Uncategorized

Hira Da Matattu Part 3 (True Life Story) By Jamila Umar Tanko

 HIRA DA MATATTU….3 ( TRUE STORY)

Neman shawara: 

Jut mai masoya, na godewa Allah. Na gode muku masu qaunar rubutuna. Na yi niyyar yin dan short story sai na ga labarin zai takure gaba daya ko rabin sakon da zan isar ba zai iso ba. Amma ban yi niyyar sakin sabon littafi ba anan kusa . 

Shin za ku siya in warware alqalamina in sakar muku labari part 123 ? Ko kawai in takure shi a kara page daya a wuce wajen. 

Na san Mutum guda ma zai iya siyewa ya ce a sake shi kawai kowa ma ya karanta 

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

0023843938

Unity bank 

Jamila umar tanko 

 

Qafata daya a cikin get daya a waje ina zare ido dan ganina ya fara dasashewa, Tabbas Sharifah nake gani da daurin qirji babu riga a jikinta, yayin da dukka jikinta tun daga fuskar har kirjinta mamaye yake da wasu baqaqen kuraje. 

Matar da a iya sanina bata da qurji ko daya a jikinta, tas-tas take fatarta mai kyau sai an wanke hannu za ka taba. 

Kanta babu dankwali tattauran gashin kanta ne ya miqe carko-carko, alhali Sharifah gashinta mai laushi ne ya sauko har kafadata.

Wannan karon tsoro ne ya hana ni gudu dan na fita daga cikin hayyacina . 

Jikina rawa yake ta yi kawai. Na kasa yin addu’a, na kasa tafiya. Na tabbatar na shiga duniyar siradin tafiya lahira ni ma. Dan ko na rayu tabbas ba zan moruba dan na zauce.

Muryar Shartifah na ji a bayana kuma a cikin kunnena, kai tsaye har hucin numfashin na ji ” matsa zan wuce .” 

Na daka tsalle na fada cikin farfajiyar gidan gami da kwalla qara na ce  ” Innalilahi, na shiga uku.’ 

Na waiwaya da sauri na dube ta, tabbas ita din ce dai ta shigo. Wannan karon sanye take da kayan makaranta. Yanzu kuma da suffar yara a bayyana ‘yar budurwar da bata wuce shekaru goma sha shida ba.” 

Kamar yadda na kula a baya Sharifah tana yi min magana ba tare da ta hada ido da ni ba, yanzu ma haka. Sannan maganar a takaice ne, kuma kalaman ba irin na mutane ba ne sak.

Na dafe qirji ina rawar dari bayan na yi nesa da ita . Muryata na rawa na tambaya “Sharifah me na yi miki? Dan Allah ki yafe min idan na yi miki laifi, mun dade ba mu hadu ba. Ban san ma ba kya raye ba.”

Ta dube ni qasa-qasa ta ce ” ba Sharifa ba ce, Sunana Hamidah ni ‘yarta ce.”

Na waiwaya da sauri wundon da nake ganin Sharifah, babu ita ta b’ace. 

Na tambaya a gigice “Ina mamarki?”

Ta yi dum kadan, yayin da idanuwanta suka yi jajawur cike da kwalla ta ce “ta ras “

Hankali ya sake tashi na na fada a gigice “Wacece ta rasu?”

 Ta amsa ” Mamata tun waccan shekarar.” 

“Wacece mamarki Sharifah ko Shariqah?” Wannan karon kallona ta yi da jajayen idanuwa mai dauke da hawaye masu kwaranya. Sai kawai na ji wani abu ya tsargo  min yarrrrr tun saga qafata har cikin kaina . 

Ta nufi cikin gida ba tare da ta sake kula ni ba . 

Na zabura na sake tambaya “yanzu wacece a cikin gida?”

Ta na tafe ta amsa min  “Mamata ce.”

Kamar daga sama na jiyo muryar Sharifa ta ce ” “Hamidah! Hamidah!! Hamidah!!! ki saka sakata a gidan nan, ki cewa baquwar nan ta shigo.”

Hamidah ta juyo da zunmar saka sakata a get sai na na zabura na ce ” Sakata kuma? Ba da ni ba, na fice da gudu.”  Sai a lokacin na shaqi iska mai sanyi don na fito daga cikin ukuba.

Hamidah ta tsura min ido tana kallo ban san tunanin da take yi ba. 

Can ta ce “Mamata ta ce ki shigo.”

Na zare ido na ce ” in shiga ina? Wacece mamar ta ki?Bayan kin ce ta mutu.”

Amsar da ta bani ita ta sake tabbatar min wadannan ba rayayyu ba ne , ta ce da ni “Mamana ta fada min akwai rayuwa bayan mutuwa ai.”

Na zazzare ido yayin da na fara nemowa kaina hanyar tsira da alama da Sharifah nake magana, ta canja suffa ta koma yarinya ‘yar makaranta. Wato rayuwa take yi bayan mutuwa kuma tare da ni take so ta yi. 

Na falfala da gudu, saura kiris adaidaita ya buge ni. 

Zai min fada ya ga ina shidewa, ban yi wata-wata ba na afka ciki na ce “kai ni unguwar ‘yankaba zan biya ka.”

Tambaya yake “Hajiya lafiya?” Dan ya ga ina ta waiwaye. 

Cikin ikon Allah mu na fara tafiya ba mu yi nisa da gidan ba sai ga Yara guda biyar sanye da kayan makaranta masu irin fuskar Sharifa na gani a jere sun shigo cikin layin mata biyu maza uku. 

“Hasbunallahu wa ni’imal wakil. Laifin me na yi miki Shafifah? Har kamannin yara kike komawa mata da maza?” Na fada a firgice yayin da na fashe da kuka. 

Yara na kallona ina kallonsu har suka shude. Babu wanda a cikinsu ba irin fuskar Sharifah gare shi ba, har dariyarsu da maganar dan su na ta surutu.

Mai adaidaita ya ga na miqe na kwanta yayin da ya fara leqe ta mudubi yana fadin “Hajiya kada ki mace min a adaidaita gaskiya. Ki kirawo wasu ‘yan uwanki su kwatanta gidanku in kaiki na ga kin kasa magana. 

Na ce “mu je na san in da zan je lafiyata kalau. Na yi gamo ne.”

“Gamo kuma? Da aljanu?” Ya tambaya cikin gatsali. Yayin da ya kwashe da dariya. Ya ci gaba da waiwayena ta mudubi. 

Daman na san na zautu ni da hankali kuma sai gyaran Allah .

Mun shiga layi ya fi sau uku na manta gidan Nanah Ahmad saboda gigicewa, dakyar na gane. 

Dubu guda na bashi zai tsaya ciniki na ce na bar masa sadaka. Ya na godiya na bar shi na shige get.

Ina shiga get din gidan masu gadi zasu tare ni suka ga alamar babu burki. Gyalena na Jan kasa yayin da dan kwali ya dawo kafada haka a wuya na sakalo jakata. Allah Ya sa ma ba zani na daura ba, doguwar riga ce. 

Falon gidan na fada ban damu da yin sallama ba ko gaishe da mijinta da abokansa, da suke cin abinci a dining.

Dakinta na fada, na iske  bata nan sai yaranta sun dawo daga makaranta suka gaishe ni ma ban amsa ba. 

Daga an yi magana ko an taba qofa sai in ji gabana ya yanke ya fadi, kwakwalwata na tafasa. Na baje akan gadonta ina ta juyi. 

“Kai ku kira min mamarku. Ku ce ta zo dan Allah kafin in rasu.” Na fada cikin galabaita. 

Ashe tuni mijinta ya shiga kicin ya ce ta zo ga Samha amma da alama an yi mata mutuwa bata cikin hayyacinta. 

A guje Nanah ta shigo tana salati, ta kori yara waje sannanta fara jero min lugudan tambayoyi.”waye ya rasu?”

Na ce “Sharifah Nasir ce ta rasu.” 

Ta dafe qirji cikin firgici ta ce “innalilahi wa inna ilaihi rajuun shiyasa mana kullum bata hawa Whatsapp, layinta a kashe kuma ko an kira ta baya shiga. 

Na ce ta dauko waya ta kira dukka kawayenmu ta sanar musu a tafi gidan gaisuwa. 

Nanah ta ce “kafin ayi sadakar uku sai a shirya ranar zuwa.”

Na ce “A ‘a a yanzu zaku tafi kuma ku kadai banda ni, kawai ku je su tabbatar din.”

Nanah ta kafa min ido tana yi min kallon rashin fahimta. “Kamar yaya mu je ba tare da ke ba, bayan kin fi kowa kusa da ita?”

Na ce ta kira dukka kawayenmu su zo gidan nan a taru. 

Nanah ta fara mamakin kalamaina amma duk da haka tana bin umarni duk wacce na ce ta kira sai ta kira ta sanar mata. 

Salati da ihu kawai suke yi yayin da nake qarawa da bayanin su zo gidan Nanah gani nima na zo. 

Rakky da Halima ne suka yi min musu cewa Shariqah ce ta rasu ba Sharifah ba kuma an dade ma fa. Sai dai in yanzu itama Sharifah ta rasu. 

Nanah ta hau musu da su Shariqah bata rasu ba fa ta hadu da ita kwanaki a umra. 

Abin dai ya sake cushe min kai. A cikin mutane tara da muka kira guda hudu sun sami zuwa muka taru. 

Amma su na ta mamakin kidimewar da na yi har ta yi yawa, amma ba abin mamaki ba ne domin an san mun shaqu kawatace ta quttan.

Su ka tambaye ni, ni waye ya fada min? Nan fa gizo ke saqar ban isa in ce na yi gamo da fatalwa ba ne. Dan kada a wuce da ni asibitin saita kwakwalwa. 

Na daure dai ban ce komai ba, da suka dame da tambaya, na ce a radio aka sanar. 

Aka tsayar da shawara aka ce a je gidan a gani. Na dage su je su kadai su bar ni anan, abinda suka gani sai su sanar da ni. 

Tabbas kowa ya cika da rashin fahimta ko kula ni ba su yi ba suka wawuri hannuna muka nufi motocinsu guda uku muka tafi.

Faduwar gaba nake kamar qirjin zai fita yayin da Nanah ke bani haquri, nan kuwa ba ciwon mutuwa ya fi damuna ba gamo da fatalwa ne damuwa ta dan nima ji nake na zama gawa.

Mu na isa muka iske get din gidan a bude, kowa na baza ido ya ga maza da yawa a qofar gida amma qamas.  

Aka Shiga jero min tambayoyi ni dai na yi musu shiru. 

Bello Nasir ne ya fito daga cikin motarsa yayin da ya gaishe mu sai aka shiga yi masa ta’aziyya, yana amsawa da Amin. 

Su ka tambaya har an yi suturar ne muka ga babu  kowa ? 

Ya maimaita “suturar wa?” Su ka hada baki “Sharifah.” 

Sai na ga ya dago ido da sauri ya dube ni ya san wannan maganar daga bakina ta fito.

Ya nuna mana get ya ce ” ku shiga ciki, su na ciki”

Nan da nan suka gasgata maganata yayin da kowacce ta dauki salati. Jiki na rawa suka fada farfajiyar gidan. Ina tafe a baya ina tafiya a hankali. 

Ina shiga farfajiyar gidan sai na ga Bello ya shigo ya na qoqarin rufe kofa ya garqame da sakata. 

Na daka tsalle na tunkude hannunsa na ce “kada ka saka mana sakata da ranar Allah.”

Ya sake cika da mamaki yayin da ya bi ni da kallo har ya shige cikin gida. 

Qafata daya a ciki daya a waje ina jiran arangamar su Nanah da fatalwa. 

Tunda suka shiga suka nutse ban ji ko tarinsu ba. Daga nan na fara tunanin sun shiga duniyar da baa dawowa.

Ban ankara ba na ji mace a bayana ta dafa ni gami da cewa “matsa zan wuce.”

 Ina waiwayawa Sharifa ce sanye da farin hijabi babu yadda zanyi in fita waje da gudu sabo ta dafe qofar.

Ta kalle ni da alamar mamaki sannan ta fashe da wata irin muguwar dariya, ganin yadda na razana na tafe kirji ina karkarwa. 

Ta ambaci sunana sannan ta shigo ciki, babban tashin hankalin sakata ta saka sama da qasa ta kulle gidan. Gami da nuna min hanyar shiga cikin gidan .

Wannan karon umarni take bani ba shawara take nema ba. 

“wuce ciki.” Ta fada cikin gadara

Zan yi mata musu sai kawai ta fisgi hannuna. Shikenan na yi ban kwana da duniya ba tare da na yi sallama da  ‘yan cikinta ba. 

Salati da yawun bakina ya qare sannan na zubar da takalma da mayafi da dankwali anan, tafiya nake kawai ba tare da na san in da zata kai ni ba. 

Madalla da ALQALAMIN JUT

To be continue…..😀😀👍🏻

Hira Da Matattu Part 2 (True Life Story)  By Jamila Umar Tanko


Also Download: Hira Da Matattu 1 to 10 complete

Back to top button