Hausa novels

Harijin Sarki Page 3 Romantic Hausa Novel

Wayewar garin tazo mata da wani yanayi na sanyin jiki da mutuwar gaɓoɓi tunda tayi sallah take zaune saman sallaya batasan me takeyi ba addu’a ko kuma zaman banza, 5:45am wayarta ta fara rurin neman agaji Miƙewa tayi cike da zullumi ta sani mutum ɗaya ne me kiranta yanzu domin kuwa shine suke da alƙawari dashi, shi ɗin ne kuwa ta danna accept yace “Ina kofar gidanku jirgin mu zai tashi shida da rabi ne Samha” amsa masa tayi da “to Yallaɓai” ba wani ɓatawa kanta lokaci tayi ba shigar tayi ta gargajiya ta gyara gashinta ta yafa mayafinta a kafaɗarta ta ɗauki jakarta da trolley bag ɗinta ta fito ta ishe Granny zaune bisa sallaya ta rusuna s gabanta ta dafa kanta tare da sanya mata albarka ba tare da tayi furuci ba ta haɗe hannunta alamar fatan alkhairi ta mike ta fito janye da trolley bag, can nesa da farfajiyar gidan nasu ta hangi motar da Dr Junaid yake ciki ta ƙarasa ya fito ya buɗe mata motar ta shiga shikuma yaja trolleyn yasa a but yaja motar suka tafi. Suna tafe suna yar hirarsu har suka je filin jirgin saman suka zauna a mazauninsu babu jan lokaci jirgi ya ɗaga zuwa Rabat, zuciyar Samha cike zullumin da ta kasa sanin dalilinsa, takas da rabi suka sauka motar asibitin tazo ta ɗaukesu haɗuwa da tsaruwar asibitin shine yafi komai ɗaukar hankalinta ta sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da shugaban asibitin ya miƙo mata hannu sukayi musabiha tare da nuna farin cikinsa da samun ƙwararriya kuma jajirtacciyar ma’aikaciya irinta, wadda ta sadaukar da rayuwarta da lokacin don rayuwar al’umma, da wannan suka rankaya suka isa katafaren office ɗin nata ta kalli office ɗin ta kuma Kallonsa ta ƙara kallo a ranta tace “Barakallah” files files ya ɗebo daga ma’ajiyarsu ya kawo mata gabanta ya zare guda ɗaya ya mayar dashi gurin daya ɗebo waɗancan ya zauna yana mata bayanin komai dalla dalla duk ta gane me yake cewa abinda takeson sani meye dalilin zare wancan file ɗin meshi ya mutu ne ko kuwa akwai wani bayani ne na Musamman a kansa” tambayar da tayiwa Zuciyarta kenan tana me kallon sashen da file ɗin yake. Dr Razeen ne ya fahimci inda hankalinta ya karkata ya koma ya ɗauko files ɗin yace “Kullum zuciya tana inda aka kangeta da zuwa Dr Samha wannan file ɗin ba na kowa bane face na wani babban mutum a garin nan wanda yake da matuƙar daraja, shi wannan mutumin ya kasance yana fama da wani irin ciwo bauɗaɗɗe kuma ɓoyayye, yana ɓoye ciwonsa a cikin izzarsa yana bayyana ƙarfinsa a cikin rauninsa saidai kuma abin kullum ƙara cin tura yakeyi, wannan mutum Mai daraja ya kasance lamba ɗaya a babbar masarautar nan ta ZIRKAN wato mai Martaba Sarki Rashid Ibn Fayyad Al Zirkan” Ɗagowa tayi da sauri ƙirjinta na bugawa tace “Sultan Rashid Ibn Fayyad Al Zirkan?” Jinjina kai yayi yace “Ko kinada labarin matsalarsa ne?” Girgiza kai tayi tace “Bansan komai game da duk wani abu daya shafi Rabat da Qasr al-Malik ta Zirkan ba, Ni mutum ce me son bincike akan tarihin masarautu da abinda ya shafi masu madafin ikonta, shin zan iya samun ƙarin sani a wajenka Yallaɓai?” Numfasawa yayi yace “Ok ki bi a hankali zakisan komai Samha” da wannan ya fice bayan ya maida File ɗinnan gurin daya ɗaukoshi cike da rashin kuzari ta fara duba tulin files ɗin dake gabanta, kowacce damuwa dai irin wacce ta baro a Fess ce babu wata sabuwa, kwantar da kanta tayi bisa kujerar tace “Ya Allah!” Lumshe manyan idanunta tayi taci gaba da juyawa bisa kujerar, sabon gurin aiki sabon bincike sabon labari, tabbas Zuciyarta ta kwaɗaitu da son sanin wani abu game da wannan file da akace mata na Sultan Rashid ne zataso sanin meye abinda yake damunsa wanda yake ɓoyeshi a cikin ikonsa yake lulluɓw rauninsa da isarsa tabbas sai tasan meye wannan. Da wannan ta tashi tayiwa kofar office ɗin nata key ta zagaya inda file ɗin yake takai hannu ta ɗaukoshi ta koma bisa kujerar ta ta zauna, ruhinta na gargaɗinta buɗe wannan file Zuciyarta na umartarta da buɗewa haka tayi ƙarfin halin yarda da shawarar Zuciyarta ta buɗe file ɗin ta kuwa zabura ta miƙe da sauri ganin wani irin jan haske ya fita daga jikin takardar farko dake bisa file ɗin take taji wata murya tana cewa da ita, “Barka da shigowa Masarautar Zirkan ƙarƙashin mulkin Sultan Rashid Ibn Fayyad Al Zirkan, tunda kika buɗe wannan kundi dole sai kin kai kanki gareshi yake wannan ƙwararriyar likita me karambani, kar kiyi tambaya ki tafi kai tsaye, Masarautar ZIRKAN tana hsmadargudu maso gabashin Morocco, inda rana ke da zafi kuma iska ke kaɗawa da ƙura me ɗauke da danƙo na turare. Masarautar ta samo asali daga zuriyar Idrisawa, amma yanzu ana mulke da ita da sabon sarki wanda ya fito daga reshen zuriyar da aka manta da ita shekaru aru-aru, Qasr al-Malik ta Zirkan tana tsakiyar birnin Amzir, ta cika da Marmara fitilun zinariya, da fale-falen Andalusian blue tiles. A cikin fadar akwai zauren manyan baki (Majlis al-kabir) inda akewa mutane jawabi. Gidan Sarki inda iyalansa ke rayuwa fadar Harem wurin matan Sarki da ƴaƴan sarauta, yake wannan Ƙwararriyar likita kiyi sani wannan bayani ina miki shine don haska Miki hanyar tunkarar shafin ƙaddarar da kika buɗo da hannunki, dole Zakije fadar Zirkan zaki haɗu da kaddarori masu kyau da marasa kyau, tunda kika buɗe wannan kundin ƙaddara kin shirya”………..

Back to top button