Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 57 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E57

💋PRISONERS💋

Ya jima tsaye jikin tagar ba tare daya motsa ba, zuciyarshi na raya mashi akan ya koma ya taimake ta, sai dai tsoro ya hana shi yin hakan, Ajiyar zuciya ya sauke tare nufar cikin toilet ɗin, wankan ma da ya shigo da niyar yi ya fasa, ƙopa kawai ya buɗe ya fito ya shiga ɗakin su.

A zazzaune ya same su saman gadajen su, angel ce kaɗai kwance saman nata gadon da alama bacci ya ɗauke ta, tunda Gabriel ya shigo idanuwanshi na akan kowannan su, damuwace danƙare akan fuskokinsu, In ka cire mutun uku, Majnun da jamima da ke ta yin rawa tsakiyar ɗakin su, yau ta biye mishi suna wasa a tare, duk da a shekaru Majnun ya girmi Jamimah.

bayan su sai Sarah dake yanke akaifar hannunta da nail cutter ɗinsu, tana zaune saman shimfidarta dake a ƙasan gado, don ita tuni ta yafe hawa gado, komai nata a ƙasa take zama ta yi shi, Hankalin ta kwance babu damuwa akan fuskarta, Danish yana daga kishingiɗe saman bed ɗinsa, ya ɗan lumshe eyes ɗinta, sam babu walwala akan fuskar shi, Azeeza tana zaune saman gadon parveen, ta ɗaura kanta saman shoulder dinta, magana su ke yi ƙasa ƙasa a takaninsu, haris da deeja suna fuskantar juna, sun nutsa cikin tattaunarsu duk dai akan Batul ne, idan muka koma 6angaren su Hanna ita da hibba da Yasmin da eve da rubina kowaccensu na kwance saman gadonta, sun yi likimo kamar masu yin bacci, Zuciya ce ba daɗi, dole jiki yai sanyi, yar gida daddy kuwa bacci ta ke yi sai dai ga dukkan alamu babu lafiya ajikinta, kamar zata faɗo daga saman gadonta, a cikin bacci take murza cikinta da hannunta na dama, idanuwanta sun kumbura, ga sahun marin da Danish yai mata gefen fuskarta kamar jini ya kwanta.

Zuciyarshi a hautsine Ya ƙarasa gefen gadon shi ya zauna, Ya rasa wa zai tunkara game da zancen haura war shi taga, so yake ya sami wanda zai faɗa mawa, ko don su je su ɗauko yarinyar nan da ya gani, tabbas yana ji aranshi cewa mutun ce ita ba Aljana ba, shiyasa abun ya tsaya masa aranshi, gani yake kamar bai kyauta mata ba, yanzu da ace sister ɗin shi ce, acikin wannan mawuyacin halin bazai ta6a ƙyale ta ba, duk runtsi duk wuya sai ya taimake ta, but why ya gaza taimakon ita wannan yarinyar, girgiza kai ya ɗanyi kamar wanda aka zunguri bayanshi ya miƙe Ya cigaba da yin zarya cikin ɗakin nasu, Ji ya ke kamar ya je ya faɗa ma Danish sai dai yana matuƙar kokwanto a kan shi, Kuma yana ji aranshi zaiyi wuya ya bashi haɗin kai don su shiga cikin kurkukun.

To waye zai iya faɗa ma zancen nan? Nutsawa yae cikin tunaninshi, nan take zuciyarshi ta Amabaci sunan ANGEL, tunawa yai da lokacin data watsa ma Giants ruwa a jikin su tana zazzaga musu masifa, hakan yasa shi yarda cewa Yarinyar ba ƙaramar jaruma ba ce, bata da tsoro kuma tana da ƙwarin gwiwa, dama tun ranar da aka kawo su ya lura da yadda take tafiyar da rayuwarta da kuma ta ƴan uwanta tamkar itace ta haife su, ta zama jagora acikin su, kuma ya fahimci cewa yarinya ce ita bata kai shekarunsu Hanna ba, amma tafi su wayau da hankali.

Tun da ya fara zarya acikin ɗakin, su parveen su ke ta kallon shi, hatta Danish ya ankara dashi, kamar akwai wani abu dake damun shi, sam bai lura da kallon na shi da suke yi ba, A ƙarshe zuciyarshi ta saƙa mishi cewa

_Ita kaÉ—ai ce zata Iya taimaka maka wurin nemo Æ´ar uwarka, tun da itama tana neman tasu Æ´ar uwar da aka É—auke, Idan ku ka haÉ—a hannu da ita, za ku iya cimma nasara, don haka karka kuskura ka faÉ—ama kowa, Ita kaÉ—ai zaka sanar mawa_

Muryar Azeeza ce ta katse mishi zancen zucin mashi ta hanyar yi mishi magana

“ÆŠan uwa, me ka ke tunani ne? Tun É—azu na lura da kai sai zarya ka ke yi mana acikin É—aki, nace anya lafiya kuwa” Murmushin yaÆ™e ya Æ™aÆ™alo akan fuskarshi tare da juyar da kanshi Ya fuskanci inda azeeza take zaune ita da parveen. Kamar wasu tagwaye

“Ina tunanin rawar da zan koya ma ku ne ko ba ku so”? Ya faÉ—i hakan ne don kar su yi tunanin wani abun ne na daban ke damunsa.

Har suna haÉ—a baki wurin cewa”Muna so mana, dama zuciyar mu duk ba daÉ—i wlh, kwanakin nan mun rasa farin cikin mu”

“Kada ku ta6a bari damuwa ta hana ku jin daÉ—in rayuwar ku, saboda kowa yana da damar da zai sanya kan shi farin ciki, yawan zama kuna tunanin zai iya haddasa muku matsala, just ku yi abunda ranku ke so, zaku samu farin ciki” acewar Gabriel

Parveen tace”Angel tana koya mana yadda zamu motsa jiki, da karatu sannan tana bamu tarihi da labarin gidan daddynta, har ma ce mata tayi wata rana zata yi Æ™oÆ™ari don mu fita daga cikin kurkukun nan………” natsuwa gabriel yai a yayin da yake sauraran maganar parveen, da alama ya Æ™ara samun wani abu da yake son ji agame da angel, da sauri ya nufi gefen gadon dasu azeeza suke zaune, shima ya zauna.

“Inaso ku bani duk wani labari da angel ta baku agame da rayuwar ta, da kuma abubuwan da ta koya maku” BuÉ—e ido sosai Danish yai daga can saman gadon shi yake kallon bayan Gabriel dake zaune gefen su parveen, Mamaki ne ya kama shi for what reason Gabriel zai dinga yi musu tambayoyi kan angel! Menene alaÆ™ar shi da ita? Why yake son ji”? MiÆ™ewa zaune Danish yai saman mattress É—in, ya jingina bayanshi jikin bango, ya tsare su da ido, Tabbas da ace yasan dalilin da yasa gabriel ya tambayi su azeeza su bashi labarin angel da ya dakatar shi.

Parveen ce ta labarta mishi komai game da angel, tun zuwanta kurkukun da irin É—awainiyar da ta yi masu, har zuwa ranar da aka kawo su Gabriel cikin kurkukun.

Jinjina kai gabriel yai alamar ya gamsu da labarin da parveen ta bashi na angel,

Azeeza tace”mu taso ka koya mana rawar? Idon shi akan fuskarta yace”nafi so mu yi tare da angel, mu bari ta farka,” su ka ce mi shi toh, zasu jira ta farka, MiÆ™ewa Gabriel yae daga gefen gadon parveen, yana juyawa suka haÉ—a ido da Danish, ya É—aure fuska, ta6e baki Gabriel yae tare da wuce wa Ya nufi nashi gadon ya zauna yana jiran farkawar Angel.

Lokacin da marece ya nutsa, suna zaune, Unaiza tafarka jikinta nata kerma hannayenta dafe da Cikinta, saukowa tai daga saman gadonta, da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, bayan ta shiga toilet ɗin agaban magudaji ta zuƙunna tana ƙwara amai, tamkar ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago, temperature ɗin jikinta ya yi zafi sosai, tana acikin mawuyacin hali, an rasa me zuwa wurinta ya taimake ta.

Tun daga cikin sashen toilet É—insu har izuwa cikin É—akin su, Sautin kakarin amanta ne Ya karaÉ—e ko’ina, Ya addabi kunnuwansu, ganin sunÆ™i motsawa suje su taimake ta, yasa azeeza ta sauko daga saman gadonta, parveen hada cewa”Zuwa za ki yi? Baki ji abunda angel tace mana akanta ba? Salon saita shanye maki jinin ki ko”? abunda suke jima tsoro kenan shiyasa suka Æ™i zuwa su taimake ta, shi kuma Danish abunda ya hana shi zuwa wurinta gudun kada yabar É—akin Gabriel ya samu damar zuwa wurin angel, saboda ya fahimci cewa so yake yayi magana da angel.

“Ai bata da lafiya, ba zata iya shan jini ba, ni dai zanje na taimake ta ne, kada ta mutu” azeeza ce tai maganar tare da kama hanya ta nufi sashen toilet dinsu, Cikin toilet É—in da take jin sautin shesheÆ™ar kukan Unaiza, ta buÉ—e Æ™oparshi tasa kai ta shiga, A zuÆ™unne ta same ta, Baiwar Allah taji jiki, Cikinta ya É—ame dama bata ci abincinta ba, jikinta sai kerma yake yi.

Ƙarasawa gabanta Azeeza tayi fuskarta da alamun tausayinta ta zuƙunna suna fuskantar juna, bata ta6a tunanin wani daga cikinsu zaiji tausayinta ba har yazo wurinta sai ga azeeza tazo, daƙyar take kallonta saboda nauyin da idanuwanta su ka yi mata, sunyi luhu luhu da su kamar ƙwayar cikinsu zasu faɗo ƙasa launin idon nata ya ciza, la66anta sun yi suntum, sai nishi take yi tana matse cikinta.

“Sannu sister, baki da lafiya ne”? Bata samu damar amsa mata ba, azeeza ta kuma cewa”Pls talk to me, I wanna help you.” Ganin taÆ™i tanka mata yasa azeeza ta MiÆ™ewa tare da nufar inda bucket É—insu yake, ta tarba shi bakin fanfo ta kunna ruwa ya soma sauka acikinsa, Sai da yai rabi ta ja bokitin tana nishi don ba Æ™aramin nauyi yayi mata ba, gefen unaiza ta ajiye bokitin, kafin ta karkatar dashi ruwan cikin ya kora aman da tayi dukan shi, Sauran da ya rage, ta taimaka mata wurin wanke fuskarta, ita kanta azeeza sai da gabanta ya faÉ—i jin irin zafin da jikin unaiza yae, lokacin da ta ke wanke mata fuskar da hannunta, kwata kwata babu Æ™oshin lafiya atattare da ita, hada baki ta kuskure mata.

“Mu koma É—aki, kinji” a wahalce ta É—ago da ido tana kallon azeeza ta É—an girgiza mata kai, yayin da take cizon lower lip É—inta, wani irin raÉ—aÉ—in azaba take ji.

“Pls ki yi min magana mana, ni inaso na taimake ki ne” runtse ido unaiza tayi na É—an wani lokaci, azeeza har ta gaji da tsayuwa, ba dan tana jin tausayinta ba da tuni ta jima da komawa dakin su,

Tana so ta yi ma azeeza magana sai dai ta kasa motsa la66anta, jini har ya fara bleeding ta hancinta, ganin hakan yasa hankalin azeeza ya tashi, da gudu ta nufi cikin É—akin su, a sukwane ta faÉ—o Ciki, Hankalinsu Naufal ya dawo kanta, muryarta har tana shaÆ™ewa wurin faÉ—in”Ƴar gidan daddy bata da lafiya, Hancin ta yana bleeding, dan Allah ku zo ku taimake ta” Shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata, duk da sun tsorata da jin abunda ta faÉ—i,

Ran azeeza ba Æ™aramin 6aci yae ba, hawaye har sun fara wanke fuskarta, cikin Æ™unar rai tace”wai ba zaku zo ku taimake ta ba”? Kamar kurame sai dai suka bi ta da ido, fuskarta a hautsine ta nufi gadon angel, tana bubbuga Æ™afarta tana ambaton sunanta

“Angel wake up, ga Æ´ar gidan daddy can bata da lafiya, ina ta roÆ™on su akan su zo mu taimake ta amma sun Æ™i saurarana”

tana kuka tana magana, DaÆ™yar ta samu Angel ta farka, tana faman yamutsa fuskarta da tayi jawur, saboda kukan da tasha, A hankali ta tsayar da idanuwanta kan fuskar azeeza dake ta kuka, Muryarta adisashe ta furta”meya faru ne”? Cikin shessheÆ™ar kuka azeeza tace”Ƴar gidan daddy ce, tana acikin toilet bata da lafiya hada jini a hancinta, ina ta roÆ™onsu akan su zu su taimaketa amma sunÆ™i su saurare ni”

Ɗaya bayan ɗaya angel tabi kowannansu da kallo, ita Sarah bacci ne ya ɗauketa bayan ta gama yankar akaifar, amma sauran idonsu biyu, lokaci ɗaya ta fahimci dalilin dayasa suka ƙi zuwa su taimake ta, saboda tace musu ita mayyace, zata iya shanye musu jini, duk da ita ta yi hakan ne don ta sanya musu tsoronta acikin zuciyar su, gudun kada ta lalata musu rayuwa.

Saukowa Angel tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi sashen toilet É—insu azeeza tabi bayanta, Suna shiga Cikin toilet É—in da Unaiza take suka same ta kwance Æ™asa, idanuwanta sun juye, Hankalin angel ba Æ™aramin tashi yai ba, zuÆ™unnawa tayi agabanta tare da sanya hannayenta biyu ta ruÆ™o kafaÉ—unta, ta É—ago da ita zuwa Æ™irjinta, ta faÉ—a, nan take angel taji zafin da ke ajikin unaiza na fitar hayyaci, hatta nunfashinta da hucin zafi yake fita, ta rasa gane wani irin ciwo ne ke damunta, kamar hada zazza6i, raba jikin su tai daga na juna, ta sanya hannu ta tallabo fuskarta, muryarta na kerma tace”Unaiza meke damun ki? Wani irin ciwo ne wannan”? Biji biji ta ke kallon angel, duk da tana acikin mawuyacin hali, sai da tayi mamakin ganinta, don bata ta6a tsammanin wani daga cikinsu zai iya taimaka mata ba, motsi ta soma yi da la66anta, sunan allura ne take faÉ—a musu wadda ake yi mata agida, idan ciwon ya tashi, sai dai sun gaza fahimtar me take cewa, koda ace ma sun gane, basu da hanyar da zasu iya samo mata allurar,

“Azeeza É—auko min mayafin nan na kayan mu,” ta amsa mata da toh, É—aki azeeza ta shiga ta É—auko Cotton scarve É—inta, ta dawo ta miÆ™a ma angel bayan ta kar6a, tace ma azeeza ta zauÆ™unna ta ruÆ™e unaiza ajikinta, a cikin bokiti Angel ta tsoma mayafin cikin sauran ruwan da azeeza ta kora aman unaiza, sai da ya jiÆ™a ta matse shi, ta É—aura shi saman jikin unaiza, ta dinga goga mata shi, ta ko’ina, ta yi mata hakan ne don ta samu relief É—in zafin jikin ta.

sai nishi take yi tana fitar da numfashi awahalce, duk in ta ɗaura mayafin ajikinta sai ta zabura, alamar bata son ruwan jikin mayafin na ta6a jikin ta, bayan ta kammala, ta miƙe taje bakin igiyar toilet ɗinsu ta shanya Mayafin, Kafin ta dawo ta sanya hannu biyu ta ruƙo unaiza ta miƙar da ita, jikin ta babu ƙwari, dama ba wata ƙibar kirki ke gareta ba, a haka taja ta zuwa cikin ɗakinsu,

Suna shiga ciki, idanuwansu Hanna suka dawo kansu, gadon unaiza angel ta wuce da ita, tare da kwantar da ita sama, ta juya ta nufi akwati nansu, ta buÉ—e ta É—auko tissue ta koma saman gadon unaiza.

Dashi tai amfani wurin goge mata sauran jinin dake a hancinta, bayan ta kammala ta nannaÉ—e wanda ta goge jini da shi ta cusa su acikin wanda ta kuma yagowa, ta miÆ™a ma azeeza tace taje ta zuba a acikin trash can, ta amsa mata da toh, bayan ta kar6a ta juya ta nufi toilet dinsu, bada jimawa ba, Azeeza ta dawo É—akin, gefen gadon unaiza ta koma ta zauna, ya kasance su biyu ne akusa da ita, jikinta ya É—anyi sauÆ™i, ta É—aura kanta saman pillow, still bata daina nishi ba, hannayenta na asaman mararta, addu’o’e angel ta karanto mata ta tottofa mata saman fuskarta da jikinta.

Hankalin Gabriel gaba ɗaya yana akan angel, yayin da shi kuma Danish nashi hankalin ke akan Gabriel, Ya kafe shi da ido ba tare da ƙyaftawa ba, sarai gabriel ya lura da kallon tuhumar da Danish ke yi mishi, amma sai ya basar.

Saukowa yai daga saman gadon shi ya nufi angel, da sauri Danish Ya miÆ™a shima Ya nufi gadon Unaiza, atare suka tsaya bakin gadon, har suna haÉ—a kafaÉ—a, Kallon mamaki Gabriel yai ma Danish, fuskar angel a yamutse ta kalle su, harara ta watsa ma Danish, muryarta Æ™asa Æ™asa tace”Shi ne ku na ganin bata da lafiya amma an rasa wanda zai taimaka mata acikin ku sai Azeeza”? Gabriel ne yace”Bansan time da ta farka daga bacci ba, hankalina baya akanta,”Danish yace”saboda ke yasa ban je wurin ta ba” ta6e baki ta É—anyi, tare da juyar da kanta, Ta kalli su Hanna tunkafin ta yi magana parveen tace”ae kin hana mu zuwa wurinta saboda mayyace zata shanye mana jini, shiyasa mu ka Æ™i taimakon ta”

Numfasawa tayi yayin da take kallonsu, Acan cikin zuciyarta tana tunanin taya zata fahimtar dasu cewa ba mayya ba ce? Kada su ɗauke ta maƙaryaciya, tun da ita ta faɗa mu su hakan da bakinta.

“Ae bance kada ku taimaka mata ba, idan bata da lafiya, a bun dana hana ku shi ne ku daina bari tana ta6a jikin ku, saboda babu kyau, wani ya kalli tsiraicin ka koya ta6a shi, Itama don batasan babu kyau ba ne shiyasa take yi, amma in muka ja ta ajikin mu mu ka fahimtar da ita zata daina ne…..” tun kan ta rufe baki, Rubina tace”Hada jinin zata daina sha”? ÆŠaga mata kai angel tai alamar eh, su ka ce toh zamu dinga taimakonta daga yanzu, amma itama kija mata kunne ta daina rashin jin magana, kuma ta daina yi mana gorin Æ™irji,” angel tace musu toh, zata ja mata kunne.

Mayar da idanuwanta ta yi akan su Danish dake atsaye, kowannan su ita ya ke kallo, ta rasa gane dililin yin tsayuwar na su akanta.

“Lafiya”? Tai tambayar tana jiran jin amsar su, kusan atare suka haÉ—a baki wurin cewa ba komai,” juyawa gabriel yai tare da komawa gefen gadon shi ya zauna, shi ma danish ya koma nashi gadon ya zauna.

Duk wani motsin Gabriel Akan idon Danish, Ya hana shi sakat, Abu kamar wasa, Ko toilet Angel zata shiga sai Danish yabi bayanta, lamarin ya ɗaure mata kai, a bakin ƙopar toilet ɗin zai tsaya har saita fito sannan yaja hannunta su koma ɗaki, hakan ba ƙaramin 6ata ma Gabriel rai yai ba, shi burin shi su zauna da ita su tsara yarda zasu ɗauko ƴan uwansu, da kuma yarda zasu gudu daga Cikin kurkukun tun da yaji cewa itama tana da wannan ƙudirin aranta, Sai dai ga dukkan alamu, akwai mutun ɗaya da baison hakan ta faruwa, shiyasa ya hana shi sukuni, dama can bai yarda da Danish ba, tun zuwanshi, daga gani yana da wayau, akwai abunda yake 6oye musu, kuma yasan komai akan gidan kurkukun kallon su kawai ya ke yi.

Lokacin da dare ya yi kowannansu yai shirin kwanciya, mutun biyu ne babu alamun zasu runtsa.

Jikin Unaiza ya É—an lafa, da taimakon su azeeza taci abinci kaÉ—an, tun É—azu bacci yayi awon gaba da ita.

A tsakiyar É—akin Gabriel ya dinga sintiri yana jiran bacci ya É—auki Danish, Ko ya samu yaje su yi magana da Angel, amma É—an tahalikin nan YaÆ™i kwanciya, Æ™arshe ma daya ga dagaske Gabriel ba bacci zaiyi ba, sai ya É—auki pillow É—inshi, Ya koma saman gadon Angel da ke kwance tana yin bacci, Ya É—aura pillow É—insa saman mattress É—inta, ya hau ya zauna tare da jingina bayan shi jikin pillow É—in,’ mamaki Æ™arara akan fuskar gabriel, Ganin wani iko na Allah, a dole ya haÆ™ura ya koma kan nashi gadon ya kwanta zuciyarshi acunkushe da tunani kala kala,.

Dare Ya nutsa sosai, Sunyi nisan kiwo acikin baccin su, har time ɗin Danish na zaune saman gadon angel, ahaka bacci yai awon gaba dashi, Ba zato ba tsammani, Unaiza tafarka tana ihu tana daddafe cikinta, wata irin kururuwa kamar ana zare ranta, a matuƙar firgice masu bacci suka soma farkawa Kowa Yana faman zazzare idanuwanshi, Haƙiƙa sunyi matuƙar firgita, ɗaya bayan ɗaya suka soma saukowa daga saman gadonsu suna tunkarar gadonta, mutun biyu ne basu farka ba, Jamima da majnun, kamar matattu sai sharar baccin su su ke yi, A kewaye da gadon unaiza suka tsaitsaya curko curko suna kallonta hankalin su yai matuƙar tashi, suka dinga tambayarta lafiya meke damunta, amma ta kasa buɗe baki ta basu amsa, Sai cizon la6en ta take yi, yayi suntum dashi, Angel tafi kowa shiga damuwa tsoranta, har ga Allah bata son wani abu ya samu unaiza duk da baƙin halinta tana ƙaunarta.

“Yanzu ya zamuyi da ita? Danish ba wani taimako da zaka iya yi mata? Angel ce tai maganar tana kallon shi, yae shiru bai ce mata komai ba,

Haris yace”ni fa inaga kamar kalar ciwon da su Hanna suka ta6a yi ne” gabansu ne yai wani irin mugun bugu jin abunda Haris yace, muryar deeja na arude tace”In sha Allah ba shi bane,” Azeeza tuni ta fashe musu da kuka, tana zaune saman gadonta, ta kasa saukowa gudun kada ta faÉ—i Æ™asa saboda lalurarta, tana jiyo muryoyinsu acikin kunnuwanta

Suna Cikin yin maganar nan, sautin motsin buÉ—e Æ™opa ya karaÉ—e kunnuwasu, hankalin su ya Æ™ara tashi, nan take ransu ya basu cewa Anzo atafi da ita ne’ jikin su duk yai sanyi, lokacin da su ka yi arba da Giant É—in dake saukowa saman benan, basamudan Æ™ato, Mai É—auke da star 1 agaban rigarshi, tunkan ya Æ™araso ciki, suka bashi hanya, Ya sanya hannu biyu ya É—auki unaiza saman kafaÉ—arshi ya juya ya fuce da ita daga Cikin É—akin, kamar wasu sakarkaru haka suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su, Suna jiyo datse Æ™opar É—akin nasu da akayi, shi kenan an tafi da Ƴar gidan daddy, Gabriel yaso ya tambaye su ina za’a kai ta? Sai kuma ranshi ya bashi cewar wata’Æ™il zasu kaita inda zasu duba lafiyarta ne, hakan yasa shi dakatawa da yin tambayar tashi, dama bai shirya yinta ba agaban Danish, don zai Æ™ara sa mashi ido ne.

Ba su ta6a tunanin zasu zubar mata da ƙwalla ba, saboda babu shaƙuwa atsakanin su da ita, Amma sai gashi yau saboda ita sun gaza runtsawa, a gefe da gefen gadonta matan su ka zauna shiru babu mai magana, Babu yadda haris baiyi dasu ba akan su koma su kwanta saman gadajen su, amma suka ƙiya, A ƙarshe nan suka kwana.

A washe garin ranar da safe, suna ta sharar bacci, wasu sun jingina bayansu jikin bango wasu kuma sun É—aura kawunansu saman cinyoyin Æ´an uwansu, WaÉ—an da suka kwana asaman gadonsu, mazan ne duka sai Jamima da azeeza, Cikin sa’a Gabriel ya riga Danish farkawa daga bacci, Ae yana buÉ—e ido ya hango Danish baje saman gadon shi, yai wuff ya duro daga nashi gadon Cikin sanÉ—a ya nufi bakin gadon unaiza inda suke zazzaune suna bacci, A hankali ya zuÆ™unna inda angel ta jingina bayanta jikin bango, hanna ta É—aura kanta saman laps É—inta, haka su kai bacci jiya, saitin kunnanta yakai bakin shi cikin raÉ—a ya shiga kwala mata kira “Angel! Angel” har cikin dodon kunnanta, ganin tana Æ™oÆ™arin buÉ—e idanuwanta yasa shi yin sauyin É—aura tafin hannun shi saman bakin ta, gudun kada ta razana ta saki Æ™ara Danish ya farka, tsantsar mamaki ne ya kamata ganin Gabriel, ZuÆ™unne agabanta, hada Æ™oÆ™arin toshe mata baki, zazzare mishi idanuwanta ta soma yi, tare da kai hannu zata ka6e mishi nashi hannun daya toshe mata baki.

(Idan kunaso A ƙara one page anjima azuba like kamar 500 haka🥱 )

Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button