Uncategorized

Ko yanzu na samu mijin aure zan ajiye fim na yi aure na – Jaruma Zee Preety

A wata hira da mujallar Fim ta yi da jaruma Zulaihat Ibarahem wanda aka fi sani da Zee Preety a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood jarumar ta bayyana kudirin ta da kuma manufarta ta shigowa masana’antar.

Jarumar ta bayyana wa mujallar cewa dalilin shigowarta harkar fim shi ne “Akwai wani saƙo da nake son isar wa da jama’a kuma alhamdulillahi nasan sakon ya isa inda nake so ya je.

Bayan wannan an tambayi jarumar ko wace shawara zata baiwa ‘Yan mata masu kuɗirin shigowa harkar fim?

Sai jarumar ta kada baki ta ce “A gaskiya harkar fim harka ce wadda ta ke buƙatar mace ta kame kanta, domin ita rayuwa bata da tabbas domin tana iya sauyawa a lokacin da baka yi tunani ba, sannan kuma ba lallai ba ace duk wanda kuka haɗu da shi mutumin kirki bane.

Hakan baya na nuna yawancin mazan Kannywood bana kirki ba ne, sai dai ba a rasa bara gurbi a ko ina.


Also Read:

Gaskiyar Magana Akan Aure Hadiza Gabon da Malam Isah Ali Pantami

Dalilin Da Yasa Na Ki Auren Adam A Zango – Ummi Rahab

Sannan ta ƙara da cewa wasu yan matan suna shiga harkar fim domin yin suna a duniya, wanda ba haka lamarin yake ba ita daukaka ta Allah ce, shike da ikon daukaka bawansa a yayin da ya so kuma a lokacin da ya so, don haka idan kika zama mai kamun kai za a sanki a ko ina har wajen da baki yi tunani ba.”

Daga karshe an tambayi jarumar ya maganar aure fa?

Sai jarumar ta ce “Shi aure nufin Allah ne, kuma lokaci gare shi, idan har Allah ya nufa zaka yi to sai ka yi, kuma ko a yanzu na samu mijin aure in har muka daidaita to zan bar harkar fim na yi aure na, domin shi ne mutuncin ko wace mace.

Bayan haka ma mahaifanmu suna buƙatar muyi auren tunda ta haka aka same mu.

Wane fata ka ke yi wa wannan jaruma?

Back to top button