Uncategorized

Dalibin Kano Ya Samu Nasara A Gasar Tambayoyi Ta Kasa Na Kungiyar Kwamfuta ta Najeriya

Abdul Yassar Yahaya Musa , Kano, NCS

Abdul Yassar Yahaya Musa

Dan asalin jihar Kano, Abdul Yassar Yahaya Musa ya zama daya daga cikin mutane hudu da suka lashe gasar kacici-kacici ta kasa da kasa na shekara-shekara na kungiyar Kwamfuta ta Najeriya.

Solacebase ta ruwaito cewa Yassar, dan asalin Kano na farko da ya zama zakara a gasar, tun lokacin da aka fara gudanar da kacici-kacici na shekara shekara sama da shekaru ashirin, dalibin SS II ne na makarantar sakandare ta Day Science, Kano.


 An kamalla gasar da aka gudanar kusan a sassa uku na Jihohi, Shiyya da na Kasa a ranar Larabar da ta gabata.

Sakataren kungiyar kwamfutocin Najeriya reshen Kano, Malam Lukman Bayero ya shaida wa Solacebase a ranar Asabar din da ta gabata cewa dalibai biyu daga makarantun sakandare 35 da ke Kano sun halarci gasar kacici-kacici ta shekara-shekara.

 “Wannan shi ne karon farko da muke samun wanda ya yi nasara a gasar da aka fara sama da shekaru ashirin da suka gabata,” inji Bayero.

”A yin Rijistar gasar ne galibi a watan Maris kuma ana iya samun dama ta shiga gasar ta hanyar shiga shafin su www.ncs.org.ng

 Ya yi nuni da cewa za a ba wa wadanda suka yi nasara hudu lambar yabo a ranar 2 ga watan Agusta a Abeokuta, jihar Ogun.

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button