Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 126 Complete Novel

Father of soldiers

🔥TAKUN ƘARSHE🔥

Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags

Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃

 

Remain few pages 😢

 

*Har weekend zanyi posting,in sha Allah Ranar Lahadi Zan saki Last page Na Abban Sojoji,😢waɗanda ke buƙatar karanta Littafin daga farko zuwa na uku Suyi mun magana ta whatsapp 08103884440*

Godiya ta musamman ga waɗanda suka ƙarfafamun guiwa tun daga farkon Littafin nan har zuwa ƙarshen shi,Saƙon godiyata yana nan tafe 😍

 

 

 

 

gaba ɗaya saida abba ya tara ma’auratan A babban Falon gidan yayi masu nasiha sosai,Ammi ma tayi masu nasiha,abusufyan ma yayi masu,gwaggon katsina dasu Aunty azeema duk saida suka yi masu nasiha,Jikin kowannansu Yayi sanyi,su jahad sunsha kuka sosai,Saboda tafiyar da zasuyi subar Iyayensu da ƴan uwansu,hatta hosana da bata da cikakken hankali sai da tayi kuka,lokacin da ake yi masu nasihar,tun a daren ranar suka fara yin bankwana da ƴan uwansu,kafin asuba su tafi,

Wuraren ƙarfe 12 da dare,Oummansu ta tarasu a ɗakinsu,Bayan sun kammala sallar nafila,kowannansu Na sanye cikin Hijabi,Sunyi kyau kamar larabawa,saboda gyaran da suka sha,fatarsu har sheƙi take yi,hannayensu akwai zanen ƙunshin jan lalle da akayi masu na bikinsu,Sae ƙamshi ke tashi ajikinsu,Suna zaune saman darduma,

“Oumma yanzu shikenan tafiya zamuyi mu barki da daddy dasu abba”?Hosana ce tayi tambayar,
Abu tace”ae tafiya ba mutuwa bace,Idan da rai da lafiya wata rana zaku zo mana,muma kuma zamu zo maku,”tuni idanuwanta sun cicciko tab da kwalla,
Fuskar jahad ɗauke da damuwa tace”Ina zullumin tafiyar nan Oumma,jikina duk yayi sanyi,Zamu tafi wata uwa duniya,inda bamu son kowa ba,bamu da dangi acan,Bamu san ya zasu kar6emu ba,”
“Jahad,ki kwantar da hankalin ki,kidaina zullumi,kuma kidaina cewa baku san kowa ba,Idan har kuna tare da Omar da Rafayet to ku ƙaddara cewa tamkar duka family ɗinku suna atare daku,domin kuwa ina tabbacin cewa zasu baku kyakkyawar kulawa,fiye damu,Kada ku manta su ɗin jininku ne,Ƴan uwanku,Yayyanku kuma mazajenku,baku da wani makusanci daya wuce su aduniyar nan,bazasu ta6a bari rayuwarku ta wulaƙanta ba,ko yatsa wani yace zai ɗaga maku Bazasu ƙyaleshi ba,shiyasa ni bana shakku akansu,na yarda dasu sosai,Kuma ina matuƙar Alfahari dasu a matsayin
Surukaina,Nasan zanyi kewarku sosai,Zan zubda kwalla akan rabuwa daku,Amma inna tuna cewa rabuwa ta zama dole,wata rana ma duniyar zaku bari,ko ku tafi koni na rugaku tafiya,Sai inga wannan bakomai bane,duk mun nisan da zakuyi indai kuna acikin duniyar nan,zamuyi iyayin waya,harma Video Call,kuma zaku dinga zuwa mana,muma kuma zamu zo maku,shi Aure ba inda bai kai mutun……’hawayen da take 6oyewa ne suka soma gangarowa asaman fuskarta,da sauri ta sanya hannu ta sharesu,
A hankali Sehrish ta ɗago da idanuwanta cike tab da kwalla tana kallon fuskar Oummansu,
“Dole sai kunsa haƙuri A rayuwar auranku,kuma kuyi biyayya ga mazajanku matsawar bai sa6a ma Allah ba,duk abunda basa so ku kiyayeshi,duk wani abu da zai faranta masu rai kuyi kokari wurin ganin kunyishi,Sannan ku dage da yin addu’a banda wasa da ibada,duk wani jin daɗin duniyar nan ƙararre ne wata rana,kada ku shagala ku manta daku su waye,wata rayuwa kukayi abaya..,…..”daƙyar abu takai ƙarshen maganarta,duk jikinsu yayi sanyi sosai,duk sun natsu suna sauraronta,gaba ɗaya idanuwansu cike tab da kwalla,
Sosai abu tayi masu nasiha,Ta kuma ƙara tunasarsu dasu game da yin tsafta,gyaran jiki,sarrafa abinci,kusan raba dare su kayi abu na koya masu rayuwar zaman aure,A ƙarshe tace”Allah yayi maku Albarka,Allah Ya baku zaman Lafiya da mazajanku,Ina roƙon Allah yasa Wannan auren da kukayi ya zama silar Shigarku Aljanna,’
Da ƙarfi suka amsa mata da ameen,
“Allah Ya albarkace ku da samun zuri’a ɗayyiba,Allah Ya kare ku daga sharrin maƙiya da mahassada,”
“Ameen Ameen Oumma”
Ganin yadda duk jikinsu yayi sanyi yasa ta soma ƙoƙarin faranta masu rai donsu sakin jikinsu,
“Kunsan wani abu”?girgiza mata kai su kayi alamar a’a,
“Lokacin dana taso rayuwata,danginmu duk sun watse,saboda talauci,kowa takanshi yake yi,babu wani haɗin kai,A wurin haihuwata Mahaifiyata Ta rasu,Mahaifina ya damƙani a hannun kishiyar Babata,Matar nan ta tsane ni,babban baƙin cikinta irin farin jinin da nake dashi,mutane har zuwa sukeyi suna roƙonta akan ta basu ni su raine ni,ganin irin baƙar wahalar da nakesha,Amma matar nan taƙiya,saboda gudun kada in samu rayuwar jin daɗi inyi arziƙi,ta tauyemun haƙƙina,Dama ance duk xakaran da Allah ya nufeshi da yin cara,Sai yayita,mutuwa ne kawai banyi a hannun matar nan Ba,nifa ban ta6a tunanin zan kawo wannan lokacin da raina ba, ban kuma ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zata zo irin wannan ba,Hasalima bansan wanene abusufyan ba Shima baisanni ba,ina nijar shikuma yana a nigeria,Kaji wani iko na Allah,babu wanda yasan da wani,ban ta6a tunanin ma zanyi aure ba balle har in haifi ya’ya har ƴan uku,Sai gashi ƙaddara takai mahaifina aiki gidansu,Ni kuma silar mahaifina dayazo ya ɗaukeni sakamakon ganin irin wahalar da kishiyar babata take bani ya dawo dani nigeria,A gidansu Abusfyan,ƙaddara ta haɗani dashi,Har mukayi aure na haifeku,Yanzu gashi har kun girma kuma kunyi aure Wata rana kuma zaku haifi ya’ya,Lamarin ubangiji da girma yake,Allahu akhbar…….”fuskarta ɗauke da murmushi takai ƙarshen maganar,
Dariya hosana tayi”Oumma,Nima Allah yasa in haifi ƴan uku,”
Buge mata baki Jahad tayi”ko kunya babu,agaban oumma kike cewa zaki haihu,”dariya abu tayi,Sehrish kuwa murmushi tasaki,
Ɗaure fuska Hosana tayi tana jifar Jahad da harara,tare da jan dogon tsoki,”
“Yakamata ku kwanta kuyi bacci,har kusan ƙarfe ɗaya da wani abu,gashi gobe tunda asuba zaku tafi,”
Amsa mata su kayi da toh oumma,

Asaman gado, oumma dasu jahad suka kwanta,Cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dasu,banda Sehrish sai da tabari sunyi bacci tukunna ta fito daga ɗakin,Jikinta sanye da sleeping dress,Riga da wando Orange,ta yafa mayafi akanta,jikinta sai ƙamshi yake yi,yunwa ce ta fito da ita,tunda tasha ruwa bata ci komai ba,saboda zullimun tafiyar da zasuyi,dayake Yau da azumi ta tashi,bata nufi kitchen kaitsaye ba,Babban falon gidan ta shiga babu kowa,shiru kake ji,Kowa yana can manne da matarshi aɗaki,A hankali take bin ko’ina na gidan da kallo,Tabbas zatayi kewarshi sosai,Bazata ta6a mantawa da rana ta farko data fara zuwa gidan aiki a matsayin namiji,In ta tuna wasu abubuwan sai tayi murmushi,wasu kuma tayi dariya,Yayin da wani abun idan ta tunashi sai ta fashe da kuka

Tajima acikin Babban falon tana zagaye shi,kafin ta juya ta nufi kitchen don ta zuba abincin da zataci,Koda ta shiga kitchen ɗin,ta soma neman abinci,bata samu komai ba duk an cinye abincin gidan,Kamar ta ɗaura hannu akai tayi ihu saboda takaici,ko kaɗan bazata Iya jure yunwa ba,rabonta da abinci tunda asuba da tayi sahur,tunanin ɗaura girki ta soma yi,batare da 6ata Lokaci ba,ta haɗa chicken pepper soup,bayan ta kammala ta ɗebo dankalin turawa acikin store ta fere shi,

A hankali yake saukowa downstairs,Idanuwanshi da alamun bacci acikinsu,daga shi sai Short ajikinshi gajeran wando,Babu riga,daga gani atakure yake,Ya kasa bacci saboda rashinta a kusa dashi,Yayi jiran harya gaji batazo ba kamar yadda ta saba zuwa suna kwana a bedroom ɗinshi,Wannan dalilin ne yasa shi fitowa domin nemanta,yana ƙarasa saukowa babban falon kaitsaye ya miƙi hanya zai nufi corridor ɗin ɗakinsu,ba zato ba tsammani idanuwanshi suka hango mashi ita cikin kitchen ta juya baya agaban Gass Cooker,Abun ya ɗaure mashi kai,Kamar wata Aljanna,duk irin tsoranta amma sai gata a kitchen kusan ƙarfe 2 na dare tana girki,

Walking slowly ya nufi kitchen ɗin,A bakin entry ɗin ya tsaya,Yana binta da kallo,kasa kunne yayi yana sauraran waqar da take raira,
“Nagode ma Allah dana cika buri,Na zama matar rafayet,Yanzu babu mai mun gorii,Sgr gashi gabana,umm umm matsayin miji mallaki na…..”
Murmushin gefen fuska ya saki har dimple ɗinshi ya lotsa,cikin sanɗa  yake tafiya har ya isa bayanta,tunani ya shiga yi taya zai ruƙota batare data tsorata ba,don yasan halinta,yanzu ko magana yace zaiyi mata Zata iya firgita,gashi tana agaban gass cooker,kada asamu matsala,
Motsi ya soma yi da lips ɗinsa yana ƙoƙarin yin magana,yaji tace”Ina nake jin ƙamshin turaren ya rafayet,kodai hancina ne…..’bata kai ƙarshen maganar ba,a hankali Sgr,ya zagayo da hannunshi ya ruƙe hannunta dake ruke da turner ɗin da take juya chips ɗin data ɗaura,
Har ta wage baki zata fasa ƙara,Yayi saurin cewa”its me,”Ajiyar zuciya ta shiga saukewa,ba ƙaramin tsorata tayi ba,kwantar da kanshi yayi asaman kafadarta,
“I ave been waiting for u,kin manta da mijinki ko”
“Am Sorry ya rafayet,kana araina”

“Reesh..u know I can’t sleep without you on my chest,saboda rashinki a kusa dani na kasa runtsawa,”yakai ƙarshen maganar tare da manna mata kiss asaman neck ɗinta,slowly ya xagayo da hannunshi saman stomach ɗinta”da kanki kike girki a irin wannan lokacin”?
“Yunwa nake ji,nayi azumi yau,shiyasa na ƙaurace maka,kuma tunda nasha ruwa,bansamu naci komai ba,”
“You did fast without my permission”?yayi tambayar tare da juyo da ita,Yadda zai samu damar ganin fuskarta,’
A hankali take bin jikinshi da kallo,har izuwa saman fuskarshi,kullum ƙara kyau yake yi,ga cikakkiyar sura,hada ƙarin kwanciyar hankalin daya samu,lips ɗinsa sunyi pink,sae faman lumshe idanuwanshi yake yi,saboda baccin da yake ji,kamar yadda take kallonshi haka shima yake kallonta,
Sunnar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannnunta,
“Am sorry,nayi laifi ban sanar dakai ba,”
“Azumin menene kikayi”?
“Nayi shine saboda kai,wannan alƙwarine na ɗaukarwa kaine,duk ranar da Allah ya mallakamin kai amatsayin mijina,A ranar zanyi fasting domin nuna godiyata ga Allah,daya bani the most greatest gift,bansamu nayi azumin ba,saboda yanayin da muka shiga,Sai yau Allah ya bani ikon yi,”
Tunda ta soma magana,ya kafe ta ido yana kallonta,kamar ya haɗiyeta saboda tsananin son da yake yi mata,shi kanshi shaidane akan irin son da take yi mashi,
“Da ace kin sanar dani,da munyi azumin atare,”
murmushi ta ɗan saki,batare da tace komai ba,sam ta manta da chips ɗin da take frying
“Ɗaya daga cikin nasarorin da nasamu arayuwata,hada mallakarki da nayi,wannan babbar nasara ce agare ni,Am so proud of u,I love u……’yana kai ƙarshen maganarshi,ya janyota jikinshi sosai yayi tighting ɗinta,kafin a hankali ya ɗago da kanta,zubawa lips ɗinta ido yayi,ba ƙaramin missing ɗinsu yayi ba,Tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana Yayi saurin haɗa bakinsu cikin na juna,zura tongue ɗinshi yayi acikin bakinta,Sosai ya shiga bata hot kissing,lokaci guda suka kacame ma juna,sosai sehrish ta shiga mayar mashi da martani,sun zunduma tsulundum,Gaba ɗaya hannayenta na acikin doguwar sumar kanshi,tamkar tana yi mashi susa,duk ta hargitsa mashi gashin da hannunta,

Tun hannunshi na a bayanta har yakai ga zagayo dasu cikin rigarta,ya soma shafa shafaffen cikinta har izuwa saman ƙirjinta,sam babu bra ajikinta,gashi abun tubarkalla,sun cika tamkar zasu fashe,tunda Sgr ya damƙesu,laushinsu ya fisgeshi,yabi ya susuce ya ruɗe,sosai ya shiga murzasu da hannunshi,sun manne ma Juna,gudun kada ta fara gajiya da tsayuwar yasa ya ɗauketa tamkar yar baby,asaman jikinshi,ƙafafuwanta na zagaye dashi,yayin da kanta ke asaman kafaɗarshi,Mayafin data yafa a kanta tuni ya jima da zamewa ƙasa,sumar kanta duk ta rufe fuskarta,gaba ɗaya ya sabule rigar jikinta,ya fito da boobs ɗinta,ya kafa bakinsa kamar jinjiri haka ya shiga sucking ɗinsu,duk ya zautar da ƴar mutane,gaba daya kalasa ta rufeta,ta lafe mashi,tana jin duk wani motsinshi ajikinta,

Chips ɗin da sehrish ta ɗaura,tuni ya jima da ƙonewa, ƙauri ya fara karaɗe kitchen ɗin,duk basu sani ba,Ana ta shan Love,

Gaba ɗaya sun fita cikin hayyacinsu,ko gajiya da tsayuwar baiyi ba yana ta biyan buƙatarshi,Kamar ance ta ɗago da kanta daga saman kafaɗarshi,Kwatsam Tayi arba da Abbansu junaid Ya nufo kitchen ɗin,Ta window ta hango Gifcinshi yana sanye cikin Jallabiya,A firgice Ta furta”Innallahi Ya rafayet Abba,’
Ya kurmance baijin abunda take cewa,kiciniyar ƙwace kanta ta soma yi don ta sauko daga jikinshi,Wani irin ruƙo yayi mata bana wasa ba,Bugun bayanshi tadinga yi tana faɗin”Yaya Rafayet ka sake ni,Ga abba nan yana zuwa,”
Sgr bai tashi ankara ba,Sai da sehrish ta gartsa mashi cizo asaman shoulder ɗinshi,Baiji zafin cizon ba,Amma Yaji koken da take yi,A firgice ya sauketa,da gudun gaske ta nufi ƙarƙashin dining table ɗin dake a cikin kitchen ɗin,ta 6oye ƙarƙashin shi tana faman sauke ajiyar zuciya,

A hanzarce Sgr ya kashe gass cooker ɗin,ƙiris ya rage Wuta ta kama, frying fan ɗin yayi baƙiƙƙirin Wani irin baƙin hayaki ke fita daga cikinshi,gaba ɗaya yabi ya ruɗe,hannu yasa yana sosa sumar kanshi,yana jiyo takun takalmin abbansu yana shugowa Cikin kitchen ɗin,
Cike da mamaki abba ya tsaya yana kallon bayanshi,farat ɗaya ya gane cewa Sgr ne,duk da ya juya bayanshi,Abun ya ɗaure mashi kai,Sgr a kitchen,
Gyaran murya ya ɗanyi mashi don ya juyo,Shiru Sgr yayi mashi,don a halin da yake ciki yanzu farat ɗaya abbansu ya kalleshi sai ya gane a wani yanayi yake ciki,
“Rafayet me kake yi a kitchen”?
Daƙyar Sgr ya iya buɗe baki yace”Dad…am cooking….’
“Girki kuma?kai da kanka?sai kace mace?dama kasan hanyar kitchen”?yayi tambayar cike da tuhuma,
Shiru Sgr yayi don baida amsar da zai bashi,
“Idan yunwa kake ji meyasa ba zaka kayi magana a girka maka ba”?
“banaso na tashi kowa ne,”ya bashi amsa a ƙule,Still bai juya ya kalli abban nasu ba,
“Amma nayi mamaki gaskiya,Wai dama ka iya girki”?ae nayi tunanin Ci kaɗai ka iya,”
Yatsina fuska sgr yayi,tamkar ya fashe da kuka,sam baiso zuwan abbansu ba,
Cike da zolaya abba ya kuma cewa”Wai tsayuwar me kake yi ne,Ka juyo mana muyi magana,”
“Ina ƙarasa Soyawa ne,”
Jinjina kai abba yayi”Masha Allah, Ashe ba iya ruƙe bindiga kaɗai ka iya ba,hada girki,bari na zauna na jiraka,don wlh nima yunwarce ta koroni,yayi maganar yana shafa cikinshi,
Da sauri sgr yace”Why not ka koma ɗaki zanzo na kawo maka dakaina,in na kammala “girgiza kai abba yayi”A’a,nafiso muci atare cikin kitchen ɗin nan,Yau zan ɗanɗani girkin General ɗin sojoji,”takaici duk ya cika Sgr,baisan ya zaiyi da abbansu ba,kamar yasan me suke yi acikin kitchen ɗin yaƙi tafiya,A ƙarshe ma wuri ya samu ɗaya daga cikin dining chairs ɗin da sehrish ta 6oye a ƙarƙashin Table ɗinsu,Nan ya zauna,yana jiran Sgr Ya kammala masu girkin”‘sam abbansu bai Lura da mayafin sehrish dake yashe kasa ba,ga kuma slippers ɗinta dake a ƙasan ƙafafun Sgr,bai kuma Lura da kaskon da Sgr ya sauke ba,
“Rafayet wai ƙaurin me nake ji ne”?
“Albasa ce ta ƙone,”
Yatsina fuska abba yayi”ƙaurin ba daɗin ji,dan Allah karka bari abincin ya ƙone,”
Amsa mashi yayi da “toh”

Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin ƙafafun abba masu sanye da slippers,sai faman karkada kafafun yake yi,duk fargaba ta kamata,ta ƙanƙame jikinta a ƙarƙashin table ɗin,tuni zufa ta wanke fuskarta,har rage numfashinta tayi duk don kada abba ya ganta

Daƙyar Sgr ya samu ya matsa,Ya ɗauko plate mai faɗi Ya zuba masu chicken papper soup ɗin da sehrish ta kammala,duk baiji daɗi ba,baiwar Allah tasha wahalar Girka abunta don tana jin yunwa,Ga abba yazo zai cinye mata kazarta,

Duk wani motsinshi akan idon abbansu ya kafe shi da ido yana kallonshi,dama saida ranshi ya bashi cewa Shi yake kallo,a sukane ya juyo hannunshi ruƙe da plate ɗin,haɗa ido su kayi da abbansu da sauri Sgr ya kawar da idanuwanshi,
Wani irin kallon ƙurulla abbansu keyi mashi,Duk yabi ya tsargu,murmushi yagani akan fuskar abbansu me haɗe da dariya,ɗaure fuska Sgr yayi tare da samun wuri ya zauna,Suna fuskantar juna shi da abban nasu,Sauke plate ɗin yayi asaman table ɗin ya turama abbansu”Gashi nan,bismillah,”
“Kai bazaka Ci ba”
Girgiza kai Sgr yayi”Na ƙoshi”
ɗaure mashi fuska abba yayi”In har bazaka ci ba,nima na ƙoshi,tun ɗazu na lura dakai sai wani shan mur kakeyi saboda kawai nace ina jin yunwa,gobe fa zaku tafi ko irin missing ɗina baka yi,”ya ƙarasa maganar yana harararshi,
Jin haka yasa Sgr ya saki fuskarshi don ya faranta mashi
“Am Sorry dad..let’s eat together,’yakai ƙarshen maganar tare da zura hannunshi ya ɗauki cinyar kazar yakai bakinshi yana tauna,abba ma ya sanya hannu suka soma Ci atare,sai faman lashe baki yake yi”Wai dagaske kai kayi girkin nan?
Jinjina kai Sgr yayi alamar Eh,
Abun ya ɗaure mashi kai”Danasan haka ka iya girki,da tun farko ban ajiye azmee a gidan nan ba…..”
Sakin baki Sgr yayi sototo yana kallonshi,shikuwa sai jin daɗi yake yi Sgr ya iya girki,.
sehrish dake la6e ƙarkashin table ɗin,ƙamshi duk ya cikata,Kamar ta fashe da kuka,saboda yunwar da take ji,ta kwalla fa rai sosai,”
“Kasan wani abu”?girgiza kai sgr yayi alamar a’a
Abba yaci gaba da cewa”ɗanɗanon girginka Sak irin na azmee ya akai haka”?
Yatsina fuska Sgr yayi,kafin yace”May be dan inacin abincinta ne,yasa taste ɗin yazo ɗaya dana ta,”
Murmushi abba yasaki”U are right…ka manta baka kawo mana abunsha ba?ƙishi nake ji,’

Har ya yunƙura zai miƙe,Abba yayi saurin dakatar dashi”koma ka zauna,Kasha wahalar yin girki nasan duk ka gaji,bari naje na ɗauko mana,”

Ajiyar zuciya Sgr ya sauke tare da komawa saman kujerar ya zauna,Abba ya mike yabar wurin,Kafin ya dawo Sgr yayi saurin ɗebo naman Ya zurama Sehrish ta kasan teburin,har saida ta tsorata ganin hannunshi,da sauri ta sanya hannu ta kar6a,ta shiga turawa abakinta tana ci,ƙasa ƙasa da murya ya furta”Am really sorry duk laifina ne,da banzo ba da duk hakan bata faruwa ba,”
Murmushi ta saki batare da tace mashi komai ba,sake ɗebowa yayi ahannunshi ya miƙa mata,ta sanya hannu ta kar6a,ta tura abaki ta lamushe,cikin sanyin murya tace”Ƙishi nake ji,kuma ina jin bacci,”_
Kafin ya bata amsa sai ga abba ya dawo hannayenshi rungume da bottle waters masu Sanyi,hada na Lemu ya haɗo masu,

Ajiyesu yayi asaman table ɗin,Ya zauna idonshi akan plate ɗin,A ruɗe yace”kai!ya akai naga an kwashe?duk kai ka cinyesu”?
Ɗaga mashi kai Sgr yayi alamar eh,Sam abba mai yarda da maganarshi ba,saboda tun da suka fara ci ko cinya ɗaya bai iya ci ba,Amma daga zuwa ɗauko lemu da ruwa harya Cinye saura kaɗan kazar ta rage,

Tura mashi lemun yayi agabanshi’Take it,”
“Ruwa nake buƙata”ya ambaci hakan tare da kai hannu ya ɗauki robar ruwa mai sanyi,mai maimakon yasha sai ya tsaya yana jiran abbansu ya fara kafa baki zai sha nashi,Shi kuma sai yayi dabarar mika mata ruwan,
Lemu abba ya ɗauka ya buɗe shi ya kwafa abakinshi yana sha,A hanzarce Sgr ya zura hannunshi ƙarƙashin table ɗin ya miƙa mata robar ruwa,ta sanya hannu biyu ta kar6a,buɗe murfin tayi kafin ta kwafa a baki tana sha,

Bayan abba ya kammala shan lemun ya ajiye robar ruwa,
Da buɗar bakinsa sai cewa yayi”kai Ina ɗayar robar take ne?Guda huɗu ne na kawo mana,”hankalin Sgr ba ƙaramin tashi yayi ba,
“Daddy uku ne fa ka kawo,”girgiza kai Abba yayi a’a,guda huɗu ne Ta lemu biyu ta ruwa biyu,Kodai ta faɗa ƙarƙashin table ne….’yakai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin leƙawa ƙarƙashin teburin,A Ruɗe Sgr yace”karka kuskura ka leƙa……”tashin hankali sam baisan Ya furta hakan ba,tsabar ruɗi ne

A ruɗe abba ya ɗago yana kallonshi”Rafayet ni kake ce ma kar in kuskura in leƙa?Saboda me”?
Muryarshi na kerma yace”bansan nace haka ba,”
“Kodai kayi ajiya a ƙarƙashin taburinne”?
Da sauri yace”A’a,
“To meyasa kace kada na leƙa”?
Shiru Sgr yayi batare daya ce komai ba,”
Sehrish dake ƙarƙashin table ɗin duk ta furgita,jikinta sai kerma yake yi,batasan ya zatayi ba idan abba ya ganta,

“Shikenan,tunda baka so na leƙa,Amma ɗayar robar fa?ina ka kaita?
Wani irin wahalallan yawu ya haɗiya,
“Abba baka jin bacci ne?dare fa yayi sosai”
“Na kasa yin bacci ne saboda tafiyar da zakuyi gobe,zanyi missing ɗinku sosai,”.
Murmushin yaƙe sgr yayi”but u ave to sleep,gobe zamu airport ba zaka rakamu ba”?
“Kada ka damu da wannan,rashin baccina bazai hana in rakaku airport ba,”
Jiki asanyaye Sgr yace”shikenan ae,”
Dariya ce ƙumshe abakin abbansu,kar yake kallonshi don tunda ya shigo kitchen ɗin ya gane cewa bashi kaɗai bane aciki,zuba mashi ido kawai yayi don yaga iya gudun ruwanshi,

Wata dabara ce ta faɗo mashi,A hankali Ya sanya hannu tare da Cire murfin robar ruwan Daya kammala sha,Sgr Duk bai Lura ba,Janye hannunshi yayi zuwa ƙasan table ɗin yasan tabbas indai macace a ƙarkashin table ɗin da zarar ya wurga murfin zata fasa ƙara,tayi tunanin Ko wani mugun abunne ya faɗo,

Daddagewa Abba yayi da ƙarfi ya wurga murfin Robar ruwan kaitsaye ya faɗa saman ƙafafun sehrish,Aikuwa A gigice ta fasa ƙara tana faɗin”Wayyo Allahna Ya rafayet 6era 6era….”
Tuntsirewa Abba yayi da dariya hada dafe ciki,Sgr dake zaune tamkar an dasa mashi aya,Sam ya kasa motsi,wata irin kunyace ta rufe shi,ya kasa ɗagowa su haɗa ido da abbansu,sosai abba keyin dariyar hada hawaye akan fuskarshi,Miƙewa tsaye yayi daga saman gujerar,Ya nufi hanyar fita daga kitchen ɗin yana tafiya yana dariya har yakai bakin ƙopar fita,ya ɗan dakata da yin tafiyar ya juyo ya kalli Sgr dake zaune Ya sanƙare duk yabi ya dabarbace,
Gyaran murya abba yayi mashi Ya ɗago suka haɗa ido dashi,
“Ɗan rainin wayau,da kace bakaso”?
Ƙayataccen murmushin gefen fuska Sgr ya saki har dimple dinsa ya lotsa
“Ashe kana nan ƙumshe da ƴar mutane,A kunnan abusufyan saina faɗa masa”yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar kitchen ɗin yana dariya tare da girgiza kai,”

Ajiyar zuciya Sgr ya sauke,A hankali ya ambaci Sunanta”Reesh….”cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi”Na’am ya rafayet,”saukowa yayi daga saman kujerar Ya zuƙunno kasan table ɗin,cikin sanyin murya ya soma magana”ya tsorata ki ko?”?
Jinjina mashi kai tayi,fuskarta sharkaf da hawaye,sai faman shessheƙar kuka takeyi,ruƙo hannunta yayi tare da fito da ita daga karkashin table ɗin,Hugging ɗinta yayi ajikin shi,Yana shafa sumar kanta”Am really sorry,if u are still hungry i can cook for u…”.
“A’a na ƙoshi,bacci nake ji,”
ɗaukarta yayi asaman kafaɗarshi ya nufi hanyar fita daga kitchen ɗin,upstairs Ya wuce da ita part ɗinshi,ko’ina a gyare tsaf,A bedroom ɗinshi Ya sauke ta,
“Zan shiga toilet,”tayi maganar tare da juyawa ta nufi toilet ɗin,bin bayanta yayi”lemme help u….’bata yi mashi musu ba,atare suka shiga toilet ɗin,bansamu damar leƙawa ciki ba, balle in gano maku me ke wakana,saboda sun rufe ƙopar,

After some minutes Sgr ya fito ɗauke da sehrish,irin ɗaukar da akeyiwa Jariri,su duka biyun Suna ɗaure da towel a qugunsu,launi ɗaya farare,

Kaitsaye ya sauketa Asaman gadonshi,Yana ƙoƙarin miƙewa ta sanya hannu ta damƙi towel ɗin jikinshi gaba ɗaya ta warwareshi,kamar jira yake yi dama bai gamsuba abba ya katseshi,komawa yayi samanta,yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinshi,Sam basu gajiya da juna, kamar zasu kashe kansu,sai da suka raba dare,kafin Allah ya kawo bacci yayi awon gaba dasu,ƙankame da juna,sai da ana kiran sallar asuba,ya tashi sehrish ya ɗauko mata kayan baccinta da kanshi ya zura matasu ajikinta,cikin sanɗa ta fito daga part ɗinshi ta sauko downstairs,sai da tafara zuwa kitchen ta ɗauki mayafinta tukunna ta wuce ɗakinsu,

Bayan Kammaluwar Sallar asuba,matafiya suka shirya tsaf,domin tafiya Airport,Dukansu matan suna sanye cikin jallabiya baƙa,Sun laga gyale akansu,Sgr Da Omar suna sanye cikin Shadda,Junaid kuma yana sanye cikin suit farare,

Gaba ɗaya mutanan gidan Sun hallara a babban Falon gidan, lokacin da kowa ya kammala fitowa,Suka ɗunguma izuwa Wajen da motocinsu suke,kusan dukansu zasu yi masu rakiya,Amma banda Amaren Gidam,tun anan Sukayi bankwana dasu,Amrish tasha kuka sosai,haka Amal ma,

A motar dr harris,gwaggon katsina da abu suka shiga,tare da saude wadda ke zaune A gefenshi
Abba kuma tare da mommy suka shiga motar Fawan,

osman da adam a motar kanal Yusif suka zauna,

Najeeb kuma a motarshi Talal Da junaid suka shiga,

Sehrish da Jahad da hosana,Suna zaune a motar abusufyan Dakanshi zaiyi driving ɗin ya’yanshi,

Hajiya azeema tana acikin motar su twins,Jahan ne ke a mazaunin driver Ayaan na a gefenshi,

Akwai motocin Security dake gaba da bayan motocinsu,
Sgr yana acikin motarshi,motarsu Marshal Da major tana a bayan tashi,

Slowly motocin suke tafiya ajere har suka fito daga cikin babban gate ɗin gidan,koda su Jahad da sehrish suka ga An fita daga gate ɗin gidan sai suka fashe da kuka atare,Abusufyan sai lallashinsu yake yi,Shi kanshi daurewa kawai yake yi,idanuwanshi cike suke tab da kwalla,

Lokacin da suka ƙaraso Airport ɗin at the same time su kayi parking ɗinsu,A tsanake duk suka fito daga cikin motocin,idanuwan kowannansu Yana akan Katafaren Privet jet ɗin da aka tanadar masu,wanda ya kasance Mallakin Rafayet ne,jigunannan gaske,Mai ɗauke da Sunanshi Ajiki da manyan haruffa akayi rubutun SGR

Tunkafin su iso Airport din junaid keta kukan rabuwa da abbansu da ƴan uwanshi,Kowa jikinshi yayi sanyi,

Rungumeshi abba yayi sosai ajikinshi yana shafa sumar kanshi,
“Junaid so kake nima inyi kukan ko”?
Cikin shessheƙar yace”Abba bansan na tafi nabarka,”
“Junaid aduk inda kake a faɗin duniyar nan,inaso ka sanya aranka cewa Muna atare da juna,zan dinga zuwa akai akai ina ganinka,”daƙyar abba ya samu ya lallashe shi,bayan ya saki abbansu Ya rungume Fawan yana kuka,kowa yayi tsaye cirko cirko gwanin ban tausayi,
Bubbuga bayanshi fawan yayi”be a man mana,Kada ka bani kunya,dan Allah kadaina kukan nan,”
“Ya fawan,tafiya fa zamuyi,”
“Tafiya ae ba mutuwa bace junaid,just calm down ur mind,Da zarar babynka ta haifu zan wanko ƙafa inzo suna”cikin raɗa yayi mashi maganar a kunnanshi,har sai da junaid yayi dariya,bayan ya rabu da fawan ya rungumesu twins atare yana raira masu kuka,
“I love u so much Ya jahan da Ya ayaan,Zanyi missing ɗinku sosai,”
Atare suka haɗa baki wurin cewa”We love u so much Our shagwa6a boy,”
Bayan yabar wurinsu Ya nufi kanal Yusouf yayi hugging dinshi”yaya yusif yanzu shikenan…..’
“Junaid banaso kana zubar da hawayenka,inda rai da lafiya wata rana zamu zo,kaima kuma zakazo,”
“Amma ae bazan dinga ganinku kullum ba,”ashagwa6e ya ƙarasa maganar,ba wanda junaid ya bari,ɗaya baya ɗaya sai da ya rungume kowa hadasu uncle da hajiya azeema dasu Osman da Najeeb,

Bayan ya kammala nashi,Su Sehrish suka Soma bin kowa suna yi mashi sallama,Gwaggon katsian hada kukanta,Za’a tafi da ƴa’ƴan abusufyan ɗinta,Sosai ta rungumesu ajikinta,Suna kuka tana kuka,babu mai lallashin wani,daga wurin gwaggo wurin hajiya azeema suka wuce,Ta haɗasu duka ta rungumesu,tana lallashinshu,daga wurinta suka nufi wurin Mommy,Itama ta rungumesu ajikinta,daga wurin mommy suka nufi wurin saude ta rungumesu,Sai da suka gama da kowa tukunna suka nufi Oummansu,ta haɗasu duka ta rungumesu,hawaye jaga jaga akan fuskokinsu,bayan sun gama da matan suka nufi wurin Daddynsu da abbansu,Kowa ya sanya masu albarka,ɗaya bayan ɗaya suka bi mazan suna yi masu bankwana,a lokacin Junaid yana manne da oummansu,ta rungumeshi sosai,kamar zai koma cikin cikinta,

Sai daga bisani Omar da Sgr suka soma bin kowannansu suna yi mashi bankwana,Lokacin da suka zo wurin abba Ya shafa sumar kan kowannansu kafin yace”Omar Rafayet”ya ambaci sunansu,Suka amsa mashi,
Kafin yaci gaba da cewa”A matsayina na mahaifinku babu abunda banyi maku ba,duk wani nauyi naku dake akaina na sauke shi,Saura ku ya rage naku,Ga Amanar ƴan uwanku nan,Ku kula da rayuwarsu,saboda ƙaunar dake a tsakaninku dasu yasa zasu bar kowa nasu,iyayensu danginsu,zasuyi rayuwa daku a inda basu da kowa sai Allah daku ɗin nan,Ku ruƙe amana,kada ku bari koda kwallarsu ce ta zuba kasa,Ku share masu hawayansu,in suna da damuwa kuyi ƙoƙari wurin faranta masu,da zarar kun bar ƙasar nan basu da wani makusanci daya wuce ku ɗin nan,Kune a matsayin Iyayensu, kuma danginsu……..”sosai amma yayi masu nasiha,duk ya kashe masu jikinsu,

Lokacin da suka je wurin abusufyan,Ya kirasu Su jahad suka jera dasu,ya kuma kira junaid shima Yazo,Ruƙo hannun junaid yayi idanuwanshi cike tab da kwalla ya ruƙo hannun Jahad ya haɗasu wuri guda,Muryarshi na kerma yace”junaid ga amanar Jahad nan na baka,”kallon juna Junaid da jahad su kayi,idanuwan kowannansu cike tab da ƙwalla
“Na yarda dakai sosai,Nasan Zaka ruƙe mun amanarta,”
Jinjina kai junaid yayi”in sha Allah uncle,zan ruƙe maka ita amana,bazan ta6a bari tayi kukan rashinku atare da ita ba,”
Kowa dake a wurin saida ya saki murmushi,Jin abunda junaid yace,Yayi magana ta hankali,

Sakin hannunsu Abusufyan yayi,ya kuma ruƙo hannun Omar Ya ruƙo hannun hosana dake ta kuka ya haɗasu wuri guda,
“Omar Na yarda dakai sosai,na yaba da kyawun halayanka,Ga amanar ƴata nan,na baka,”
Tuni idanuwan Omar suka ciko tab da kwalla,daƙyar ya iya buɗe baki yace”In sha Allah Uncle,Zan maye gurbinku a wurinta,Zan bata kulawa fiye da yarda zan kula dakaina,”

Murmushi abusufyan yayi bayan ya saki hannun Omar ya ruƙo hannun Sgr,tare dana Sehrish wadda ke ta faman shessheƙar kuka ya haɗa hannayensu cikin na juna,Kallon Sgr yayi yayin da shima Idanuwanshi na akan fuskar Uncle ɗin
Cikin Zolaya abusufyan yace”Surukina nakaina”murmushin gefen fuska sgr ya ɗan saki,
Mayar da idanuwanshi yayi kan Sherish”My daughter,”cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi”Na..na…am daddy..”

“Rafayet Bana kokwanto akanka,Na yarda dakai kuma na yarda da irin ƙaunar da kake yi mata,Ga amanar Sehrish nan na damƙa maka,”

In sha Allah Uncle,i will take care of her,bazan ta6a bari tayi maraici atare dani ba”
Murmushi abusufyan ya saki tare da cewa”Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku,”sosai yayi masu addu’a,Kafin daga bisani su kayi Sallama da kowa,Omar na ruƙe na hannun Hosana suka nufi stairs ɗin jirgin,Junaid yana abayansu hannunshi ruƙe dana Jahad,Sgr na ruƙe da hannun Sehrish,a haka suka hau matattakalar jirgin, sai da suka kusa shiga ciki,Suka juyo su dukansu suna kallon Iyayensu da ƴan uwansu,Atare suka ɗaga hannu sunayi masu bye bye,

Suma su Abba suka Ɗaga hannuwansu suna yi masu bankwana,da gudu abu ta shige cikin motar abusufyan tana kuka,komawa su kayi cikin motocinsu,A jere suka bar Airport ɗin,Tun suna akan titin komawa gidan,Jirginsu Sgr Ya gifta ta Saman iska,Suna jin ƙararshi,🛫😭

Bayan sun koma gidan babu wanda ya iya cin abinci acikinsu,tamkar anyi mutuwa,gidan duk babu daɗi,Babu Junaid babu Ya Omar babu Babban Yaya,Babu Sehrish babu hosana babu Jahad,Kewarsu duk ta kama ƴan gidan,oummansu har maganin ciwon kai tasha Saboda kukan da tayi,

Los Angeles

California🛬

💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫

Back to top button