Hausa novels

Mejo Najeeb Page 9 By Autar Alheri

“Tana cikin wannan tinanin tajuya ganin Isseta tasunkuya alamar Tayi bacci, shiru Tayi tana tinanin yazatayi da ita? Amma ganin batasamu wata mafitarba kawai seta gyara mata kwanciyarta tareda komawa gefe tana kallonta, sedai ko minti 20 batayi awurinba wani mugun zafi yataso mata sabida Bata Sababa ba yadda za’ayi Ta’iya zama a tudu ba’acikin ruwaba. Amma ahakan tadaure kusan minti 35 sedai zafin naneman illatata Hakan yasa tafad’a cikin ruwan babu shiri….seda Tayi nitso nakusan minti 3 kana tafito bayan wasu minti 3 tak’ara komawa ruwan akayi wasu minti 3 tak’ara fitowa,, atakyaice dai ahakan suka kwana har inda gari yawaye tashiga ruwa tafito tana gadin Isseta d’in…sedai abunda yabata mamaki shine shigarda Tayi ruwan na k’arshe Koda tafito tasamu Isseta kwance akan wata y’ar katifa me kyau sosai Kuma anyi mata shimfid’a kamar wata y’ar baby. Abun yayi bala’in Bata mamaki sedai kafin tasamu zarafinyin wani abun Sega wata kyakkyawar mace tafito itama rabinta kifine rabinta mutin sedai banbancinsu ita maah taruwace itako wannan ta tudu ce( gawanda Basu fahimta ba ga takyaitaccen bayani. “Dama ita wannan aljanar wato hajo ruwa kala biyu ce Allah yahalitta d’aya acikin ruwa take d’aya Kuma a bakin ruwa take ma’ana akan dutse wadda Sam Bata damuda ruwaba Amma Kuma tanashiga ciki. Itako taruwa Sam batason Tasha iska sedai Kuma ahakan tana fitowa waje. To kunji yadda suke sabida Hakan idan Kun fahimta ita wannan data fito ayanzu takan dutse ce🧏)Ajiyar zuciya maah tasauke ganin aminiyar tata domin ko acikinsu akwai way’anda Allah ke had’a jininsu sukasance abokanai ko k’awaye…..k’arasawa Tayi wurin maah suka gaisa kama tagayamata itace tayima Isseta Hakan Dama tinjiya tana kuleda ita Bata cikin ruwa Bata waje Hakan yasa taduba abunda takeyi awajen ganinta tareda wannan yarinyarne yasata fito domin Taga ko wacece sekuma Taga Ashe maryama ce…hakane kam wlh anan takwana domin matsala sukasamu da babanta a,nan maah tabawa wannan k’awar tata labarin abunda yafaru agidansu maryama….sosai tajajanta abun inda tad’auki alkawarin Tayata kulada Isseta.To acan gida kuwa mama bintu Bata rintsaba yadda Taga Rana haka Taga dare tin lokacinda yah Kabir yasanarda ita shikam bega Isseta ba gashi Kuma bataji dagasu sulaiman ba Hakan yak’ara hanata samun nutsuwa inbanda addu’a babu abunda takeyi..misalin k’arfe 8:00am halima tashigo gidan Domin itama da Isseta takwana aranta Sam takasa samun sukuni ayadda Taga Isseta cikin tashin hankali jiya bayan sundawo Hakan yasa tazo tinda safennan Dan Taga Isseta d’in taji mike faruwa sedai tana shiga taji abunda Sam hankalinta baze d’auka ba, wai Isseta Bata kwana agidaba Suma nemanta sukeyi acewar mamansu Yah balah. Inda iyya hassi tak’ara dacewa tinda safe tafita ajiyan Kuma haryanzu batadawoba…tofa wannan zancen shine yasaka kokwanto azuciyar halima domin dai jiya tareda ita suka fita Kuma atare suka dawo to miyasa yanzu sukecewa wai tinsafe ne batanan? Wannan abun yayi bala’in d’aga hankalin halima Hakan yasa Takoma gida tana kuka bilhaqqi tasanarda innarta abunda yafaru……..mama bintu kuwa se yanzu su sulaiman suka kirata suna sanarda ita cewar Sam basuga Isseta ba sunnemeta sama da k’asa Amma Basu gantaba. Tofa awannan lokacin tashin hankalin mama bintu yak’aru yadda bakwatinani Tayi kuka harta godewa Allah, cikin tashin hankali da mugun b’acin Rai tanufi d’akin Malam Musa Abba kenan, azaune tasameshi Shima yabuga uban tagimi. Cikin takaici da bak’in cikin wannan abun dayayi tace “wlh Malam Bakaga komaiba tagumi yanzu kafara tinda kakori maryama daga gidannan nasan kanada yak’ini akan cewar lokacin bukatar ta yakusa Kuma idan wannan lokacin yazo sekatanadi amsar badawa akan b’atanta domin wlh bazan tab’a rufamaka asiriba akan wannan al’amarin, kabiyewa son zuciya da makircin matanka kajefamu cikin tashin hankalin da bamusan lokacin fitarshiba. D’an shiru Tayi kamun tanisa tacigabada fad’ar inaga kunshiryawa k’are rayuwarku ne agidan kaso konace kashiryawa k’are rayuwarka agidan kaso shiyasa kayi hakan, domin idansu basusan wacece maryama ba aikai kasani Amma katake sanin, shikenan zamuga yadda abun zek’are, tana gama fad’ar Hakan tafice warta ranta amugun b’ace…Abba kuwa da tinda tafara magana hankalinshi yak’ara tashi matik’a se ayanzu yake K’ara danasani akan abunda ya aikata tabbas yad’ebo ruwan dafa kanshi zekuwa dahu idan ba Allah yaceceshiba. (Humm Malam Musa kenan🙄seyanzu kasan Hakan😏 tukunna ma wacece maryama dahar kuke wannan zantukan akanta?🤔)LagosBanana islandKwance yake akan makeken gadonshi Yana sharar bacci sedai daga ganin yadda yake baccin kasan cewar bayajin dad’in yinshi kawai de yanayine…wayarshi ce dage kan bedside table tafara rurin neman d’auki akarona biyu, cikin baccin yaji Kiran wayar yadameshi Hakan yasa yad’aga batareda myyaduba me kiranshiba tareda Kara wayar akunnenshi. Daga D’aya b’angaren general aliyu yace “hello mejo zanfito yanzu muhad’u a airport please lokaci yakusa karmu rasa jirgi. “Okay kawai yace tareda yanke wayar seyanzu ma yatinada yaune tafiyarsu, Hakan yasa yamik’e jikinshi duk badad’i yanufi bathroom tareda rufo k’ofar. Seda yayi brush kana yayi wanka domin tinda yayi sallar asuba Yakoma bacci betashiba seyanzu da general aliyu yatadashi, seda yagama wankan yatsaya kallon halittarshi dake atsaye kullun kamar abunda yake ciyarwa. D’an k’aramun tsaki yaja kamun yajanyo towel ze D’aura kawai idonshi yasauka akan k’ofar bathroom d’in inda akad’an bud’e k’ofar kad’an ana lek’enshi, wani Irin waro Ido yayi kamun yad’aura towel d’in ahanzarce yanufi k’ofar, Amma kamun yak’arasa tuni akabar jikin k’ofar. Yana fitowa wulgawar mace kawai yagani ta glass din window d’akin, Hakan yasa yajanyo jallabiyyarshi kawai yazura tareda fitowa daga bathroom d’in amugun hasale. Yana fitowa parlor yayi turuss ganin Ummi kawai a perlor Tama goge’goge ga dukkan alamu sharace zatayi….k’ank’ance golden eyes dinshi yayi kamar yadda yakeyi idan zeyi wata tijarar Yanabinta dawani mugun kallo cikin mugun mamakinta datafasar zuciya. Allah sarki baiwar Allah itako se aikinta takeyi batamasanda yanayiba…shikuwa gabaki d’aya k’wak’walwarshi tagama bashi cewar itace ke lek’enshi kawai tanason renamai hankaline shiyasa Tayi kamar shara zatayi mishi, sabida tasan kafin tagudu yakamata bari tayimishi pretending.Cikin bala’i yadaka mata tsawarda seda tasaki glass cup d’inda ke hannunta tana zare Ido, cikin tafasar da zuciyarshi keyi yabud’e Baki babu alamar rahama a murmushi yace “Ummi ni sa’arkine? Sabida Kinga nabaki damar shiga part na shine zakimaidani abokin wasarki? Mikike nema ajikina? Mikikesan gani ataredani dahar Zaki iya lek’e na abayi? Ina yayanki Ummi har renin dakikayimun yakai Hakan? Yatambaya Yana wani Irin huci kamar kumurci…..Ido Ummi tazaro cikin tashin hankali da mugun fargaba tabud’e Baki cikin inna’inna take fad’ar “wlh..wlh Allah ya najeeb narantse da Allah bani ba…gum Tayi dabakinta tanaja Baya ganin yayo kanta gadan gadan kamar mayunwacin zaki.”Dakata najeeb karka kuskura katab’amun yarinya wlh kaji nagayamaka. Yatsinkayo muryar dadynsu Hakan yasa yatsaya cak batareda yak’arasa gurintaba Kuma besauke hannunshi dayayi niyyar marintaba….shikuwa dady karasowa yayi cikin parlor yazo gab da najeeb d’in kana yace “wai miyake damunkane najeeb? Kanada hankali kuwa? K’annen Nakane zaka Saka agaba damugun alkaba’i? Jiya kadaki mansura kana fad’ar wai tazo gunku tsirara yanzu kuwa zaka daki Ummi kana fad’ar tana lek’enka abayi shinwai minene matsalar kane? Kodan kaga nasaka maka Ido shine Zakayi abunda kaga dama, sokakeyi kalalatamun yarane ko Yaya? Awannan karon d’agowa najeeb yayi arazane cikin mugun mamakin kalaman mahaifin nashi yake kallonshi. “Yes najeeb kallon me kakemun? Koba hakabane? Inba lalatamun su kakesanyiba zaka zauna kana musu wannan furucinne? idan mace kakeso atareda Kai bazaka nema awajeba se acikin gida? Humm shikenan ai nasan maganinka, Yana gama fad’ar Hakan yacewa Ummi Maza tawuce seda yasakata agaba kana yabi bayanta sukabar part d’in nashi.Da kallo mejo najeeb yabisu harsuka b’acewa ganinshi gabaki d’aya yadaskare awurin da mamakin mahaifin nashi domin Sam beyi tinanin k’iyayyar da dady kemasa takai Hakanba, shinkodai bashine yahaifeshiba? Yayiwa kanshi wannan tambayar dabame bashi amsarta ayanzu…ganin tsayuwar ba’abunda zata k’ara mishi Sema b’ata lokacinshi dayake k’arayi gaya sekiranshi general aliyu keyi Hakan yasa Yakoma bedroom dinshi kawai cikin kunar Rai yashiga shiryawa komai beshafaba tirare kawai yafesa tareda Saka kayan yafito janyeda jakar kayanshi, Yana fitowa yaga captain Jameel nazaune a perlor cikin sauri yataso tareda d’aukar jakar sukafito a general parlor yagasu Hajiya Umma da mama zaune se Munir da siyana ga mansura gefe da bandage d’inta duk ajiki. Kallo D’aya yayimusu tareda d’auke kanshi yace “Umma zamuyi tafiyane, semun dawo mama daga Hakan yasakai zefice batareda yajira cewarsuba. “Allah yakikeye Kuma yasa ayi akan nasara, cewar mama…yayinda Umma kuwa tamik’e cikin sauri tana fad’ar zonan my son. Haryakai bakin k’ofar fita parlor yatsaya, shikuwa captain Jameel yayi ficewarshi. Tana zuwa kuwa hannunshi takama tareda nufar bedroom d’inta dashi seda tamayarda k’ofar tarufe kana tad’auko fruit salad a wani D’an jug tabashi tareda manna mishi kiss a ride lips dinshi kamar yadda tasaba kana tarungumeshi ajikinta tsam kamar wasu mata da muji, Kuma tak’i sakeshi kusan minti 2 seda yanemi cire jikinshi daga nata Dan kanshi kana tasakeshi, tareda k’ara manna mishi kiss a kumata tace “adawo lpy yaron Umma…shidai k’ala bece mataba kawai juyawa yayi tafiyarshi..da kallo tarakashi tana tasbihi ga uban gijinda yabata wannan yaron Allah yasani tana mugun son najeeb cikin y’ay’anta tana rokon Allah yabata ikon b’oye soyayyar shi kar Y’an uwanshi sugano tafisonshi akansu domin tasan tabbas Hakan zehaifarda matsala atsakaninsu.Shikuwa Yana fitowa yafice daga gidan kotakan k’anenshi bebiba dayaji suna masa adawo lpy Allah ya kiyaye…a perking space yasamu captain Jameel tareda zugar yaranshi, ruwan roba yakarb’a ahannun captain Jameel d’in yawanke bakinshi kana yashiga motar domin befito da Hankey ba Kuma shidai yatsani wannan kiss d’in da Umma kemishi akan lips sedai ba yadda zeyida ita mahaifiyarshi ce babu abunda zatayi agareshi yace aa Amma Badan Hakanba tayaya zebari wai mace ta tsotsar masa Baki, Allah yasauwak’e mishi wahala da kayan K’azanta. Dawannan tinanin motocin su sukabar gidan inda suka nufi airport kaitsaye acan suka samu general aliyu datashi zugar. Suna Isa kuwa babu wani b’ata lokaci jirginsu yatashi zuwa k’asar nigar……!

Visit Kundin Hausa Novel For More Novel

Back to top button