Fentin Zina Page 32 Hausa Novel
***Mai napep din yaja suka tafi, a hanya sai sake sake take yi a zuciyarta kana tana auna abubuwan da suka faru daga jiya zuwa yau ko zata hango ko akwai laifin data aikata masa yasa ya dauki wannan hukuncin akan ta amma ko kadan tunaninta bai kawo mata kuskuren ta ba a haka har suka isa kofar gidan su ta sauka ta ciro kudi daga karamin pos dinta ta mika masa bata tsaya karban canji ba taja akwatinta ta shige gida, mai napep din ya girgiza kai yace a fili Allah ya yaye miki abunda ke damunki. Domin tunda ya dauke ta ya lura tana cikin damuwa.Inna tana kwashe tuwo fateema tana zaune a kan dakalin kofar dakin su shureim na zaune saman cinyar ta Ameena ta fado gidan da sallama. Inna ce tayi saurin daga ido tana duban kofar gidan jin muryar Ameena din. Fateema ma da mamaki take kallon Addan nata wacce ta shigo rike da karamin akwati. Duk su biyun babu wanda yayi karfin halin amsa sallamarta sai da ta kusan kaiwa ga dakalin nasu inda fateema ke zaune.Zillon da shureim yayi ya isa gareta da ihun kiran sunanta da yayi shi ya dawo dasu daga dan duniyar tunanin da suka fada a cikin dakikun da basu wuce uku zuwa hudu ba.Ajiye akwatin tayi ta daga shureim sama sannan ta ajiye shi ta manna shi da jikinta tana jin kaunar yaron na ratsata tace shureim wannan tsallen kana so ka balla ni ne? Baka girma ko?.Ya girgiza kai yace ina girma ai ina jin magana ki tambayi mummy ma kiji. Ta kai idonta kan fateema wacce itama nata idon ke kanta tace wai haka mummyn shi?Fateema bata samu damar bata amsa ba sakamakon inna data shiga zancen da cewa Ameenatu ina dai fatan lafiya don na ganki da jaka.Ta girgiza kai tace babu lafiya inna! Lafiya bazata kawoni gida ba a irin wannan lokacin har ku ganni da jaka sam babu lafiya ban san meya shiga kanshi ba inna nidai nasan tsakanina da ubangijin daya halicce ni ban aikata komai ba sam ban aikata komai ba, ta fada tana girgiza kai hawaye suna kokarin zubo mata amma ta mayar dasu ta karfi.Ajiye aikin inna tayi dama ta gama tace zauna. Ta nuna mata kusa da fateema, babu musu ta zauna tare da daura shureim a kafafun ta still tana kokarin maida hawayen da take jin suna kokarin zubo mata.Meya faru? Wani abune ya hada ku yace kizo gida ko ya akayi?. Inna ta tambaya cikin son sanin menene…Murmushi yake Ameena ta saki tace bamu samu sabani ba hasalima cikin raha da walwala muka rabu dazun akan zai fita ganin abokin shi kafin ya dawo mun cikin yanayin da banida masaniyar daga ina ya samo shi.Toh yanzu meya kawo ki? Cewar inna cikin dan fada don ta fara hassala.Sakina yayi! Ta fada kai tsaye.Dafe kirji inna tayi ta shiga jero salatukai ta dora da cewar saki dai? Dududu yaushe akayi muku sulhu ne Ameena kofa sati ba’ayi ba. Fteema tayi caraf tace shekaran jiya ne fa inna.Alamar tunani inna tayi tace kwarai kuwa shekaran jiya ne toh amma meya,,,,,, kai me kuma…….. Toh ma garin yaya, duk inna tama rasa abunda zatace. Ameena ta karbe zancen da cewa inna nifa komai ya faru na barshi a matsayin kaddara kuma na tabbata tunda har ban zalunce shi ba Allah bazai kamani ba.Inna itama tayi saurin cewa duk naji amma meya hadaku?.Nan Ameena ta kwashe duk yadda sukayi har kawowa inda take zaune a gabansu yanzu ta fada musu. Salati fateema tayi tace amma mutumin nan sam bayi da tunani bayi da uzuri ai kamata yayi ya tambaye ki cikin sanyi idan ma kinsan shi said ki fada masa gashi ya jawo ballewar ragowar igiyar dake tsakaninku.Daga inna har Ameena juyawa sukayi suna kallonta don duk sun mance wannan itace igiyar karshe, inna tagumi ta buga tace ayi mutum da daukar mataki ba tare da bincike ba karshensa nadama ne amma kuma wanene zai biyo ki har gida Ameena yayi sallama dakeko kin fita ne a yau din. Ta girgiza kai tace ban fitaba ko kofar gate ban leka ba. Fateema ta daga kai kamar tana tunani can tace amma kamar naso in gano meke faruwa.Dukkansu suka maida kallonsu kanta, inna ta riga cewa me kika gano din?. Ta jinjina kai tace rannan zan shiga gidan adda wani mutum ya parka motarsa ya biyoni har bakin gate amma ban saurare shiba na shigewata cikin don a lokacin ina tsoron mijinta ya dawo ya tarar dani tsaye dashi a gurin ma saboda nasan duk masifar shi kan adda zai sauke.Hum Ameena ta sauke ajiyar zuciya kana ta cigaba lallai babu shakka dolema shine tunda yace har suffanta mishi kamannina mutumin yayi tun anan na soma zargin kila dake yake yi shi kuma sarkin fushi da fusata ya hau sama ba tare da bincike ba koda yake dama ya jima yana son rabuwar mu sai dai banso rabuwar tamu ta kasance a irin haka ba amma Allah shine masanin daidai bani da ja akan hukuncin ubangiji.Ai Adda shine zai sha wahala domin baki cutar da shi ba sannan abunda ya faru din ba laifin ki bane don haka ki kwantar da hankalinki sai yayi nadama.Inna tace toh babu abunda zance nidai a yanzu kaddara dai ta riga fata amma yaron nan bai kyauta ba bari malam yazo muji me zaice dukda dai bakin alkalami ya riga ya bushe saki uku kam ai babu kome.Hum Kasai Ameen tace ta mike ta zaunar da shureim inda ta tashi taja akwatin ta ta shigar dakin su ta fito ta dauki buta tace inna ko zan samu ruwan zafi?. Inna tace ai kuwa dai akwai don itama fateema yanzu bata yadda tayi tsarki da ruwan sanyi wai kaikayi yake saka ta. Ai inna ruwan sanyin nan yana iya saka ma mutum cutar sanyi koda bayi da shi, idan kuma mutum nada shi yakan karu sakamakon amfani da ruwan sanyi. Ameena ta fada lokacin da take shiga daki domin zuba ruwan daga flask.Bayan sallahr isha’i baba malam ya dawo gida koda yaga Ameena a gida yayi mamaki sosai shiyasa bai bari saiya shiga daki ba ya tambayi inna tun a tsakar gidan inda yake zaune saman tabarma ya jingina bayanshi da bango. Inna ta jero mishi dukka bayanin da Ameena ta mishi da kuma wanda fateema ta kara akai game da mutumin da yake zarginta dashi.Allah yasa hakan shine yafi zama alkhairi ga rayuwarta da tashi gaba daya, amma bai kyauta mana ba koda yake tun ranan daya saketa ta dawo gida bai kamata na takurashi ya maida ita ba don sam shi kan shi bai san akan wani tubali ya ajiye rayuwar shiba a yadda na fahimce shi kenan, cewar baba malam.Hakane malam nima dai kada kace na katse kane kuma bana son saka baki a duk hukuncin daka yanke domin ina ganin hakan shine daidai.Rukayya indai hakane baki kyautawa zaman mu ba domin duk inda zama yake indai ana so a ginashi akan tubali mai kyau toh fa sai an dage da fadawa juna gaskiya koda hakan zai sosa rai domin ita gaskiya dai a ko ina sunanta gaskiya don haka ina so daga yanzu kome nace ko nayi nufin aikatawa idan kin hangi kuskure a ciki ko rashin dacewa a ciki ina rokon ki kiyi gaggawar fahimtar dani ni kuma nayi alkawarin zan duba inda keda gyara in gyara insha Allah.Hakane insha Allahu zanyi kokarin gyarawa malam.Allah ya bamu ikon gyarawa gabadaya yanzu kira ita Ameenar tazo.Daga inda inna ke zaune ta dan daga murya ta shiga kiran Ameena.Fitowa tayi ta karaso ta zauna tace gani inna!.Nine nike kiranki Ameenatu, kasa tayi da kanta tana wasa da ‘yan yatsun ta. Yaci gaba, naji dukkan bayanai a gurin mahaifiyar ku don haka abunda nike so dake shine kiyi hakuri ki sanyawa ranki dangana sannan ki natsu ki kama mutumcinki kinga yanzu sabon rayuwa zaki kama ba iriyar wacce da can kike yi ba lokacin kina budurwa ba don haka ki kula sosai da kanki yanzu kin girma kinsan abunda zaiyi kyau ga rayuwar ki kin kuma san abunda zai gurbata ta dan Allah ki rike tarbiyyar ki na maimaita ki kama kanki ki tsare mutumcin ki kinji ko? Ta gyada kai a kasan zuciyart tana cewa ita dai zina koda ta shekara dari ne tabon na nan a sabon shi kamar yau akayi, ta tabbata da bata aikata zina ba baba malam bazai zaunar da ita yana karanto mata irin wannan jawabin ba………. ……..EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI✍️



