Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 18 Complete Novel

*ASM Bk2018*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

 

………A ranar Fatuu na dawowa daga Makaranta da yamma bayan taci Abinci gwaggo ta k’wala mata kira ta isketa a cikin d’aki ta zauna kan kujera tace ma gwaggo dake zaune a bakin gado ga ta,

 

“Dama Maganar tafiyarmu ce Habuja, d’azun nan Abbas ya kira Amadu yake sanar dashi gobe da Asuba zai zo mu wuce duk nayi tunanin sai jibi to amman wai a goben in munje zasu wuce Lagos ne akwae shagalin da zasu yi acan to kinga ba yadda za’ai ba zai fasa tafiyarshi ba saboda mu tunda dae hidimar ta su ce, tuni ma na gama kintsawa Amadu bai dad’e daya dawo ba bayan na kirashi a waya gwara yazo ya shirya don bansan a 6atawa Abbas d’in lokaci daga abun Arziki” shiru Fatuu tay lokaci guda jikinta yay wani irin weak gwaggo taci gaba “ni gaskiya bazan barki ke kadae a cikin gidannan ba kaman yadda kika ce rannan sai kace ana hauka dae, da tunanin da nike ko in kai ki gidan Zaliha to amman can d’in zai maki nisa da Makaranta gaskia to amman dae k’arshe dole hakan za’ai tunda nasan ai ba’a rasa masu zuwa Makarantar taku daga can ba” sadda kanta tay k’asa batare data ce komae ba gaba d’aya ba abunda ke mata dad’i tafi buk’atar taji ta ita kadae,

 

“Kinyi shiru kin d’ukar da kai” taji gwaggon ta fad’a, a hankali ta d’ago idonta har sun canja don ma ta cije ta hana kwalla su zubo mata cikin rawar murya tace “to ko inje gidansu Haulat kafin ku dawo” d’an jimm gwaggon tay sai kuma tace “ba wai na k’i bane ni kaina zanso ki zauna can zaifi maki sauki to amman nayi duba ne da halin da ake ciki na babu kar kaje ka k’ara ma Mutum nauyi kan wanda yake fama dashi”, Fatun tace “ai ma har munyi Magana da Haulat din dana ji kince ba zaki barni in zauna anan d’in ba kuma tace tana komawa zata fad’i ma innarsu” gyad’a kai gwaggon tay tace “shikenan to zan ga abunda za’ai yanzu zaki islamiyya ne?” girgiza mata kai tay tace “ina son in yi wanka ne kuma naga lokacin ya k’ure” gwaggo tace “to je kiyi wankan sai ki had’a kayan da zaki amfani dasu anjima sai munje in kai ki” mik’ewa tay kawae har ta nufi kopa sai kuma ta juyo tace “ko ba sai na d’auki kaya ba sai in rink’a zuwa ina yin wanka anan” shiru gwaggon tay tana nazari hakan yasa Fatun cewa “sai mu rink’a zuwa da haulat” gyad’a kai gwaggon tayi alamar amincewa Fatun ta juya ta fice tana kukan zuci wanda yafi na fili ciwo, tana fita gwaggo ma ta fita ta nufi kitchen ta fara tunanin yi ma Fatun cin cin dama suna da lemuka a fridge tasan zata ji dad’in shi, Bayan sallar Isha suka nufi gidansu Haulat din lokacin duk suna a tsakar gida suna cin Abinci innarsu na jin sallamar gwaggo ta mik’e tana mata maraba fuskarta d’auke da fara’a haka ma gwaggon, innar tace su shiga daga ciki gwaggo tace ba komae su tsaya a wajen tunda duk anan ake innar ta nufi daki da sauri ta d’aukko mata darduma bayan ta shimfida tace mata Bismillah ta zauna, gaisawa suka shiga yi a mutunce tayi mata ya aiki gwaggon ta amsa da Alhamdulillah bayan sun gama gaisawar tace “dama zuwa nai rokon Alfarma, gobe in Allah ya kaimu zamu tafi bikin su Hajiya shine nake son in ba damuwa Fatuu ta zauna anan kafin mu dawo tunda bazata samu zuwa ba Saboda jarabawa da zasu fara” yar dariya innarsu haulatun tay tace “Haba gwaggo wannan ai ba wani abu bane da har sai kin taso kin zo, nan ai gidansu Fatima ne ko kina nan taji tana ra’ayin tazo ta kwana ai hakan ba matsala bane wllh, ba wani abu Allah ubangiji ya tsare ya kiyaye hanya shima babansu zasu je da sauran limaman su Malam Tanimu amman sai ana gobe d’aurin auren ni kaina naso zuwa to amman yace basai naje ba sai dae in yi Addu’a kawae Allah ubangiji yasa Alkhairi ya basu zaman lpy da zuria dayyiba, amman yaron yana da kirki wllh da ya barni koda iya kud’ina kenan sai naje har bashi ma zan iya ci wllh don inje bikin nashi” gwaggo na yar dariya ta amsa da Amin tay mata godiya kafin ta dasa yabon Haisam har tay mata tayin Abinci tace Alhamdulillah a k’oshe take, duk abun nan Fatuu na cikin dakinsu haulatu tun bayan da suka shigo ta gaida innarsu haulatun ta jata d’aki, zaune sukae a gefen yar katifar Haulat sukae jugum a hankali kwalla ke gangaro ma Fatuu haulat na kai hannu tana goge mata tana bata hak’uri suna cikin hakan taji muryar gwaggo tana cewa tafito su tafi ta mik’e bayan ta gyara fuskarta haulat ta bi bayanta suka fita, sosae gwaggo ta k’ara yima innar tasu godiya kafin ta fiddo kud’i ta bata amman tak’i amsa tace Allah ya kyauta don Fatima zata zauna gidan ta amshi kud’i gwaggo tace wllh ba don haka ta bata ba, da k’yar dae ta kar6a sanin dama tana yi mata Alheri, a tare suka rakosu innar na fad’in ai tayi zaton Fatun tazo kenan gwaggo na murmushi tace sai gobe in zasu tafi innar tace Allah ya kaimu goben lafiya daga haka suka k’ara sallama ta koma haulat kuwa saida ta rakosu har bakin lungu sannan gwaggo tace ta koma tay masu saida safe tace ma Fatuu sai sun had’u gobe ta d’aga mata kai kawae suka tafi.

 

 

Zaune suke gaba d’ayansu kan Dining table suna cin dinner har saida aka k’ara wani table d’in shima mai kujeru sha biyu a haka ma wasu saidae zama sukae kan kujeru a falo, a Table d’in farko anan Senator da matanshi da kakanninsu Haisam sai Her Excellency Hajiya Zainab, Hajiya da Sameer da Haisam duk suke, lafiyayyun Abincine aka jere don musamman dama anyo hayar kwararrun chefs Saboda bikin to wasu tun yau sun fara aikinsu, yau dae dole kowa Serving nashi ake Saboda Hajiya Zainab ko ba don ita bama ba yadda za’ai Sameer yay serving kanshi Abinci Never yanzu ma a hakimce yake umarnin ma sai ya mula yasha iska yake iya badawa shima da kai ko hannu, tsit kake ji sai karar cokulla can sun yi nisa kakansu ya dakata idonshi akan Sameer da turanci yace “shi wannan sai yaushe zai yi auren ne?” Kakar mace tace “ya kamata ace shima yay Aure gaskiya” yar dariya Hajiya Zainab tay tace “wannan ina tunanin har yanzu ba’a haifi Matar da zai aura ba” waro ido duk sukae Senator yace “kar dae kice man baida wadda ya tsayar zai aura har yanzu?” Girgiza kai tay tace “I don’t think so” tay Maganar idonta akan Sameer d’in da ko kallonsu ma bai yi ba tunda suka fara Maganar, jinjina kai Senator yay kafin yace “duk laifin Son ne ya zaka tsaida mata shi ka barshi ko baiso sai ka tursasa mashi ai” d’an guntun murmushin gefe Haisam yay yasan kawae dad d’in nashi ya fad’a ne amman ba wanda bai san halin Sameer ba ba yadda za’ai ayi masa dole don kuwa rai zai 6aci ne,

 

 

“Ai kuwa ba zuba mashi ido za’ai ba k’ato dashi yay ta zama ba mata yakamata a nema mashi tunda shi baida Niyya, Akwae k’anwar wadda D’an uwan nashi zai Aura ita yakamata a nema mashi” duk suka yi murmushi sai lokacin Sameer d’in ya d’aga ido ya kalli Senator da yay Maganar bakin shi ya d’an d’aga kad’an wai a hakan murmushi yay shima na mamakin jin shi za’a had’a da mata, can sai ma ya mik’e don baison kallonshi da ake d’agowa anayi ya nufi upstairs yana taka staircases d’in cike da isa suma sunga ta kansu, duk bin shi sukai da ido Haisam dae d’an murmushi yay cikin ranshi yana imagining yadda zaman Aure zai yiwu tsakanin Sameer da Farha, kuma abunda basu sani ba shine yana da yan mata kawae ra’ayin Auren ne baida shi, bayan sun gama shima Haisam upstairs din ya haye part d’inshi nan ya iske Sameer d’in kan gado yana latsa waya dama duk in yazo a part d’in Haisam yake sauka yana shiga wayarshi ta fara ringing Amarya tay kira bayan ya d’aga tace tana son suyi Video call ya amsa da Ok kafin yay connecting da laptop d’inshi dake kan bedside suka fara magana akan program d’in gobe da za’ayi a Lagos duk abun nan ko kallonsu Sameer bai yi ba tamkar bai ma jin abunda suke can Fanan tace waye a bayanshi yace mata Sameer ne tace bari su gaisa, d’an janye jikinshi yay ya juya yace zasu gaisa ko tanka shi bai ba har saida Fanan d’in tace”Hi Sameer!” sannan ya d’an juya ba yabo ba fallasa ya bita da ido saidae yanayin fuskarshi ya d’an canja a hakan wai murmushi ne yay mata tana murmushi tace “hope u’r coming to Lagos 2morrow” D’an jinjina mata kai yay kawae daga haka ya maida kanshi kan wayar Haisam ya juya suka cigaba da Magana kafin daga baya sukae sallama ya juya ya kalli Sameer ya kai hannu ya kwace wayar yana fad’in bari yaga abunda yake da ya janye attention d’inshi ya kasa sakin jiki ya gaisa da bride d’inshi sosae, d’an d’age bakin dae yay Haisam ya kai idonshi kan screen d’in wayar da sauri ya d’aga kai yay mashi wani kallo Sameer d’in ya d’age mashi gira sigh Haisam yay yace “Bro stop decieving people and ur self Just get married” wani guntun murmushin gefe yay ma sha Allah ashe k’ilan yasan kyaun da yake in yay murmushi shiyasa bai cika yi ba shima dae yana da dimples kaman Haisam d’in saidae nashi biyu ne mik’ewa yay ba tare da ya ce mashi komae ba walking majestically ya nufi hanyar toilet, aje mashi wayar yay ya d’aura kanshi akan pillow yana son ya kira Fatuu yaji halin da take ciki amman yana ganin kaman dare yayi can dae ya kai hannu ya d’auki wayarshi yay sending mata kira baiwar Allah lokacin tana kwance kan gado tayi lamo don ta kasa bacci sai tsumayen kiranshi take don kwana biyu kullum da wayarshi take bacci tana haka taji ringing alamar kira da sauri ta kai hannu

tana ganin shine tay murmushi kafin tay picking ta kifa wayar a Kunnenta,

 

“Zaraah” a hankali tace “na’am ina wuni” amsawa yay yace ya akai batayi bacci ba tana murmushi tace hakanan baccin ne bai zo ba, d’an murmushi yay kawae ya tambayi ya take tace mashi lpy lou daga haka suka ci gaba da wayar yana cikin yi Sameer ya fito k’ugunshi d’aure da towel ya nufi press sai lokacin ya juya ya kalli Haisam lokaci guda ya gane da mace yake Magana jin ya ambaci Zaraah cikin husky voice d’inshi don ba irin muryarsu d’aya ba yace “U what do you think u’r doing, ain’t u deceiving??? Wani kallo Haisam d’in yay mashi shi kuma ya ta6e baki ya juya yana kokarin sa short da sauri Haisam ya juyar da kai don yasan ba kunya ta ishe shi ba kimono yasa iya gwuiwa ya d’auki laptop d’inshi ya fice daga bedroom d’in ya nufi Parlor, sosae suke fira har yake ce mata gobe su Abbas zasu zo he isn’t happy da batare da ita za’a zo ba saidae tay murmushi kawae daga baya yace ta kwanta gobe akwae skul sukae sallama sai gashi kuwa tayi bacci bada jimawa ba.

 

Ana kiran sallan Asubar farko wayarta tay ringing har saida gabanta ya fad’i ganin lokacin da aka kiratan gashi bata san lambar ba, can dae ta d’aga tay shiru tana son jin waye ya kira on the Other hand taji an kirata da Zarah lokaci guda ta gane Abbas ne cikin muryar bacci ta amsa ta gaidashi yace gasu nan kopar gida a bud’e ma Feenah da sauri tace to ta saukko daga gadon, d’akin gwaggo ta nufa ta fad’i mata suka fito tare gwaggo ta nufi wajen taje ta bud’e Abbas ya fito yazo wurinta suka gaisa yace zai wuce Masallaci gasu Feenah nan zasuyi salla in ya dawo sai su wuce tace to ya juya Feenah ta shigo tana ruke da hannun Abdul ta rungume Nasreen gwaggo ta kar6eta Fatuu kuma taje ta kama hannun Abdul suka nufi d’akin gwaggo gaba d’aya bayan sun zauna suka shiga gaisawa Fatuu ma ta gaishe da ita tace “Allah sarki Zarah banji dad’i ba dake za’a ba wllh” Abdul ma yace “nima haka momy” ita dae d’an murmushi tay haka gwaggo ma Feenah ta sake cewa “Amman dae ba gida zaki zauna ke kadae ba ko” gwaggo tay saurin cewa “eh zata zauna a makwabta ne gidan kawarta da suke Makaranta d’aya” Feenah tace yauwa hakan yayi daga baya suka tashi jin an kira salla, bayan sun gama gwaggo tace kota dafa masu wani abu Feenah tace a’a bata iya cin abu yanzu amman akwae Abinci a Mota a hanya sai su ci, su Abbas da Amadu na dawowa daga Masallaci Amadun ya shigo ya fara fita da kayayyakinsu ba 6ata lokaci suka fito don tafiya gwaggo tace ma Fatuu ta d’aukko jakarta da uniform sai a ajeta gidansu Haulat, da tace zata zauna in safiya tayi saita shirya ta tafi Makaranta in ta dawo sai ta wuce can amman gwaggon ta k’i amincewa don gaba d’aya ma don ba yarda zatayi ne yasa zasu tafi su bartan, bayan ta daukko komae suka fita Amadu ya kulle gidan gwaggo tace ya ciri makullin guda yaba Fatun yace to, Amadu ne ya shiga gaba sai su kuma suka shiga baya Abbas na ganinta yace da ita za’a kenan gwaggo tace a’a za’a ajeta can gaba gidan da zata zauna yace Ok yayinda a ranshi yake jin wani irin tausayinta in ba so da rashin Adalci ba ya za’ai ace Mom Zarah bata je bikin Haisam ba da ranta da lafiyar ta, a daidai bakin lungunsu Haulat aka ajeta duk jikinta yay wani iri gwaggo tace taje ganin tayi tsaye rungume da jaka cikin breaking voice tace ” Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya….” Da sauri ta juya jin tana niyyar fashewa da kuka Abdul ya kwala mata kira ta juya ya fito da hannunshi yana mata bye bye itama ta d’an d’aga mashi sai kuma Feenah da gwaggo har da Amadu suma suka d’ago suna yi mata kawae sai ta juya ta fashe da kuka saida suka ga shigarta gidan sannan suka tafi, kopar Marusa low-cost suka wuce aka d’auki Nana kaman yadda Haisam ya ba Abbas sak’o sai fatan a sauka lafiya.

 

Tana shiga d’akinsu Haulat ta aje jakar gefe ta kwanta kan katifa ta rufe fuskarta da bakinta tana ta kuka, haulat dake gefenta tana ta bata hak’uri itama kaman zatayi kukan har saida wata k’anwar haulat taje ta gayo ma innarsu ta shigo tana fad’in “Fatima ya da kuka kuma da girmanki don an tafi unguwa an barki ai kaman gobe ne zata dawo ko haba daina kuka k’annenki nata kallonki sai suyi maki dariya ma” jin hakan yasa ta sassauta kukan, da gari ya idasa wayewa da k’yar haulat ta samu tasa ta tashi suka fara shirin tafiya Makaranta bayan sun gama aka kawo mata abun kalaci biredi da kosai da tea don Haulat ta fad’i ma innarsu Fatun bata shan koko, bata wani ci da yawa ba tace ta k’oshi haulat taitai da ita ta k’ara ta kafe akan ta k’oshi amai take ji dole ta kyaleta da aka kai ma innar tasu tace suje su ci, k’arfe bakwai da rabi suka fito suka iske innar a yar barandar da take sana’ar koko haulat tace zasu tafi har ta k’irgo kud’i zata basu cikin disasshiyar murya Fatuu tace ta barshi gwaggo ta bata kud’in da zasu rink’a yin break innarsu haulatun tace kuma dae banda wanda ta bata, godiya tay tayi masu a dawo lafiya kafin ta k’ara ba Fatuu hakuri suka tafi, jikinta sukuku suka nufi bakin hanya wai kuma sai take jin dama ta bisu don kwata kwata ta rasa mike mata dad’i a haka suka k’araso bakin titi bada jimawa ba sai ga School bus suka tafi.

 

Tafiya yankin Azaba,Amadu sai dae ya d’anyi bacci ya farka ya kalli hanya yayin da cikin ranshi yake ta Murna yau dae Allah yayi zaije Abuja, akan hanya suka samu wuri acikin wani gidan mai da bai aiki suka yi breakfast don Abdul nata kukan yunwa harda Nana don bata wasa da cikinta shiyasa gata nan tubarkallah, bayan sun gama suka sake d’aukar hanya aka dasa baka jin komae sai muryar Nana da Abbas dake ta hira abunsu don ita Feenah tafiya galabaitar da ita take sai jefi jefi take saka masu baki, Alhamdulillah Allah yayi an iso a Abuja wuraren Azahar, sakin baki Amadu yay yana kallon ikon Allah da kafin su shigo Abujar a garuruwan bakin hanya har yana ce ma Abbas dama haka Abujar take Abbas na dariya yace ya jira tukun kafin ya yanke hukunci, sakin baki yay sai faman kalle kalle yake kaman d’an kauye yazo birni Abbas na ta faman yi mashi dariya gwaggo ma dae bata ta6a zuwa ba amman bata nuna k’auyanci kaman Amadu ba don shi fa tsakaninshi da Allah a k’asar waje yake ganinshi ba kaman shimfidaddun tituna masu girma da bai saba ganin irinsu ba, ko ina titi haka yake ta fad’i can kuma yace wai ba Keke Napep ne da babura sai motoci kawae yake gani Abbas dae dariya kawae yake yace mashi akwae bangaren da keda akwae su nan dae inda suke babu, saida suka sake 6ata kusan awa Saboda go slow na Motocin ma’aikata kafin suka iso gidansu Haisam d’in, “Ya ilahi ya rabbil alamen” haka Amadu ya fad’a acikin zuciyarshi saidae baisan ya fito fili ba Nana ma cewa tay “kan uban nan!,wai anan Zakee ke rayuwa shine don cutar kai ya koma Katsina ya tsugunna” gaba d’aya ta basu dariya, gwaggo ma dai ta yaba ba abunda take fad’i sai “Ma sha Allah” da alama fa Amadu yay mutuwar tsaye don mamaki ya gama cikashi tunda uwar data haifeshi bai ta6a ganin gida irin wannan ba nan take ya fara jinjinawa hali irin na Haisam harma da yan uwanshi yadda basu d’auki Duniya da zafi ba, bayan Abbas ya parker Motar a wagegen parking spot d’in gidan mai d’auke da jerin jigunannun motoci duk suka fito Abbas ne ya hangi Nameer yana nufar Mota dake can gefe ya k’wala mashi kira ya juyo yana yin arba dasu ya washe baki ya nufesu, yana zuwa ya shiga gaishe dasu yana yi masu sannu da zuwa duk suka amsa Nana tace “yauwa mai kama da Zakee” still dariya yake ya kai hannu ya dafa shoulder d’in Amadu yace “Mutumina barka da zuwa” murmushi yay mashi wanda yafi kama dana yak’e yace mashi yauwa, Nameer d’in ya kuma cewa “Ya banga yar gidan ya Haisam ba mai kumatu?” Dariya duk suka yi gwaggo ta sanar dashi bazata samu zuwa ba Saboda jarabawa da zasu fara yace baiji dadi ba, Abbas yace “zaka wani wuri ne?” Yace “No bakin gate zanje akwae wadanda zan shigo dasu wai security sun hanasu shigowa” Abbas na dariya yace “Ok muma saida aka tantance mu, amman ya naga ansa security sosae lafiya dae ko?”

 

“Eh lafiya lou akwae na Momyn Nasarawa ne” D’an bud’a ido Abbas yay “kace her Excellency na nan ashe” kai ya d’aga alamar eh yace yaje bari ya shiga dasu Nameer d’in yace bari ya kai Amadu d’akinshi sai ya dawo ya d’aukar mashi jakar goyonshi Amadun na cewa ya bari ya d’auka yace ya bashshi ai shi bak’on shi ne suka nufi part d’inshi dake saman bene, ta baya suka bi don akwae benen da zai kaika saman Amadu dai na biye dashi zarare zarare tamkar rakumi da akala,

 

Suna akan hanyarsu ta shiga mai Entrance na gidan Nana ke tambayar Abbas wacece Her Excellency d’in data ji suna Magana don Mutum yay taka tsantsan, sosae Abbas yasa dariya kafin yay mata bayaninta harda alak’arsu da Haisam ita gwaggo dama tasan labarinta, suna shiga parlon sukae kacibus da Jidderh cike da Farinciki ta nufosu tana masu sannu da zuwa ta gaishe su duk suka amsa suna mata Murmushi Abbas yace ta kaisu wurin Hajiya tace to tay gaba suka bi bayanta har part d’in da Hajiya take, lokacin da ta gansu sosae tay murna sai sannu da zuwa take masu harda rungume gwaggo bayan sun gaggaisa da Mutanen dake a parlon nata ta jasu cikin bedroom tace su huta duk suka ce salla zasu yi, kafin su gama sallar an jere masu Abinci da abun sha suna gamawa suka hau cin Abincin don suna buk’atar shi, saida suka samu natsuwa sannan Hajiya tay masu jagora part d’in Mahaifiyar Haisam d’in lokacin duk suna zaune a k’ayataccen parlonta harda Hajiya Zainab da Auntynsu Haisam nan su Nana suka ga ikon Allah sun rasa gane wacece ma Mahaifiyar Haisam d’in har saida Hajiya tay masu bayani suma Matan gidan ta gabatar masu dasu gwaggon duk da sun santa Feenah ma ta ta6a zuwa sau d’aya wani zuwa da sukai da Abbas ya kawota suka gaisa Nana ce dae ba’a sani ba duk ta wani natsu sai kace ba ita ba, faram faram suka amshe su sunata godiya da Addu’ar Allah ya bar zumunci ita dae First Lady d’an murmushi kawae tay masu daga baya Hajiya ta koma part d’inta dasu,

 

Abbas na fita part d’in Haisam ya wuce anan ya iske shi da Sameer da Saleem dama shi yana a gidansu na Abuja, duk sunyi mamakin ganinshi don bai gaya masu sun iso ba last wayar da sukai da Haisam basu kaiga isowa ba hannu ya ba kowannen su suka gaisa harda Sameer don sun san juna ta dalilin Haisam daga baya yay joining nasu cin Abincin, Nameer na shiga da Amadu part d’inshi duk ya k’ara shan jinin jikinshi ganin kyawawan yan gayun samarin dake ciki harda yan Ethiopia bedroom ya wuce dashi nan ma dae ya iske wasu kyawawan guda biyu kan gado suna game a laptop cikinsu d’aya d’an Hajiya Zainab ne, Nameer ya kallesu da murmushi yace “Guys meet my Friend from Kt” d’aya ne ya d’ago yace mashi an zo lpy shikam d’an uwan Sameer d’in ko ci kanka bai ce ba da alama duk haka suke, Nameer ya lura da yanayin Amadu hakan yasa ya dafa shi yace “just feel at home” d’an murmushin yak’e dai kawae yay ya kai jakarshi cikin press kafin ya nuna mashi toilet yace ko zaiyi amfani dashi bari yaje ya shigo da mutanen yanzu zai dawo yace to Nameer d’in na fita ya shige toilet, farko jigum yay saman seat dake rufe hakanan duk sai yaji ya raina kanshi can kuma ya mik’e yay abunda zaiyi ya d’auro Alwala ya fito, yana fita cikin sa’a yaga basu saman gadon ashe yana shiga toilet Ashraf k’anin Sameer yace su koma d’akinsu nan ana interrupting nasu dama ba anan suke da zama ba shine suka fita, wani sanyi Amadu yaji ya fara kokarin gane inda gabas take saidae ya kasa dole ya zauna gefen gado har Nameer ya dawo d’auke da tray d’in kayan Abinci bawan Allah shi yaje ya amso mashi, tambayarshi gabas yay ya nuna mashi ya zauna ya jirashi har ya gama sannan yace ga Abinci nan yaci ya k’oshi bari yaje ya dawo aikuwa wa Allah ya had’a da Abinci ba Amadu ba sosae ya saki jiki ya kwashi gara ganin shi kadae ne a d’akin yana gamawa cike da karfin hali ya d’auki tray d’in ya fita bayan ya sauka k’asa ta baya cikin sa’a yaga d’aya daga cikin ma’aikatan dake aiki a babban Kitchen d’in dake bayan ta amsa tray d’in shi kuma ya juya ya koma upstairs yana shiga bedroom ya haye gado nan da nan kuwa bacci yay awon gaba dashi. Ana gama sallar la’asar masu tafiya Lagos suka fara shiri duk Abokan Haisam ne banda iyaye ko su Jidderh baza’a dasu ba sai dae Laila da Amal k’anwar Sameer itama kusan sa’ar Lailan ce da wasu daga cikin yan Ethiopia, haka Nameer ma banda shi da alama sha’anin na manya ne Jidderh harda kukanta taje ta fad’i ma Mom dinsu tana son zuwa don Allah tasa aje da ita tace tay hak’uri tunda ance baza’a da ita ba Hajiya Zainab tasa baki tace yakamata aje da ita itama ai yan mata ce da kanta ta kira Haisam tay mashi Magana akan a sama mata ticket itama sannan akace za’a tafi da ita, kusan su goma sha biyar harda Nana aka kaisu Airport wasu dama already suna can Najeeb ma acan ya sauka don bai k’asar, ba 6ata lokaci jirginsu ya tashi.

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button