Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 35 Hausa Novel

Baya baya yayi ya jingina da kujerar tare da relaxing, idanunshi har lokacin zube a kanta yana aikin kallon yadda ta ruɗe sai haƙuri take bashi tana share wayan da hijab ɗinta, he is surprise a lokaci daya kuma he’s amuse bai taɓa ganin halittar dake tsoron shi irin ta ba, shi ba dogon magana yake mata ba shi ba dukan ta ya taɓa yi ba amma yadda take yi akan wayan sai ya ga kaman cewa yayi zai sa bindiga ya harbe ta.A hankali ya miƙa tattausan hannunshi ya ɗora a kan nata da ke riƙe da wayan, abin da taji shi ya sakata natsuwar dole ta ɗago ido ta kalleshi suka haɗa idanu, for some seconds ya janye idanunshi ya zare wayan ba tare da ya ce komai ba.Ita har ga Allah tana mamakin shegen miskilancinshi ayi mutum babu magana ai sai yayi ciwon baki, ganin bai ce mata komai ba sai ma kokarin saka abincin yake tayi saurin ɗaukan spoon ta shiga serving ɗin shi bayan ta tura mai ta juya za ta bar wurin ta ji ya ce “Ina za ki je?”Juyowa tayi ta kalleshi kaman ba shi yayi maganan ba hasali ma abincin shi yake ci hankali kwance, ganin tsayuwar ba zai mata ba sai ta nufi kujeran dake nesa dashi ta zauna ta ɗan saka abincin kadan ta shiga ci a hankali. Bai fi mintuna ashirin ba ya miƙe ya bar dining ɗin ta bi shi da kallo har ya shige ɗakinshi.Washegari kuwa da Mammi ta faɗa mata saleem zai zo har gidan ta shiga kitchen ta musu girki ta sake yin tofin a ruwan abincin da ta shirya musu, a dining ta jera musu ta wuce ɗakin Mammi tana shiga bata zauna ba yana shigowa, a ƙasa ta zauna wurin kafafun Mammin shi kuma ya zauna daga gefenta Mammi ta amsa gaisuwar da ya fara yi mata ta ɗora da “Ya jiki?””Alhamdulillah Mammi, ya naki?”Ta amsa cikin kulawa.”Afeefah kawowa mijinki ruwa mana”Wani irin dukanta kalmar yayi a hankali ta ɗan kalleshi shima ita ya kalla jin wani mijinki da Mammi ta faɗa ya janye ido, ta miƙe ta isa fridge ta ɗauko zobon nan da Cup ta kawo mishi tana ajiyewa ya furta “Thanks”Yana ɗan lumshe ido saboda kamshinta da ya shige shi, yana mamakin kalar turaren da take amfani dashi ko yaya ta matso kusa dashi sai yayi perceiving smell din, tsiririn tsaki ya ja. Ta juya zata fita Mammi ta tsayar da ita “Ina kuma zaki je Afeefah ba kin zo taya ni hira bane?”Dukkansu basu yi tsammani ba suka ji muryarshi yana cewa “Dodonta ya shigo dole ta fita.”Calmly yayi maganan, ta ɗan wara idanunta bata ce komai ba sai da Mammi ta ɗan yi dariya ta yi rau da fuska a ɗan karye tace “Mammi akwai abin da na manta ne ban yi ba a kitchen shiyasa zan fita fa”Ya ɗago cup na zobon yana sha suka haɗa idanu da sauri ta fice, ya juya ya kalli Mammi “wannan yarinyar ta cika tsoro da yin abu a zabure, ko ina haɗiye mutane ne?”Shi dai da gaskiyar shi yayi maganan yana mamaki kuma.Dariya sossai Mammi tayi “Ka haɗiye mutane ai babu zaman lafiya kawai yadda kake ɗaure fuskar ne yayi yawa Saraki, ya kamata ka sakar mata tunda matarka ce”Bai tanka ba chan ya ɗaga cup na zobon “Yayi daaɗi.””matarka ce tayi!”Ya kalli Mammi yana maimaita matarka a zuciyarshi Mammi har ta haddace kalmar, zai yi magana ƙira ya shigo wayanshi saleem ne, Miƙewa kawai yayi ya fice.Chan sai gasu sun shigo babban parlorn, Mammi ta fito suka gaisa tana ta mishi magana baya shigowa yanzu ya dube ta yana murmushi mai nauyi yake furta “In shaa Allah zan ke zuwa Mammi””yauwa gwara kam ka zo Saleem, idan ba damuwa ma ina so in roƙi alfarmarka”A kunyace yace “Mammi kun wuce alfarma ai a wurin mu sai dai umurni””Yauwa toh na gode da wannan matsayi, idan har ba zaka takura ba ina so in dinga ganinka kullum for seven days akwai maganin kariya da Saraki ke sha ina so ku sha tare duk aikin naku ɗaya Fatan mu dai Allah ya kare mana ku ya sa ku gama lafiya”Suka amsa da Ameen, cike da biyayya da yake da shi tun chan yace “Na gode sossai Mammi kuma in shaa Allah zan ke shigowa har kwana bakwan””yauwa Allah ya muku albarka, ku isa ga abinci chan an shirya muku a dining”Tana kai nan ta miƙe ta koma sashenta, hira suke ɗan yi kaɗan kaɗan a hankali ya ɗan lumshe ido ya buɗe kan chak ya miƙe yana furta wa saleem “Ina zuwa!”Corridor da zai kai ka side ɗinshi daga nan babban parlorn yayi aiko a gab wurin fitowa parlorn suka yi karab da ita har tana Buge mishi ƙirji, baya baya tayi tana ɗagowa suka haɗa idanu sanye take da wani riga da skirt na lace da bai wani kamata ba amma yayi masifar amsarta kasancewar shi Red colour tayi ɗaurin ture ka ga tsiya, ɗan kunne ne kawai a kunnenta bata saka sarƙa ba sai wuyan nata ya fita fresh yana ɗaukar idanu, ga mamakin ta mugun kallo ta ga yana mata sai ta sake shan jinin jikinta.”Ina kike tunanin zuwa?”Tambayar sai ya sakata cikin duhu dama ina take zuwa a gidan da ya wuce wurin Mammi ko Abeeha.”Ina magana kin yi min banza? Na fara wasa dake ne?”Da faɗa yayi maganan sai ta matsa baya idanunta na cika da kwallah tace “wurin Mammi za ni””Daga yanzu har nan da kwanaki bakwai ko da wasa bayan gaisuwan safe da za ki je yi wa Mammi ki bari mu yi ido huɗu dake a main parlor sai ranki yayi mummunan ɓaci, wuce ki bani wuri”Hawayen da take ta riƙe wa na tsoron ne ya zubo mata da sauri ta juya ta koma, bai bar wurin ba sai da ya ga ta ɓace ya ja tsaki mai ƙarfi ya juya ya koma parlorn, inda ya tashi ya zauna yana sake jan tsaki.”Lafiya kam?””Ƙalau, mu je mu yi lunch azahar ya kusa”Miƙewa saleem yayi suka isa dining ɗin Rayyan yayi serving ɗinsu suka zauna suna ci saleem sai yabon girkin yake har suka gama suna ɗan hira tsakaninsu daga nan suka shiga wurin Mammi ta haɗa su da zobon Dukda sun sha a dining bayan ta basu maganin a cup masu kyau duk su biyu suka sha saleem yayi mata sallama suka fito tsakar gidan.Suna shirin fita masallaci Motar Abeeha ya shigo gidan tayi parking tana saukowa fuskarta a ɗan washe ta gaishe su, duk suka amsa saleem na tambayarta school ta amsa da Alhamdulillah daga nan ta shigo ciki su kuma suka fice daga gidan, sai bayan sun yi sallah ya zo ya ɗauki motar shi ya wuce gida, shima Rayyan mota ya ɗauka ya tafi duba Mommy ya samu da sauƙi sossai ma akan idanunshi aka bata sallama shi ya biya duk bills ɗin kasancewar akwai mota bai kaisu gida ba sai kwantar wa mommy hankali yayi suka tafi shima ya nufi gidan.Ita kam Afeefah ɗakinta ta koma ta zauna akan kujerar mirror tana kallon kanta, a hankali ta sa hannu ta dafa saitin zuciyarta da har yanzu bai daina bugawa ba hawaye ne taji suna silalo mata, bata san wani mataki zata ajiye kanta ba a wurin Rayyan tsanar ta yayi ko kuma haushin kusancin ta da mahaifiyarshi yake ji bata sani ba, Meyasa zai saka mata boundry da shiga cikin gidan? Me tayi? Da kyar ta kauda tunanin ta tashi ta fara kokarin shirya wardrobe ɗinta tana janye tunanin, a wayanta ta saka karatun qur’ani tana aikin har la’asar kan ta gama ta adana akwatunan ta tafi tayi alwala ta zo tayi sallah, tana zaune taji ana mata knocking ta miƙe taje ta buɗe sai ta ga Abeeha ce murmushi suka sakarwa juna ta shigo ciki.”Cigiyarki na zo yi tun fa jiya rabon da mu haɗu matar bross”Tana ɗan murmushi tace “Da kin taimakeni in kika daina dangantani da wannan Yayan naki, Mammi ma da take faɗa bani da yadda zan yi ne””Toh Meyasa? Ke ba matar tashi bace?”Abeeha ta faɗa tana zama kan couch na ɗakin.”Gabana faɗuwa yake a duk sadda aka dangantani da shi, ban sani ba tsabar yadda nake jin shakkarshi ne ko yaya””ke fa ba mu bane Afeefah, ya kamata ki rage wannan tsoron nashi wlh ko mu bama mishi irin tsoron da kike mishi ke matarshi ce sirrin shi, a ina kika taɓa ganin matar dake shakkar mijinta? Lalalalala idan kika tafi a haka ke za ki cutu””Adda Abee ba za ki gane bane ke kam, ya saleem ɗin ya shigo? Kin ganshi? Ya ci abincin?”Kallonta Abeeha tayi “Eh ya shigo, sun ci har ya tafi ma tun azahar”Ajiyar zuciya ta ɗan sauƙe suka cigaba da hira da Abeehar, Abeehar na nuna mata tayi amfani da trainings da aka yi mata kar kudin Mammi ya tafi a banza ita dai sai dariya take don ko tsireta za’a yi ba za ta iya ba wlh, sai Magrib Abeeha ta tafi ita dai Afeefah bayan tayi isha ta fito ta samu an kawo musu abinci kaɗan ta ɗiba ta koma ɗakin don ko haɗuwa bata so su yi.Daga ranar kullum Saleem sai ya shigo kuma Mammi bata taɓa ƙasa a gwiwar basu tofin ba yayinda bayan an gama abin kari Abeeha ke shiga kitchen da kanta ta musu girki tunda anan yake cin abincin rana har kwana bakwan, kafin ta gama girkin take zuwa ta gaishe da Mammi bayan ta gama ma ta kan leƙa ta kan ta wuce sashenta bata sake zuwa sai gobe tunda ya hana gwara ta bi umurninshi ba tare da ta san dalili ba, a sashenta take zama tayi karatu tayi bacci ta gaji gashi bata iya zaman parlorn don bata so su haɗu kuma kaman ka’ida tun daga ranar basu sake haɗuwa da shi ba har kwana bakwan ya wuce don ko abincin dare ana kai musu zata je ta diba ta shiga ɗakinta ta rufe. Adu’ar ta kuma a koyaushe shine Allah ya dubi Saleem ya yaye mishi wannan bala’in.Ta ɓangaren saleem tun daga ranar da ya fara zuwa wurin Mammi yana shan tofin kuma yana ci a abinci ya fara jin wannan nauyin na zuciyarshi na raguwa, kanshi da kaman an daddaure baya wani tunani mai kyau ya ji kaman ana kwakwance jijiyoyin, bai dai nuna komai ba don tun bayan kwana biyu da ya fara zuwa Sabreena ta saka shi gaba Meyasa yake zuwa gidan aboki yake cin abincin rana bayan bata Gaza ba wurin cinshi? Meyasa ma yake zuwa gidan su Rayyan ɗin abin da baya yi da kaman ka’ida kullum sai ya je?”Sabrina yaushe ya zamana in zan fita ko zan yi mu’amala da wani sai na bi ra’ayinki ne kam? Meyasa za ki damu da abin da bai shafe ki ba? Yau na fara cin abinci a gidan aka ce miki? Toh bana son damuwa da ciwon kai idan maganan da zaki cigaba da yi kenan ki tashi ki bani wuri”Da wani irin tsantsar mamaki take kallonshi Za Ta yi magana ya daka mata tsawa “Ki fita nace!!”Da sauri ta miƙe ta fita har tana haɗawa da sassarfa bata tsaya ko ina ba sai wurin Gaje don babanta baya nan ya fita.”Mun shiga uku! Gaje Ya Saleem yau ni yake yi wa tsawa! Me yake shirin faruwa?””Ke ki natsu dallah chan me zai faru kuwa? Ya wuci kin je kin dameshi ne yana so ya huta, ki fa sani ko da mallakarshi da muka yi sai kina bin shi a hankali””Gaje bai fa taɓa ɗaga min murya ba tunda na shigo gidan nan ina tsoron kar wani abu ya faru ne””Babu abin da ya faru daga ni har mahaifinki muna da yakini kan aikin da aka mana har abada ba zai kwance ba, ki bashi lokaci sai ki koma”Ko da ta bashi lokaci ta koma bai yi mata magana ba, sai ta yarda da cewa ita ce ta takura mishi don haka bata kara magana akan zuwa gidan su Rayyan ba, yau ya shigo gidan sai ya tsaya chak a parlorn yana bin sababbin kujerun da kallo, a hankali ya tsayar da idanunshi kan kujerar da mommy ke yawan zama, tunanin mommyn ya fara sai yaji kanshi ya wani irin sara gabanshi ya shiga faɗuwa zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi daidai Sabrina ta fito ganinshi dafe da kujera ya sa tayi hanzarin isa kanshi “Ya Saleem lafiya? me ya sameka? Menene?””Ƙira min Mommy!”Darammm ta ji zuciyarta ya buga…****Kawu Labaran ne riƙe da Ghana most go yana kallon Inna Larai dake ta juya kai tana fama da suntumemen ƙafarta da kudaje ke ta sukuwa a kai yace “Ki yi min adu’ar dacewa ai na ji unguwar da ɗaya kawun nashi ya ambata chan zan je in tabbatar da gidan da Afeefar take sai na dawo da ita ta kai ki asibiti don ni dai ba ni da wani kudin asibitin birni! Kin ga dama ke ce uwar ɗakinta…”Inna Asabe ta katse shi “Malam anya za ka yi hankali kuwa? Wani irin zance ne kake yi hakan? Taya Afeefah zata fara taimakon mu bayan duk abubuwan da suka faru? ka manta ita da kake ikirarin itace uwar goyon nata ko ɗakinta bata taɓa bari Afeefar ta taka ba?””Amma dai mun ciyar da ita kuma mun tufatar da ita, har ɗaki sukutum muka ware mata tayi rayuwa kaman ‘ya’yan gidan nan ni ko hassada kike yi min ne ma kin ga zan je birni?””Allah ya kyauta in maka hassada, ina dai tunatar da kai ne ita Larai ɗin me ya hana ‘ya’yan ta yi mata? Mugun alkaba’in da muka bi yarinyar nan dashi shi muke gani a wurin namu yaran daga masu shaye shaye sai masu cikin shege ana ɓararwa a maimakon mu fara tunanin laifin mu mu fara neman hanyar gyara ka sabi jaka don son zuciya zaka tafi neman kudi wurin wacce ka yiwa korar kare a gidan nan…””Na rantse ko ki min shiru ko in saka sandata in Buge ki, ni zaki faɗawa maganar banza? Idan wulakanta Afeefar ne duk wa ya more ta bayan ku? Ina ce anan kullum take dawo muku da kudaden da take samo muku ni me na taɓa sakata sayar min? Ko ba kece kullum dare kike hayaƙin tafarnuwa da kuka da Ƙashin kifi ba duk saboda Afeefar? Idan akwai waenda ba zata yiwa abu ba sai dai ku, ni kam dolenta idan ma bakin ciki kike min sai na je… Ke kuma Larai ki jirani in dawo”Yana kai nan ya juya ya fice, inna Asabe ta bi shi da kallo kan ta mayar da kallonta kan Inna Larai dake zaune varender ɗinta a yanzu ko tafiya bata iya yi, komai sai an yi mata ga yaran nata kan su yi mata sai ran kowa ya ɓaci sun yi ta mita da kananun maganganu kenan, abinci wannan tunda kawun ba wani ciyar dasu yake ba sai in Asaben ne taji tausayinta ta bata daga wanda ta dafa a ‘yar sana’ar da take yi na cikin gida.Wa’azi taji a redio ranan da ya sakata zurfafa tunanin akan sharrin dake bibiyar ‘ya’yensu gashi dai sun haifa amma a yanzu babu ɗaya da za’a cire na ƙwarai, sai yanzu wani abu ke shiganta akan neman ilimi barin ma da taji neman ilimin addini farilla ne kan kowani musulmi kuma baka da hujjar kare kanka da rashin sani a wurin ubangiji muddin baka nemi ilimi ba, tunda ta san lokacin da ake sa wa’azuzzukan sai ya zama kullum da hantsi sai ta ji anan ta fara tunanin daga ina ne rayuwarsu ya kuskure tun farko…?Shi dai Kawu Labaran machine ya hau har ya fito kauyen gaba da su ya samu mota da ya kawo shi farkon garin Kaduna ya dire, nan ya tsaya zare ido tunda yake bai taɓa shigowa cikin Kaduna ba bari dai kauyuka yana zuwa sossai musamman na bayansu amma bai taba zuwa babban birni haka ba, zare ido yake tayi yana kalle-kalle wani mota ya tsaya kusa dashi wasu maza huɗu ne ciki”Ya dai ina ka nufa?””Na zo wurin ‘yata ne tana nan cikin gari””Wani unguwa?””Ni dai ban tabbatar ba amma kaman unguwar masu kuɗi ne wai G….A…R”Da kyar ya fadi alpabets ɗin suka tuntsure da dariya “GRA kake son cewa?””Yauwa eh nan fa dai…””Shigo”Shiga yayi yana washe haƙora yau dai Allah ya nufa gashi a birni basu yi nisa ba ya ga duk sun saka facemask kan yayi magana sun ja window suka fesa mishi wani powder nan ya sulale ya sume…****Tsaye yake gaban madubi, wanka ya fito daga shi sai towel jikinshi, ginannen jikinshi fari tasss sai daukar ido yake saboda ruwan dake bin murdaddun damatsanshi zuwa parks da ya tara a ciki, madubi ya kurawa idanu yana tunanin irin yanayin da ya shiga a daren jiya wanda rabon da ya ji kwatankwacin hakan sama da shekaru ashirin da biyar, da ƙarfi ya runtse idanunshi da suka yi wani irin jajazir yana fesar da huci daga bakinshi tsaki ya ja a karo na babu adadi ya miƙa hannu zai ɗauki mai kenan aka turo kofan aka shigo da sauri ya ɗago sai idanunshi suka sauƙa kan….!

Back to top button