Mejo Najeeb Page 26 By Autar Alheri
“Mama bintu kuwa zama tayi awurin tana nata kukan bakomai ketada mata hankaliba illa yadda taga ɓacin rai datashin hankali ƙarara a idon aminiyar tata tasan tabbas akwai tashin hankali agaba domin tasan wacece Hajiya Hannah…Abba kuwa inbanda salati babu abinda yakeyi domin ya san idan za’ayankashi a yanzu be Isa yanemo Isseta acikin 24 hours ba shiko yazeyi darayiwarshi? Dama wannan ranar bintu keguje musu gata kuwa ta bayyana. Shin wai yama akayi harya kori maryama shikam ? Salihar yarinya wadda yanada banbacci duk acikin ƴaƴanshi bame tarbiyyarta da kamun kanta. (To mlm Musa se ayau kafahimci hakan🙄)Shinwai wacece maryama (Isseta) Shekaru ashirin dasuke wuce baya Alhaji Abdussalam idiris ya auri wata yarinya yar wani attajirin me kuɗi agarin yamai dake cikin ƙasar Niger wato Hannah. Hannah itace ƴa ɗaya tak agun mahaifinta wanda yayita Auren mata dayawa amma Allah bebashi haihuwa ba se akan mahaifiyar Hannah wanda Allah yakarɓi rayuwarta bayan tahaifi Hannah koganinta batayiba Hakan yasa mahaifin Hannah wato Alhaji madu yaɗauki son duniya yaɗorawa Hannah kasancewarta marainiya kuma itace kawai ƴarda ya mallaka aduniya. Wannan soyayyar dayake nunawa Hannah kuwa ta haddasa tsana mafi girma tsakanin Hannah da matarshi wato Hajiya tabawa….wannan matar taɗauki ƙiyayyar duniya yaɗora akan Hannah haryakai yakawo Hannah Takoma tamkar baiwa agidan ubanta, idan Alhaji madu na gidan sosai Hajiya tabawa kenunawa Hannah so dakulawa amma idan bayanan seta gwammace mutuwa da rayuwarta.Bayan Hannah tazama budurwa ne Hajiya tabawa tafara biyar bokaye da malaman tsibbo akan ta hallaka Hannah domin kuwa tanada tabbacin itadai bazata haihuba kuma idan yau Allah yakarɓi ran Alhaji madu Hannah ce kawai zatayi gadonshi sedai ita a ɗanmata ɗan abinda baza’arasaba. Hakan yasa tunanin hallaka Hannah yazo mata arai. Bayan takarɓo wani mugun sihiri wurin wani boka tayiwa Hannah aiki dashi wanda yayi sana diyar kwanciyar Hannah doguwar jinya wadda babu wanda yaɗauka zata rayu seda Alhaji madu yatashi tsaye sosai wurin nema mata magani tukunnah Allah ya haɗa shi da wani malamin addini amma fa da iska yake aiki sedai kuma baya mugun aiki abu ɗaya yakeyi warware asiri ko cire gagararrin iska wanda suke cutarda mutane….to bayan Allah yahaɗa Alhaji madu da wannan malamin yace akawo mishi Hannah gidanshi akako kawota kallo ɗaya yayi mata yagane cewar wani mugun sihiri ne ajikinta, anan yabazama neman iskan dayake aiki dasu domin acire wannan sihirin sedai duk wanda yazo seyace baze iyaba, daga ƙarshe dai wani tsohon iska bawan Allah ne Yagaya mishi cewar bawanda ze iya warware wannan sihirin se aljanar ruwa wato (hajo ruwa kenan) yaƙara dacewa kuma idan yasamu me kirkine zata yadda tayi wannan temakon amma idan bahakaba sedai taƙara lalata aikin…..wannan malamin najin Hakan yashiga tashin hankali Sosai domin Alhaji madu yabashi tausayi gakuma yarinya kwance agabanshi kamar gawa, ganin dai bayada wata mafitarne yasa yakira wannan tsohon aljanin akan yatemaka mishi wurin neman wadda zatayi wannan ceton ran tawarwarewa wannan yarinyar wannan sihirin…aiko tsohon ya amince inda yabazama nema amma besamuba kusan mako ɗaya harya fidda ran zesamu sewani abokinshi yabashi labarin gimbiya laweesat maaah kenan sa’anan Yagaya mishi yadda Zasu nemeta batareda gidansu ansaniba domin ɗiyar gidan sarautace….hakako akayi bayan yazo yabawa wannan malamin wannan labarin suka shiga Kiran gimbiya laweesat cikin inkon allah ko tazo, sedai sunsha fama da ita sosai kafin ta’amince da aikin Shima seda Taga Hannah tukunnah ta amince sabida yarinyar tabata tausayi. Tofa anan gimbiya laweesat tacirewa Hannah wannan sihirin wanda yazama sana diyar samun lafiyarta..Hakan kuwa baƙaramin daɗi yayiwa Alhaji madu da wannan malamin ba, shiyasa Alhaji madu yace gimbiya laweesat tafaɗi komi takeso afaɗin duniya indai befi karfinshiba zemata…sedai buɗar bakinta secewa tayi ita dan Allah tayi badan wani abun ko abiyataba domin bayada abinda ze iya bata sedai Allah yabiyata daga Hakan tayi tafiyarta….sedai me Hannah taƙi barin ranta kullun cikin tunaninta takeyi akan waye yayi mata wannan mugun aikin na mutuwa?? Amma batada wannan amsar Hakan yasa taroƙi aminiyata umaima akan tariƙa yimata bibiyar yarinyar domin bata kariya dakuma gano wanda ke neman hallakata.Bayan Alhaji madu yayiwa wannan malamin goma sha biyu ta arziki kuma yaroƙi alfarmar Hannah tazauna gunshi naɗan wani lokaci domin zeyi tafiya ne bayaso yatafi yabarta gidanshi sabida ya fara kokwanto acikin lamarin gidan…Hakan mlm ya amince da zaman Hannah agidanshi inda yahaɗa ta da ƴarshi suna komai atare har suka zama ƙawayen juna wannan ƴa tashi bakowa bace face mama bintu…bayan Alhaji madu yadawo daga tafiyar dayayi yazo ɗaukar Hannah Seya samu cewar tasamu wanda kesonta kuma da aure har mlm yasa anyi bincike akanshi angano cewar ɗan babban mutunne acikin garin maraɗi…. Alhaji madu yayi matukar farin ciki da jin wannan labarin koba komai Hannah zatayi aure takaucewa idon makiya adena bibiyarta damugun nufi…aiko atake ya amince da wannan zancen Auren inda aka kira mijin yaturo iyayenshi akayi komai na aure asirrance a gidan mlm wanda yasa Hajiya tabawa batasan komai akan zancen Auren Hannah ba seranda aka ɗaurawa Hannah aure da Alhaji Abdussalam idiris tukunnah tasani…dudda cewar abin yaƙona mata rai sosai amma bata nunawa kowa komaiba sabida tanada mummunan ƙudiri arayuwarta sabida zamanta makirar mace tashige gaba akayi komai da ita lafiya har aka kai Hannah ɗakin mijinta agarin maraɗi..Hakan yacirewa Alhaji madu zargin dayakeyi agareta, yasakankance mata komai na yadda tabata 💯Bayan Aurensu Abdussalam idiris da Hannah Allah ya arzitasu dasamun haihuwa inda afarko suka samu ɗa namiji wanda yaci suna nazeer, bayan shekara 2 da haihuwar nazeer Allah yasake yabawa Hannah wani ɗan wato sapwan daganan kuma bata ƙara haihuwaba kusan shekaru goma kuma binda zebada mamaki anan shine Sam Alhaji madu beyi farin ciki da haihuwar waƴannan yaran na Hannah ba duddacewar kuwa bashida ƴaƴa..kuma har ila yau Hajiya tabawa bata dena bibiyar Hannah da mugun nufinba sedai duk abinda tayi baya samunta sabida wani kafi da umaima tayi mata akan bawani sihiri daze ƙara tasiri akanta, kuma takasance mace ma’abuciya addini ta tsare askar da ibadunta yadda yadace wannan shine makami megirma da Hannah ke yaƙar Hajiya tabawa dashi..bayan tsawon wannan shekaru goma da Hannah tayi bata haihuba harta fidda rai da haihuwar sekawai gaciki ya ɓullah ajikinta. wannan cikin yayiwa alhalin Hannah da mijinta harmada yaranta daɗi inda kowa yaɗauki burin duniya yaɗora akan wannan cikin na Hannah cikin kuwa dayabata matukar wahala kafin tahaifeshi. Bayan cikin ya isa haihuwa ne Allah yabawa Hannah haihuwar ƴa mace, wadda ɗimbin mutane suka yi farin cikin haihuwar wannan kyakkyawar yarinya me matuƙar Kamada uwarta, sosai Alhaji Abdussalam idiris yaji daɗin zuwan wannan yarinyar duniya hakama agun kakanta Alhaji madu Shima a wannan karon yayi matuƙar murna da haihuwar wannan jaririyar Hakan yasa yazo dakanshi har garin maraɗi yaganta kuma yayi mata kyauta mafi girma wadda ta girgiza ilahirin family nasu, domin kuwa kashi huɗu yayiwa duk abinda ya mallaka yace yabawa wannan yarinyar ukku daga ciki shi ya ɗauki ɗaya inda ta mallaki manyan company shi da manyan gidaje gakuma tarin dukiya…da Alhaji Abdussalam idiris yayi mishi ƙorafin akanmi zeyi Hakan…buɗar bakinshi secewa yayi shiyanzu tsufa yazo mishi bayada abinda zeyi da dukiya kuma dama duk abinda ya mallaka aduniya mallakin Hannah ne to bawani abun bane Dan yabawa ƴarta….tofa wannan kyauta tatuno tsuhuwar ƙiyayyar da Hajiya tabawa keyiwa Hannah inda abin Yakoma akan wannan jaririyar dako mako ɗaya batayi aduniya ba. Haka dai akayita sha’anin hidimar bikinda akeson shiryawa wannan yarinyar inda ranar suna yarinya taci Sunan gwaggonta wato MARYAMA domin Hakan buzaye kekiran Maryam..sosai akayi biki akayi komai cikin jin daɗi dafarin ciki inda akayi komai lafiya aka ƙare lafiya…kasancewar MARYAMA Sunan gwaggonta ne yasa ƴaƴunta suke kiranta da *letteiy* abar ƙauna kenan dayarensu.Amma asalin sunanta MARYAMA ABDUSSALAM IDIRIS haifaffiyar ƙasar Niger ce maryama kuma cikakkiyar buzuwa saɓanin damuke mata kallon bafulatana.Sunan Isseta kuwa yasamo asiline agun Kabir wato yaron mama bintu bara kuji asalin faruwar zamanta ƙasar Nigeria agarin gombe.Bayan Maryama tayi shekaru biyu aduniya za’ayayeta daga nono se Hajiya tabawa tashiga yiwa Alhaji madu daɗin baki akan cewar abata maryama zata yayeta domin su samu yaron kallah agidan sunajin daɗi ita sam batajin daɗin zama ita ɗaya tunda yanzu girma yazo musu…aiko tayi nasara akan wannan zancen nata dudda cewar ba’abanza tazo mishi da zancenba seda tahaɗa da sihiri, Hakan yasa atake Alhaji madu ya amince da buƙatarta inda ya kira Alhaji Abdussalam idiris dakanshi yasanar mishi bukatarsa takarɓar Maryama. Shikam Alhaji Abdussalam beyi tunanin komaiba ya amince inda yazo yagawa Hajiya Hannah buƙatar mahaifinta akan tilon ƴar tasu, tashin hankalin kenan wanda ba,asaka mishi rana domin sosai hankalin Hajiya Hannah yatashi akan wannan zancen domin tasan bayin kanshi bane aikin Hajiya tabawa ne kuma tanada tabbacin da wata mummunar manufar tayi Hakan. Taso ta fahimtarda mijin nata amma yaƙi fahimta Hakan yaƙara lunka tashin hankalinta akan wannan lamarin tarasa yazatayi bazeyu tacewa mahaifinta bazata iya bada yartaba kuma ba zata iya badata agun Hajiya tabawa ba domin tasan idan ta yadda tabada ƴarta totakaita mahalaka ne…Hakan yasa tayanke shawarar Kiran ƙawarta bintu tagaya mata ko akwai shawarar dazata bata….bayan takira bintu tasanar mata abinda ke faruwa ne sesukayi shawar cewa bintu zata karɓi yarinyar tayayeta Hakane kawai zesa Alhaji madu baze zargi wani abunba sedai matsalar ɗaya ce bintu a Nigeria take aure amma dudda Hakan tafison Kaita Nigeria gun bintu dadai takaita gidansu gun Hajiya tabawa.Bayan Alhaji Abdussalam yadawo gidan take shaida mishi cewar aminiyarta bintu keson tayaye letteiy kuma idan tahana mata ita zataga kamar tana guduntane tunda tafita kuɗi kuma mijinta yafi nata kuɗi zataga kamar ƙyanƙaminta takeyi kilama yazama sanadiyar rushewar amintakarsu kuma tasan abbanta bazeji daɗi ba dubada irin temakonda mahaifin ita bintu yayi musu…da Alhaji Abdussalam yaji Hakan seyace shibaze iya gayawa Alhaji madu Hakanba sedai ita takirashi dakanta tagaya mishi…hakanko akayi bayan takira Alhaji madu tasanar mishi seyaji daɗin da tayadda zatabawa bintu ƴarta yaye koba komai amin takarsu zata ƙaru. Sosai Hajiya Hannah taji daɗin amincewar mahaifinta sedai da Hajiya tabawa taji wannan labarin jitayi kamar tasakawa kan wuƙa sabida baƙin ciki sedai dudda Hakan bata karaya ba mummunan kuɗirinta nanan maƙale aranta.Alhaji Abdussalam kuwa dayaji cewar Nigeria ne bintu ke aure sosai hankalinshi yatashi akan kai ƴashi Nigeria inda yace sam besan wannan zancenba, seda Akakai ruwa rana tukunnah ya amince Hakan suka shirya tafiya Nigeria shida Hajiya Hannah gidan mama bintu……….bayan zuwansu Nigeria da kwatance dakiran waya suka gano garin gombe inda sukazo gidan mama bintu suka samu itada mijinta mlm Musa dayaronsu ɗaya Kabir sedai mlm Musa nada wasu matan daban, mamansu yah balah dakuma iyya hassi wanda be haɗesu gida ɗaya da mama bintu ba sabida bayada gidan daze ɗaukesu su ukku….da Alhaji Abdussalam yaga gidanda mama bintu kezaune hankalinshi bekwanta dazaman ƴarshi agidanba Hakan yasa yasiyawa mlm Musa wani gidan ƙato sosai wanda ba mace ukku ba ko goma ze iya ɗauka kuma yabashi jari tare da kuɗin daze kulada ƴarshi kafin yakarɓi abarshi, ahakan suka damƙawa mama bintu da mlm Musa amanar maryama kana sukabar kasar Nigeria tare da ɗimbin kewar ƴarsu da alkawarin bana da mama bintu za’aje aikin hajji. ahakan suka tafi Hajiya Hannah na kukan rabuwada ƴarta.Bayan tafiyarsu Hajiya Hannah Abba wato mlm Musa yanemi alfarmar mama bintu akan yahaɗesu gida ɗaya itada matanshi…bata kawo komai aranranta ba ta’amince Hakan yasa yamaida mamansu yah balah gidan da iyya hassi daga baya kuma ya auro mama salmu wadda duk itace ƙarama acikinsu….alokacinda su iyya hassi suka samu mama bintu da ƴarta ƙarama basuyi tunanin ba yarta bace kasancewar ko lokacinda tahaifi Kabir a ƙasar su Niger Basu saniba seda Kabir ya shekara biyar aduniya lokacinda suka dawo Nigeria dazama ne sukasan dashi shiyasa basu tambayi kowa akan yarinyar dasukanta da itaba. Kabir ne kejiran maryama da Isseta wato (ƴar uwata) dayaren filatanci Hakan yasa duk yaran gidan kekiranta da hakan sekawai Isseta yabita..maryama tun tana ƙarama batada rigima kuma shiru shiru takai batason haya niya sedai duk wanda yatsokaneta seta rama gatada ƙarfin tsiya. sosai mama bintu taji daɗin yadda Isseta keramawa idan yara sa’anninta sukayimata wani abun domin bataso tayi magana ace tashiga faɗan yara kasan cewar gidan Yakoma gidan yawa yanzu tunda mamansu yah balah yaranta biyar. Yah balah shine babba agidan gaba ɗaya, se Hashimu, badauyi, hafizu sa’annan bilkisu…iyya hassi kuwa yaranta ukku hawwa’u zubaida sekuma juwaira..yayinda mama salmu keda ɗaya jidda….ita kuwa mama bintu Kabir ne kawai ɗanta sekuma Isseta ayanzu.To ganin yadda Isseta ke dambe dayaransu kuma babu me iya doketa harmanyan rawar ƴan bori suke tsakaninsu da ita yasa iyayen fara tsanarta gaya kuma duk tafi yaran gidan kyau hakama abba yana nuna mata so dakulawa sosai kasan cewarta ƴar amana.Bayan shekara ɗaya mama bintu tabuƙaci mayarda Isseta agun iyayenta sedai abin mamaki sam sunƙi amincewa dahakan Sema cewa sukayi taci gabada zama agunta domin tasan minene rayuwa kuma tayi karatun addini dana zamani anan bazasu karɓeta ba seta gama ƙaramar makaranta, Hakan yasa Alhaji Abdussalam aikowa da Abba maƙodan kuɗaɗe akan yasaka maryama makaranta dakuma bukatunta na yau da kullun…wannan abin baƙaramin mamaki yabawa su mama bintu ba amma Hakan suka danne inda Abba yasaka Isseta makarantar kuɗi dake cikin garin gwambe yayinda yaranshi keyin tacikin rugar tasu……Hakan kuwa yaɓullo da wani sabon tashin hankalin acikin gidanshi domin sosai su iyya hassi suka ɗauki abin da zafi inda suke faɗar yafifita Isseta akan sauran yaransu kamar itace ɗaya ƴarshi kokuwa ita ƴar gwalce. Da wannan ɓarakar takunno kai mama bintu taso sanardasu cewar Isseta baƴar mijinsu bace abbantane yabada kuɗin sakata makarantar ba mlm Musa ne yasakataba…..amma se mlm Musa yace tabarsu karta gaya musu domin ayanzuma dasuke kallon ƴarshi ce suna hantararta inaga sukasan baƴarshi bace….da mama bintu taji Hakan setace to lallai sedai yamaidasu makaranta ɗaya domin kawo zaman lafiya acikin gidanshi.Haka kuwa akayi inda suma dukkansu yasakasu makarantar kuɗin tare da Isseta sukaci gabada karatu tare ananne Isseta tahaɗu da Halima har jininsu haɗu suka fara ƙawance sekuma yazama Halima ƴar umguwarsu ce basuda nisa tsakaninsu. Ahakan suke karatunsu hankali kwance suna ƙawancensu….bayan shekara ɗaya Isseta na class 2 amakaranta sunfito breakfast aka Nemi Isseta akarasa har akatashi daga makarantar babu Isseta babu dalilinta wannan abin yayi masifar ɗagawa malaman makarantar hankali sabida mlm Musa amanarta yadamƙa musu, Hakan yasa Basuyi ƙasa a guywaba suka kirashi sukasanar dashi abinda kefaruwa. Humm wannan lokacin kuwa mlm Musa yashiga tashin hankali marar misaltuwa inda yabazama neman Isseta lungu dasaƙo tare da kai repond awurin police ɗin garin….da labari yariski mama bintu kuwa ƴar ƙaramar hauka tayi akan wannan al’amarin domin kuwa har suma seda tayi inda daƙyar akasamu tafarfaɗo sedai fa firr anƙi samun kanta domin gabaki ɗaya ta birkice musu…abinda yaƙara ɗagawa waƴannan bayin Allah hankali shine har aka kwana biyu da wuni babu Isseta babu dalilinta kuma anyi neman duniya ba’agantaba…akwana na ukku ne bayan sallar magarib….!



