Hausa novels

Matar Hariji Page 6 Romantic Hausa Novel

________📝Tajima kafin taga zaman bazai kaitaba ta tashi ta nufi gidan tana haɗa hanya ta shiga ɗakin gwaggonta ta kwanta tanata sauke ajiyar zuciya zazzabi me zafi ya rufeta zuciyarta cike da tunanin Lameer da maganganunsa da suketa yimata yawo a ƙwanya.___________Kada ya shiga gari kai tsaye gdansu yanufa yayi saa kuw ya tarar da Alh a falon ƙasa yana hutawa ya zauna suka gaisa dashi sannan suka gaisa da hajiya yayi shiru gabansa na faduwa yana tunanin ta inda zai fara.Alh ne ya katseshi da cewa “Magaji meye yake faruwa ne kamar bakinka akwai magana ince dai ba matsala bace a gdan naka?”Girgiza kai yayi yace “ba wannan matsalar bace Alh don allah alfarma nake nema a gurinka”Da mamaki Alh ya dubesa yace “tame babana?” shafa sumarsa yayi yanason faɗar sirrin ransa yanajin tsoron tujarar hajiya.Yanda yake kallonta ne yasa alh cewa hajiya abamu guri yaron nan tsoron masifarki yakeji” taɓe baki tayi tace “bashida gsky ne shiyasa yake tsoron faɗa a gabana” tana faɗin haka ta miƙe tayi shigewarta ɗakinta shikuma alh ya zubawa Lameer ido yana nazarin damuwa kwance saman fuskarsa yace “kai nake sauraro magaji Allahu yasa dai lfy”Sumarsa ya shafa yace “lfy lau Alh dama inason na sanar dakai ne….” sai kuma yayi shiru bakinsa ya sarƙe murmushi Alh yayi yace “kamar ba namiji ba kana mgn kana fargaba ita faɗuwar gaba asarar namiji ce ai Lameer ka fito kayi mgn darect mana”Cikin in…ina yace “in…inason zanyi au…r…e ne dama…” zuba masa ido uban yayi cikin naƙaltar yanayi da mamaki yace “aure wanne irin aure Lameer kana zaune ƙalau zaka tashi hankalinka ƙanƙaninka dakai zaka tarawa kanka iyali meye damuwarka da matarka ta gda?””Bashida wata damuwa da ita saima ita da yake tatawa rashin mutumci kullum cikin ƙorafi take alh kai shaida ne basa wata guda baayi musu sulhu ba wani sabon tashin hankali ma watnnin nan daya sawo kai kaga yaron nan sai suyi watada watanni bai sauke mata haƙƙin aureba kuma wlh ba yau aka fara ba dama duk gdan da kaji an fiya samun saɓani to ɗaya yayi watsi da haƙƙin ɗaya, yo bandama iskancinsa Alh da tsabar ya raina mutane Lameer har nawa yake da zaice zai auri mace sama da ɗaya kuma bayqn ɗayar bata ƙoshi ba, eh mana bata ƙoshi ba mana Alh ci da sha ai duk mace tana samu a gdan iyayenta kwanciyar aure itace aure ai”Tuda ta fara faɗan jikin Lameer yayi matuƙar sanyi baisan sanda hawaye ya fara fita a idanunsa ba tsoronsa Allah tsoronsa suce zasu hanashi auren Hauwah ya tabbatar rayuwarsa ta shiga kwale-kwalen masifa da tashin hankali saboda yanzu hakan jinsa yake kamar ransa hade yake dana Hauwah.Muryar Alh ce ta katseshi da cewa “wai hakane Magaji?” ɗagowa yayi da manyan idanunsa da suka kaɗa sukayi jah cikin sanyin jiki yace “eh hakane Alh amma don Allah kada ka yankemin ƙauna da samun dawwamammen farin ciki Alh Hauwah yarinya ce ƙarama batasan komai ba kafin lkcn da zata fara buƙatata insha Allahu nasamu lfy tunda ina neman magani”_Kuji fa wata gwari_Ajiyar numfashi Alh yayi yace “Wannan falsafar taka akan qarya kayita ka nemi maganin kafin ka buƙaci ƙara aure shi aure meye yakesa ayisa ne Lameer anya ma kuwa kasan sharruɗan aurevoir? To bari kaji wani abu Magaji ko matarka ta gida wato Mubaraka indai kayi wata shidda baka kusanceta ba warware aurenku ya kamata ayi saboda hasashen masana halayyar ƴa mace na duniya ya tabbatar mace lafiyayiya watanni uku take iya jure rashin namiji a tare da ita wannan dalilin yasa kaga addini ma ya sassauta musu yace suyi iddah watanni uku idan rabuwar aure ta gifta”Ɗagowa yayi yace “amma Alh…” katseshi yayi da cewa kaje ka Lameer banson shirme fah” hawayene ya zubo a idanunsa sharrrr ya miƙe a matuƙar sanyaye ya nufi ƙofar ya buɗeya fita ya shiga motarsa ya zauna tare da buga kansa da sitiyari yace “innanillahi wa innah ilaihir raji’un”Daƙyar ya iya yima motar key ya nufi gdansa cikin wani yanayi dashi kaɗai yasan ya yakeji a zuciyarsa yana shiga ya buɗe motar ya fita ya buɗe ƙofar falon ya shiga daƙyar ya iya sallama ya hangi Mubaraka zaune da apple a hannunta Fadwah nata wasanta ta nufoshi da tafiyarta da batayi ƙwari ba ta riƙe masa ƙafafu ya ɗagota a hankali yana amsa sannu da zuwan da Mubaraka takeyi masa ya nufi sama da ƴartasu a hannunsa ya sauketa a saman gado ya dauko choculate ya bata ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa sannan ya dawo ya zauna a ƙasa dirshen yana kallon yarinyar jikinsa yana rawa saboda a rayuwarsa bai iyasa abu a ransa ba.Tunda yake bai taɓajin ciwo da takaicin rashin mazantaka ba sai yau wannan wacce irin masifa ce, shidai yasan yace zai hƙr da Hauwah ma zance ne bazai iyaba yanzu meye abinda ya dace yayi?……………..________📝Daqyar ya tashi ya haura gadon ya kwanta yana tufka da warwara zuciyarsa cunkushe da abubuwa kala².Wannan dare shidai bai rintsa ba asubar fari yayiwa gdansu tsinke mahaifinsa yana dawowa daga masallaci ya tarar dashi zaune tare da maigadi ya tashi da sauri ta tareshi.Shikam Alh saida gabansa ya fadi ya zubawa dan nasa ido yana ayyana wanne irin abune wannan me yake damunsa haka da zai baro gdansa cikin duhun asubar nan.Shiga gdan sukayi yajashi har dakinsa yace “babana meye ya fito dakai da sanyin safiyar nan” shafa kansa yayi ya durqushe yace “Alh na kasa jurewa jiya ban iya rintsawa ba don Allah ka taimakeni ka amince da aurena da Hauwah wlh zuciyata ta kamu da qaunar yarinyar fiye da inda kake tunani Alh komai zai iya faruwa dani idan ka hanani auren Hauwa”Mamaki ne ya cika zuciyar Alh Lameer dinsa me kunya wai shine yake roqonsa ya amince yayi aure to yanzu idan ya amince da wannan aure me yayi kenan? Da ace baisan matsalar Dan nasa ba dasai ya shige masa gaba yayi aure amma yasan matsalarsa.Towai meyema ya dauki hankalinsa haka har ya damu da auren? Katseshi yayi da cewa “kace wani abu don Allah Alh wlh aure suke shirin yimata kuma itama ni takeso zata zauna dani a duk yanda nake nasan bazan samu matsala da itaba tunda yarinya ce wlh nayi maka alqawarin daganan hsr bangon duniya zanci gaba da neman magani kuma duk yanda zanyi naga na sauke haqqinsu duka zanyi insha Allah” Kada kai yayi yace “naji magaji kaje zanyi tunani akai yauwa ya maganar tafiyarka Lagos?” Numfashi ya sauke yace “sunyi posting dina tun sati daya daya wucce wannan mgnr ta hanani tafiya nafiso a gama komai kafin na tafi inyaso tunda Mubaraka tana aiki idan aka daura sai kawai na wucce da Hauwah can”Shiru Alh yayi kuma fa a mgnr dannasa akwai abin dubawa duk lalacewar namiji mace kusa dashi garkuwa ce ko banza sayi hira yace bani kaza ta bashi” ajiyar numfashi Alh yayi yace “kaje idan nayi nazari zan nemeka”Gdy yayi tare da miqewa ya fito sukayi kicibis ds Hajiya itama ta fito saida gabansa yayi wata muguwar faduwa ya tsugunna yace “ina kwana Hajiya” tabe baki tayi tace “lfy meye ya kawoka gidannan da asubar nan?” Shafa kansa yayi yace “nazo naga Alh ne” tsaki tayi tace “au dama mgnr nan tun jiya baa barta ba to wlh tallahi kaji na rantse wannan auren bazaayishi ba indai nice na haifeka bazan yarda da wannan kwadon hatsin barar ba ta gdanma baka iya da itaba balle ka kawo wata” A hassale ya kalleta yace “wai waye yace miki bana iyawada da iyalina ne meye na ragesu dashi ci ko sha ko sutura? Me takeyiwa kanta a rayuwarta to nidai don Allah ki cire bakinki a mgnr aurena Hajiya ni namiji ne kuma tsayayye a gdansa sannan nakai lkcn da yakamata ace nasan daidai nasan akasin daidai”Tafa hannu tayi cikin salati tace “ehhh lallai Lameer kakai harma ka isa wato ni kake fadawa cewa kai namiji ne ko tabdi lallai da aiki a gabana dannan tunda nake dakai baka taba tsallake mgnta ba sai yau saboda kaso qara aure har kake yimin tsawa”Kallonta yayi yana mamaki wai yayi mata tsawa shikam ya rasa wacce irin uwa Allah hadashi da ita da kullum burinta taga kasawarsa tayi masa gori akai.Miqewa yayi ya fice tanata sababin bala’inta ya nufi gdan wan babansa don yasan tunda Hajiya taqi mgnr idan bata sama ya biyowa Alh ba to baza ayiba.Bai boye masa komai ba ya zayyane masa harda takun saqar da suke fuskanta da dangin Hauwah Mal Yahaya yayi qwafa yace “aikuwa ka taro March bakada fili Lameer shi aure nufin Allah ne amma fa zaakai ruwa rana saboda Rugar Sambajo munsansu sanin gaske tun duniya na kwance basa bawa Kado aure ni kaina na nemi aure a rugar amma daga qarshe cin mutunci ya biyo baya da qage hadi da qazafi sufa sun tsani Bahaushe musamman wanda ya hada alaqa da garin Alqalawa Lameer abubuwa da yawa sukaja wannan gabar fah saboda haka indai zakaji shawara ka janyewa auren yar gdan Ardo Jibbo saboda tujararren bafulatani ne fiye da kwatance shi duk cikin yayan Moddibo Durange shine baudadde har ya baudar da yan uwansa wlh ni kaina tsoronsu nakeji sau uku suna fasamin glass din motata saboda wani dalili nasu mara kan gado……………

Back to top button