Gargadar So Chapter 52 By M Shakur
She wants to be Hawwarh’s best friend, wannan abubuwan da ada zatai sharing da Ni’ima gwara tayi da ita, tabata labaran hakan zaisa ta manta da Ni’ima, Ammi ta karba tana budewa tarike baki tace “au dan gidansu yartawa yake cewa Yar Sanda Kulu lallai Ibrahim yacika sarkin tsokana” Ammi tabude kwalin agogon taciro tana kama hannun Hawwa ta dauramata tace “masha Allah cip cip idan gobe yazo saikisa yaganki dashi yaji dadi haka akeyi ma miji” Hawwa tadan turo baki tana tauna baki batadai magana ba gudun karta batawa Ammi rai Ammi tasamata bracelet din shima yamata kyau sannan ta bude turarukan ta feffesa mata itama Ammi ta fesa anata jikin tace “uhm ni Maman Amarya nima nayi kamshi” dan murmushi kadan tayi Ammi tace “kai gaskiya mijinki ya san kan turare Hawwa kinji kamshi” dasauri tace “Ammi nabaki ki daukesu ni dama inada turare na” dakuwa Ammi tamata tace “kwal ubaki Hawwa mijin naki yamiki kyauta zakimin, kaji yarinya inga kin bama wani saikin sani” turo baki tayi ta tashi kawai tana rage kayan jikinta Aminu yayi sallama yashigo wani waya daban yakawoma Hawwa yace “Ya Ibrahim yace nakawo miki” wayan takalla Iphone ne bamatasan wanne ba ganin Ammi na kallonta ta wutsiyan ido yasa tasa hannu ta karba tace “to” ta ijiye tawuce bayi.Around 10 duk sun kwanta ita Hawwa sabida zatai azumi gobe Ammi kuma sabida zatai tafiya gobe, sabon wayan dataki bi takanshi tuntuni ne yahau ringing ita batamasan sim dinta ne ciki ko wani dabanba hakanan dai taji bazata dauka ba, wayan na karewa yashiga ringing again Ammi tace “wai ba ke ake kira ba Hawwa nafasan ba bacci kikeba” tashi tayi ta sauka daga gadon tasa hannu tadauki wayan akan mirror tadawo gadon ta kwanta sannan ta danna wayan takai kunnenta sabida Ammi yasa ta kwantar da murya sosai hakan yasa muryanta yayi wani irin dadi ahankali tace “hello” lumshe idanu Khaleel yayi yana gyara kwanci afalo ashagwabe yace “I’m hungry Kulu” wani iri Hawwa taji yanda yayi magana hakan yasa tayi shiru, Khaleel ahankali tace “I don’t feel like eating abinda chef namu suka dafa, nazo kimin girki Kulu?” Runtse idanu Hawwa tayi tace “nace banson sunan nan” ahankali yace “but Hawwah is Hawwa Kulu” Shiru Hawwa tayi the way yake kiran Hawwa dadi, sabida Ammi tadaure tace “bacci zanyi zan tashi nayi azumi anjima good night” zata cire wayan daga kunnenta yace “but it’s not Ramadan, azumin me kikeyi ramuwa?” Shiru tayi ta lumshe idanu kaman bazata amsashi ba tace “nafila ina azumi Monday and Thursdays” cikin yar karaman murya yace “nima zanyi” yayi shiru jin batace komiba Khaleel yace “sainai addu’a Allah karya baki ikon bata auren mu, I want to live my life with you” yafadi ahankali baimasan mesa yake fadin hakaba but kawai yanaji ajikinshi bazai iya rabuwa da ita ba dan juyawa Hawwa tayi ganin Ammi tayi bacci ga ijiyan zuciyanta tanaji hakama Ramla yasa ahankali tace “you’re a liar! Kaida ke wulakanta mata bakasan darajansu ba, imagine locking your Baby Mama in jail, Allah bantabaji I hate someone kaman the way na tsaneka ba” shiru Khaleel yayi sai kuma chan yace “do you love my gift?” Cikeda tsana tace “I will never love anything that comes from you” shiru yayi baice komiba Hawwa kawai tazare wayan daga kunnenta daidai yasake kira kaman bazata daukaba tadauka kafin yayi magana tace “how could you send that video to Nursing Council don’t even deny it nasan aikinka ne, why would you do that to my friend?” Hamma taji yayi yace “zan fita I know you don’t have friends so bansan wat you are saying ba bye” Hawwa tace “aikin kenan party giya da mata” murmushi yayi yace “gashi na aureki” zatai magana ya katse wayan jitayi ranta yana kuna yana susa tasan yanzu club zaije maybe Allah kadai yasan time dazai dawo shiru tayi sai chan ta tuna yanda yamata kiss a kumatu a mota dasuri takai hannu tashiga share kumatunta kaman yasamata dafi ahaka tai bacci.Washegari around 8 suka fito dudda tanajin bakin cikin shiga motan nan haka ta shiga Ammi tafara kaiwa park sannan tawuce office.Tundaga gate ake mata yajiki ana mata Allah kyauta tana zuwa direct office na DIG tayi tai knocking yabata izinin shigowa yana ganinta yadakatar da rubutun dayake yace “Hawwa are you sure you’re strong enough kidawo aiki?” Murmushi tamai tace “yes Sir thank you” anatse yace “welcome back” gyadamai kai tayi ganin ta tsaya bata wuce ba yasa yace “akwai wani abu ne?”Gyadamai kai Hawwa tayi cikeda damuwa, seat dake gabanshi ya nuna mata hakan yasa ta zauna akan kujeran ya ijiye pen na hannunshi yace “I’m listening Miss Hawwa” gyadamai kai tayi anatse tace “Sir I have a very serious problem I need your help” gyara zama DIG yayi dan yana bama Hawwa respect da girma dan ijiyan zuciya ta sauke tace “Sir I’ve never been to Senate President house banda time din nan damukaje aiki, I know nothing about them or household nasu” with so much anticipation DIG yace “what’s with Excellency Hawwa?” Ijiyan zuciya ta sauke cikin raunin murya sosai tace “Sir ranan danai accident ina hospital Babana yabasu aurena, sai bayan mun dawo gida anyi discharging dina ake sanardani wai wannan yaron nasa Khaleel aka auramin” tayi maganan hawaye mai zafi na sauko mata DIG kanshi was in shock yazaro idanu yana kallon Hawwa yace “you mean Khaleel Baban Noor”? Gyadama DIG kai tayi bakinta na rawa tace “I have no idea me suka gayama Babana, banso Khaleel yake yakarani acikin sahun matansa sabida yayi using dina and dump me bayan 1 or two weeks” Ko kadan DIGGG baiji dadin news dinba but still cikeda damuwa yace “Hawwa akanme mahaifinki zai bada auren ki batare dayayi bincike ba? I’m not saying that because maybe zasu miki mugunta or something no su basa wannan, kawai dansu baisan menene aure ba, baisan darajan auren ba, mata are like papers zai iya bude this page ya yaga and open another page, so why will your father get your married to such kind of man”? Bayan hannu Hawwa tasa tagoge idanunta tace “sabida he’s tired of me, yagaji da yanda nake zaman mai agida ba miji” DIG ko kadan baiji dadi ba yasakeyin shiru sai chan yace “to wani help kike magana zan miki”? Share fuskanta tayi tass kaman batai kuka ba takalleshi tace “I want you to come with me Sir muje ka gayama Babana the type of Man Khaleel is cus wai on 23RD this month za’ayi biki zan tare, I don’t want this marriage I don’t want to be victim of circumstance na gayama Babana all I know yaki yarda I’m sure ka tayani gayamai zai yarda”.



