Fentin Zina Page 18 Hausa Novel
*****Wayar zulaihat tayi amfani dashi ta kira lambar sa har sai da tayi kira uku kafin ya dauka lokacin kiran na dap da tsinkewa.Hello waye?.Abunda ya fada kena.Dan Allah Kada ka kashe mun waya ba rokon ka zanyi ka cigaba da soyayya dani ba muhimmin maganace nike so mu tattauna.Ameena kenan ina sauraren ki yi sauri ki fadamun bani da lokaci.Hawayene suka zubo mata sakamakon abunda ya fada din, kenan ta tabbata ya more ta ya watsar, saurin kawar da tunanin tayi don bashine a gabanta yanzu ba.Tace ina so in sanar dakai ina dauke da ciki kuma naka yanzu nayi gwaji kuma na tabbatar, shiyasa na kiraka musan abunyi tun kafin ‘yan gidan mu su sani.Ke dalla dakata mun! Ya fada da fusataccen muryar shi, tun wuri ki nemo uban cikin ki bani Ahmad din ba, in banda ma king raina mun wayo yaushe za’a ce daga yi daya har ciki ya shiga ai tunda kika iya bani kanki nasan zaki bawa masu yawa ma tunda baki da kamun kai, ballagaza ce ke.Kuka Ameena ta fashe dashi sosai zulaihat na tayata don duk itama tana jin abunda yake cewa.Tace Ahmad ka dubi girman ubangiji ka saurare ni kai kanka ka sani cewar banida wata mummunar alaka da wani kaine ka keta haddina kai ka,,,,,,,, ta kasa karasawa saboda kukan daya ci karfinta.Kashe wayar yayi yana jan tsaki.Ba karamin rudu Ameena ta shiga ba zulaihat tana lallashin ta karshe dole zulaihat din ta yarda akan zasu je asibiti da ita ameenan a cire cikin kafin kowa ya sani.Har gida zulaihat din ta rakota saida ta shiga ta gaida inna kana ta wuce ita kuma Ameena ta shige daki ta kwanta ta lula duniyar tunani.Kamar yadda suka tsara kuwa asibitin kudi sukaje dake dan nesa dasu sosai gudun su hadu da idon sani.Saida layi yazo kansu kafin suka shiga office din likitar.Farar macece mai dan shekaru kimanin hamsin da doriya, fara ce kyakkyawar ‘yar gayu idanunta sanye da gilashi.Da fara’a ta dubesu domin haka dabi’ar ta take akwai faram faram da mutane musamman patients dinta tana basu mahimmanci sosai.Waye ba lafiya a cikin ku.Zulaihat ce ta nuna Ameena tace wannan na rako.Ta jiya ta dubi Ameena tace ina jin ki, meke damunki?Dan muskutawa tayi tace zazzafar zazzabine sai ciwon kai da kasala kuma ina dan jin jiri kadan.Jinjina kai likitar tayi wacce ake kira da AMINA ABDULQADIR tace yaushe rabon da kiga al’adar ki?Wata daya daya wuce, Ameena ta bata amsa cikin murya mai matukar sanyi gabanta na faduwa.Ok zan rubuta miki test sai kije lab kiyi ki kawo sakamakon, tayi wasu ‘yan rubuce rubucen su na likitoci ta mika mata takardar tace kuje kuyi sai ku kawo ku hanzarta domin na kusa zuwa break.Toh! Suka hada baki wajen fada suka fita, da kudin da Ahmad din ya bata rannan sukayi amfani kasancewar da yawa kudaden.Bayan sunyi suka jira fitowar sakamako inda suka zauna a jerin kujerun da aka tanada a gurin, Ameena tace cikin raunin murya.Wallahi zulaihat gabana faduwa yakeyi.Babu abunda zai faru insha Allah zamu samu nasara ki kwantar da hankalinki.Yaya zakice in kwantar da hankalina abunda kika san bazai taba yiwuwa bane, shikenan tawa ta kare muddin cikin nan bai fitaba wallahi na tabbata inna kasheni zatayi bare baba malam binne ni zaiyi da raina na tabbata na shiga uku.Kinga Ameena ki rufa mana asiri kada ki jawo hankulan mutane kan mu, daidai inda aka kira Ameena ibraheem suka mike suka shiga aka basu result din suka kai office din likita.Tana zaune tana duba wani littafi don ta gama duba marasa lafiyar yau suka turo kofar, ta ajiye littafin tana dubansu tace yauwa karaso.Zama sukayi Ameena ta mika mata pepar.Karba tayi ta duba sai ta dago tana murmushi tace congratulations kina dauke da juna biyu so za’ayi scanning domin musan adadin watannin cikin kafin a dauraki akan magani har zuwa lokacin da zaki fara awo.Zuface ta ko ina ya shiga karyo mata cikin tashin hankali ta soma cewa.Likita na rokeki da girman Allah ki taimaki rayuwata ki cire cikin nan wallahi bana son sa.Da mamaki likitar ta dubeta tace a’a ya Allah ya baki kyauta mai tsada kina kokarin butulce masa ta hanyar kin karba beside ma bama zubar da ciki a asibitinnan sai bisa ka’ida ta lafiya da shari’ah and ina mijin ki don nasan shi bazai yadda da wannan shawarar taki ba.Dukawa Ameena tayi akan gwiwowinta ta hade hannayenta biyu tana kuka tace likita ki rufa mun asiri kamar yadda Allah ya rufa miki naki dan Allah ki cire mun wannan cikin.Da madaukakin mamaki da tuhuma at same time take kallonsu duka biyu, Ameena tana duke tana kuka ita kuma zulaihat tana zaune saman kujera amma hawaye takeyi.Tace ban fahimci abunda ke kokarin faruwa a cikin wannan ofishin ba ina bukatar bayani kuma gaskiya zaku fada mun idan ba haka ba in hada ku da jami’an tsaro.Ai dajin jami’an tsaro hankulan su suka tashi, zulaihat ce tayi karfin halin goge nata hawayen tace kiyi mana rai likita ki taimakemu domin Allah! Bata da aure tsautsayi ne ya gitta tsakanin ta da saurayinta sai ciki ya shiga kuma a gida idan aka sani wallahi kasheta zasuyi ki taimake mu domin Allah ki cire mata cikin.Tun daga mummunan kallon da likitar ta jefe su dashi jikunan su suka yi sanyi daga bisani tace.Lokacin da zaki aikata mummunar aikin baki tuna da halin da zaki tsinci kanki a ciki ba sai yanzu? Ina wayonki ya tafi? Ko fyade ya miki?Ta girgiza kai tace ba fyade ya mun ba yaudarata yayi har ya samu shawo kaina na amince mishi amma wallahi tun ranar da abun ya faru nike nadama har yanzu dan Allahki taimake ni.Bazan boye miki ba kin cuci kanki sannan kin cuci iyayen ki kinci amarnar su kin wulakanta su yanzu ina shi saurayin naki yake? Yasan da cikin a jikin ki?.Kuka ta kara fashewa dashi kamar zata shide tana bude baki amma ta kasa magana don kukan da takeyi ta kasa hana kanta, sai zulaihat ne ta fada mata duk yadda sukayi da Ahmad din.Murmushin takaici likitar tayi tace inace ga irin ta nan, shi ya sanya ki a damuwa yana can yana jin dadin shi kuma yana dadamar kin amincewa sai dai hanya daya tak da dole zata gasgata shine uban dan itace bayan kin haihu ayi DNA test kuma kafin lokacin zai iya bacewa ganin ki gaskiya banji dadi ba ina taya iyayen ki jimami.Sai yanzu ta samu tayi magana tace dan Allah ki cire mun cikin ba sai sun sani bama.A fusace kuma a kausashe likitar ta nunata da yatsa tana cewa, ki dubeni da kyau na miki kama da jahila? Nan asibitin ba’a zubar da ciki kuma ko ina kika je bazasu karbi case dinki ba karshe in kin dage sai cikin ya fita ki iya rasa ranki ta dalilin hakan kinga sai ki tanadi amsawa mahaliccinki amsar dalilin sakarcin ki.Kuka sosai Ameena takeyi tana rokonta akan ta cire mata cikin nan ta taimaketa zulaihat ma tana taya ta bada baki.Tausayin sune ya ziyarci zuciyar likitar ta sassauta murya tace kuyi shiru muyi magana ta gaskiya.Dip sukayi suna jiran jin me zata ce musu.Abu daya zan fada miki wanda nayi imanin koda diyata ce ta cikina abunda zan fada mata kenan.Kiji tsoron Allah! Kiji tsoron Allah!! Kiji tsoron Allah!!! Koda a ina kike kiyi hakuri da batun cire cikin nan domin baki san me Allah ya nufa da abunda zaki haifa ba ki bari Allah yayi ikon shi, kada kiji tsoron kunyan duniya fiyeda ta lahira, duniya gajeriyar rayuwace mai cike da karairayi ita kuma lahira gaskiyace dawwamammiya, kiyi istigfari akan laifin da kika aikata yafi kiyi kokarin tsunduma kanki a cikin wani laifi, ki sani duk hukuncin da iyayenki zasu miki yafi miki saukin dauka amma baza ki iya daukar hukuncin ubangiji idan yaso kama ki ba don haka ina mai baki shawara da kiyi hakuri kiyi tawakkali mai yiwuwa abunda zaki haifa zai haskaka duniya kila malami ko likita, alkali ko lauya baki sani ba, kiyi ta addu’ah Allah yana sane dake kema bai kamata ki manta shi ba kinji ko?.Share sauran hawayen tayi tace insha Allah likita zanyi kokarin bin shawarar ki na gode sosai da kika tunatar dani ta kalli zulaihat tace tashi mu wuce.Bayan kwanaki zazzabi na cinta sosai amma duk da haka ta daure sosai don kada kowa na gidan su ya fahimci halin da suke ciki.Da yamma suna zaune a tsakar gida dukkan su, goggo tayi sallama ta shigo, goggo yayar mahaifin sune tana zaune a layin gaba dasu, sukan jima basu ziyarci juna ba wani lokacin sakamakon ba wani shirine a tsakanin goggon da ita inna ba, yauma ta zone domin ta gana da dan uwanta.Lale bismillah kune a tafe, fateema dauko mata kujera.Dauko kujerar tayi ta ajiye mata ta zauna suka gaisa.Ina shi baban nasu yake?Ya dan fita ne kuma ina jin baiyi wani nisa ba ko za’a kira miki shi a waya? Inna ta tambaya.A’a ki barshi kawai zan jira shi, ta fada tana bin kowannen su da kallo idanunta suka tsaya akan Ameena data yi fayau saboda zazzabi tayi haske sosai ta dan rame kadan idanunta sun danyi launin kore kore.Ta maida dubanta kan inna tace zamu yi magana a ciki kafin ya dawo.Dagowa inna tayi tace toh mu shiga daga cikin.Bayan sun shiga sun zauna goggo ta dubi inna tace wannan yarinyar Ameena meke faruwa da ita, ina nufin meke damunta?.Zazzabi ne kawai amma dai lafiya ko kika tambaya.Eh toh bana ceba gaskiya amma kin bincika da kyau kuwa?Goggonsu kin tsoratani dan Allah me kika gani ki mun bayani.Hum kedai kam ga dukkan alamu sun nuna Ameenatu cikine da ita.Dummmm………Haka gaban inna ya buga ta dafe kirji tayi salati tace a’a gaskiya bana tsammanin haka.Ki dai binciketa na fada miki.Ameena…….Inna ta kwalla kiran Ameena hankalinta a tashe bugun zuciyarta na karuwa.Shigowa Ameena tayi ta zauna daga ta kasa gefen goggo zuciyarta na bugawa cikin sauri kamar ace kyat ta gudu.Ameena yaushe rabon ki da ganin al’ada? Inna ta jefo mata wannan tambayar.Wani irin faduwa gaban Ameena yayi gumi na karyo mata daga dukkan jikin ta dakyar ta bude baki tace….. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️


