Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 2

 ZUCIYA DA KWANJI 
BOOK 1___2

Na Maimuna Idris Sani Beli

MUN TSAYA A INDA:  

Shekarunsu biyu a haka, Fatima ta kammala service, ta kuma nemi izinin kawu na neman aiki. A nan ne kawu ya yi ta maza ya ce sam bai san wannan zance ba, ya ma ba ta wata guda ta fito da miji, idan ba haka ba sai dai ta ji taron daurin aureta. Fatima ta dauke maganar kawu wasa, har ta bari watan ya share a wasa, sai rana tsaka ta ga taron jama’a a gidansu, labarin ya zo mata an daura aurenta da Alh Sulaiman.

ZAMU CI GABA DA LABARI:

Tarihin auren ke nan, wanda labarin zamansa sam babu dadi, Alh sulaiman ya cimma burinsa na mallakar “KYALLI HUDU”. Sai dai kash! Kyalli daya ya hana shi natsuwa, wato fatima, ta hana shi kwanciyar hankali sam. Ta tarwatsa dukkan farin cikin da sauran kyallin suka samar masa. Ga shi Allah ya jarrabe shi da masifar kaunarta, shi yasa ta ke dama garinta a sha yadda ta ke so ko da babu gasara balle sukari. Duk abin da Fatima ta shimfida Ko ba ya so sai ta aiwatar, ga jarabar kasaita kamar ‘yar sarkin santanbil, sai ya yi magana hamsin Fatima ba ta tsinka daya ba, idan ma ba ta so ba, sai su kwashi kwanki ba su ga juna ba, don babu ruwanta da duk wani abu da ya shafe shi, cinsa ko shansa da kula da dawainiyarsa duk ta sallama wa masu yi masa hidima. Kamar yadda bai isa sanin wani abu game da shige da ficenta ba bu ruwanta da daukar damarsa, ko yana cikin gidan sai dai ya hangi ficewarta da mota, ko kuma duk sanda ya shigo gida ya binciki masu gadi, “Hajiya na ciki, ko ta fita?” Su kansu ma’aikatan gidan hakan na bala’in bakanta masu rai, ballantana danginsa wadanda Fatima ba ta dauke su a bakin komai ba, ko gidan suka zo kashi ma ya fi su daraja a idonta. Gaisuwa kadai ke hada su, babu duka babu zagi, amma babu ruwanta da mutum har ya karaci kwanakinsa ko wuninsa ya bar gidan.

Mahaifiyarsa ce kawai ta ke samun arzikin kallon kirki, shi ma a wani yanayi na kamar dole don ita kanta mahaifiyar tasa tasan fatima ta tsane ta, kamar yadda ta tsani danta. Duk wadannan munannan dabi’u na Fatima ba su taba rage matsayinta a zuciyar Alhaji ba, da zata yi mugun bata masa rai, idan ya hangi murmushinta ko tsakinta da wani ne sai ya ji ta wanke masa zuciya. Don haka duk yadda mahaifinyarsa da sauran danginsa ke nuna masa illar fatima ba ya gani, idan ma ba a yi wasa ba sai reshe ya juye da mujiya, ma’ana ya tsani me kawo sukar, har dai kowa ya fahimci shi aka daina kawo masa sukar,illa addu’ar ganewa. 

Duk wata biyayya da mace ya kamata ta yiwa mijinta Fatima ba ta santa ba a tsakaninta da Alhaji kuma ta kan yi komai domin ta bata masa, wanda tana yin hakan ne domin ya ji zafi ya saketa, kamar yadda ta ke iya keta idonsa ta fada masa.

“Ba a nemi amincewa ta ba kafin a hada mu rayuwa tare, saboda haka har abada kada ka saka ran zaka mallaki karamar kofa koda kamar ta allura ce daga kofofin zuciyata. Raina ba ya sonka, kuma ni mutum ce da ban iya boye kiyayya ba.”

Bai taba daukar wani mataki akan Fatima ba ko da na zare ido ne, sai rarrashi da lallabawa tare da yi mata manya manyan kyauta masu motsa zuciya kamar su; gwala-gwale, kadarori, manya kudade ita da duk wanda ya rabeta, amma Fatima kamar dutse, zata karba ta kalmashe, idan ta ga dama ko godiya ba zata yi masa ba. A haka suka yi rayuwar, sai su kwashi watanni ba su hada shimfida ba, wanda a nan ma tana kara tafiya da imaninsa ya ci gaba da kwadayin zaman har abada tare da ita, saboda baiwar da ta ke da ita na kasancewa daga cikin matan da ake kira sa’ida. 

Shekarunsu uku tare ta sami ciki wanda ya bare a lokacin da yake shiga watanin hudu, cikin shekarun ukun da suka kuma biyu bayan shidda ke nan da aurensu, ta jera bari sau hudu, har kasar waje ya fita da ita, amma lamarin ya ci tura. wannan ya sa ta kara tsanarsa, musamman idan yana lallabata da cewa rabo ne ya kaddara aurensu, takan ce “Rabon wahala ba, tunda akalla ko dan tsako na kasa haifa”. Bayan wannan aikin da aka yi mata kawai sai ta dinga munafintarsa tana karbar allurar hana daukar ciki, saboda yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani haihuwa da shi, saboda ta rayawa ranta haihuwarta zata tilasta mata zaman gidansa.

 Shakarun da suka yi goma tare, bai zama wani sabon abu da zai hana a yanka kaza ba, don babu abin da ya canja, Fatima ba ta fasa nuna masa iyakarsa ba, shi kuma ko kwayar zarra bai rage a sonta ba, duk da ta dalilinta ya sami hawan jini. Kai ko a murnar cikar su shekara goma da aure wani katoton gidan gonarsa ya mallaka mata wanda kudinsa ya kai miliyan ashirin. Kuma wannan ne yasa mahaifiyarsa tashi tsaye wajen farraka su, don ta hakikance Alhaji zai iya mallakawa Fatima dukkan dukiyarta da ya mallaka, ko da kuwa yin hakan ba zai amfane shi da komai ba. Ta dinga ziyartar bokaye da malaman surkulle amma shiru babu labari, dole ta koma wa gaskiya, ta sa aka dinga yi mata rokon Allah ana neman idan akwai alkhairi ya shirya fatima idan babu ya farraka auren. 

Sai da kura ta yi kamar ta lafa, ku san Alhaji bai taba mallakar Fatima irin yadda ya mallake ta a wannan shekarar, kai kamar ma ita ce shekarar zumarsu, wadda bai dandana a farkon aurensu ba. Fatima kan yi hira da shi ba tare da bakar magana ba, sannan takan yi masa rakiya idan tafiya ta same shi, sannan uwa – uba ta daina gudunsa a shimfida duk lokacin da ya bukace ta.

Allah mai yadda ya so, ranar wata Alhamis da sasanyar la’asar ta shirya ta fice bikin kanwar wata kawarta. A lokacin ne wasu miyagun ma’aikatan gidan suka sami damar shiga dakin

Alhaji ta hanyar amfani da (master key) suka kwashe wasu makudan kudaden waje da ya shigo da su safiyar ranar. Ya dawo karfe biyar zai fita da kudin, amma sama ko kasa ya nemi kudin ya rasa, ya shafa a gidan babu Fatima. Haba! Sai hankalinsa ya yi mugun tashi, ya tabbatar kudin nan daukarsu aka yi, ya hada dukkan ma’akatan gidan ya fara surfar su da masifa. A karshe ya tabbatar musu in dai ba su fito masa da kudinsa ba sai ya salwantar da rayuwarsu. Ya sallame su kaca-kaca bayan ya sanya masu gadi sun garkame kofar gidan tunda sun tabbatar masa babu wanda ya fita bayan Hajiya, wadda ta tuka mota da kanta. Bai ko iya halarta sallar magariba da isha’i ba, yana ta faman safa da marwa cikin yanayin tashin hankali…

Alhaji sannu da gida”. Ya juyo ya dube ta cikin matsanancin bacin rai, cikin tsawa ya ce, “Fatima daga ina kike?” 

Ta yi saurin juyowa ta dube shi cikin tsananinr mamaki, bacin ran da ke fuskarsa ya sa ya kara Muni a idonta. Ta ga kamar babu mutumin da ya kai shi muni a duniya, sai ta ga ma babu hujjar da zai mata wannan tsawar ko wannan gizagon, kawai sai ita ma ta taso masa cikin bala’i. “Ban sani ba, idan ka halicce ni ne sai ka dauki mataki a kaina”. 

Nan fa Fatima kara hada masa bacin rai, Hankalinsa ba ya tare da shi ya ce, “Au haka kika ce? To zaman uban wa kike yi a cikin gidan tunda ban isa na yi iko da ke ba?” 

Ita ma cikin tsawa ta ce masa. “Kai ne ka fi kowa sani, zaman kaddara nake ba zaman uban wani ba….. Ko ka manta ne ba so da kauna ya kawo ni gidan nan ba, bare wani ya dinga yi min wannan ihun”.

 Jikin Alhaji ya dinga bari kamar mazari, gaba daya Fatima ta sauya a idonsa da zuciyarsa, ya ga ma gaba daya ba ta da wani amfani a wajensa ya fara mata bala’i. “Ke bana son iskanci da rashin tarbiyyar da kika saba kin ji! Matukar ba zaki zauna a gidan nan kamar ko wace mata ba, to tun wuri ki san inda dare ya yi miki, don ba ki da wani amfani a wajena, kullum ki dinga ficewa kina bar wa ma’aikata gida kina janyo min asara…..ke dai ba ki da wani amfani wallahi”. 

Ta tare shi cikin hawaye saboda tana da saurin kuka, ba domin nadama ba. “Ai ni ban taba daukar aurenka wani abin a zo a gani ba, balle na yi abin da matan aure suke….. Sai ka daina yaudarar kanka da zan yi wani abu da zai yiwa ranka dadi…….” 

Kai tsaye ya amsa mata “To shi ke nan, tafi gidanku na sake ki saki UKU, don kin san ni ma yanzu na mayar da soyayyarki tarihi, don iyayenki bace min da gani!”

Shi ke nan, da shigowar Fatima da saki nata ba a fi mintina biyar ba, Alhaji ya haye sama ya barta nan tana kuka matsannanci. Sakin ya girgizata matuka! Alhaji ya saketa a lokacin da ta daina sha’awar barin gidansa, ma’ana ta yarda ta karashe rayuwata da shi duk da ba ta jin kaunar sa cikin ranta. Ita ma ba ta jima a wajen ba ta fice, tunda dama ko mayafi ba ta sauke ba, makullin motar ma yana hannunta, sai gida wai an daki kare a ka.

Koda Kawu ya sami labari, amma bai gaskata Fatima ba, sai ya kira Alhaji a waya, wanda har wannan lokacin yana kulle a dakinsa cikin mugun bacin rai”. Da gaske ne ka yiwa matarka saki uku sulaiman? “Inji kawu. 

Ba tare da lissafin abin da zai tafi ya dawo ba, Alhaji ya ce “Kwarai da gaske, ku zo ku kwashe kayanta, ba na kaunar duk wani abu da zai tuna min na rayu da ita, mts!”

   Ya kife wayar cikin bacin rai. Wannan ne ya kashe bakin tsanyar kawu dangane da fadan da ya tanadarwa Fatima. Ba sai ya bincika ba yasan Alhaji ya gama ganin damarsa bai kuma dauke shi a bakin kamai ba tunda ya iya keta idonsa ya yi masa wannan cin fuskar. 

Kawu ya sauke ido akan Fatima, idonsa cike da kwallah ya ce “Tashi ki shiga gida Fatima, Allah ya sa hakan ne alhairi gare ku gaba daya”. 

 Washegari ranar Alhaji ya fito zai je sallar asuba ya tarar da jakar kudinsa a korido, ya dauka ya shigar falo sannan ya fice masallaci. Har aka idar da sallah yana zubar da hawaye, sai da ya dawo gida ya kara fashewa da wani sabon kuka kamar wanda aka yiwa albishir din ranar mutuwa. Ya tabbatar Allah ne ya jarrabe shi akan Fatima, daukar kudin nan ba ya nufin komai sai rabuwarsa da Fatima, wadda a zahiri da badini ta fi karfin wadannan kudin a wajensa. 

Lamarin kamar alamara kamar kuma mafarki, ya rabu da Fatima, rabuwa mai kama da almara, ta ya ya zai karbi wannan kaddarar?.

 Kawu mutum ne mai zuciya kwarai, da sanyin safiya ya turo a tattare masa kayan Fatima, Alhaji ya yi tsalle ya ce bai san wannan zancen ba, har sai da ta kai sun kira kawu a waya sun sanar da shi. 

A fusace ya kira wayar Alhaji ya ce masa “Ban gane abin da kake nufi ba?” 

Kawai sai Alhaji ya sa kuka yana cewa “Kawu ayi min rai, a binciki malamai ko akwai gyara cikin lamarinmu, wallahi kawu cikin mayen bacin rai na yi sakin nan, sam hankalina ba ya tare da ni……” 

A kufule kawu ya amsa. “Shi ke nan, yanzu ka bar su su debi kayan in yaso idan malam sun budo maka kofar halaccin ci gaba da zamanku tare sai mu dawo da kayan”. Bai jira cewar Alhaji ba ya kashe wayar, dole Alh ya barsu suka kwashe kayan Fatima tas, yayin da kamar sun bude kofar kukansa da bakin cikin sa.

Rayuwa ta yi kunci gare shi matuka. A wajen Fatima ma haka lamarin yake, ranar da aka yi sakin ba ta iya runtsawa bacci ba. A zatonta zafin kalmar da ya hada mata da sakin ce ta ke damunta wato. “Don ki san nima na mayar da soyayyarki tamkar mafarki….. Don iyayenki bace min da gani”. A hankali sai ta gane ba kalaman sa bane ke sanya ta tashi hankalita ba, akwai batutuwa da dama, kuma na shekaru da yawa, yadda ta jima tana taka rawar da ta ke so a gida da rayuwar Alhaji, shi kuma yana saka mata da tarin kauna da farantawa…..me yasa ya dawo daga rakiyarta yanzu? Kuma zata kuma samun namiji mai nuna mata kauna kamar Alhaji kuwa? Wadannan lissafe-lisafen ba su barta haka ba sai da suka yi tasiri manna mata kaunar Alhaji ta dinga yarda wa kanta lallai ta tafka asarar masoyi. Ta rasa sukuni kwata-kwata, hakki ne kawai yake dawainiya da Fatima, hakki irin na mai laifi cikin ma’auratan da suka sami kansu tsakiyar kaifin almakashin saki uku! Duk da haka ba za a ce Fatima ta kai Alhaji damuwa ba, tunda ba ta yi wani yunkurin ba, bayan na fatan ina ma jiya ta dawo yau, ta mayar wa da Alhaji raddin soyayyarsa? Ba ta yarda ta yi zurfi cikin kaunar Alhaji ba sai da ya nemeta da tayin yadda za su mayar da aurensu tare da bayyana mata fatawar da ta bayyana cewa, saki uku lokaci daya sakin bidi’a ne, kuma a matsayin saki daya yake. 

Sai kawai ta bayar da kai bori ya hau, ta kuma iya jure tunkarar kawu da maganar, Allah ya sa kawu ba mai karamin sani ba ne, sai ya dubeta da kyau cikin nazarin ta sosai, sannan ya ce “To ni ban gamsu ba, ba kuma na karyata fatawar da ya kawo ba ne. Sam! Ni hankalina ya fi kwanciya ga wadda ta haramta aurenku har sai kin auri wani namijin kin tare da shi. Wadda wannan fatawar jamhurun malamai suka tafi akai kar ki kara kawo min irin wannan maganar, ban son rudu.”

 Dole ta karkade zani ta mike cikin hawaye. Daga nan ne kuma cira kafa ita da Alhaji ta bin hanyar da duk suka sa zata mayar musu da aurensu. Amman wani abin takaici shine duk hanyoyin da zasu bi sai kawu ya dago logarsu saboda farin sanin da ya yiwa Fatima da irin mijin da ake zaton zata zabawa kanta. Sau hudu tana kawo masa samarin da zata aura, amman idan kawu ya saka su a kwana da tambayoyi sai ya dago su. Don haka ya tattara dukkan lurarsa akan Fatima, ya alkwarta wa ransa sai iyakar inda karfinsa ya kare.

Also Read:

Zuciya da kwanji Chapter 1


Abdullahi ya hadu da Alhaji ne a wani tsadadden asibiti lokacin da ya je dubo wani abokinsa da aka yiwa aikin kaba, shi kuma Alhaji ya je bisa larurarsa ta hawan jini, wadda ta matsa masa yanzu. Tun da Alhaji ya ga Abdullahi ya dora dukkan burinsa a kansa, don ya tabbatar in dai Abdullahi ne kawu ba zai taba dago yawarsu ba, tunda bai rasa komai da ake bukata kafin a ba wa mutum aure ba. Ya dinga ribatar Abdullahi har ya samu suka kebe, sannan ya kora masa bayani. 

“Dan halak ke nan, shekaran jiyan nan ka fado min a rai, dama cikin satin nan nake son na neme ka”. Cikin fuskar rashin fahimta Abdullahi ya ce,” Allah sarki, ina fatan kalau?” 

Fuskar Alhaji na bayyana jimami ya rangwada kai ya ce. “To lafiyar mahaukaci ba, wani aikin lada da ceton rai nake son baka, don a duniya ba ni da mai yi min sai kai”. 

 Kallonsa kawai Abdullahi yake cikin rashin fahimta, har sai da ya daure sanan ya kuma dorawa. “Allah ne mai saka soyayya a zukatan bayinsa Abdul, Allah ya jarrabe ni da son mace daya a duniya, wato matata. Wani tsautsayi yasa na yi mata saki uku. To yanzu duniyar ta yi min kunci, na gane ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba….. Shi ne nake rokon ka taimaka ka halarta min ita”.

 Kallon Alhaji kawai Abdullahi yake yana sauraron wannan rainin hankali da na wayo. Jim ya yi kafin ya shawo kan fushin zuciyarsa sannan ya yi magana mai ma’ana. “Me yasa sai ni zan yi maka wannan aikin?” 

Yana rufe baki Alhaji ya amsa “Saboda zumuncin da ke tsakaninmu, nasan ba zaka so akan wannan lafiyata ta salwanta ba…. Kawunta ne ya matsa matukar bai ga mutum mai kamata irin ta gidanku ba, ba zai bayar da aurenta ba, don ya sanya mana ido…. Ni kuma wallahi ba zan iya hakura da ita ba… Sai inda karfina ya kare wallahi….” 

Abdullahi ya tare shi da cewa. “Ba ka ganin hakan zai zubar da martabar gidanmu……?”

 Alhaji ma ya tare shi kamar zai yi kuka. “Ka fansar Abdullahi, ka ceci raina wallahi na yi maka alkwarin biyanka makudan kudade…… Zan daga darajarka a garin nan sai ka shiga sahun attajirai”. 

Abdullahi ya jima yana tunani, sannan ya dube shi da kyau ya ce “Ka fa san halin mahaifa, babu yadda za’a yi na kawo matar da ta girme min da zummar aure bai nemi ba’asi ba. Na kuma san duk wahala dole matarka ta girme ni”. 

Cikin doki Alhaji ya ce “Au ba ka santa ba?” 

Kallonsa kawai Abdullahi ya yi cike da takaici. To ta wacce hanyar zai san matar wani? Musamman Alhaji kawai don yana abokin wansa? Sai ya girgiza kai kawai.

Alhaji ya ce “Shekarunta talatin da biyu, kuma da yake tana da kyan jiki zaka zaci ba ta fi shekaru ashirin da biyar ba”.

 Abdullahi ya kara jan fasali sannan ya ce “Da yardarta a ciki?” 

Alhaji ya yi saurin gyada kai “Eh, idan ma ka amince sai na gabatar maka da

ita kafin ku fara magana”. 

Kai tsaye Abdullahi ya amsa “To, na amince”

 Farin cikin Alhaji ya tsananta, kawai sai ya rungume Abdullahi yana godiya. A nan suka shirya haduwa da yammaci a gidan namun daji, a haduwar su kuma suka jaddada kudirinsu, sannan suka yi musanyar lambar waya tare da shirya a washe garin ranar Abdullahi zai fara zuwa tadi.

***************** ****************

 Washe gari da yamma bayan sallar la’asar, Fatima na kwance kan kujera 3 sitter a kasalance ta ke kwarai, kasala irin wadda ke tasowa daga zuciya sakamakon bacin rai da damuwa. Ta sanar da mutum gidan cewa, tana da bako kowa murna yake yana dokin ganin bakon cikin zakuwa,wanda ta tabbatar da biyu suke yi… Kowa sai hidimar tarensa yake daga kan masu aiki akan abincinsa, har jama’ar gidan sai murna da doki. Wannan ya sa fargabarta ta kara tsananta….. Tasan kawu sarai akwai dora ido. Da zun da safe Abdullahi ya yi mata waya ya ce, karfe uku zai zo, amma ga shi hudu da rabi babu labarinsa, sai bacin ranta ya kara baci, ta kuma kara jin tsanar Abdullah a cikin ranta.Ta tsani mutumin da ba ya daukarta da muhimmanci, ko kuma ba ya girmamata. Ta lura da Abdullahin mugun dan tsaurin ido ne…… Ya iya dizga mutane. To idan ma halinsa ne dizga mutane ai tana jin ta fi karfin hakan, don ba ta rasa duk wani abu da ke janye so da biyayya ba, ko ba domin Allah ba. Tana da kyau, kuma tana da kudi, sannan ta iya takunta. 

Da damuwar ta isheta sai ta janyo waya ta hau facebuk domin debe kewa, tsawon mintina goma, sai ga safiya kanwar momi matar kawuta shigo da karadinta “Anti wannan yayan namu zai tilasta ni kwannan gidan don ba zan wuce ba sai na ganshi, don Allah ki yi masa waya ya karaso mu gaisa.” 

Fatima ta dago ta dube ta, sai ta rasa ansar da zata bata, akan me zata yi masa waya, kuma ta ce masa me? Sai kawai ta yi shagare tana kallonta Cikin zancen zuci, safiyya ta bude baki tana kallonta ta ce “Anty….. Wannan mutuwar ido biyun fa? Duk yayan ne da wannan aikin?”

Fatima ta yi murmushin karfin halin da ya yi kama da na shauki, sannan ta juya baya ba tare da ta tanka ba, safiyya ta mike tana tuntsura mata dariya. 

Sai shidda saura Abdullah ya iso, ya yi kiran wayarta tana ta kallon wayar saida ta katse ya sake kira, sannan ta daga a kule, koda ta daga wayar shiru ta yi ba ta tanka ba.

 Muryarsa a sake ya ce. “Fatima na iso”.

 Haushin gatsa sunanta da ya yi kai tsaye ya sa ta taso masa da bala’i. “To me zan yi maka? karfe nawa ka ce min zaka zo?” 

Ya yi Shiru, sannan ya nisa a zafafe ya ce “Ki yi hakuri, amma don Allah ki dinga yi min uzuri, bana son masifa wallahi”.

 Sai ta saki baki cikin al’ajabi, ta ma rasa abin da zata ce masa, koda yake ko tana da abin fadar bai ba ta damar fadar ba, tunda ya kashe wayar…….

Wannan wanne irin dan zafin kai Alhaji ya hadata da shi? Duk mazan da ya kawo mata a bayan masu ladabi ne, amma wannan yana jin kansa shi wata tsiyar ne.

 Ta fi mintina ashirin tana faman neman madafa tare da tunanin turbar da zata bi da wannan dan hayaniya, har ta kai ga zargin kanta. Sai ta gama babu wani dalilin da zai sa ta dinga damuwa da zafin kansa, ya karaci jaridarsa ya gama. Ta sa baki ta yi kiran safiyya, sai gata a guje, tana zuwa ta ce

“Ya zo ko Anti?”

 Ta yi murmushi, tukunna ta ce. “Ya zo, sai ki shigo da shi, don na ga alamar kin fi ni dokin ganinsa”.

 Safiyya na dariya, ta ce “A’a bazan fi ki ba anti, ke da har zazzabi ya kamata saboda rashin zuwansa. Tsegumi kawai ke dawainiya da ni in ga dai dan talikin nan da ya rikita mana ke”.

Fatima ta hadiye takaicinta, ta ce “Nasan ba zan ba mara danki kunya ba, shigo da shi sai ki kare masa kallo”.

 Safiyya ta fice Fatima na binta da kallo cikin kunar rai, haka kawai ta ji sam ba ta kaunar ganinsa. Tana jiyo jama’ar gidan na ta kara-kaina a kansa. Da akwai alamun sun yaba, can sai ga safiyya da sauran ‘yanmatan gidan sun shigo, suna mata kaudi. 

“A’a Anti kin yo wawan kamun, ya ya muka ganki haka? Don Allah tashi ki canja tsari, domin ya gane gidan da ya tarar”.

Ta yunkura ta tashi zaune ta rafta tagumi hannu biyu tana sauraron shagwabar da suke mata.

“Na rantse Anti yanzu kika yi mijin da ya dace da ke, ko babu kudi akwai kyau da iya taku……” “Sannan ga fara’a da iya shirya zance kalma bayan kalma….” Irin kalaman yabon Abdullahi da suke ta jero mata ke nan, wadanda suke faranta mata, sannan suke bakanta mata, karbuwar da ya yi a gurinsu ne ya faranta mata, tana kuma jin haushin yabon da suke masa don bai cancanci yabon na ko dayua, sai dai babu damar ta bayyana. Haka suka yi ta ribatarta sai da ta canja shiga, ta yi kyau tamkar ranar walimar aurenta. Ta same shi a falon momi durkushe a gabanta, kamar zai kwanta mata saboda ladabi.

Momi na ganinta ta hau zolayarta. “Kin gaji da jira kika biyo bayansa ko?” 

Ta yi murmushi kasaita, ba ta tanka ba ta nemi kujera ta zauna tana kallon ikon Allah. 

Momi ba ta jira cewarsa ba, ta juya ga Abdullahi ta ce “Ina fatan ka shirya da kyau, wannan yarinyar shan kamshinta ya yi yawa”.

 Ya kara kan – kan da kai, muryarsa a ladabce, ya ce “Na sani momi, a taya mu da addu’a”.

 Cikin fara momi ta ce “Idan Allah ya so, kar ka ji na ce haka, Fatima na da saukin kai ga wanda ya iyawa dabi’arta da tarbiyyarta, ina tsammatar muku zaman lafiya da saukin fahimtar juna, domin dukkanku kun fito daga gidan tarbiya da sanin ya kamata. 

“Mun gode”. Kalmar da Abdullahi yake ta maimaitawa ke nan, ya yin da Fatima ta yi shagare tana kallon momi zuciyarta cike da tambayoyi. A ina momi tasan Abdullahi, kuma dan gidan waye?

 “Don Allah ka rike amana, ka ga marainiya ce, nasan kawunta ma nasihar da zai yi maka ke nan. To kafin ka ganshi ma ni na fara yi maka. Ka rike ta amana don Allah ku zama masu hakuri hat ku fahimci juna”. Abin da momi ke ta jaddada masa ke nan, idon Fatima a kanta, yayin da kunnuwanta ke sauraron Abdullahi cikin ladabi yana amsar amanar yana kuma tabbatar mata da yarda Allah ba zasu yi nadamar ba shi aurenta ba. Har cikin ran Fatima ta yarda yana kirari yana dabawa kansa wuka ne kawai, don bai kamata ya furta ko kalma daya a cikin maganar momi ba matukar ba zai iya toshe kunnensa daga saurare ba.

Also Read:

Zuciya da kwanji Chapter 1

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.

Back to top button