Mejo Najeeb Page 54 By Autar Alheri
“Gabaki ɗaya mutuwar tsaye mejo da Munir sukayi harmada sajad, Abba kam ba’amagana,,,yayinda Ammi da Hajiya mama keta rusar kukan takaicin zamada maƙiyinka batareda kasaniba. “Yanzu Jamila dama kece sanadin haukana? Dama kece sanadin danabar gida nabar yarona jinjiri? Nabar mijina dangina dakomai nawa? Mina aikata agareki hakan Jamila tun zamanada dake? Alokacinda ake zancen aurena da abban jazlan dakin gayamin har izuwa wannan lokacin kinason Jamila mize hana ya auremu dukanmu? Amma sekika nuna bakomai sabida mugun nufi, yanzu jalima har kika reni ɗana dawata mummunar manufa? Jalima kike sha’awar ɗan cikina wanda koba kece kika renishiba bazanyi tunanin hakan agarekiba, kilalatamin rayuwar yaro why jalima why please?? Ammi taƙarasa zancen tana koma sakin sabon kuka….Abba kam dajikinshi yarigada yayi sanyi cikin ƙarfin hali yazo gabanta kamar ze shiga jikinta yace “jalima, shiru bata amsa Mishi ba, ƙara kiranta yayi akaro na ukku kana tace”jalima kika sakawa yarona ciwon wanda ke gabda kaishi lahira kuma kina hanani tausaya masa kana kuma kinuna cewar kinfi kowa jin tausayinsa bayan kece silar komai, duk ina soyayyar dakikeyiwa najeeb Jamila? Da har zakiyi ƙoƙarin cutar dashi jalima miyasa hakan mimuka Miki dazafi hakan? Yatambaya idonshi na cika da ƙwallah….cikin takaici Hajiya umma tace bantaɓa son najeeb ba dededa ƙwayar azzara acikin raina sedai sha’awa, bantaɓa yimishi kallo ɗa ba sedai farka shiyasa bantaɓa yimishi addu’a ba balle fatan nasara, akulle idan yacemun tafita kozeyi tafiya iya kacina dashi sekadawo yaron umma,,,amma ita wannan munafukar hadda wani kinibibin yimasa addu’a bayan kuma addu’ar ki bazata ƙareshi dakomai domin bazata hanashi shiga farko naba, seka bani jarumtarka najeeb najika acikina shine cikar burina shine mafalkina zoka lasamun zumarka najeeb zokabani zo kacin…dasauri Munir yatoshe mata baki ciki kukan me nunida tsantsar bakin cikin dayake ciki nasamun mujirimar uwa irin Hajiya umma yace “sedai bakin cikin rashin samun yah najeeb amatsayin namiji agareki yakasheki umma yah najeeb baze taɓa aikata fasiƙanciba ko a gun wata daban balle ke dayake yiwa kallon uwa mahaifiya idan dai har wannan shine zezamo ajalinki to muna jira kiƙarasa cikawa semuje musadaki da mahaliccinku keda wa’yanda kika zalunta shine yasan abinda ya dace dake, kincucemu umma kin tozaltardamu kin wulakanta muna rayuwa umma najima ina zargin wani abu akanki tun lokacinda kike yawan yiwa yah najeeb wasu abubuwan dakuma yadda kika nuna kishinki ƙarara akan anty Maryam wannan yasa naƙara zarginki segaya kuma hasashena yazama gaskiya kinbar mana tabo umma kinbar mana Miki da dafi azuciya wanda zayataɓa goguwaba kincucemu umma kin cucirayurm…cikin sauri mejo yajanyo jikinshi tare da rungumeshi suna sakin kuka atare memugun tada hankali, dasauri sajad yazo yarungumesu duka shima yana sakin nashi kukan….kowa yayi tsitt awurin se sautin kukansu kawai ketashi.Dasauri general Aliyu dayashigo gidan tun ɗazu yana kallon wannan badaƙalar yariƙe Hajiya umma yana faɗar “subhanallah please umma kitsaya Dan Allah, domin iya kacin gaskiyar ta nema takeyi ta yaga kayan jikinta….dukkansu juyowa sukayi suna kallon yadda yake kokawa da ita amma ba wanda yayi yunƙurin tayashi. Cikin marairaice fuska yace “please mejo kutayi mutafi da ita domin nemanta ma akeyi a office nazo zan kiraka bagayama cewar mejo tanimu yayi bayanin wacece Hajiya jamila domin bakowa bace face Hajiya umma ina tunanin yadda zan tareka da wannan zancen ne Captain Umar yakirani yana gayamin little mom tafita yanzu yaduba begantaba,,,shine fa naje gidan bansameta ba nazo nan koda nan tayo segaya kuma nasameku anan duka gakuma wannan rikitaccen al’amarin dan Allah kutayani muje da ita kartayi tsirara anan, yaƙarasa zancen cikin takaici shima…..ƙwallah Abba yashare a idonshi kana yace “wato wancin tsafi dabin bokaye har ta addanci kikeyi Jamila ? Innalillahi wa’innailaihi raji’un Allahumma ajirni fi musibatih wa’ahaliqni Khairan minhaa. Kinrigada kingama yimana tabo Jamila sedai kije zakiga abinki, sajad kuje da ita, cewar Abba.”A’a kudakata karku fita da ita agidan domin zatayi muku tonon sililine kawai kurufeta awani ɗakin tukkunnah har zuwa wani lokacin….dukkanku juyawa sukayi suna kallon me magana, Umaima ce tsaye abakin ƙofar shigowa ɗakin, kafin wani yayi magana halima tace “Umaima tafaɗa cikin zumuɗin ganinta, hakan yasa isseta data farka tunɗazu takaicin Hajiya umma yahanata tashi yasata miƙewa yanzu itama tana kallon Umaima da halima tanufa. “Wacece wannan? cewar Abba. “Umaima ce ƙawar maah ɗin su Maryama Ammi tafaɗa tunda ita tasan Umaima tun a Gombe gidansu halima. “Da mamaki yace wacce maah kuma wacece ? Kuma miyasa ita wannan ɗin shigowa cikin zancenmu kaitsaye dami tazo?? Isseta tabuɗe baki zatayi magana kenan Umaima tarigata ta hanyar faɗar”yishiru Maryama ƴar Maryama shalelen gimbiya laweesat wannan bayanin nikaina banawa bane barasu daga bakin jiga jigan abin tafaɗa tana nuna bakin ƙofar inda gimbiya mardeeya tashigo cikin shigar bil adama ashe kamarta ɗaya sak da gimbiya laweesat dan bata yawan bayyana ne a shigarta yasa ba’sfahim hakan. Fuskarnan Tata aɗan kame babu yabo babu fallasa, murmushi Umaima tayi aranta tace mehali baya fasawa gimbiya mardeeya. “Maaah halima tafaɗa cikin zumuɗi, aɗan kaikace ta kalli halima sedai batace komaiba. Itakam isseta batayi maganaba domin tagano ba maah ɗinta bace sedai Batasan ko wacece ba amma dudda hakan bataji tsorontaba…sukuwa duka mutanen dake perlor kallonta kawai sukeyi anrasa wanda zeji magana, ahankali tabuɗe baki cikin muryarta me furgita ƴan maza tace “ba maah ɗinku bace gimbiya mardeeya ce kanwarta. Tunkafin tarufe baki general Aliyu yawani zaro ido tareda dafekai besan lokacinda yace “maciya ba domin bemanta haɗuwarsu agidan mejo ba…. dukkansu kallonshi sukayi har ita amma batace Mishi Komaiba. Magana taci gaba dayi “nibazance Komaiba domin magana abakin me ita tafi daɗi kufito bakin swimming pool ɗinku gimbiya laweesat najiranku, tana gama faɗar hakan takama hanyar fita, cikin sauri isseta tabi bayanta hakama mejo da halima…Ammi kuwa kallon general Aliyu tayi kafin tayi magana Abba yace Aliyu kurufeta a ɗaki kaida sajad kusamemu a swimming ɗin…to Abba yafaɗa kana suka nufi bedroom ɗin dazasu rufe Hajiya umma aciki tanata ihun se mejo yazo yakwanta da ita, Abin takaici.Abakin swimming pool ɗin suka samu Hajiya Hannah da Alhaji abdussalam mama bintu…cikin mamaki Alhaji abdussalam yace “au Alhaji khamis dama baku tafiba?? Shima Abba da mamaki yace”kamarya bamu tafiba bayan gamu a Nigeria kainedai zan tambaya dama tare mukazo? Kafin wani yaƙara yin magana gimbiya mardeeya tace nice nan nakawosu, sabida hakan kunutsu. Tsit kowa yayi awurin amma banda isseta da gabaki ɗaya hankalinta na kan inda Ataga maah ɗinta.Wani irin rugugi swimming ɗin suka farayi dama wurin babba be kamar wani Teku hakan aka yi shi… dukkanku kallon ruwan sukeyi cikin tsoro da mamaki yayinda isseta da halima suka washe baki domin sunsan alamar bayyanar maah ɗinsu ce….aiko basu gama tinaniba jelar kefinta ta bayyana shirgegen kifi asaman duk seda yakusa cinye rabin su, kafin tabayyana gabaki ɗayanta fuskartata ɗaukeda lallausan murmushi kamar yadda tasaba…amugun razane wasu daga cikinsu sukaja baya zasu arce sedai tozali dasukayi da gimbiya mardeeya tazama wata irin ƙatuwar macijiya amma daga samanta tana anan a yadda take yasakasu haɗiye wasu miyagun yawu cikin mugun tashin hankali da tsoro.. isseta kuwa tuni takai inda maah take har acikin. Ruwan tarungumeta ciki matsanancin farin cikin ganinta..shafa kanta tayi kana tace “wai yoshe Maryama ƴar Maryama zata girma ne kose jikar Maryama ko jikinta sunzo duniya tukkunnah? Tafaɗa cikin sigar tsokana tana mannawa isseta kiss a goshi, kana ta ɗago tana karewa mutanen wurin kallo kafin tamayarda dubanta ga gimbiya mardeeya”Miye hakan mardeeya zaki razanasune?? Cewar maaah…baki gimbiya mardeeya ta ɗan taɓe kana tace “ko ɗaya zasu gudune sanida ganinki batareda munyi abinda yakawomuba kuma idan razanarwane kece ai kika fara Kinwani zo kamar zaki tada gidan daruwa… murmushi kawai gimbiya laweesat tayi kana tace “assalamualaikum jama’a dan Allah kunutsu magana mukazo muyi daku ba’abinda zamuyi muku domin muma Musulmai ne bazamu iya cutarda kowaba se wanda yacuci kanshi, taƙarasa zancen da alamar roƙo. Cikin sauri isseta tace “Ammi maah ɗitace fa wadda tabaki magani mama bintu maah ce wadda nazauna wurinta alokacinda Abba ya koreni…se lokacin suka san saki jikinsu…cikin sakin fuska Ammi tace Masha Allah tabba Maryama da halima suna bani labarinki ashe Allah yayi zanganki baiwar Allah ngd sosai da ɗawainiyar ki akan ahalinmu Allah yabiyaki da aljana..Ameen ya Allah.”Maah Kinga little mom kinshareniko? Cewar mejo idonshi na cika da ƙwallah… murmushi tayi kana tamiƙa Mishi hanninta alamar yazo…bamusu kuwa yasaka hannushi anata. “Najeebullah tafaɗi sunanshi tare da shafa kanshi. “Na’am maah. “Yayane yaron maah? Tatambaya domin tasan izuwa yanzu zuciyarshi atunkushe take da ƙunci amma idan yasamu yayi magana abin ze ɗan faɗa Mishi. “Maah naganota Maah duka zancenka gaskiya ne tabbas nagano wannan yarinyar kuma na tabbatar bazata taɓa barinaba kamar yadda kika faɗa kuma tadawomin da giɓin dana rasa arayuwata wato mahaifiya gashi kuma ta hanani ita duka kamar yadda kika faɗa itama taba duƙarta, Maah ashe dama little mom ce wannan yarinyar dake bani kariya a mafalki amma kikaƙi gayamin sedai kika bani ita? Ashe dama Hajiya umma itace keson ta hallakani itace cikin mace ta huɗu bayan yayun little mom? Maah wai Hajiya umma keson nayi lalata da ita? Wai itace ke leƙani abayi idan ina wanka wai itace keson nayi ma’amala da ita tamkar little mom Maah miyasa rayuwata tazo ahakan? Miyasa baki gayaminba tun farko na ƙauracewa wannan matar? Miyasa baki gayamin cewar ba ita bace mahaifiyata ba? Miyasa duk kika ɓoye mun wannan abun?? Yaƙarasa zancen yana sakin wani sabon kuka.Kanshi gimbiya laweesat tashafa cikin rarrashi tace “ya isa najeebullah kayi haƙuri da yadda ƙaddara tazoma hakan Allah ya tsara ba abinda ze canjata, awancan gaya maka wacece jalima da aikinta ko abinda ke hannun Maryama duk bashida anfani sabida zaka kalli abinne a hagunce shiyasa nace ma kayi haƙuri komai Lokacine ze bayyana makashi zaka Ganshi da idonka kuma gaya kagani. Ɗan shiru tayi tana kallon mutanen wurin kana tacigabada da faɗar “yanzu ba kuka yadace kayiba godewa Allah ya dace kayi, mahaifiyarka ta bayyana agareka Hajiya jalima batasamu nasarar abinda takesoba akanka, yarinyar dakakeda burin mallaka tazama mallakika kaga kuwa ai addu’a yadace kayi da godiya ga Allah bawai kukaba…sekuma ta ɗago tana kallon mutanen dake wurin wanda suka maidasu kamar tv, murmushi tayi kana tace Bara dai nafara gabatar muku da kaina domin nasan shine abinda kukafi ƙaguwa kusani ayanzu.”Sunana gimbiya laweesat taredani akwai ƙanwata gimbiya mardeeya gakuma ƙawata Umaima, Bara kuji yadda akayi nashigo rayuwar ahalinku…anan gimbiya laweesat tafara basu labarin tun farkon lokacinda mlm Mahaifin mama bintu yafara nemota akan aikin Hajiya Hannah hartayiwa Hajiya Hannah magani da yadda tarinƙa bibiyar rayuwar Hajiya Hannah har izuwa inda Takoma bibiyar isseta dakuma yadda akayi tasaka isseta nemawa Ammi magani harkawo lokacinda mlm Musa yakori isseta da lokacinda ta haɗa ta da nejo, har akazo inda gimbiya mardeeya tafara maidawa Hajiya jamila martanin abinda take yi dakuma lalata duk wani mugun aikinta tun lokacinda taraba mejo da ciwon data turo Mishi har inda ta kashe tsijuju harkawo yanzu da komai ya bayyana, seda takai ƙarshe kana tanisa tace kunji yadda akayi gimbiya laweesat da sister’s ɗinta suka shigo rayuwar ahalinku.Aitunda maaah tafara magana Ammi Hajiya Hannah Hajiya mama ke kuka wiwi hadda mama bintu,,,,su isseta da halima jidda Ummi kuwa duk ba’azancensu domin kuka sukeyi kamar wa’yanda ake zarewa rayuwa… Alhaji abdussalam da Alhaji Khamis ma kukan sukeyi hakama mejo da general Aliyu…gabaki ɗaya kowa kuka yake yi suna tunanin wannan ifta’in daketa faruwa acikin ahalinsu daga gefe ɗaya kuma suna godiya ga Allah daya turo wasu daga cikin bayinsa suke temakonsu akan abinda basu isa suma sandashi ba balle suyi ƙoƙarin yin maganinshi…sosai suka bawa gimbiya laweesat da Umaima tausayi dudda gimbiya mardeeya da bata cika damuwa da abubuwa ba awannan karon seda ta tausaya musu, daƙyar gimbiya laweesat ta rarrashesu cikin kalamanta masu sanyaya zuciya…bayan duk sun natsune tashiga yimusu nasiha meratsa zuciya akan rayuwa da abinda ke cikinta kana ta gaya musu bazasu bar rayuwarsu sunatare akoda yaushe domin sun rigada sunzama ƴan uwan juna….sosai su Abba suka shiga yimusu godiya dukkansu cikin soyayyar bayin Allah da Allah ya saka musu azuciarsu lokaci ɗaya….isseta kuwa cikin sanyi jiki tasaki Maah tare da nufar gimbiya mardeeya dake naɗe amacijiyarta..tana zuwa bata tsaya komaiba tafaɗa jikinta tare da rungumeta sosai tana sauke numfashi..se ayanzu gimbiya mardeeya tayi murmushi ganin isseta bataji tsorontaba se abin ya birgeta tashiga shafa bayanta, ahankali tace “i love You momma, tafaɗa tana ƙara ƙanƙame ta ajikinta… Murmushin gimbiya mardeeya yafaɗaɗa yau isseta takirata da uwa, cikin jin daɗi tace “i love You more ƴar lelen anty lawee, tafaɗa cikin barkwanci. “Nifa momma? Tatsinkayo Muryar mejo najeeb… murmushi taƙarayi kana tace “i love You yaron Maryama kuma mijin Maryama ɗan gaban goshin gimbiya laweesat shalelen Hajiya Hannah da abdussalam. Wani irin daɗi ne yarufe mejo wanda yakusan mantar dashi damuwarda yake ciki….duka mutanen wurin seda sukayi dariya, cikin nishaɗi Umaima tashafa kan Munir wanda kallo ɗaya zaka Mishi kasan cewar yana cikin kunci..aiko se yaji kamar ancire Mishi ƙaya azuciya, yasaki jikinshi aka cigaba da fira…sosai su gimbiya laweesat suka jima awurin suna tattaunawa akan rayuwa da abinda yashafeta kafin suyi musu sallama suka tafi cikeda kewar juna.Bayan tafiyarsu Abba yasaka General Aliyu ɗauke Hajiya umma akaita gidan ma haukata sedai suna buɗe ɗakin tabankesu tare da kwasar akuge tana ihu tana wlh seya cuta itabaza yardaba seya kwanta da ita tanayi tana tura hannunta gaba gareta,,,dagudun gaske suka dafa mata sedai kafin su risketa tuni ta ɓacewa ganinsu, hakan sukayi bulayin nemanta suka gaji doli suka dawo gida.Bayan mako biyu… acikin wannan makon biyu sosai wannan ahalin sukayi jimamin abinda ya faru dasu daga ƙarshe kowa ya watsarda abin tunda Allah yakawo musu shauƙinshi, acikin wannan lokacin ne akayi neman auren general Aliyu da halima haka mutanen Niger sukazo nemawa general Faruk auren Ummi aka nemawa nazeer auren mufeedah hadda Alhaji abdussalam hakan yasa aka wuce Gombe aka nemawa Sapwan auren zubaida agidansu isseta, daganan aka tsayar da rana wata ukku masu zuwa…awannan lukacin gidansu isseta yakoma kamar inda ake zaman makoki domin kuwa kowa yayi karatun ta nutsu, tsaida wannan ranar ne yasa mlm Musa cewar su anty hawwa sufitarda miji domin aranarda za’ayi auren zubaida aranar suma ze ɗaura musu aure da koma waye….jidda koda tadawo gida taga gidan ya canja bawanda yayi yunƙurin gaya mata abinda ya faru dubada mahaifiyarta ce tayi wannan aika aikan.A Lagos kuwa sosai ake zaune lafiya cikin farin ciki da ƙaunar juna tsakanin Ammi da mama,,,,hakama yaransu kamar ba wani abinda ya faru har auta siyana dabatasan abinda yafaruba kuma bata tambayi mahaifiyar tataba fidda cewar bata gantaba Allah yashafe mata abin aranta….Munir ne ma wani lokacin abin ke ɗan taɓashi domin yana masifar jin kunyar mejo najeeb da Ammi…fahimtar hakan yasa Ammi sakashi ajikinta tamkar itace ta haifeshi tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali domin karya saka abin Aranshi….hakama mejo sosai ake sakashi ajikinshi fiyeda yadda yake yi ada…. Isseta kuwa kusan kullun tana gidan Abba se mejo yayi da dagake takebinshi gida ko in jarabar Tata tashi domin abin har mamaki yake bawa mejo…yau ma kamar kullun suna zaune a perlor gidan Abba dukkansu Itako tana kwance tayi matashin kai da cinyar Ammi, ta kalli Ummi tace “please Ummi wai akwai garin rogo gidannan? “Garin Togo kuma cewar Hajiya mama? “Eh mama wlh teba nake sha’awarci se muje muyi. Ikon Allah lallai kam babu garin rogo agidannan sedai anemo miki. “Hhhh barana siyo mata Ammi ai inaga cin garin rogon namune mune sila Munir yafaɗa cikin nishaɗi domin shi yajima yana yimata kallon me ciki, kuma dama ba kunyace dashiba, dariya mutanen perlor sukayi,,,,shiko Munir yamiƙe yafice…..ko minti 40 beyi da fitaba yadawo ɗaukeda manyan ledojo da kayan ƙwalam bayan garin rogon…aiko tashiga buɗewa agwaima ce da mango se samiyan birai se kayan chocolate masu shegen yawa acikin…cikin farin ciki yashuga wankin agwaima tanasha kamar wata zarriya…Itako Ummi taɗauki garin rogon tanufi kitchen domin tayi mata tebar…!


