Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 9 Hausa Novel

Wannan wunin da kowa yake yi a gida ba karamin takurawa Khadeeja yake yi ba; tana cikin laulayi sannan ga hidimar gida da ta yara. Wuni suke cin abinci don haka gidan kullum kace-kaca ga wanke-wanke baya yankewa. Wasu lokutan tana samu ta danngyara amma wasu lokutan haka take kyalewa saboda ba zata iya ba.Yau kwana biyu kenan dan almajiri da ta dauka yake zuwa yayi mata wanke-wanke da sharar tsakar gida bai zo ba; bata sani ba ko suma lockdown din ya shafe su don da dai suna fitowa tunda makarantarsu nan cikin unguwa take. Gidan gaba daya yayi kaca-kaca don kitchen har warin lalatacce abinci yake yi. Suna gama cin abincin safe Abbansu ya mike ya shige daki. Nan da nan ta saka yaran a gaba suka tayata suka fitar da wanke-wanken suka kai fanfon waje, ta turasu waje ta gyara cikin gidan tsaf. Tana yi tana hutawa tana tofar da yawu, zuwa karfe goma na safe ta gama. Ta fito tsakar gidan ta tara yaran a waje daya, ta dubesu tace ‘Afaf muje fanfo ni da ke mu wanke kwanukan can, kai kuma Yaya Habib dauki tsintsiya ka share compound din nan, ka fara daga kan baranda. Nasreen da ke da Shukra ku tsince toys dinku ku zuba a kwando, duk wadda bata tsince ba ba zan bata sweet ba.’Nan da nan kowa ya fara aiki.Ta saka kujera a bakin famfo tana wanke kwanukan Afaf tana mata dauraya. Sai da suka cika karamin kwando da kwanukan ta kirawo Habib wanda ya kusa gama sharar tace ‘Ya Habib zo ka dauki wannan kwandon ka kai kitchen ka kwashe kwanukan a kan sink sai ka dawo da kwandon mu cigaba da zubawa.’Ya dauka a nufi cikin gidan; a kan baranda suka ci karo da Abbansu yana fitowa. Ya dan ja baya don ya bawa Abban hanya ‘Kai ina zaka da kwanuka haka.’’Anti ce ta wanke zan kai mata cikin gida.’Yana daga kansa ya hango Afaf a tsakiyar kwanuka suna ta wanke-wanke ita da Khadeejan. A fusace ya karasa wajen, cikin tsawa yace ‘Ke Afaf me kike a nan? kalli yanda kike jika jikinki sai kin gama kiyi ta mura.’ Ya dubi Khadeeja yace ‘Ina yaron naki?’Ta tofar da yawun bakinta a gefe sannan tace ‘Kwana biyu bai zo ba, nima ban san dalili ba.’Ya dubi Afaf wadda ta cigaba da aikinta ba tare da ta kula da shi ba, ya daka mata tsawa yace ‘Ki fita daga cikin ruwan nan nace, me kika iya?, sai sanyi ya kama ki kina ta faman jika jiki. Fice kije ki canza kaya kuma kada ki sake fitowa nan.’Ta dubeshi tace ‘Kwanukan ne da yawa, ni din kuma ba dadi nake ji ba idan muka gama gaba daya zata canza kayan ai.’Habib ya karaso ya ajiye kwandon yana cewa ‘Anti gashi.’Ya juya ya cigaba da shararsa.Abbansu ya sake dakawa Afaf tsawa don haka ta fice daga wajen wanke-wanken ta shige gida. Har ya bude baki zai cigaba da magana ya hango Habib yana kwashe shara ‘Kai Habib wa ya saka sharar nan?’Yace ‘Anti ce Abba, ai na ma gama kwashewa zan yi.’’Ajiye tsintsiyar nan ka shige cikin gida ka bani waje.’ ya fada a fusace.Ya jefar da tsintsiyar ya shige gidan.Ya juya kan Khadeejan wadda take cigaba da wanke-wankenta yace ‘Wai me kika mayar da yaran nan ne? Habib ne zai iya share wannan tsakar gidan ga kura ga komai. Itama Afaf din wannan uban ruwan ai sai tayi mura. Ke kika ce a bar mai aikinki ta tafi gida, da kin bari ai da yanzu tana nan; sannan kuma ki dinga basu aikin da ya fi karfinsu? Bana son irin wannan; bana son ki dinga yiwa yaran nan kallon wasu manya, ki dauke su kamar ke kika haifsu shine zaki iya yi musu adalci. Idan an ji wani almajirin yana bara sai a kirawoshi ya karasa wannan aikin ko kuma tunda kun kusan gamawa ki karasa zuwa gobe a sami wani almajirin.’Ko kallonsa bata yi ba ta cigaba da wanke-wankenta, ya ja tsaki ya juya ya nufi cikin gidan. Ta share hawayenta ta cigaba da wanke-wankenta.Ba zata iya dogon surutu ba sannan kuma bata son tana biye masa suna fada a gaban yara, ita yanzu duk wani abu da zai sa ayi magana ma bata so; shi yasa ta gwammace tayi masa shiru.Sai da ta gama wanke-wanken nan tsaf sannan ta kwashe sharar, ta debi kwanukan ta shigar cikin gida.Suna zaune a parlor suna kallon TV.Tana kitchen din tana kife kwanukan Afaf ta shigo ta sameta, ta dauki kwanukan ta fara kifewa. Ta dubeta tace ‘Afaf je ki zauna ai na kusa gamawa.’Tace ‘Bari na tayaki Anti, ai nan babu ruwa.’Ba don ta so ba ta kyaleta sai da suka kife kwanukan gaba daya ta mayar da komai inda yake sannan ta wuce daki su kuma suka cigaba da kallonsu.Can wajen 1pm bayan sun yi sallar azahar ta fito daga daki ta shiga kitchen; tuwon alkama da miyar danyen kubewa ta dafa jiya da daddare amma duk sai suka ki ci. Da yake akwai biscuits da cake sai kowa ya ci ya sha lemo, ita da abbansu ne kawai suka ci tuwon gashi ta dafa shi da yawa. Da safe kuma da kwadayi ta tashi don haka wainar fulawa ta soya kowa yaci. Wannan ragowar tuwon shi ta dauko daga fridge ta dumama shi, ta dumama miyar wadda ta sha kaza da nama. Ta zubawa kowa abincinsa sannan ta kirawosu kowa ya dauki nasa suka zauna a table.Kallon tuwon kawai Habib yakeyi yana juyashi amma yaki ya fara ci, tana kallonsa tayi banza da shi ta cigaba da kai lomarta tana bawa Shukra don ita tuwon yayi mata dadi. Jimawa kadan ya dubeta yace ‘Anti tuwon jiya ne fa?’’Eh, shine, ko ci ko bari.’ ta fada a gajarce ta ci gaba da cin abincinta.Daidai nan Abbansu ya fito ya zauna a table din, ta tura masa flask da plate. Ya bude flask din ya kalli fuskokin yaran sannan ya kalleta yace ‘Wannan ai tuwon jiyane, ba a yi abincin ranar bane?’‘Shine abincin ranar ai, dumamawa aka yi tunda babu abinda yayi.’Nasreen wadda itama take ta juya nata tuwon tace ‘Abba wallahi tuwon ba dadi, ni bana son bakin tuwo gaskiya.’Shi din yana son tuwon alkama don shine ma ya sa aka yi tuwon da daddare, don haka ya zuba malmala guda ya fara ci. Ya sake duban fuskokin yaran, bayan ya hadiye lomar da take bakinsa yace ‘Yanzu ba wani abu da za a iya dafawa yaran nan, Afaf ce kawai take cin tuwon nan.’Ba tare da ta kalleshi ba tace ‘Babu.’Ta cigaba da cin tuwonta kamar bata san da su ba a wajen.Jimawa kadan Nasreen tace ‘Abba ni a hada min cornflakes.Ya dubi Khadeeja yace ‘Akwai cornflakes ko?’Cikin halin ki in kika tace ‘Akwai.’’Da Allah a hada mata ta samu ta ci kafin ayi abincin dare.’Tace ‘To.’Ta ci gaba da cin tuwonta tana bawa Shukra a baki, yayinda ita kuma Nasreen ta tashi ta koma gaban TV. Jimawa kadan Habib ma ya mike, ya dauki kwanonsa da na Nasreen yana cewa ‘Abba nima na sha cornflakes din kawai.’Ya wuce ya kai kwanukan kitchen ya dawo shima ya zauna a gaban TV.Bai dade da tashi ba kuma itama Khadeejan ta gama cin nata tuwon, ta dauke kwanonta ta kai kitchen. Ta fito daga kitchen din ta wuce daki ba tare da ta kallesu ba. Tana shiga ta saka pillow ta kwanta a tsakiyar gadonta, da yake ta gaji sannan kuma ta koshi tana rufe ido bacci ya kwasheta.Bata sani ba ko ta dade da kwanciya ko bata dade ba, kamar a mafarki taji Mustapha yana dan buga kafarta yana cewa ‘Khadeeja, Khadeeja, barci ma kike yi? Kin bar yara da yunwa fa ki zo ki hada musu cornflakes ko ki dafa musu indomie.’Ta dan janye kafarta tana kokarin tashi; kafin aurensu fa baya kiran sunanta sai dai yace ‘yan mata, mekyau ko kuma yace babe. Tayi zaton idan sun yi aure next level zasu shiga a kara mata matsayi amma zata iya cewa tunda ta shigo gidan nan sau daya ya kirawota da babe a daren da suka tare. Yanzu kam yaci duba sai ceto don gatsal yake kiranta Khadeeja……

Back to top button