Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 32 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                           THIRTY-TWO📍

     “HIV?!”…..

Ta maimaita ba ko alamar mamaki….

    “You heard me right!”….

        “Ok”…

Ta fada tana kokarin tashi daga gadon…..

Dan turata yayi ya maida ita kwance, ba alamar wasa yace;

      “Where the hell do you think you’re going? Ina fadamiki kinada HIV you’re telling me ok kamar wacce akace malaria na damunta!”…..

         “Who cares?”…..

Ta fada murya kasa kasa…..

      “Who cares? For real? Are you out of your senses? Ko kinsha wata kwayarne kafin ki fito? Toh ki bude kunnuwanki da kyau ki saurareni you’re not just suffering from HIV, you’re having a kidney failure too!”………..

Lumshe idanunta tayi chan kasa maqoshi ta furta ‘ya salam’…….

     “Kidney failure?”…..

    “Yes, wasu kwayoyi kike sha da sukayi damaging kidney dinki haka?

         “Kwaya?”….

Ta sake maimaitawa absent mindedly……

    “Idan ina magana kina maimaitawa without concrete answers Allah zan babballaki a gurinnan in zubar a shara nonsense!”……

Shiru tayi batace komai ba dan she was just speechless, ko kwakkwaran tinani ta kasayi sannan har a lokacin ta kasa comprehending abinda yace……..

A hankali ta sake tashi dan tariga tayi making up mind dinta gwara ta tafi cuz she needs space to digest what he said, wai HIV da kidney failure kamar a film? Nooo…..

     “Why’re you so stubborn? Bakida lafiyan ma bazaki nutsu ba? Get back to the bed now!”….

Deen ya fada a tsawace……

     “ Ya isheka haka mallam! Who the hell do you think you’re are da zakazo kanamin ihu anyhow, why’re you so jobless to be so concerned about people’s life? Idan bakada abunyi I can help you with a job, bani hanya in wuce!”……

Sosai maganarta ta dakesa, dukda rashin karfin jikinta da kuma yanayin sanyin muryarta ya hana maganar fitowa yanda takeso, amma maganganunta sun masa zafi, wai shi ake cewa jobless harda she can give him work, imagine! A take yaji ya fara loosing kansa abunka da wanda zuciya ke kusa dama, sai ya fara fadin duk abinda yazo bakinsa……

      “Bantaba danasanin sani wani a rayuwa kamar yanda nake danasanin saninki!… See let me make this clear to you tinda kika shigo rayuwata kika tarwatsa min nutsuwa da walwala da jindadina, baki haifarmin da komai ba sai masifa da bala’i da takaici! I can’t believe I’m having sleepless nights for a whore,drunker like you! Da zan iya dawo da komai baya dana goge haduwa dake a tarihin rayuwata, I don’t know why I’m wasting my precious time for someone who is about to die soon cuz you can’t survive this with your stupid ways! I don’t know who your father is but I know harya mutu bazeyi irin arziki na ba, so give the job to yourself you need it more, lastly na cire hannuna daga lamarinki!, I promise you ko me kama dake nagani I won’t look twice sannan ko a hanya muka hadu karki sake ki nuna kin sanni ko da ido ne, now I’m saying goodbye to my problems! go and die!”…..

Yana fadin haka ya matsa yana bata hanya…….

Sandarewa tayi a tsaye tsabar shock din data shiga, tunda take baa taba fadamata maganar daya mata zafi irin wannan ba, tsabar yanda maganar ta daketa sai taji komai ya kafe mata, ga tarin maganganu a bakinta amma maganar taki fita, she thought she just dislike him amma yanzu tagane this is more than dislike, it’s what we called ‘intense hate’ tsana sosai, bata tabajin ta tsani mutum kamar yanda takejin tsanarsa har kasan zuciyarta ba, yaci mata mutunci iya cin mutunci da ko a mafarki bata taba tinanin wani ze kalli idanta ya fada mata abinda ya fadaba kome tayi, hardasu ce mata whore(karuwa)? Kamar ya taba kamata da wani?…….

        “I said GET OUT!!!”….

Firgit ta dawo daga maganar zucin da take, tafiya tashigayi a hankali harta karasa bakin kofar, sai a lokacin ta juyo ta kalleshi tace;

       “Let me make my own confession too;I hate you! Natsaneka irin tsanar da ko kasheka naga zaayi zan bada gudunmawata, I hate you is an understatement!, dama bani na gayyatoka cikin rayuwata ba kaika gayyota kanka amma dukda haka zan bace bit daga rayuwarka kamar yanda ka bukata, don’t forget that I hate you so much, bye!!”……….

Tana fadin haka ta fice holding her self so tight not to breakdown………..

        “Eesha dama ba soyayya kuke da Doctor ba duk bragging din da kikeyi?”…..

Billy da tun jiya abun ya tsaya mata arai tun bayan sundawo daga gidan mami ta tambaya……

     “Duk bake kika janyo komai ba? Meyasa daga ganinta kawai zaki rungumeta harda taba mata gashi!”……

     “Toh meye danna rungumeta, mace ce fah yar’uwata ba namiji ba, kidaiyi bincike ki gane abinda yasa yayi hakan, banaso inyi jumping into conclusion da nace wani abu”…..

    “Gwara kiyi shiru in kinsan ba alkhairi zaki fada ba, amma meye a tsakaninsu daya daga hankalinsa haka akanta?”…..

    “Nima abinda yake damuna kenan”….

   “Yo meye a tsakaninsu inba soyayya ba? Ana tamin wulakanci akansa ashe yana chan shi wata yake so”…..

Umaima da tundazu take dariya akan maganganunsu tasa baki…..

      “Stay away from this umaima, he’s mine alone, ni nasan ba santa yake ba”…..

     “Keep deceiving yourself, ko ki yarda ko kar ki yarda sonta yake”…..

Ta fada tana fashewa da wani mugun dariya….

Rufeta da duka eesha tayi tsabar takaici billy na tayata….. 

    Yana tsaye a inda ta barshi hartayi slamming door din bayan ta fita, sai yashiga tambayar kansa ‘can he really let her go a wannan condition din?’… ‘Does she really mean what she said, wai ta tsaneshi?’… Toh ai shi bece ya tsaneta ba, sai yakejin maganganunta kamar sunfi nashi zafi dukda abinda ya fada yafi nata yawa, babban abinda yake masa ciwo kuma yanda take jaddada masa ta tsanesa, babu wanda ya taba gayamasa ya tsanesa despite the way he always mess up sai yau wata da besan WACECE ITA BA take gayamasa zata iya bada gudunmawa a kashesa, how cruel!…… Amma kuma sai yaji he can’t let her go dukda tace ta tsanesa, tausayinta yakeji har cikin jikinsa kodan health condition dinta, she needs someone to be there and he wants to be there, wata zuciyarce tace masa ‘she hates you!’  dayar kuma tace ‘she needs you’…. Rasa abunyi yayi at the end ya bawa daya zuciyar dama, kawai ya fita yabi bayanta da sauri hoping to see her karta bace daga rayuwarsa kamar yanda ta fada…….

         Sun kai su gurin hamsin ko wannensu zaune a kasa, mutum dayane kawai akan wata kujerar karfe dake dauke da zanen maciji a ko ina…….

    “Boss ataimaka a bani last chance, nayi alkawarin zanyi komai yadda ya dace”…..

Daddy ya fada yana gyara zamansa a kasa…..

 Nan sauran yan gurin sukasa baki aka shiga bawa boss din hakuri akan a bawa daddy last chance….

     “Ya isa! Kowa yayi shiru, zaa baka last chance, amma kasani idan aka kara samun matsala hmmm!”…..

Wanda ke zaune akan kujera ya fada yana karkada kafa……

     “Na amince! Nayi alkawarin ba za’a kara samun matsala ba”…..

    “Sai kaga text message, tashi kaje!”……

   “Nagode boss”….

Daddy ya fada yana mikewa sannan ya fita da baya…..

         Yana zaune har lokacin yana jiran fitowarta dukda yaga wasu sun fara fitowa sai yayi tinanin kila bata gama bane, kiran daddy ne ya shigo wayarsa, ya dauka yana kara wayar a kunne tareda fadin……

     “Are you ready to explain yourself dad?!”…..

    “Son ba abinda kake tinani bane!”….

    “Dad in baka shirya fadamin gsky ba kindly stop calling”……

     “Naji zan fadamaka gsky, kana ina yanzu?”….

     “Na fita!”….

   “Ita fah?”….

   “Who?”….

    “Daughter”

    “Itama ta fita!”….

   “Ina taje? Ko school taje? Naga zaa fara exam a school dinsu yau”….

    “Bansan inda taje ba!”….

Haka kawai ya samu kansa da kin fadawa daddy gsky…..

     “ok idan na dawo zan kiraka sai kazo muyi magana”……

     “Alright”….

Ajye wayar yayi har lokacin hankalinsa yaki kwanciya da daddy, ita kuma ya mata tambayar duniya tace batasan abinda yake faru ba…..

       A hankali take tafiya kasancewar batajin karfin jikinta har lokacin, haka ta daure harta karasa bakin gate din asibitin, rasa yanda zatayi tayi dan jakarta na motar khaleel bare ta hau cab ta wuce ko kuma ta kirasa a waya, wata ce tazo wucewa fortunately ta mata sallama, sai tayi using opportunity din tace ta ara mata wayarta tayi kira, ba musu kuwa ta bata, number khaleel ta kira dan ta haddaceta da dadewa, bugu biyu ya dauka ta masa bayanin inda take bayan ta karanta sunan asibitin, mikama matar wayarta tayi ta samu guri ta jingina tana jiran isowar khaleel.

 Tana tsaye taji taku a gefenta, kin juyowa tayi harya karaso inda take…. 

Kallon yanda ta dauke kai yayi, ya sauke ajiyar zuciya, calmly kamar ba arrogant Deen ba yace;

     “Are you lost baby girl?”….

Juyowa tayi da sauri tana karyata zuciyarta da take fadamata muryarsa taji, sai kuwa taga shi dinne abinda ko a mafarki batayi tinanin zata kara ganinsa ba duba da cin mutuncin daya mata…..

Juyawa tayi ta fara tafiya ya bita da sauri har suka bar asibitin… 

Ganin yaki daina binta tajuyo rai a bace tace;

    “Wai kai wani irin mayene? Ba yanzu kace ka fita daga harkata ba, why are you following me again?”…

    “Because you’re sick, bazan iya barinki a wannan condition din ba, but I promise you kina samun lafiya zan fita daga rayuwarki for real”…..

    “Hold your promises to yourself you liar!”…..

   “Relax, shouting isn’t good for your health okay?”…

Ya fada yana kamo hannayenta…..

      “What’s your problem with my health, idan na mutu who cares?!”…..

     “I do care, I know you’re angry for all I said, but trust me I don’t mean it”……

Dukansa tashigayi a kirji at the same time tana kokarin kwace hannunta……

Kin sakin hannunta yayi saima marin kansa daya farayi da hannunta ganin neman abinda zata wuce takaicinta akai take……

    “Idan dukana zeyi calming dinki down you’re free to, idan marina zakiyi I promise I won’t complain indai zakiji sanyi a ranki, idan kinaso kiyi fashe fashe ne I can take you to my biggest mansion ki fasa komai, I promise I won’t say a word, just tell me abinda kikeso in miki ki wuce”……

      “Let go off me! Go away from my life, go away from your problem”…….

      “Count that out baby girl, I agreed you’re my problem but not just ordinary one, you’re my ‘pretty problem’ that I’ll never get tired of, bring me more problems zan karba da hannu bibbiyu, just allow me to take care of you baki da lafiya sosai”…..

     “Banaso! Banaso! Why are you wasting your precious time on a whore and drunker like me?”…..

      “I never mean it, ni nasan keba karuwa bace, and your kidney problem isn’t from shaye shaye”…….

     “You’re a bloody liar! Ka sakeni!”…..

     “It’s ok zan sakeki, but promise me you’ll go to the hospital straight from here!”…..

     “Bazan jeba, meye amfanin zuwa nida zan mutu very soon, is that not what you said?”…..

Dafe goshinsa yayi cikin dana sani, wai ya akayi wayennan mugayen kalaman suka fito daga bakin sa?, gashi girman kai ya hanasa ya bata hakuri sai kokarin kare kanshi yake…

      “Bazaki mutu yanzu ba, you’ll leave long, I’ll do anything to make sure you’re alright, I’ll give you my kidney, if it takes in baki duka biyun zan baki, bazaki mutu ba believe me”……

       “Banaso! Banaso! I hate you so much, go away from my life!”….,.

Rungumeta yayi trying to control himself karya cutar da ita bayan abinda take ciki, shi kadai yasan yanda I hate you dinnan yake dakar zuciyarsa……

     “Shhhhh! Don’t provoke me baby girl!”….

Ya rada mata a kunne bayan yayi hugging dinta……

Nitsuwa tayi kamar dama hug din take jira yayi calming dinta down……

Murya chan kasa ya sake rada mata;

     “Will you marry me?”….

Itama murya chan kasa kamar wacce zata fadi abin arziki tace;

     “Ko maza sun kare gwara in saura ba aure, besides me zakayi da HIV patient, and the last time I checked we were not dating”…..

    “I just want to marry you to protect you because it’s only a Doctor that can deal with your health condition, I never loved you too!”…..

    “I have someone I love and we’re all HIV patients, kaje ka nemo me lafiya daidai kai!”…..

Tsabar yanda maganar ta dakeshi wai she has someone she loves besan sanda ya hadata da bangon dake kusa dasu ba, hannunsa ya daura a wuyarta amma be shaketa ba, cikin daga murya kamar wani zautacce yace;

     “And who tell you kina da HIV dagaske?!”…..

Fashewa tayi da kukan da taketa rikewa tun dazu dan ta gaji da wannan mugun halin nasa abun kadan ya shake mutum, itama cikin daga murya tace;

     “Ka kasheni kawai ka huta dama rayuwar ta isheni, ka kasheni nace!!”…..

Da sauri ya zare hannunsa daga wuyarta yayi cupping cute face dinta sannan ya matso da fuskarta dab da tata har karan hancinsu na gogan na juna…

     “I’m sorry baby girl, I’m sorry! you’ll live long, I promise”…

Ya fada yana lashe hawayenta…. 

So take ta hanasa amma ta kasa saima wani hawayen dayake zubomata, shi kuma yaki dena lashe mata fuskar saboda taki dena hawayen……

A hankali yaji abinda yake dannewa na neman fin karfinsa saidai it’s a promise he made to himself baze kara barin emotion yayi taking over him ba, but the question is can he?…… 

A hankali ya dora hannunsa a bayanta yana dan shashshafata…..

Wani iri taji kamar ana mata tafiyar tsutsa, abin dai ba dadi, saurin turesa tayi ta kwasa a guje tabar gurin, batasha wahalar turesaba dan he was already weak……

Luckily tana zuwa gaban hospital din taci karo da motar khaleel da zuwansa kenan yana tinanin ta ina ze ganta, saurin shiga motar tayi ganin ya biyota tacewa khaleel yaja da sauri su tafi….. 

     “Lafiya? Meya faru?”…

Khaleel ya tambayeta dan shi be kula da Deen ba….

    “Bakomai, meka gani?”…..

    “Me kika zoyi a asibitin nan”…..

   “Kace naki yarda muje hospital akan headache dina, shine nazo akan haka”….

Gyada kai yayi yace;

    “Oh that’s good! But what happened to your lips?”..

Saida gabanta ya fadi daya mata tambayar amma ta dake tace;

    “What about it?”….

    “It’s so red and somehow”….

Sauke madubin side dinta tayi dan ta duba lips dinta, ta kuwa tabbatar da abinda ya fada, amma ya akayi haka? Wanchan dan iskan ya taba lips dinta ne toh? Tasan babu inda be lashe mata a fuska ba but she can’t recall him kissing her, tayaya hankalinta ya gushe da har takasa gane komai?……

      “Jambaki nasa”…..

Ta fada cikin kokarin kare kai……

     “Ok, yaushe kika bar school bansani ba?”…..

Shiru tayi taki basa amsa dan batasan me zatace ba….

Deen na biye dasu har suka karasa gidan daddy basu san yana binsu ba…. 

Parking yayi a dan nesa da gidan, ya bada few minutes sannan ya nufi gidan shima, kwankwasawa yayi me gadi ya bude masa ya shiga….. 

Da daddy yaci karo, fitowarsa kenan daga part dinsa… 

Zaro ido daddy yayi yace; 

     “Wa nake gani haka kamar Doctor? Dama baka mutu ba?”………

Kallon mamaki Deen ya masa bece komai ba…..

Ganin irin kallon da Deen yake masa yasasa saurin gyara maganarsa da fadin;

      “Naji mummunan labari ne akan an kona prison din da kake”…….

     “Eh, fortunately enough ban mutu ba!”….

Deen ya fada yana bin daddy da kallon tuhuma dan sam be yadda da yanda yace masa be mutu ba? Sannan kuma ya akayi yasan an kaisa prison bayan case din was so private…….

     “Masha Allah, na tayaka murna son, Allah ya kara kiyaye gaba”…..

    “Ameen dama nazo gaisheka ne”….

    “Toh mushiga daga ciki”……

Suna zaune suna dan taba hira sukaji sallamarta….

Turus ta tsaya ganin Deen a parlourn, a ranta tana fadin ‘wannan wani irin maye ne, ko ina sai yabi mutum?’……

     “Karaso mana daughter, ya kika tsaya kina kallonsa ko kin sansa ne?”……

Girgiza kai tayi alamun bata sansa ba sannan ta karasa cikin parlourn ta nemi guri ta zauna tace;

      “Gani”…

     “Daddy zan tafi, sai anjima”….

Ya fada dan haka kawai yaji yanaso ya labe yaji kiran daya mata a matsayinta na budurwar dansa….

   “Yauwa son, bakazo da mota bane insa akaika?”…

       “Nazo da mota a waje nayi parking”….

     “Ok toh, ka gaida gida”…..

        “Alright”….

Fita yayi ya bar kofar a bude kadan yanda daga nesa bazasu gane a bude take ba, ya kuma kasa kunnensa sosai dukda yanada karfin ji dama……

       “Ya maganar auren mu dake?”….

     “Wani irin aure?”…..

 “Auren da akayi niyar daurawa jiya da khaleel yazo ya bata”…….

    “Ni bansan wannan ba, I can’t marry you!”….

Murmushi yayi yace;

    “Ko bazaki aureni ba I need something from you and it’s really urgent!”…….

     “Wai me kake nufi ne daddy?”…..

Wani abu ya dauko da niyar shaka mata yaji an buga masa abu a ido, murza idonsa ya shigayi ko kafin ya bude ido bata dakin, tini Deen ya dauketa ya fita da ita….

Yana rike da hannunta har suka karasa gate sai wani cijewa take, shikuma yaki sakinta….

     “Ki denamin taurin kai, I’m trying to save you! Then I’ll come back for him later, saiya fadamin abinda yake shiryawa akanki, tsohon banza kawai!”…

Haka yayita mata fadan ta nitsu har suka karasa gate, me gadi da besan komai ba ya bude musu kofa suka fita…. 

Suna fita daddy ya fito da sauri waya rike a hannunsa har lokacin baya gani sosai dan ba karamin dakar idonsa abin yayi ba…

Saurin karasawa gurin me gadi yayi yana tambayarsa….

     “Ina fatima zainab”..

   “Ta fita”…

  “Ita dawa?”..

Dan yasan dole wanda ya buga masa abu ne ze fita da ita, haka kawai kuma zuciyarsa ke gayamasa Deen ne dan yana sane da tantirancin yaron..……

     “Ita da bakon dayazo dazu”…

Bece komai ba ya juya da sauri dan ya gane Deen yake nufi, toh me yaronnan yake nufi? Kodai ya sake gano wani sirrin nasu ne? Toh amma ba ya fita ba? Ya akayi ya dawo, inko ya gano abinda suke shiryawa toh akwai babbar matsala, dole ya bakunci lahira a yau dinnan!…..

Ganin yana bata lokaci ya sashi saurin daga waya ya kira wata number……

       “Yauwa kiran da nake maka kenan”…..

Ya fada yana gyara zaman wayar a kunne…..

      “Good! A kashe shi, ita kuma akawo min ita yanzu!!”…..

~Uniquebarakancy~

Back to top button