko bai saurareni ba ya fada daki a guje. Na waiga hagu da dama banga ko mage ba, a zuciyata ina tunanin abinda yake wa gudu. Banyi aune ba sai ji nayi anja hannuna da karfi cikin dakin, saura kiris in fadi har kasa. Bukar ne da wannan sakarcin, na kalleshi a fusace yayin da yake ta faman makala sakata domin rufe dakin, “Bukar Lafiyarka kuwa? Me kakewa gudu ne haka, dallah ji yadda ka jawoni saura kadan ka kada ni”.

 

Ina binshi da kallo bayan ya kulle dakin, ya saki ajiyar zuciya kana ya zaune a bakin katifa yana haki domin ya sha gudu yace, “Wai kai ka zata duk abinda nake fada maka karya ne ko? To wallahi bari kaji mu a garin nan anfi shekara 5 babu wanda yake kara fita waje daga gida idan har karfe 9 na dare yayi”. Ya dan lumfasa kana ya ce, “Bakaji karar gudun mutane ba? Ai saboda karfe tara tayi shine kowa yake kokarin ya gudu gida ya kulle saboda gudun gamo da wannan mummunar annobar Fatalwa Delu, domin gamo da ita tamkar gamo da ajali ne”.

 

Na yi shiru ina sauraren bayanin nasa kana na ce, “Wai kana nufin wannan karan gudu da naji da hayaniya duk ba wani abu akewa gudu ba face a shiga gida a rufe saboda tsoron fatalwa?”. Bukar ya ce, “Ka ga ni dai aje naji baka yarda da labarin duk da na baka ba, rokona daya shine Dan Allah Dan Annabi karka fita waje cikin dare”. Na kalleshi cikin rashin fahimta hade da cewa, “Idan Bahaya ko fitsari ya kamani a daren fa?”. Da sauri ya nuna min bayan kyaurensa, “Ga fo nan, kayi a ciki da safe sai a zubar a jeji”.

 

Ai bansan lokacin da na bushe da dariya ba, wani bangare na zuciyata na kara tabbatar mini, duk zancen da yake gaskiya yake fada min, “Bukar fo ne fa na bahayan yara”. Ya ce, “To ba ka ganshi kato ba, ai mu nan duk yawancin gidaje zaka samu da fo a daki, don wasu ko a cikin gida basa yarda su fito waje in dai karfe 9 ta wuce. Yanzu ma da ka ganni a guje bayan gari naje na yo bahaya, shine na yi gaggawar dawowa da naji ana buka kararrawa”. Dariya na tuntsire da ita bayan gama jin dogon bayanin nasa, munyi ja inja da shi sosai a kan na ce wallahi ba zanyi kashi ko fitsari a fo ba in ya kamani fita zanyi, daga karshe da na lura ya bata rai sosai sai na ce masa naji zanyi a fo din amma a raina babu wannan batu bukata na kamani fita zanyi.

 

 

A haka muka kwanta na saka mana india hausa a wayata muna cikin kallo bansan lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba. Yanzu da na farka na ga shi kansa Bukar yayi bacci bayan ya kashe wayar. Cikina ne ke wani irin murdawa ba shakka bahaya nake ji, hala dai alalar da na ci a hanya ce ta bata min ciki. Da sauri na lalubo wayata na kunna, karfe biyun dare agogo ya nuna. Bayan na haska fitila nan take idanuna sukayi arba da katoton fo dake ajiye a tsakar daki harda murfinsa. Dariya nayi a raina na ce, wato yanzu saboda kazanta da kawai sai in jawo fo din nan in tsugunna a kai na bulbula abinda ke cikina kuma in rufe duk wari har sai gari ya waye? Kai ina ba zai yuyu ba.

 

Da hanzari na yunkura domin jin cikina ya sake murdawa, kai tsaye na dau buta na bude kofar ba tare da fargabar komai ba nayi waje hade da ja masa kofar na rufe. Kasancewar garin kauye tafiya kadan nayi na samu wajen kebewa, ai kuwa na ajiye buta a gefe na tsugunna na fara sauke abinda ke addabata a kasa. Daga kai nayi garin tsit kake ji sai kukan gyare, ko ina ka waiga sai itatuwa babu alamar hasken fitila ko kadan balle ka saka ran ganin mutum. Ni kuwa hankalina kwance tamkar ina bandakin gidanmu nake gudanar da lamurana. Ba zato ba tsammani sai ji nayi anyo jifa saitina, da hanzari na haska wajen da nake tunanin ta nan jifar ta fito amma sai na ga wayam babu kowa.

 

Da kashe fitilata ba’a fi sekonni ba naji an sake yo wata jifar, ni kuwa a lokacin kokarin yin tsarki nake. Cikin daga murya na ce, “Waye mai yo jifar nan, baka da tarbiyya ne?”. Shiru ba’a amsa ba lokacin ne na mike tsaye na dau buta hade da nufar hanyar da zata mayar da ni cikin gari shagon abokina, domin na danyi nisa kadan da gidajen mutane. Ina cikin tafiya kwatsam sai ji nayi jariri ya kwala kuka a bayana. Nan take ja na birki na tsaya hade da waigawa inda naji kukan ya fito. Duhu ne rudun dan haka na haska fitilata, a hankali na fata takawa har na isa wajen da nake jin kukan na fitowa, tsayawa nayi cik! Ina kare musu kallo. Jariri ne ajiye a cikin tsumma yana ta tsala kuka, a gefe kuwa wata yarinya da bazata wuce shekara 8 ba fuskatar fari fat, sai kace tayi wasa da gari, ina haskata na ga ta zubo min manyan idanunta masu kalar ruwan dorowa…………………

 

🧐

 

Sorry to say idan na lura ba’a so ba zanci gaba ba, domin free ne, like and comment

Back to top button