Halysaah Page 84 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 84…Karfe tara da kusan rabi na dare Khaleesat ta shigo dakin Ummanta da sallama tana rike da ledan tsire wanda babanta ne ya siya mata, tun bayan isha’i take wajen baban nata tare da Nenne sai yanxu ta dawo daki, Jay sai da ya jira har Malam Ali ya dawo suka gaisa sannan ya bar unguwan daxu, zaunawa Khaleesat tayi kusa da Aunty Farida tana bude ledan naman tace “Su Islam har sun yi bacci” Umma dake kallonta tace “Nennen “Ne inen ta tafi ne?” Khaleesat ta girgiza kai tace “A’a tana can bata tafi ba” Aunty Farida tace “Baza ki ci tuwon naki ba?” Khaleesat ta langwabe kai tace “Nama zan ci” tuwon masara da miyar kuka Umma tayi, tana ganin tuwon daxu kawai tasan bazata ci ba, Aunty Farida tace “Ina kawarki Hajiya Safiyyah” Murmushi Khaleesat tayi tace “Tana can Maryland” Aunty Farida tace “Haba? Ita bata dawo hutun ba kenan?” Khaleesat tace “Yayanta yace sai next week za su taho gaba daya” Aunty Farida tace “Allah sarki, Allah ya kawo su lafiya, na zata tare ku ka dawo ai… Wai saura wata nawa yanxu ku kare karatun gaba daya?” Khaleesat tace “Bai wuce wata hudu ba, final semester kawai ya rage mana” Aunty Farida tace “Toh Allah Ubangiji ya baku sa’a, ya sa ku gama lafiya, ai kun kusa” Khaleesat tace “Ameen Aunty” Aunty Farida tace “To amma me yasa baku dawo har Junaid ba ya riga ku tahowa shi” Umma ta rike haba tana kallon Aunty Farida tace “Ikon Allah, kika san uzurinsa?” Ita dai Khaleesat murmushi kawal tayi bata ce komal ba ta matsar da takardan naman gabanta kusa da Aunty Farida bayan ta debar ma Umma nata…. Bayan Khaleesat taje tayi alwala ta dawo dakin Umma tayi shirin kwanciya, ta kwanta ta dau wayarta zata bude WhatsApp don rabonta da hawa tun da asuba da suka sauka Abuja kuma tasan Safiyyah dole zata yi mata magana, tana shiga WhatsApp din ta ga status din Ajay, sosai tayi mamaki don bata yi zaton yayi saving numberta ba, ta bude status din, daily reminder quote taga ya dora, ta tura masa Sticker sai taga yana ma online, WhatsApp call tayl ma Safiyyah bayan sun gama magana still bal mata reply ba, dama bata sa ran zai yi ba ta kashe data dinta ta kwanta. Washegari Khaleesat na idar da azkar din da take ta kira Jay, don yace mata karfe shidda zai wuce Bauchi kuma driving zai yi, bayan sun gaisa tace “Are you still leaving early?” Yace “In sha Allah Halysaah, har na gama shiryawa ma” Tace “Toh Allah ya tsare hanya, Allah ya kai ka lafiya, don’t forget to pray please….” Yace “I won’t dear” Tace “Amma kayi breakfast?” Yace “Yea, I took tea, idan na fita gida zan kira ki in sha Allah, ko za ki koma bacci ne?” Ta girgiza kai tace “A’a” Yace “Ohk then, I will call you” Daga haka ya katse wayar. Karfe goma sha daya Nenne ta shigo gidan ta nemi kujera er tsugunno ta zauna tana kwalo ma Umma kira, Khaleesat dake wanke wanke a tsakar gidan ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace “Ahamad din ya tafi Bauchin kuwa, yace min da sassafe zai bi hanya yau” Khaleesat tace “Har ya isa tun karfe goma” Nenne tace “Maa sha Allahu haka ake so, in kun yi waya ki ce ina gaishesa don Allah, ni ba waya gareni ba balle in kirasa, amma kar ki ce masa haka, kawai kice ina gaishesa ina masa bangajiya” Khaleesat na dauraye kwanon hannunta tace “Toh” Sai da Umma ta fito sannan Nenne ta amsa gaisuwan su Mama Zubaida a dakile ba tare da ta kalli inda suke ba, Umma ta zauna kan tabarman dake shimfide ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace “Ina parida” Bata rufe baki ba sai ga Aunty Farida ta fito dakin Umma, ita ma ta gaida Nenne ta amsa sannan tayi kasa da murya tana kallon Umma tace “Zaura’u, ina ga fa lallai lallai yau za mu bi dare mu bar unguwan nan, don daxu almajirina ke ce min yaga Awdul ya shigo unguwan nan da safe” Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon Nenne gabanta na faduwa, Nenne tace “Don haka baza mu biye All ba, In yaga duk mun tattara mun tafi ya biyo mu da dan akwatinsa, don ba irin maganar da ban masa jiya da daddare ba kan ya hakura ya amshi gidan nan da bawan Allahn nan ya siya masa hannu bibbiyu don da zuciya daya ya siya masa, amma tsoro ya hana Ali sakat, yace shi tsoro yake gaskiya….” Umma dai tayi shiru don bata san me zata ce ba, ita kanta hankalinta ba a kwance yake ba tunda Khaleesat ta dawo jiya don bata san wani mugun abun ke ran Abdul ba, tana ta tsoron kar ya samu labarin ta dawo ma, Nenne tace “Sabili da haka cikin dubara a kira makota duk a basu sadakar abubuwan da baza mu koma sabon gidan da shi ba, irinsu rubabbun tukwanen ku da katifa da tarkacen kwanukan ku, don babu abinda yaron bai zuba mana a gidan ba har kujeru da kayan gado, sannan na aika aje kasuwa a kira min Ali yayi maza ya dawo babu lafiya, so nake ya dawo mu ji yanda zai yi da matansa don baza su bi mu gidan nan ba gaskiya, in ma kauye zai maida su ya dinga zuwa can duk sati yana duba su to” Daga Mama Zubaida har Mama Shatu suka juya suna kallon Nenne, Nenne tace “Don ban ga inda za a kunna icce ko kuma a dafa abincin talla a wannan tanfatsetsen gidan da yaron nan ya siya mana ba, ko ina tas ne malale a kasa, komai sabo dal” Umma dake ta kallon Nenne tace “Ki dai yi hakuri Nenne don da mu da su Shatu duk daya muke a wajen Malam, dakuna shidda ne a gidan banda gini daban me daki daya da parlor da bandaki da kitchen, duk zai ishe mu Nenne” Nenne tace “Ke in baki da hankali ni ina da shi Zahra’u, banda karamin tunani irin naki kinga gidan yayi kalan Shatu da Zubaida? Kinga alamar kazanta zata samu muhalli a wannan tanfatsetsen gidan kamar a kasar waje?Na kirga dakuna biyar a gidan da katon parlor sal wawakeken kitchen, sannan har da bangaren me gida duk a cikin gidan, shima naga parlor ne sai daki da bandaki, to wannan na Ali ne, ke kuma ki dau daki daya, Farida daki daya, Khaleesah daki daya, yan biyunki ma a basu daki daya, daki daya da ya rage ya zama na saukan baki, ginin dake waje dama nace nawa ne ni zan zauna ciki kada wanda ya saka ma ginin ido, to a ina kika ga dakunan da za a zuba su Zubaida da ‘ya yansu rakacaa idan ba dai baki de nankali ba? Ai babu guri a gidan, kai ko da wurin ma ni sam bazan amince in zauna da su Shatu ba sai dai ni in hakura da tarewa a gidan inyi zamana a Mariri har wa’adin da Allah ya dibar min a duniya ya cika in koma garesa, in kuma ance lallal lallai sai sun bi mu ta sai dai Malam Ali ya siyar da wnn gidan da nawa ya tafi unguwan yaku bayi ya siya masu gida me dakuna uku ya ajiye su da ‘ya yan su, amma wannan gida kam ta silan Khaleesah aka siyesa ba wani shege ba, yau in tace níma bazan shiga ba ya zauna balle wasu yan iska Zubaida da Shatu, da ma suna ganin mutuncin mijinsu ne balle ni, balle ke karan kada miya da suka rena, yau watanni kusan hudu kenan babu abinda Ali ya rage su da shi a gidan nan, tun da Allah ya saka ma hatsin da ya fara siyarwa a kasuwa albarka bai ragi iyalinsa da komai ba komai korrai yi masu yake, amma sun ki dena abincin siyarwa don su yi ta ja masa zagi a gari, kudin makarantan yara idan ya basu sai su bi su kwace su bar yaran suyi ta yawo kamar almajirai a unguwa suna talla, to ina amfanin matan nan? Shi dai wannan yaro da ya basa jari Allah yayi masa albarka…” Nenne te kalli Khaleesat tace “Ya sunan abokin Ahamad din nan mara fara’a?” Khaleesat ta daga ido ta kalli Nenne, Umma dai tayi shiru don bata san me zata ce ba kuma, Aunty Farida ma dai is speechless, Nenne ta mike tsaye tace “Duk ki fito da tarkacen ki Zahra’u a bada su sadaka, in sha Allahu baza mu kwana a gidan nan ba, gwara mu koma gida me get yanda sai an kwankwasa ma za mu bude, shi kuma Ali ya dawo yasan yanda zai yi da matan nan nasa, bari inje in fara harhada nawa kayan, ina nan dawowa nan ba da dagowa ba, ni dama ba shirgi ne da ni ba, ai ‘ya mace abar alfahari ce in dai ka tsaya kayi mata tarbiyya yanda ya dace, da Khaleesat bata da tarblyya uban wa zai kalleta balle har ayi mana wannan abun arzikin ta dalilinta, wannan kadai ya ishi yan baya izini, in za su tsaya su tarbiyyantar da ‘ya yansu su zama na kwarai to su za su ci riba ba wani ba” Nenne na kai wa nan ta kalli Aunty Farida tace “Dauko gyalenki mu tafi ki tayani parida, in akwal abinda zan bayar kawai aiken ki zanyi kiyi sallama gida ki kira matar gidan ku taho tare, cikin sirri nake son ayi komai” Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida ta mike ta dauko Hijab dinta ta bi bayanta ta fita, Bayan yan mintuna Mama Zubaida ta mike ta tafi ta bude kofar gidan tana leka waje taga Nenne da Aunty Farida har sun sha kwanan gidanta, dawowa tayi tsakar idanta, gidan tana ma Umma matsiyacin kallo tace “”Aikin banza, aikin hofi, kurı zauna kun tsara kayan ku shine kike son ki mayar da mu yan iska ke ga er slyasa, bayan duk kin san da tsarin, kin ga wannan sabon gidan In anyi duniya don manzon Allah sai ya zame maku bala’l da fitinar da yafi karfin ku, sai kun gwammace ba a baku ba, kuma waye bai san me Khaleesah tayi aka bata gidan ba? Mu duk bamu yi mamaki ba don mun san ba yanxu ta fara karuwanci ba, kuma muna nan dake sai ta jajibo maku abun kunyan da har ku mutu bazai goge ba daga ke har Nennen, bakin cikin abun kunyan ne kuma zai kar ki har lahira” Umma ta mike tana murmushi tace “Ni dai kullum ina maku tuni da ku koma islamiyya ko za ku samu saukin jahilcin nan, in sha Allahu kuma ni da zuri’ata babu abinda za mu gani sai alkhairi, Allah ya baku lafiyan cutar hassadan dake neman nakasa maku zuciya…” Mikewa Shatu tayi, Umma bata sake bi ta kansu ba ta shige dakinta, Khaleesat dai murmushi kawai take ta mike ta wuce daki ita ma, hayaniya Mama Zubaida da Mama Shatu suka dinga yi a gidan suna batanci da fadin mugaven kalamai har sal da makota suka shigo bada hakuri, ita dai Umma tuni ta sake labulen dakinta tayi kamar bata san da ita suke ba. Bayan la’asar Nenne ta dawo gidan da Aunty Farida, sai ga sha’awa da wasu makotansu Umma su uku sun shigo gidan su ma, duk Nenne ce tasa Aunty Farida ta shiga gidajen su ta kirasu, Nenne na tsaye har Umma ta gama fiddo duk kayan da zata bada, Nenne ta dau zannuwan gado biyu ta wurga ma Sha’awa da wata tukunyar Umma, haka ta dinga rarraba kayan tsakanin makotan da tasa aka kira mata suna girmamata awa enda ke ganin mtuncinta suna girmamata a unguwan, bayan sun kare ta mike tace “Toh gasu nan saboda Allah, shirgi ne suka mata yawa take bayarwa…” Su Mama Zubaida dai na tsaye bakin kofar dakin su fuskokinsu a murtuke suna kallon ikon Allah, Nenne ta sallami makotan duk suka fita gidan suna godiya kaca kaca, sal kuma ta kalli Umma tace “Kin gama hade kayayyakin naku na sa wa dake da yaran ki? Har fa mun je mun samo motar da zata kwashe mu anjima, karfe sha daya da rabi na dare muka yi da me motar” Umma tace “To Allah ya kai mu” Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne tace “Yauwa Ali, mu dai anjima za mu bar gidan nan kamar yanda na gaya maka jiya, yanxu ya za kayi da shirga shirgan matan nan naka? Kauye zaka tura su zuwa sanda zaka samar masu gidan haya ne ko ya zaka yi da su? Don babu wanda zai saura gidan nan balle Awdul ya samu kishin kishin din inda muka koma” Malam Ali dake kallon Nenne yace “Kauye kuma Baaba, kin fa ce min dakuna bakwal ne a can gidan” Mama Zubaida ta gyada kai tana girgiza kafa alamar atoh dai, Nenne ta saki baki tana kallonsa, can tace “Sai aka yi yaya da nace maka dakuna bakwal ne Ali?” Malam Ali yace “Kawai ayi hakuri duk a koma can din tunda kince a bar unguwan, don ni gaskiya yanxu bani da isasshen kudin kama haya Baaba” Umma ta kalli Malam Ali tace “To kuwa sai kasan yanda zaka yi da su Malam, don wallahi babu warce zata bi mu gidan nan, in ko kace sai sun bi mu sai dai duk a fasa shiga” Nenne tayi wani dariyar keta har da kyakyatawa sannan ta ja kujera ta zauna tana kallon Umma da mugun mamaki kamar ranan ta fara ganinta, Aunty Farida kanta kallon Umma take da mamaki, Balle Malam All da yayi shiruu shi ma yana kaitonta ya kasa cewa komal, Nenne ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Allah ya mak albarka Zahra’u, in ya ga dama ya basu kudi ko wacce ta kama hanyar kauye, duk sanda Aliah ya hore masa sal ya nema masu hayan a birni” Malam Ali yace “Toh Shikenan, sai ayi hakan kawai” Mama Shatu ta fashe da kuka tace “Amma ka cucemu ka ci amanar mu Malam, wallahi sai Allah ya mana sakayya” Mama Zubaida ma ta fashe da kuka tace “Kuma kar ka manta hukuncin wanda baya adalci cikin iyalansa, wato ka fifita Zahra’u da ‘ya yanta a kan mu kenan kake nufi, alhalin duk matsayinmu daya a wajenka tunda mu ma matan ka ne, kaji tsoron Allah Malam” Nenne tace “Ji bakaken jahilai, Alin ne ya siya gidan ko kurra shi ya zuba kayan cikin gidan da ya maku rashin adalci? Gida al na Khaleesah ne da uwarta kuma yanda suka ce haka za ayi, ko Ali bashi da ta cewa tunda babu biyar dinsa a gidan, balle ni uwarsa, don ma ku ji in gaya maku” Malam Ali dai ya nufi kofa ya fita daga compound din, Aunty Farida tayi murmushi ta koma ta zauna, har sannan Umma bata gaya mata abinda su Mama Shatu suka mata ba shi yasa ma tayi mamaki da action din Umma…. A daren ranan Malam Ali ya ba su Mama Zubaida da Mama Shatu kudin motan zuwa kauye da tulin ‘ya yansu, gidan mahaifinsa na can kauyen har yanxu sai dai ginin kasa ne me dakuna hudu kuma babu kowa cikin gidan, sun ci kuka har sun gode Allah, karfe sha daya na dare motar da Nenne da Aunty Farida suka tafi suka yo haya can cikin gari ya iso kofar gidan, aka kwashe su gaba daya sai sabon gida, babban bakin cikin su Mama Zubaida basu san Inda su Khaleesah za su koma ba balle su yada a Mariri kowa ma yasan inda suka koma. Jay na zaune parlon Maminsa yayi nisa tunanin da yake, a karo na farko a rayuwarsa kenan da yaji sa kamar ba a parlon Maminsa ba don gaba daya he is not comfortable ya kasa sakewa, tunani iri iri ne ke yawo a zuciyarsa, tun jiya da ya iso Bauchi kawai gashi nan ne gashi nan dai, lokaci lokaci yake kallon Ajay dake zaune gefensa comfortably yana danna wayarsa, Ajay har ya mance rabon da ya shigo bangaren Mamin Jay a masarautan, duk da bata fiye zama ba sai tayi wata biyu ma bata gidan, Mami ta fito parlon daga Bedroom dinta don tana waya Jay ya shigo dakin sai kuma ya koma parlor shiru shiru kuma bata ga ya sake shigowa dakin ba bayan ta gama waya, dama yace mata da maganar da za su yi daxu saboda hakan ne ma bata fita ba don akwai inda zata, sai bayan da ta fito ne taga ashe shi da Ajay ne, Ajay ya ajiye wayarsa va gaisheta ba tare da ya kalleta ba, kallo daya tayi masa ta amsa sannan ta zauna tana kallon Jay tace “Ina ta jiran ka tun daxu Jawwad, yanxu in tafi inda zan je kenan sai na dawo kawai?” Jay ya daga kai ya kalleta yace “Ai yanxu za mu yi maganar da nace Mami” Marni ta kalli Ajay, sai kuma ta kallesa tace “Yanxu? Ka dai bari da daddare don fita zan yi yanxu gaskiya” Ta fadi hakan ne don bata ga dalilin da zai ce zai mata magana duk da bata san ko na menene ba kuma ya shigo mata da Ajay, tana bakin cikin yanda sam Jay bashi da sirrin kansa kamar tare aka haifosu duniya da Ajay, Ajayn da babu wanda ke sanin komai game da tasa rayuwar, bata jira cewar Jay ba ta mike ta wuce dakinta zata dauko mayafi, kafin ta fito har Ajay ya bar parlon, Jay ya bi sa da kallo, har cikin ransa baya jin dadin yanda Mami ta dauki Ajay, he felt really heartbroken, mikewa yayi kawai ya bi bayansa….
