Hausa novels

Halysaah Page 77 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 77…Bayan Khaleesat tayi karatun da zata yi ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan ta saka hijab ta fito daga dakin don tun da ta dawo bata ci abinci ba gashi har karfe goma ya wuce, downstairs take leke ko zata ga Housemate dinta, Ajay ta gani yana danna wayarsa, hannunsa rike da Can din soft drink, tana ta tsaye a corridor din don da ba don yunwan da take ji ba komawa dakinta kawai zata yi ta hakura da abincin, after a while ta fara saukowa staircase din trying not to make any sound, tun daga nesa take kallon screen din wayarsa ganin kamar hoton da suka yi da Jay daxu a park, tsaye tayi tana ta kallon wayarsa da mamaki, after some seconds taga ya fita daga hoton kasa gane inda ya samu hoton tayi, tasan dai Jay bazai tura masa pictures din ba, to kaddai a status Housemate dinta ya dora hoton, ta shiga uku, sosai taji gabanta ya fadi, lokaci daya Ajay ya juya bayan yayi sensing kamar mutum na tsaye bayansa, ta ɗan koma baya kamar munafuka tana kame kame tace “Kitchen zan je dama” Ajiye wayarsa yayi ya juya da kyau yana kallonta da mamaki, ta langwabe kai sai kuma ta nufi kitchen din da sauri tana ɗan waigen sa, ko da ta fito bata gansa a parlon ba, bayan ta koma daki ta ajiye shayin hannunta ta dau wayarta da sauri ta bude WhatsApp dinta, status din Housemate dinta ta bude taga hoton amma ya rufe fuskarta with the caption “Halysaah” da yayi ma hoton, to amma wanda ta gani a wayar Ajay fuskarta a bude yake, ta dinga kallon hoton duk da fuskarta a rufe yake, bata san sanda murmushi yayi escaping lips dinta ba don sun yi kyau sosai, har ta ajiye wayar sai kuma ta dauka tayi masa reply din picture din tace “What if gal frnd dinka ta gani” ajiye wayar tayi ta dau cup din shayin da ta ajiye tana juyawa a hankali, taji wayarta yayi vibrate alamar shigowar message, daukan wayar tayi taga ya mata reply yace “Ke ba Gal frnd dita bace? Ai ke zabina ce, ita kuma zabin iyayena” Hmm kawai ta mayar masa sannan ta kashe data dinta ta ajiye wayar, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi tana maimata zabin iyayensa da yace a ranta, duk yunwan da take ji haka nan ta neme sa ta rasa shayin ma bata wani sha sosai ba, bayan ta gama shirin kwanciya ta dauro alwala ta fito sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, wayarta taji na vibrate ta jawo wayar a hankali tana dubawa taga Housemate dinta ne ke kiranta, sai da ya kusa katsewa tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, yace “Why did you go offline Halysaah?” Ta ɗan yi murmushin karfin hali tace “Na je nayi alwala ne zan kwanta” Yace “Ohk, kina da class gobe ne?” Ta ɗan yi shiru, duk da bata da shi tace “Eh ina da….” Jay yace “Yaushe?” Tace “Da safe” Yace “Ohk, na tsaya wani aiki ne a system dina shi yasa ban dawo ba, may be we will meet in school tomorrow in sha Allah” Tace “Allah ya kai mu” Yace “Ameen, Good night Halysaah, naga kamar kin fara jin bacci ko?” Cikin sanyin murya tace “Uhm, sai da safe” Yace “Allah ya kai mu lafiya” Daga haka ya katse wayar sa, Khaleesat ta ajiye wayar hannunta ta juya ta lumshe ido. Da safe Khaleesat na saukowa downstairs taga parlon soo tidy, kamshi sai tashi yake ta ko ina via diffuser da ta gani a parlon, makalewa tayi jikin staircase tana ta kallon parlon, ai kuma ta shiga uku da gori, after a while ta nufi kitchen, ta window din kitchen din take kallonsa don karamin garden ne a waje, entrance din garden din yana ta wajen Garage, tunda ta zo apartment din bai fi sau biyu ta shiga wajen ba, press up yake yi a wajen, juyawa tayi ta kalli Yoghurt da diff kind of berries da granola da nuts sai kiwi and apple dake ajiye kitchen din, nan ta gane parfait zai hada, har zata hada masa wata zuciyar tace ta kama kanta tayi abinda zata yi ta fita, noodles ta dauko zata dafa, tana cikin dafa noodles din ta daga kai taga ya fita daga garden din, bayan ta gama girkin ta fita daga kitchen din zuwa dakinta, after almost 20 mins ta sake saukowa downstairs ta shiga kitchen din, har sannan fruits din suna wajen, ta ɗau karamin bowl ta fara tsinkar different berries din wajen ta yanda bazai gane ta taɓa masa ba, tana wankesu a sink ta fara sha, da sauri ta juya tana kallon kofar kitchen din tayi ido hudu da shi, ita kanta bata san dalilin da yasa ta fara dariya ba, ta ciro berry din da ta kai baki tace “Wanke maka su zan yi fa, so that i can help you dice them” Tana fadin haka ta ajiye bowl din hannunta ta dau wuka zata fara fere Kiwi fruit dake wajen, taji yace “Zo ki fita ki ban waje” Ta ɗan kallesa tace “I want to help you wash them….” Tana ganin kallon da yayi mata, ta ajiye wukan ta wanke hannunta a sink sannan ta ajiye masa bowl din Berries din da ta diba a kofar sauran fruits din, kofa ta nufa ta bi gefensa ta fita daga kitchen din ya bi ta da kallo yace “Ke da baki iya gyaran gidan da kike ciki ce zaki wanke ma mutum abinda zai ci” Khaleesat ta juya ta kallesa dama tasan sai yayi maganar nan, tace “Tun da kai ka gyara ba shikenan ba, ai don ina zuwa school ne….” Yace “You are dirty dai Malama, do not use school to cover ur untidiness” Yana fadin haka ya karasa cikin kitchen din, ta tsaya bakin kofar tana kallonsa taga ko da Liquid wash zai wanke fruits din karewar tsafta, sai da ya fara tura bowl din Berries din da ta diba zuwa can far end of the kitchen yanda bazai dinga ganinsa a kusa da shi ba sannan ya fara wanke fruits din a sink, bayan gishiri har da Venegar yayi using wajen wanke fruits din, a ranta tace to ai wannan ba sabon abu bane kowa na yi, ita tsakaninta da Allah take jiran taga ya zuba liquid wash wajen wanke fruits din, amma taga bai yi hakan ba, tana ta tsaye jikin kofar kitchen din har ya gama hada lafiyayyen parfait dinsa, ta shiga kitchen din ta dau bowl din Berries dinta da ya gantalar gefe daya ta ajiye kusa da shi ta kallesa, ko kallonta bai yi ba, can ta ga ya jawo sauran Yoghurt da ya rage ya tsiyaya mata a bowl din ya ci gaba da abinda yake yi, dariya ya bata amma ta dake bata yi ba, tana ta kallon rich parfait dinsa da yaji fruits da Granola da Nuts, tana kallo ya dau zuma ya tsiyaya a kai, dai dai nan aka bude kofar parlor, ya ajiye zuman hannunsa ya karasa kofar kitchen din don ganin wanda ya shigo, da sauri Khaleesat ta kai hannu ta lakaci honey din da yoghurt, akan idonsa don har ya juyo ya dawo cikin kitchen din, komawa baya tayi da sauri, bai ko kalleta ba ya dau spoon yayi scoping dai dai inda ta saka hannu sannan ya ajiye spoon din a sink, ita dai bata san ya aka yi ba kawai ganin bowl din parfait din tayi ya kife a kasan kitchen, ya koma baya yana kallon parfait babu ko kiftawa, tun tana daurewa har ta kasa ta dafe base cabinet din kitchen din ta tuntsire da dariya kamar an aikota, Ajay dai kallon Parfait din kawai yake a kasan kitchen din, after some seconds ya shafa kansa trying not to laugh too, don dariyarta kadai ya isa ya saka mutum yayi dariya bai yi niyya ba, irin dariyar muguntar nan kawai take yi, ita kuwa ba abinda ya bata dariya ganin bai tsam mata ba gashi duk sun tuntsire a kasan kitchen, kuma shi ya kifar da kayansa da alama, kawai ya juya ya fice daga kitchen din ta bi sa da kallo tana kyalkyala wani sabon dariya, sai kuma ya sake dawowa yana kallonta yayi kasa da murya yace “Kin ga idan ina abu a kitchen kika sake shigo min i will fling you out of this window, ai ni ban san ke mayya bace” Yana fadin haka ya sake ficewa daga kitchen din, Khaleesat dai bata fasa dariyan da take ba, da ta kalli bowl din da ya ɗan tsiyaya mata zallan yoghurt sai ta kalli rich parfait dinsa dake kasan kitchen a kwance, sai ta kara kwashewa da dariya, ta dade abu bai bata dariya kamar haka ba, tayi dariyarta ma’ishi sannan ta fara gyara kitchen din, sai kuma ta fara jin tausayinsa don duk effort dinsa bai sha ko spoon daya ba, gwara ita ta ɗan lasa zuma da yoghurt, the incident was so funny to her, haka duk ta kwashe fruits din da granula dake kasa tayi disposing a shara, bayan ta gama goge kitchen din ya dawo fess ta fito parlor taga Housemate dinta zaune a parlon yana danna wayarsa, tana murmushi ta karasa cikin parlon ta zauna sannan ta gaishesa, ya daga kai ya kalleta ya amsa, bata sake cewa komai ba, shi ma haka, after a while yace “Ba kince zaki school da safe ba?” ta langwabar da kai tace “Kawai fasawa nayi” Juyawa tayi ta kalli Ajay dake saukowa downstairs fuskarsa babu yabo babu fallasa yana rike da makullin motarsa, ta bi sa da kallo trying not to start another laugh har ya fice daga parlon, sai kuma ta kalli Jay ta fara basa labarin abinda ya faru a kitchen, she couldn’t hold her self anymore ta dinga kyalkyala dariya har da saukowa daga saman kujera, shi dai Jay kallonta kawai yake, sai kuma ta dena dariyar da take tace “Isn’t it funny?” Jay yayi murmushi wanda iyakarsa lips yace “It is, sai yace maki me?” Tace “He was very shock too, nasan da ya san abinda zai faru kenan da ya debar min, Allah ne ya kamasa, ga shi yayi stressing kansa ya gyara gidan nan gaba daya yau” Tana dariya ta kare maganar, Jay yace “Gaskiya ne, amma baza ki je school ba me yasa kika ce min za ki je?” Shiru tayi, sai kuma tace “Kawai da gari ya waye na canza mind” Jay yace “Ohk” Wayarsa ne ya fara vibrate ya mike yace “Zan fita sai anjima” Khaleesat na kallonsa tace “Kayi breakfast ne?” Yace “Nayi” Tace “Ohk, byee” Juyawa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita…. Khaleesat na kitchen da yamma bayan ta dawo school taji an bude kofar apartment dinta, sosai taji gabanta ya fadi don dama tunda ta dawo taga ba kowa apartment din take a tsorace, sai da taji muryar Ajay a parlon sannan hankalinta ya kwanta, jingina tayi jikin cabinet din kitchen din tana kirga kwanakin da taga Jay last, after a while ta kashe wutan girkin don ta gama, ta dan leka parlon taga Ajay da wani abokinsa ne bayerabe yana gwada masa abu a Laptop dinsa da alama shima Phd yake yi, fitowa tayi daga kitchen din ta gaida abokin ya amsa yana kallonta, sai kuma ya kalli Ajay yace “Is she ur sister” a takaice Ajay yace “Yeah” Yana ci gaba da nuna masa abinda yake nuna masa, da broken English abokin yace bazai basa ita ya aura ba, Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat yace “Ke dalla malama wuce ki ba mutane waje” Khaleesat ta kallesa da mamaki don ita dai ba tsayuwa tayi a parlon ba, sama ma zata wuce, Femi na kallon Ajay yace “I am very serious Prince, i will marry her as far as una go give me, she’s very beautiful, is she Halfcast?” Ajay yace “Meet Jay about that Femi” Femi ya gyara zama yace “Jay no get joy at all, he isn’t as straight as you” Ajay yace “He will listen, since it’s about you marrying his sister…” Femi yayi dariya sosai yace “I will definitely visit Bauchi soon be that” Ajay dai bai sake ce masa komai ba.A kwana a tashi lokacin Exams din su Khaleesat ya matso don satin da za su shiga za a fara jarabawan, tun ranan da ta mari Abdul har zuwa yau bata sake ganin ko giftawarsa a school din ba, ita dai har sannan hankalinta yaki kwanciya don gani take kawai jira yake ta koma Nigeria before doing anything to her, sosai tayi da ta sanin marin da tayi masa, she wish bata yi hakan ba, da kawai ignoring dinsa ta dinga yi since he is not harming her, da ta tuna sati biyu kawai za su yi suna jarabawan sannan ta koma Nigeria sai taji jikinta yayi sanyi sosai, During all this time haduwanta da Jay ya ragu sosai ba kadan, ko apartment din nata sai in zai kai mata abu yake zuwa kuma ba dadewa yake yi ba, but tayi masa uxuri tunda yace mata su ma a wannan period din ne External defense dinsu may be he is concentrating on that and also giving her space to concentrate on her own studies too, amma abinda ke bata mamaki kafin taga Ajay da laptop ko wani abu da zai nuna karatu yake sau daya to ta gansa da remote din TV da bowl din fruit yana ci yana kallon football ko wrestling sau goma, gashi kamar baya bacci, abokansa kuwa in suka xo baya shigowa da su apartment din…. Ranan Friday Khaleesat na school tare da Safiyyah suna studying course din da za su yi exams dinsa ranan Monday, hadari ne sosai a garin, Khaleesat tace “Mu je apartment dina sai mu ci gaba da karatun a can ko?” Safiyyah tace “Tabb, ni ce zan je apartment din ki wannan Uztaz din na nan? Ni har yanxu kin ki gaya min dalilin da yasa suka yi switching da Housemate din ki” Khaleesat na kallonta tace “To ta yaya nima zan sani, na tambaye Housemate dina yace kawai sbda he is busy because of his upcoming defense ne baya samun time sosai he is always in the Library” Safiyyah tayi dariya tace “Shi kadai zai yi defense din? Shi ma Ajay ba defense din zai yi ba ko ba lokaci daya za su yi bane? Ni har na gano dalilin da yasa yaki zama a apartment dinki wallahi” Khaleesat tace “Meye dalili?” Safiyyah tayi dariya tace “Gaskiya na kara respecting Housemate dinki, wallahi iya da addini da sanin ya kamata, kinga a baya ai babu komai tsakaninku shi yasa ku ke zaune kowa na harkar gabansa a tsohon Apartment din ki, iyaka kuyi mutunci, yanxu kuwa da ya fara son ki yana tsoron kada shaidan yayi using Opportunity din zaman ku gida daya ya cuce ku, kinga hakan bazai haifo ɗa me ido ba, gaskiya yaya Housemate iya da addini” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi kawai, Safiyyah tace “Abinda ya guje ma kenan kawai ba wani abu ba, don shi zuciya ba shi da ƙashi, shi kuma Ajay masifarsa da fitinarsa kadai ma bazai sa ya shiga harkar ki ba a gidan, shi fitinarsa ma zai iya zuke mutum wallahi” Khaleesat na maida wayarta cikin jaka tace “Sai ka masa abinda baya so yake masifa ai, he just love being on his own kar a shiga harkarsa that’s all, but he is kind, caring and down to earth, sai da muka zauna yanxu na gane haka” Safiyyah ta saki baki tana kallonta, can ta gyara zama tace “Ikon Allah, yau ke kike yabon Ajay da kanki, to me da me yayi maki da kika ga he is caring and kind zaman ku a apartment din naki” Khaleesat ta daga ido ta kalleta, can tace “Kilan baza ki yarda ba idan na fara gaya maki wallahi” Safiyyah tace “Ai ina jin ki, gaya min yanda aka yi kika gane hakan in ga ko zai yi convincing dina…” Wayar Khaleesat ya fara vibrate a jaka, ta bude jakar ta ciro wayar, Safiyyah ta leka screen din don ganin me kiranta, sae kuma ta riƙe haɓa tace “Ikon Allah”_Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda Ur evidence_07087865788*Hakika duk wacce ta Bari aka barta abaya ita taso domin mu mata da ado da kwalliya aka sanmu. Assalamualaikum, barkanmu dai Yan uwana ma masu albarka, ayau na zo maku da batun sababbin kayan da na kawo Mana masu matukar kyau da kuma inganci,oum eman collection 🤝😍, takawo maku jakunkuna da takalma,hadi da abayas da kuma sarkoki masu matukar kyau da kuma sauki,07018872587 Ena amare da uwayan gida masu capacity’s toh duk wacce ta yarda da tacika mace da wacce takeso ta zamo ma abociyar kwalliya toh ta garzayo gunmu domin hadewarki cikin ado da kwalliya kedai nemeni a wannnan number domin kisami kayayyaki masu kyau da kuma quality akan kudi kalilan hajiyata 07018872587 ngd 🤝 ado da kwalliya shine takenmu*

Back to top button