Hausa novels

Halysaah Page 162 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 162…Karfe sha daya da few minutes Ajay ya fito bandaki yana kallon Khaleesat dake kwance tayi bacci, ya gama goge gashin kansa sannan ya shirya cikin jallabiya ya fesa turare ya karasa kusa da ita ya gyara mata gashinta that was scattered, ya ja mata duvet ya lullubeta sannan yayi kissing forehead dinta a hankali, cup din tea da ta ajiye masa daxu kan table ya dauka ya nufi kofar dakin don shayin yayi sanyi, ya bude kofar ya fita ya sauka downstairs, Jay ya gani kwance kan 3 sitter ya kafa ma PoP din parlon ido, suna hada ido Ajay ya sauke idonsa ya nufi kitchen walking slowly ya shiga, ya hado wani shayin after standing for another 5 minutes a kitchen din ya juya a hankali ya fito parlor, karasawa yayi ya zauna kan kujera without looking at Jay dake kallon TV this time around, bayan minti biyar Ajay yayi breaking silence din parlon yace “Ya ake ciki about ur Confrontation with Hadiyah?” Idon Jay na kan TV da yayi muting yace “Ana nan yanda ake” Ajay yace “Ta tafı Lagos din ne?” Girgiza masa kai kawai Jay yayi without saying anything, Ajay bai sake cewa komai ba ganin he is not creating any room for the conversation, suna ta zaune parlon har karfe sha biyun dare, daga karshe Jay ya ajiye remote din hannunsa ya mike yace “Sai da safe” Ajay ya daga kai ya kallesa yace “Allah ya tashe mu lafiya” Sama ya tafi Ajay ya bi sa da kallo, yafı minti talatin zaune parlon bayan tafıyar Jay sama, ko shayin hannunsa bai sha ba, daga karshe ya ajiye shayin a hankali kan table, ya mike ya kashe kayan kallon parlon sannan ya kashe wuta walking slowly ya wuce sama…. Washegari karfe bakwai saura Jay ya bar gidan, Khaleesat ta sauko downstairs kusan karfe takwas da rabi tana kallon Ajay dake zaune parlor ya jinginar da kansa da kujera, har ta karaso kusa da shi bai san ta shigo parlon ba, ta zauna gefensa sai a sannan yayi realizing presence dinta ya gyara zamansa a hankali yace “Har kin gama baccin?” Cike da damuwa tace “Tunanin me kake yi haka? What are you always thinking of pls?” Ajay yayi shiru bai ce komai ba kuma bai kalleta ba, ita dai sai kallonsa take, don in dai yana zaune shi kadai to zaka samesa carried away in his thought har sai ka zauna kusa da shi ko kuma kayi masa magana sannan zai dawo senses dinsa, after some seconds Ajay ya dan kalleta, ganin damuwar fuskarta yayi murmushi ya ja dogon hancinta yace “I am thinking of how we will make beautiful babies, kamar su takwas haka, bakwai su yi kama da ni, daya tayi kama da ke, kuma duk mata nake so…..” Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, ya matsa kusa da ita a hankali yace “Kin yi shiru Milady” Ta daga idanuwanta cikin sanyin murya tace “Saboda nasan ba tunanin da kake ba kenan, akwai wani abu dake damun ka da baka son gaya min, i noticed that since we were in Tanzania, am i not worthy of knowing ur worries my prince?” Ajay ya dauke idonsa daga kanta yayi shiru, ita dai Kallonsa kawai take…. and she could see the disturbance clearly on his face, can ya daga ido ya kalleta ganin idonta har sun kada ya jawota jikinsa a hankali, cikin sanyin murya yace “Jeeddah” Rufe fuskarta tayi a kafadarsa muryarta na rawa tace “Plss ka gaya min what the problem is, menene yake damun ka haka?” Cikin sanyin murya yace “But….. You know our bond with Jay Khaleesat” Daga kai tayi tana kallonsa jin ya kirata Khaleesat abinda bata taba jin ya kira ba, ya sauke idonsa yace “That’s my problem, I’ve tried to move on for a long time but it seems i am deceiving my self, even at that kasantuwar ki tare da ni yasa nake iya controlling damuwar making it not to be obvious, though yace min he hold no grudges against me, definitely that might be true…. but may be he doesn’t want me in his life anymore” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace “Amma ai ba laifinka bane kuma baka ce kana sona ba aka aura maka ni, me yasa bazai yi considering hakan ba? Tunda nima nayi move on why don’t he try do so too?” Ajay ya daga ido ya kalleta jin abinda tace, ta sauke nata idon tace “Dama Allah bai kaddara ni matarsa bace shi yasa abinda ya faru ya faru, we were never destined to be together, Allah ya rubuta kai ne mijina, me yasa bazai duba haka ba shi? Ni da nake karama ma na gane haka balle shi” Ajay yace “Jeeddah” Tayi shiru tana kallonsa, calmly yace “Ina son maki tambaya ki amsa min tsakaninki da Allah” Ta gyada masa kai tace “Ina jin ka Ya dan yi shiru kafin yace “Let’s assume idan na rabu dake yau, zaki iya… auren sa?”Khaleesat ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, ya sauke idonsa, Jin tayi shiru na kusan second talatin ya sake daga ido ya kalleta da kyar yana girgiza kai yace “Ina son Jay kuma ina jin sa a raina fiye da yanda kike tunani Jeeddah, he was once my shield from every angle, he was there for me always, words alone can’t express the kind of bond i have with Jay, I don’t think I can keep on seeing him being depressed cause Jay is depress, I know he is depress, babu wanda ya fi ni saninsa har Maminsa, bazan iya ci gaba da ganinsa a halin da yake ciki ba, dalilin da yasa na danne nawa son a sanda muke Amurka ba komai bane sai ganin yanda yake sonki with all of his heart” Khaleesat ta sauke idonta har sannan bata ce komai ba, cike da karfin hali Ajay yace “Ba wai bana sonki ba Jeeddah, i love you soo much, I don’t know what will become of me idan na rabu dake, amma for Jay’s happiness i think I can do that not minding what will happen to me afterward, beside i am no longer the crowned prince in our Emirate hakan zai bani damar barin kasar nan, zan koma gun dangin Mahaifiyata in ci gaba da rayuwata a can, i can stay far from Nigeria, i am not the only child or son of my father balle ya damu, i think I can do this for Jay….” Kai kawai Khaleesat ta gyada masa bata daga kanta ba don bata son ya ga hawayen idonta, Ajay ya dinga kallonta babu ko kiftawa, nan da nan idanuwansa suka kada, cike da karfın hali yace “Kin fahimce ni Jeeddah?” Tace “Sure, i understand, zan hada breakfast a kitchen” Tana fadin haka ta mike ta nufi kitchen, ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, dafe kansa yayi yaji wani irin sanyi na shigarsa, har zuciyarsa ya gaya mata abubuwan da ya gaya mata amma reaction dinta ba karamin shocking dinsa yayi ba, irin kamar she doesn’t care din nan, meaning she still have a place for Jay in her heart, da kyar ya mike ya wuce sama yana ganin blurr a idonsa, Khaleesat na shiga kitchen ta kulle kofar ta jingina jiki tana shesshekan kuka a hankali, ta fi minti goma haka tana jin wani zafi a zuciyarta hawaye na zuba idonta, da kyar ta fito daga kitchen din bayan ta goge hawayenta, ganin baya parlon ta wuce sama, slowly ta bude kofar dakin da suka sauka, bata gansa cikin dakin ba, ta dau handbag dinta ta mayafi, ta saka wayar cikin jaka sannan ta fice daga dakin ta sauka downstairs ta fita compound, tana isa gate mai gadi ya mike da sauri yana jera mata gaisuwa sannan yace “Hajiya fita zaki yi ayi ma Dreba magana?” Ta dake tace “Ba nisa zan yi ba, bude min gate din Ba musu ya bude mata gate din ta fita, hawaye na zuba idonta take trekking din dogon titin layin, a haka har ta isa babban titi, duk bata ga alamar adaidaita sahu ba a wajen ta ci gaba da tafiya, bayan tafiya me nisa ta fara ganin tricycle ta tsayar da guda daya tana kallonsa tace “Sharada zaka kai ni” Nan ya lafto mata kudi sanin a unguwan masu kudi ta tsayar da shi, shiga bayan adaidaita sahun tayi ya ja suka wuce, tana goge sabon hawayen da taji yana taruwa idonta…. Bayan tafiya me nisa suka isa Sharada, ta sauka daga adaidaita sahun tace “Bari in shiga in amso maka kudin, ko zan iya maka transfer?” Yace “To yi transfer din Ta bude app din bankin ta, ta sa ya karanto account number dinsa sannan ta tura masa kudin, babu bata lokaci yace yaga alert, ta nufi gate din gidan tayi knocking, Mai gadi ya bude mata ta shiga, bata tarar da kowa parlon gidan ba hakan yasa ta wuce sama ta bude kofar wani daki that was at the far end of the corridor ta shiga, Safiyyah ta zaro ido da mamaki tana kallonta tace “Waye wannan nake gani haka” Khaleesat bata ce mata komaiba ta karasa cikin dakin ta cire mayafinta ta ajiye da jakar hannunta ta zauna kan Carpet, Safiyyah ta sauka daga kan gadonta ganin yanayinta tace “Lafiya Khaleesat?” Khaleesat bata san sanda kuka ya taho mata ba, nan da nan Safiyyah ta rikice tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, me ya faru Khaleesat? Ina Ajay din? Daga ina kike?” Kuka kawai Khaleesat take sosai tana jin zuciyarta na mata wani irin zafi, Safiyyah ta durkusa kusa da ita tace “Na shiga uku, don Allah ki gaya min menene ya faru, wallahi hankali na ya tashi, speak to me plss” Cikin kuka sosai Khaleesat tace “Ni tawa jarabawar kuma ta bangaren aure ne kenan Sophie” Sosai gaban Safiyyah ya fadi ta dinga kallon Khaleesat babu ko kiftawa a ranta kuwa ta dinga nanata Godforbid din abinda ya fado mata, don babu inda tunaninta ya tafi sai ko sakinta Ajay yayi, Safiyyah ta zauna gabanta don ta ma kasa cewa komai, Khaleesat dai kuka kawai take kamar ranta zai fita, har sai da tayi calm down tana shessheka sannan a hankali Safiyyah tace “Ki gaya min me ya faru kawata, tell me piss Khaleesat ta hade kanta da gwiwa tana wani sabon kukan, Safiyyah ta fara patting bayanta calmly tace “Kiyi hakuri, speak to me pls” Khaleesat ta dago kanta, sounding so bitter ta fara gaya ma Safiyyah duk maganganun da Ajay ya gaya mata, haka Safiyyah ta bude baki tana kallonta, can ta gyara zama tace “Ko dai kaf yan gidan sarautar nan basu da saiti ne basu da hankali? Na shiga uku ni Safiyyah, abinda ya gaya maki kenan Khaleesat?” Cikin kuka Khaleesat tace “To ni ball na zama da za a dinga passing passing da ni? Ko da ya rabu da ni yau yana tunanin zan yarda in auri Jay? Allah Ubangiji ya sauwake wallahi, That will be the least thing I will do in this life wallahi wallahi, gwara in mutu ba aure…. Safiyyah dai tayi shiru don ta ma rasa abun cewa, Can ta girgiza kai tace “Gaskiya Ajay bai yi tunani ba akan maganan nan da ya gaya maki, haba sai kace wasu marasa addini, to su masarautar tasu ta mahaukata ne da za a yarda ya sake ki Jay ya aura? Yau naga fitina kiri kiri” A fusace Khaleesat tace “Kar ma su saka na fara regretting haduwata da su gaba daya wallahi…” Wani kukan ta fashe da shi cikin rawan murya tace “Saboda ya ga na fara son sa shi yasa zai gaya min wannan maganar, is it my fault da na fara son sa” Ita kanta bata san ta fadi hakan ba cause she was soo hurt, bata taba tunanin zai gaya mata irin wannan maganan ba wataran, Safiyyah ta dan yi murmushi, ta rungumota tace “Shi ma kawai yana fadin haka ne amma bazai iya rabuwa da ke ba Khaleesat, don son da yake maki ma yafı naki, but Jay needs to move on like seriously sai kace ba Musulmi ba, me yasa bazai dau kaddara ba ya bar ku kuyi zaman auren ku, har ma ya bada tasa gudummawar ta hanyar shawarwari” A hankali Khaleesat ke kuka a jikin Safiyyah maganganun Ajay na dawo mata kai tana jin wani zafi a ranta, ashe zai iya cewa zai rabu da ita, bata san sanda ta fashe da wani sabon kuka ba sosai, nan Safiyyah tayi ta aikin lallashinta sun fi minti talatin Safiyyah na abu daya daga karshe Khaleesat ta jinginar da kanta da gado tana sauke ajiyar zuciya, Safiyyah tace “Ki hau kan gado ki kwanta, kin yi breakfast?” A hankali tace “Na koshi” Daga haka ta mike ta hau kan gadon Safiyyah ta lumshe ido, Safiyyah tayi tagumi, ita kuma kaddarar kawarta kenan a rayuwar nan, ta yaya ma Ajay zai ce zai saketa saboda Jay, daga karshe Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta fita daga dakin, ita kadai da masu aiki ne a gidan daga Abbanta har Momy da Cousin sister dinta dake gidan duk sun fita aiki don Monday morning ne, downstairs ta sauka taga abinda aka yi for breakfast. Wajen karfe sha daya Ajay ya sauko downstairs ganin har sannan Khaleesat bata hauro sama, sosai idanuwansa suka kada kana ganinsa kaga damuwa karara a tare da shi, kitchen ya bude a hankali ya shiga yaga bata ciki kuma babu alamar anyi girki a kitchen din, ya fito parlor yana kallon bakin kofar fita yaga babu takalminta, sama ya tafi zuwa daki da sauri a nan yaga babu handbag dinta da wayarta, zaunawa yayi gefen gado ya rike kansa dake masa wani irin ciwo, yafi minti goma a haka daga karshe ya mike da kyar ya fita daga dakin ya sauka downstairs, gun Mai gadi ya nufa yana tambayarsa yaushe ta fita daga gidan, Mai gadi yace “Ai Hajiya ta kusa awa daya da fita ranka shi dade” Ajay bai ce komai ba ya juya yana jan kafa da kyar ya koma cikin gidan, ya tafi sama ya dauko makullin motarsa sannan ya sauko, kansa na juya masa haka nan ya fita daga compound ya nufi parking space ya bude mota ya shiga nan ma ya hade kai da steering na kusan minti sha biyar, dagowa yayi ya goge hawayen da yaji a idonsa ya tada motar, Mai gadi na jin haka ya bude masa gate cikin hanzari, Ajay ya ja motar ya bar compound din. A hankali Khaleesat ta bude ido wajen karfe sha daya da minti sha biyar, Safiyyah dake zaune gaban madubi tana shafa mai bayan ta fito wanka ta juya tana kallonta tace “Kin tashi? Ga breakfast nan na ajiye maki tun daxu” Khaleesat ta mike zaune tana yatsine fuska, sai kuma ta kauda kai, Safiyyah tace “Me ya faru?” Bata juyo ba kuma bata ce ma Safiyyah komai ba, Safiyyah ta zaga inda take kallo tace “Khaleesat” Kara kauda kai Khaleesat tayi da sauri still tana yatsine fuska tace “Wannan wani irin mai kike shafawa?” Safiyyah ta zaro ido tace “Cream din nawa ne kuma yau baki sani ba?” Khaleesat ta fara kokarin sauka daga kan gadon tana rufe hancinta da arm dinta tace “I don’t like the smell Safiyyah bata san sanda tayi wani dariya ba, sai kuma tayi saurin dena dariyar tace “Ke dalla, saboda ranki a bace yake shi yasa baki son kamshin cream din, amma ai kin san cream din tun a America” Khaleesat dai bata ce mata komai ba ta nufi bandaki tana rufe hanci, Safiyyah ta bi ta da kallo tana murmushi, tana shiga bandakin sai ga ta ta fito da sauri still covering her nose tace “Na ji kamshin a bandaki kuma” Safiyyah tace “To ba da sabulunsa nayi wanka ba, mu je in kai ki dakin Aunty Salaha….” Khaleesat ta jira sai da Safiyyah ta fita sannan ta bi bayanta leaving a reasonable gap between them saboda kamshin cream din jikin Safiyyah, Safiyyah na murmushi ta bude mata kofar dakin Cousin sister dinta tace “To shiga” Khaleesat tace “To ki matsa daga bakin kofar Da sauri Safiyyah ta koma can nesa da kofar ta tsaya, sannan Khaleesat ta shiga cikin dakin tana sauke numfashi…..

Back to top button