Ruwan Zuma Page 28 Hausa Novel
(28) Laila ta zauna a kan kujera tana cizon yatsanta har maigadi ya shigo yake fad’a mata ga mai Adaidaita a waje. Kamar tace ta fasa sai kuma tace tana zuwa. Komawa tayi cikin d’akinta ta sako hijab sannan ta fito ta kulle gidan ta shiga suka tafi. A k’ofar gidan ya tsayar da ita zuciyarta na dukan uku-uku domin bata san ko Madu na cikin gidan ba. A hankali take tafiya ta wuce sashen matansa ta tasamma sashen Ammi wanda yake bayan d’akunan matan nasa. A cikin falo ta samu Ammi tare da amaryarsa wato matarsa ta biyu Jamila, suna had’a ido suka kawar da idanunsu domin babu jituwa tsakanin mata biyun, dalilin itama Jamila halin Madu take dashi. Sannan akwai ranar data ta6a yiwa Laila magana cikin wasa wanda take cewa, “Yanda kike zaune tsawon shekarun nan babu miji ai nasan akwai mai rage miki zafi a gefe.�? Wannan magana ta 6atawa Laila rai sosai har ta furta mata cewa bata son tana kawo mata wannan magana ko a cikin wasa. Hakan yasa tsakaninsu har gobe babu jituwa sai dai a gaisa kowa yayi harkarsa. Ummii kuma data ganta fuska babu kwalliya sannan ga ido yayi jaa alamar tayi kuka sai ta sallami Jamila wacce dama k’arar kishiyarta ta kawo wato uwargidan Madu mai suna Hannatu. Bayan tafiyarta ne Laila ta gaishe da Ummii tana tambayar lafiyarta. “Hamdallah, kwana biyu inata son kiranki a waya amma ban samu dama ba. Ina fatan duk kuna lafiya?�? Wannan tambaya da Ummii tayi shi yasa Laila zubar hawaye tace, “Ummii ina cikin tashin hankali, Abul d’ina ya fara shan kayan maye, jiya har giya yasha yazo yayi ta d’iban albarka a gabanmu.�? “Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.�? Shine abunda Ummii take nanatawa tana kama kanta da dukkan hannayenta. “Abul d’in?�? Ta tambayeta don kamar bata gaskata kunnenta ba. Laila ta bata labarin shan wiwin daya fara da abunda yazo ya musu jiya da yamma. “Ummii ban san ya zanyi in 6ullowa wannan al’amarin ba, wallahi na kasa nitsuwa hankalina baya jikina. Shiyasa nazo na fad’a miki ko kinsan wani abu da za’a mishi kafin ya fad’a harkan da yawa.�? Shiru Ummii tayi tana tunani sannan can tace, “Yana gidan Mas’ud ko?�? Laila ta gyad’a kai tana share hawayen fuskarta. “Ki barshi a can d’in, zan kira kawunku Abdi ya nema mishi magani, in ma turashi can za’ayi sai Mas’ud ya kaishi a killaceshi a can, shi da kanshi zai k’i kayan maye ko ajiyewa aka yi a gabanshi. Na rasa gane me yake damun yaron nan, haka kawai ka k’i jinin mahaifiyarka tayi aure? Ki kwantar da hankalinki, da yardar Allah zai daina kinji.�? “Allah yasa Ummii. Sai ina ganin kamar ban kyautawa Aliyu ba dana bari d’anshi ya fara shaye-shaye.�? “Wannan ba iko ko sakacinki bane Laila. Kici gaba da mishi addu’a domin ke uwace, addu’arki bazata ta6a fad’uwa a k’asa banza ba.�? Sai da Ummii ta tabbatar Laila ta nitsu wanda ita kanta Lailan mamakin yanda Ummii ta sake da ita take yi. “Ya zamanku ke da mijin naki?�? ‘Dan daburcewa tayi na wani lokaci sannan tace, “Lafiya, muna zaman lafiya.�? Ummii ta kalleta da kyau wanda Laila ta k’i su had’a ido tana kawar da kanta gefe. “Laifi biyu baya gyara d’aya Laila. Sannan ki gyara ayyukanki sai Allah ya kar6i addu’o’inki.�? “Ummii..�? “Shawara na baki ban buk’aci sanin komai daga gareki ba. Amma ki daina rik’o, abunda ya wuce ya wuce kisa a ranki haka Allah yaga dama yayi kuma ya fiki sanin me yake yi. Komai da kika ga ya faru akwai dalili, ki bi yanda Allah yayi sai kiga kin tsira kin kuma yi nasara a k’arshe.�? Sunkuyar da kai Laila tayi k’asa tana aikin tunani, a nan ta gane har lokacin akwai halinta da bata daina ba wato al’amarin ‘yayanta na affecting life d’in makusantanta ba tare da tayi la’akari da suma suna buk’atar kulawarta ba. Sannan ta yaya Allah zai amsa mata addu’arta alhali ita da kanta ta tauyewa wani bawa hakkinsa? Ina laifi biyu zai gyara d’aya? Ummii ta fita gaskiya kuma zata gyara nata domin itama Allah ya gyara wanda take neman ya gyara mata. “Shukran Ummii. Sa’usluhu.�? “Allah ya kad’a fitina ya shiryeshi shi kuma.�? “Ameen Ummii.�? Sai data k’ara awa d’aya a gidan sannan ta kira Haydar tace ta gama abunda zata yi. “Ki jira bari in tashi a aiki sai in biyo in d’aukeki.�? “Amma kai kace inna gama in kiraka, kuma ina son komawa gida in d’aura maka abinci ne.�? Ta dafe goshinta domin yana neman saka mata ciwon kai. “Na d’auka baza ki jima bane, amma yanzu na kusa tashi ki jirani ina zuwa bayan azahar.�? “Baka ji me na fad’a bane?�? “Me kika ce?�? Wani haushi ne yazo ya tsaya mata a wuya tace, “Shikenan sai ka zo.�? “Baki fad’a mini abunda ban jin ba Laila.�? “Don Allah mu bar maganan sai ka zo kawai.�? Tana fad’in hakan ta kashe wayarta tana rufe idanunta. Ummii ta bita da kallo tana murmusawa domin hakan ya tabbatar mata cewa Laila na k’ok’arin yin biyayya ga mijinta. “Kin fasa tafiya yanzun kenan?�? Laila ta d’ago ido ta dubi Ummii wacce har lokacin ke murmusawa sai itama taji dariya yana son kwace mata. “Wallahi Ummii haushi ya bani yau, kafin in fito na kirashi na fad’a mishi zan fita yace zai zo ya d’aukeni nace ya bari, duk don ina tausaya masa kar ya fito yasha wahalan kaini kuma ya koma office. Wai daga baya yake cewa wai kar in fita da laffaya in saka hijabi, kiji mini kinibibi fa Ummii.�? “Mijin naki ne yake kinibibi Laila? Ashe baki d’aukeshi shugaba kuma babba a gareki ba?�? A nan Laila tayi dana sanin fad’awa Ummii wannan batu, domin ganin murmushin da take yi ne yasa ta fad’a mata ba don tana tunanin zata goyi bayanta ba. Fad’a ta mata sosai tamkar dama jira take yi, ita dai kanta na k’asa tana bata hak’uri. “Ayi hak’uri Ummii bazan sake ba.�? Da haka suka yi shiru suka koma gidan jiya wanda dama magana mai tsayi bata shiga tsakaninsu. Bayan an idar da sallah Haydar yayi sallama ya shigo falon, yanda Ummii ta k’ar6eshi cikin farin ciki da mutuntawa yasa Laila tayi rolling idanunta tana shiru. Wani kallo Ummii ta watsa mata bayan sun gama gaisawa ta dubi Haydar tace, “Sannu da zuwa, ya hanya?�? “Lafiya kalau. Ya kike samesu?�? Ciki-ciki ta amsa kana ta kawar da kanta gefe tana neman inda ta ajiye jakarta. “Karka yarda ka bari tana juyaka kana yin abunda take so domin kaine babba kuma shugaba a kanta. Idan tayi laifi ka gyara mata kar kaga yawan shekarunta domin matarka ce a k’ark’ashin k’afarka take. sannan idan ma hukunci ne ya kamata ka mata daidai da laifinta. Allah ya k’ara had’e kanku ya kauda fitina.�? Shi dai Haydar kanshi na k’asa sai kad’awa yake yi yana cewa, “Insha Allah, Insha Allahu Ummii.�? K’atuwar ledar daya shigo da ita ya kai mata gabanta ya ajiye tana saka masa albarka. Ganin haka yasa Laila ta mik’e tsaye tayi mata sallama ta barsu a falon domin taji haushi ba kad’an ba. A yanzu ma Haydar na nuna mata ikonshi inaga yanzu kuma da Ummii ta mara masa baya? Ta kai minti biyar a waje sannan ya fito yana washe baki ya shiga motar ba tare daya kulata ba. Tana ganin hakan ta shiga baya ta zauna amma ya k’i kunna motar. “Laila ki dawo gaba.�? “A nan nake son zama.�? Fita yayi daga motar ya bud’e k’ofarta kana ya shiga bayan ya zauna yace, “Dama baki san yanda nayi missing d’inki ba, hijabin ya miki kyau sosai.�? Ya fad’i hakan yana tura hannunshi cikin hijabin nata. Mutsu-mutsu ta fara dolenta ta fita daga motar ta koma gaba ta kunna motar zata yi driving. Shima fitan yayi ya shiga gaba ya zauna yana kallonta yana murmushi. Sun fara tafiya ta juyo kad’an ta dubeshi taga ya gyara zama yana kallonta kawai. “Me Ummii ta fad’a maka kake ta murna?�? “Kawai ta mini nasiha ne tare da bani wasu shawarwari.�? Kwafa tayi taci gaba da tafiya yace su shiga wani restaurant zai musu take away. Ba musu ta tsaya ya shiga ciki, dama tayi niyyar kyaleshi ne taga gudun ruwansa idan ya koma gida bai ga abinci ba. Minti kad’an ya fito daga gurin wasu ‘yan mata biyu suka biyo bayanshi suka tsaya suna magana. Wata irin mummunar fad’uwar gaba Laila taji data lura yana musu magana yana murmusawa kuma yana shafa sajensa. Ko da ya dawo mota ya samu ta dawo gefe ta bar mishi driving d’in. Bai ce komai ba ya kunna motar yana bata labarin yanda abincin gurin yake da dad’i shiyasa ya saya musu. Ko uffan bata ce masa ba har ya gama surutunsa yayi shiru, can kuma yace, “Meya faru Laila? Bakya jin dad’i ne?�? “Eh.�? Ta bashi amsa domin har lokacin zuciyarta na k’una Idan ta tuno yanda yake yiwa ‘yan matan dariya suna binshi da kallo. “Bari mu koma gida kici abinci kisha magani sai ki kwanta.�? Suna komawa gida ya zagaya ya bud’e mata k’ofa ya kar6i jakanta suka shiga falo, yanda yaga take cije fuska ya tabbatar bata jin dad’i. “Ki shiga d’aki bari in d’auko tray sai in kawo miki abincin.�? Ba musu ta shige d’aki shi kuma ya wuce kitchen da ledojin hannunsa. Band’aki ta shiga ta canja pad sannan ta fito ta sameshi a k’asan carpet yana danna wayarsa. Fita tayi ta jefar da pad d’in a dustbin sannan ta dawo ta zauna a gefenshi ta jawo abincinta. “Nikam d’azu menene ya hanaki tashi daga kan gado kika ce sai na dawo zaki fad’a mini?�? “Period d’ina ne ya dawo.�? “Menstruation?�? Ya tambayeta. “Eh.�? “Kwana nawa yake miki Laila?�? “Bakwai.�? Taci gaba da cin abincinta. Ajiye cokalinshi yayi fuskarsa a kwaye ya tashi ya fita daga d’akin. “Baza kaci abincin bane?�? “Na koshi. Ga maganinki a kan tray.�? “Kai ka sani.�? Ta fad’a a hankali yanda bazai ji ba tana dariya. Bayan ta gama cin abincin ta kira Mas’ud kan labarin Abul. “Yana nan tare dani a Pharmacy, babu inda zai je balle ya samu abunda yake so.�? Wata ajiyar zuciya ta sauk’e har idanunta na taruwa ta hawayen farin ciki tace, “Nagode Mas’ud. D’azu naje gurin Ummii take cewa Khalii Abdi zai bashi magani ko kuma a aikashi can su kula dashi.�? Sun jima suna magana sannan ta kashe wayar tana jin sanyi a zuciyarta tamkar ta bud’i ido an fad’a mata Abul ya shiryu. Abincin ta kwashe zata kai kitchen ta samu Haydar a falo yana kwance ya kwa6e kayanshi ya bar boxers kad’ai wanda dama haka d’abi’arsa take kamar Inyamuri. Har zata wuce ta dawo ta zauna kusa dashi bayan ta matsar da k’afafunshi tace, “Meya hanaka cin abincin?�? “Na k’oshi ne.�? “Ka tashi kaci abinci nasan yunwa kake ji.�? Ta fad’i hakan tana dariya k’asa-k’asa. Bai kalleta ba yace, “Ina jin dariyan da kike yi kuma kici gaba da yi.�? “Yi hak’uri Ruwan Zuman Laila, tashi in baka a baki.�? Da kyar ta lalla6eshi ya tashi yaci abincin yana harararta. “To mena maka ne kake ta hararata? In ban manta ba d’azu kai ka mini laifi kuma ina cike da kai.�? “Me na miki?�? Gyara zamanta tayi ta fuskanceshi fuskarta so serious tace, “Haydar saka laffaya shigata ce na tun asali kuma shine suturar yarenmu. Bai kamata rana d’aya ka hanani sakawa ba sannan kayi tunanin zan kar6a haka kawai ba. Gaskiya ka daina mini irin haka, domin tun daa a hakan ka ganni kace kana sona, bai kamata kuma kazo kana hanani wasu abubuwa dana saba dasu ba matuk’ar hakan bai kaucewa shari’a ba.�? “Kina nufin juya duwawu da kike yi maza na binki da kallo ba haramun bane? Karki manta ke matar aure ce wacce in banda fuska da tafin hannu da ka k’afarki duk jikinki al’aura ce. Gaskiya ko a daa abun yana ci mini tuwo a kwarya don dai kawai banida ikon hanaki ne, amma a yanzu da nake da iko dake na hana fita da laffaya sai hijabi.�? Takaicin da taji ba’a iya fasaltashi, kallonshi kawai ta tsaya tana yi tana mamakin yanda ya juye ya zama rik’ekk’en mutum ba Haydar mai sunkuya mata idan zai gaisheta ba. “Yayi kyau, duk laifina ne.�? Ta fad’i hakan cikin harzuk’a. “Da kika yi me?�? Ya tambayeta yana nazarinta a lalace. “Wasu ‘yan iskan yaran ne na ganka tare dasu kuna tsaye a bakin restaurant?�? Ta canja maganan domin itama tana son mishi iyaka kamar yanda ya mata. “Laila karki musu shaidar iskanci domin yaran kirki ne.�? Ashar ta kwaza a ranta kana ta tashi zata bar gurin ya rik’ota ta fad’o k’anshi. “Ashe ana kishina haka?�? Ya fad’i hakan yana dariya. “Ka sakeni Haydar, bana son wasa.�? Ranta a 6ace tayi maganar tana neman kwace kanta. “Don ki fini nama a jiki bashi zai sa ki fini k’arfi ba. Ki gama kokawar idan kin gaji zaki daina.�? Ya k’ara k’arfin rik’on daya mata yana lasar wuyanta wanda take jin hakan kamar cakulkuli. “Bana so Haydar.�? “Ni kuma ina so.�? Yanda yake mata yasa ta fara dariya tana nok’ewa sai ya canja guri. Sosai take dariya har tana k’ok’arin fad’ar dasu daga kan kujerar ya d’auketa yayi d’aki da ita tana cewa zai fad’ar dasu. “Jiya kuma ai baki fad’i ba.�? Ya bata amsa yana rufe k’ofar. A kan gado ya direta yana murza hannayensa yace, “Ashe dai kina da nauyi.�? Matsawa tayi can gefe ta fara had’e fuska tuno da abunda ya mata duk a yau na 6acin rai. Shima hawa gadon yayi ya kashe wutan d’akin ya jawota jikinshi yana cewa, “Baki san yanda maza suke kallon bayanki bane idan kika saka laffaya Laila. Wallahi idan naga wani na kallonki a yanzu da kike matata sai na fasa mishi kai, shiyasa maganin bari kar ma a fara. Amma bazan hanaki sakawa gaba d’aya ba, idan zaki fita shagonki ko gidan bikinku na mata ki saka, amma In har kinsan zaki shiga gari ko kasuwa inda wani namiji zai ganki to ban yarda ba. ‘Yan matan nan kuma ‘yan ajinmu ne wanda muka yi jami’a tare, maganar da muke yi kuwa murna suke mini na auren da nayi har suke fad’a mini suma an saka ranar aurensu zasu aiko mini kati. Haydar naki ne ke d’aya sai yanda kika yi dani.�? Ajiyar zuciya ta sauk’e kana tayi shiru tana jin yanda yake bin jikinta da hannunsa yana ta6a duk inda ya masa. “Bacci nake ji.�? Tace dashi tana kawar da hannunsa daga k’irjinta. “Yau kam a tausaya mini ko dabarun matan a mini.�? “Haydar.�? Ta kwa6eshi tana jin jikinta na canja yanayi. “Please Laila.�? Juyowa tayi ta kalleshi taga yanda yayi kalar tausayi kamar bashi yake auna mata doka d’azu ba. “A tausayawa Ruwan Zuman Laila.�? Murmushi tayi kana tace,“Kaje kayi wanka tukun.�? Kafin ta rufe baki ya tashi da sauri ya shige band’aki. Sai daya wanke jikinshi tsaff sannan ya fito ya sameta zaune a kan gadon hannunta d’auke da goran Zuma tana lasa. “A ajiye wannan abun. Ya fad’i hakan yana hawa kan gadon. “No, dashi zan maka dabarar tamu ta mata.
Mum Fateey 👌




