Ruwan Zuma Page 42 Hausa Novel
(42) Laila ta jima tana zaune a gurin da Haydar ya barta zuciyarta na duka gami da k’una tuna irin tashin hankalin da zasu samu kansu a gaba idan har ya kasance cikin ne gareta. “Ya Allah ka sassauto da zuciyarsa ya gane me nake gudu. Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un.” Dafe kanta tayi da dukkan hannayenta tana addu’a da kuma rok’an Allah a zuciyarta kan yasa ba ciki gareta ba. Ita kanta tasan tayi son kai da bata son haihuwan ‘yayan Haydar. Amma shima ya kasa fahimtar inda ta dosa ne dalilin son ‘ya’yan ne a ransa. Itama tashi tayi ta d’auko Hijab d’inta daga d’aki ta fita a motarta zuwa chemist mafi kusa dasu can bakin hanya. A can ta sayo PT strip guda biyar ta dawo gida ta fara gwadawa cikin son sanin gaskiyar al’amarin, domin tana damuwa ne akan gaibu yayin da shi kuma Haydar yake fushi akan gaibu. Sannan bata son Haydar ya k’ara fushi da ita kamar na kwanaki domin ta wahala ta kuma shiga damuwa yanda baya tsammani. Tana zaune a bakin bathtub har minti biyar bata dauki PT strip d’in ba sannan bata ko kalli gurin ba dalilin bugun da zuciyarta yake yi babu kakkautawa, k’arshe shahada tayi bakinta d’auke da duk wata addu’ar data tuna ta d’auki tsinkayen duka ta duba. Sauk’owa tayi k’asan tiles d’in band’akin tana cewa, “Ya Allah!!” Haydar tun fitanshi daga gida tuk’i kawai yake yi har ya fita daga cikin gari gaba d’aya ba tare da kwakwalwarshi ta bashi location d’in da zai je ba. Sai da yayi nisa da gari sannan ya tsaya yayi parking a bakin hanya ya fito ya tsaya yana kallon dajin Allah. A wannan lokacin ko za’a kasheshi ya bada amsar meya kawoshi gurin bashi da ta cewa. Sai dai abu d’aya ya sani wato Laila ta tsaneshi kuma bata sonshi ko kad’an. Yasan idan ciki gareta zata iya cewa zata zubar, wannan tunanin zubar da cikin ma kad’ai yasa yaji kamar ya doki abu ko zai ji sanyi a ranshi dalilin ba zai iya ganin an kwararar da gudan jininsa ba. A lokacin ya gwammaci ace bata da cikin da ace tana dashi, domin rashinsa yafi musu sauk’in dealing akan tabbatuwarsa. Yana tsaye shiru shi kad’ai babu hayaniya sai motoci da suke shiga da fice daga garin. Tun bayan la’asar yake gurin har goshin magrib sannan ya canja akalar motarsa ya koma cikin gari. A bakin k’ofar gidansu yayi parking sannan ya shiga masallaci yayi sallah, ya jima yana addu’a sannan ya fito ya shiga gurin Ammi. Yau ma a rumfarta ya sameta ita da Meenat suna cin tuwo suna hira da alama har sun yi sallah. Meenat tana ganinshi ta rage fara’ar fuskarta kana ta gaisheshi bayan ya zauna a kujerar tsugunno yana fuskantarsu. Gaishe da Ammi yayi wacce tun shigowarsa take kallonsa kuma ta daina cin abincin dalilin ganin yanayin d’an nata kamar ba lafiya ba. “Lafiya Haydar na ganka haka? Baka da lafiya ne?” Ta fad’i hakan tana k’are masa kallo. Yak’e yayi kana yace, “Babu abunda yake damuna Ammi, kawai gajiya nayi. Mun sameku lafiya?” “Lafiya kalau, yaushe kuka dawo?” Ta tambayeshi ba don ta yarda da zancensa ba. “D’azu da azahar.” “Shine bari ka huta ba in yaso kazo gobe? Jiya mutum ya tafi Maiduguri kuma ya dawo a yau ai yana bukatar hutawa. Ya yaron kuka barshi?” Kafin ya bada amsa Meenat ta tashi ta nufi inda buta yake ta wanke hannunta kana ta yiwa Ammi sallama ta fita daga gidan. “Kayi shiru ina maka magana Ali.” “Yana can an killaceshi, ku tayamu da addu’a.” “Muna kan yin addu’a bamu fasa ba Ali. Allah ya shiryeshi ya d’aurashi kan hanya.” “Amin.” Ya amsa mata yana d’auko wayarsa da take ringing. Sunan Laila ya gani a jikin screen d’in amma ya saka wayar a silent ya mayar cikin aljihunshi. “Ali lafiya kam?” Ammi ta k’ara tambayarshi. “Ammi na fad’a miki lafiya kalau kawai gajiya ce, kuma yanzu zan tafi saboda akwai gurin da zan je.” Yana fad’in hakan ya mik’e tsaye ya mata sallama ya tafi. Koda ya fita daga gidan Ammi yawonsa yayi tayi a cikin gari saboda baya son komawa gida ya samu Laila wacce tunda ta mishi waya sau d’aya bai d’auka ba itam bata sake kiranshi ba. Bai koma gida ba sai k’arfe sha d’aya na dare a lokacin da yayi tunanin Laila tayi bacci. Sai dai yana shigowa falo ya sameta zaune tana jiranshi, yana ganin fuskarta ya d’auke kai yayi hanyar shiga d’aki amma ta kira sunanshi. “Haydar.” “Na’am.” Ya amsa mata ba tare daya tsaya ba ya shige. Tu6e kayanshi ya fara yi Laila ta shigo ta samu guri ta zauna tana kallonshi, band’aki ya shiga bai jima ba ya fito ya d’auki pillow ya koma falo ya kwanta. Hakan ba k’aramin 6atawa Laila rai yayi ba domin ta lura yana avoiding d’inta ne, sai dai me? Dolene su yi magana su fuskanci juna domin idan har suka cigaba da tafiya a haka duk lokacin da maganar haihuwa ta gifta tsakaninsu zasu cigaba da samun matsala. Bata daddara ba ta koma falon ta samu ya kwanta. “Haydar ka tashi muyi magana.” Ta fad’i hakan tana zama kusa da k’afafunshi. “Bacci nake ji sai gobe.” “Yanzu nake son muyi maganar saboda ina son mu fahimci juna ne mu ajiye magana d’aya.” “Ba komai kike so zaki samu ba.” Ya bata amsa ba tare da kalleta ba. “Me kake nufi kenan?” Shiru yayi bai ce mata komai ba illa ma juyawa da yayi ya bata baya. “Zamu k’ara yin irin na kwanaki kenan? Yau kuma yarintar ta motsa.” Ta fad’i hakan domin tasan ya tsani ta kirashi yaro. Sai dai a maimakon yayi lashing out sai wani shirun ne ya biyo baya mai kaifi wanda Laila bata so hakan ba. Sun kai minti uku suna shirun sannan Laila ta yanke shawarar mishi magana koda kuwa bazai amsa ba. “Bayan fitanka nima na fita chemist na sayo abun gwada ciki. Haydar na gwada duka biyar dana sayo sun nuna mini result d’aya.” Shiru tayi tana kallonshi ko zai nuna wata alama na kulawa amma ko motsin kirki bai yi ba balle ya tambayeta result d’in. Ajiyar zuciya ta sauk’e kanta k’asa taci gaba da magana a hankali, “Kai da kanka kwanaki ka fad’a mini ka hak’ura da maganar haihuwata, kai kace kuma baza ka sake fushi akai ba Haydar, amma ina fad’a maka fears d’ina ka d’auki fushi ka daina kulani. Kenan haka zamu cigaba da rayuwa duk lokacin da maganar haihuwa ya shiga tsakaninmu sai munyi fad’a? Yaushe aka yi auren da har zamu fara fad’ace-fad’ace irin haka Haydar? Kuma idan ka fahimceni ba wai bana son haihuwa da kai bane Haydar, tsoron haihuwar nake yi da kuma abunda zai je ya dawo gaba a ganni tsofai-tsofai da ciki ina yawo. Wallahi daka aureni a younge age d’ina dana haifa maka yara koda goma ne bazan damu ba saboda wannan ne daidai lokacin haihuwar mace without risk. Don girman Allah wannan karon ka fahimceni ka kuma saurareni muyi magana d’aya a ajiyeta.” Ta k’arisa maganar hawaye na taruwa a idanunta tana d’aura hannunta kan k’afarshi. “Menene result d’in?” Shine abunda ya tambaya ba tare daya juyo ba. “Ka tashi muyi magana ina so ne muyi magana ta fahimtar juna.” Ta fad’i hakan cikin lallashi. Bai musa ba ya tashi ya zauna yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa amma da zata d’aura hannayenta kan k’irjinsa zata tsorita dalilin bugawar da zuciyarsa take yi. He is restless ta ciki domin ya k’agu yasan result d’in. “Haydar result d’in ya nuna ina d’auke da juna biyu.” Ta fad’i hakan tana kallon cikin idanunshi wanda lokaci d’aya suka zama glassy alamar hawaye na taruwa a cikinsu. Haydar kasa motsi yayi domin ya rasa me zai ji a wannan lokacin, farin ciki ko bak’in ciki dalili kuwa first; yasan hakan na nufin yana haihuwa kenan, second; ba lalle bane Laila ta bar cikin tunda ta nuna ta tsani haihuwa a yanzu. Wannan mixed feelings d’inne yasa hawaye ya zuba a k’uncinsa amma nan take ya goge fuskarsa ta zama normal tamkar bashi bane yayi losing guard ba. “Ya zaki yi da cikin?” Ya yiwa Laila tambayar da take tsoron ji domin amsarta bata da dad’in sauraro ga Haydar. In-Ina ta fara ta rasa me zata fad’a guda d’aya tak’amaimai, “Shine nace zamu yi magana tunda kwanaki kace ka hak’ura da maganar haihuwar, kenan yanzu ma maganar bata canja ba. Haydar ina fatan zaka mini kyakkyawan fahimta?” Gyad’a kai yayi ya hard’e hannayenshi a k’irjinshi yace, “Ina jinki.” Shiru ta sake yi wannan karon itace ta fara hawaye kana ta matso daf dashi tace, “Zan zubar da cikin.” Mummunan kallon da bata ta6a ganin Haydar yayi mata ba wannan karon shi ta gani a kwayar idanunsa, numfashinsa ne yake fita da sauri k’irjinshi na hawa da sauk’a dalilin bak’in cikin kalaman Laila da kuma tausayin kanshi da yake ji. Nuna Laila yayi da yatsa ya fara magana cikin murya mai amo, “Karki kuskura ki kashe mini d’ana Laila, domin daki kasheshi gwanda ni kin kasheni.” Kamar walkiya kuma muryarsa ta koma ta rarrashi yaci gaba yana had’e hannayensa guri guda alamar rok’o, “Don girman Allah laifin mena miki da kike gudun haihuwa dani Laila? Me kuka zan miki kiyi hak’uri ki bar mini d’ana ya fito duniya? Wallahi zan miki duk abunda kike so zan kuma nuna miki son da ba’a ta6a yiwa wani kamarsa ba in har kika bar cikin nan Laila. Ki tausaya mini ki cika mini wannan babban burin nawa.” Zuciyarta ce ta k’arye ganin Haydar na zubar kwalla har yana k’ok’arin sauk’owa daga kan kujerar zai rok’eta, itama hawayen ta fara tana girgiza mishi kai amma bai daina magana ba, “Na rantse zan kareki daga duk wanda zai miki ba’a akan cikin nan Laila, Karki bari maganar mutane ya hanaki rainon albarkar aurenmu domin d’an halal ne ba shege ba. Ki tausaya mini don Allah Laila.” Ya k’arisa maganan yana rik’o hannayenta duka biyu fuskarsa abar tausayi. “Haydar shine maganan da nake son muyi tun d’azu saboda kai da kanka kace ka hak’ura….” bata k’arisa ba ya katseta. “Saboda a wancan lokacin baki da ciki ne Laila, amma yanzu ga cikin a jikinki and it will kill me idan kika ce zaki zubar dashi.” “I’m sorry Haydar, amma bazan zauna da cikin nan ba. We have to face reality saboda tun farko na nuna maka bana son haihuwa kai kuma ka nuna mini kana so. Wannan shine abunda nake jin haushi akai saboda munyi aure cikin rushing ba tare da munyi wannan maganar mai muhimmancin ba. It has to be done and I’m sorry.” A hankali ya d’age hannunsa daga na Laila fuskarsa with so much hurt yayin da zuciyarsa yake jin kamar ana hura mata wuta. Nan take yaji gumi na karyo mishi yayi saurin tashi tsaye yayi hanyar d’akinsa na daa. Har yaje bakin k’ofa ya tsaya ya juyo ya dubi Laila wacce itama a cikin tashin hankalin take, yace, “Idan har zaki iya kashe abunda yake cikinki duk soyayyar da kike nuna mini k’aryace. Sannan wallahi kika kuskura kika cire cikin nan daga ni har ke baza mu ji dad’in abunda zai biyo baya ba.” “Aure zaka ce zaka k’ara ko?” Ta tambayeshi kafin ya bud’e falon. “Wannan mai sauk’in kika fad’a.” Ya bata amsa yana shigewa ya rufe k’ofar ya barta zuciyarta na dukan uku-uku tana tunanin me zai iya aikatawa. Me zai mata daya wuce yace zai k’ara aure? Kenan abunda zai mata zai fi haka? Rabuwa da ita zai yi kenan? Shin Haydar zai iya rabuwa da ita? Wannan karon tasan ta wuce gona da iri, sannan tana tsoron abunda zai faru dasu. Haydar yana shiga falon ya zauna a kujera ya dafe kanshi da hannunsa biyu zuciyarsa na tafarfasa, Laila tana son 6aro musu aiki, idan kuma ta aikata abunda tace zata yi dukansu zasu yi dana sani. Haka Haydar yayi ta kwancewa yana sak’awa domin yayi tunanin ya kai k’ararta gun mahaifiyarta tunda ya lura tana tsoronta. Da asuba Laila na zaune akan sallaya ta gama sallah Haydar ya shigo d’aki yana d’aukan kayanshi. “Ina kwana?” Ta gaisheshi kamar yanda take yi kullum. “Lafiya.” Ya bata amsa a takaice kana ya shiga band’aki ya d’auki brush d’insa ya fita. K’arfe bakwai da rabi ya shigo falon cikin shirin tafiya office ya samu Laila na jera abinci a kan dinning table yace, “Kin hak’ura ko har yanzu kina kan bakanki na kashe mini d’a?” “Ka daina kiran kisa kamar wuk’a zan d’auka in kashe mutum, sannan cikin wata d’aya ne wanda ko fara mishi halitta ba’a yi ba balle a busa mishi rai.” Ta fad’i hakan cikin 6acin rai ganin yana k’ok’arin kiranta murderer. “Duk d’aya ne. Ki bani amsa.” “Ban fasa ba.” “Then ki saurari hukuncin da zan yanke.” Ya fice daga falon ba tare daya k’ara cewa komai ba. Hankalin Laila ne ya tashi tayi saurin samun guri ta zauna tana dafe k’irjinta, me Haydar zai iya aikatawa? Can kuma wata zuciyar ta fad’a mata cewa kuri kawai yake yi babu abunda zai yi saboda yana sonta ita kanta ta sani. Bata jima ba itama ta fita daga gidan zuwa asibiti tana fad’in a ranta duk abunda zai faru ya faru. Haydar yana fita ya wuce kai tsaye gidan Ammi, bayan ta bud’e mishi k’ofa ya shiga har d’akinta ya zauna akan kujera ya dafe kanshi, a haka tazo ta sameshi tana tambayarshi lafiya cikin tashin hankali. “Ki zauna tukun Ammi.” Yace da ita ba tare daya d’ago kanshi ba.Babu musu ta zauna a gefenshi amma bata fasa tambayarshi ba, “Ali me yake faruwa ne?” “Ammi jiya na miki k’arya don a tunanina zan shawo kan matsalar da nake ciki ba tare da kowa ya sani ba. Amma wannan karon abun yafi k’arfina domin Laila ce ke k’ok’arin zubar mini da cikina Ammi. Na rarrasheta har barazana na mata amma bata daddara ba zata kasheshi. Ammi kije gidan mahaifiyarta ki sanar mata halin da ake ciki ta hanata kafin lokaci ya k’ure tunda ni ban isa in kafa mata doka ba.” “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Lailan ce ta fad’a maka da bakinta?” “Ehh.” Shiru Ammi tayi tana tunani yanda za’a 6ullowa wannan al’amarin, ba tare da an kai maganar gidansu ba. “Nasan Laila zata ji maganata bazata tsalleka ba, mik’o mini wayata a k’ark’ashin pillow in kirata. D’auko mata wayar yayi yana fatan Laila taji kunyar Ammi ta bar mishi d’anshi da rai. Ammi ta kira layin Laila amma aka ce mata wayar a kashe. Haydar yana jin haka hankalinshi ya k’ara tashi domin yasan ta kashe wayar ne don kar a nemeta. “Ammi kin gani ko? Ta kashe wayarta ta tafi.” Yanda yayi maganar sosai ya bawa Ammi tausayi domin tasan yana mugun son yara, yasha fad’a mata cewa zai cika mata gida da jikoki sai ta ture saboda baya son ya k’arisa rayuwarsa bai ganshi cikin zuriyarsa ba. “Yanzu ko naje gidan nasu mahaifiyarta bazata sameta a waya ba Haydar tunda ta kashe, ka koma gida ka duba in bata tafi ba ka d’aukota ka kaita gidan nasu sai kuyi maganan a can.” “Ammi ni nasan Laila ta bar gidan amma bazan miki musu ba zan je na duba, amma kema kije gidan nasu ko akwai abunda za’a yi.” Yayi maganar kamar zai yi kuka. Ammi shiru tayi tana kallon yanda d’anta ya birkice lokaci d’aya, tausayinshi ne taji sosai har ta fara dana sanin rabashi da abunda yake so a yanzu, sai dai tayi hakan ne don shi ya rayu ba tare daya gane cewa itama tayi sacrificing wani sashe ne na rayuwarta ba. A k’ofar gidan Ya Madu Haydar ya sauk’e Ammi kana ya shigar da ita har sashen Ummii ya barta a tsakar gidan tana sallama. Daga ciki aka amsa mata tare da mata iso ta kutsa kai cikin falon da d’an murmushin ta, sai dai Matar data gani zaune a kujera yasa ta d’auke fara’arta lokaci guda cikin kid’imewa. “Suwaiba?” Shine abunda Ummii ta fad’a tana tashi tsaye Ya Madu dake zaune a gefenta yayi saurin rik’ota don kar ta fad’i dalilin ba lafiya bane ya isheta. “Ummii lafiya? Kin santa ne?” Madu ya mata tambayar yana kallon Ammi da har lokacin ta kasa furta ko kalma d’aya. “Suwaiba ce, Suwaiba nake gani Madu. ‘Yata ce, baka ganeta ba?” Ta fad’i hakan tana takawa kusa da ita tamkar bata gaskata idanunta ba. Madu da dama bincikensa akan Haydar yasa ya gane Ammi yace, “Ummii wannan ai mahaifiyar mijin Laila ce ba wacce kike tunani ne ba.” “Taimaka mini in zauna Madu ina jin hajijiya.” Fad’in Ummii ba tare data k’arisa gurin Ammi ba dalilin sarawan da kanta ya mata nan take. Haydar gida ya koma amma bai samu Laila ba kamar yanda yake zato duk da cewa wani gefe na zuciyarsa na fad’a mishi tana nan. “Shikenan ta tafi.” Ya furta yana lalumo wayarshi ya kira Mas’ud wanda babu 6ata lokaci ya d’auka amma muryanshi a ciki da alamar bacci yake yi yace, “Kai baka gaji bane da ba zaka kwanta kayi bacci ba?” “Mas’ud wani asibiti Laila take zuwa in bata da lafiya?” “Bata da lafiya ne? Meya sameta?” Shine abunda ya tambaya yana sauk’owa daga gadonshi har yana k’ok’arin fad’uwa. “Lafiyanta kalau amma ta tafi zubar da cikina ne.” “Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.” “Ka fad’a mini wani asibiti take zuwa?” Ya k’ara maimaita tambayan cikin gaggawa domin baya son 6ata lokaci. “Asibitin da aka kwatar da Abul, ka jirani…..” bai k’arisa maganan ba Haydar ya kashe wayarshi yayi saurin fita daga gidan ya shiga motarshi kamar wanda bashi da hankali a jikinshi. Yanda yake sharara gudu a kan titi saura kad’an ya had’a hatsari amma a haka ya isa asibitin cikin mintuna bakwai, bai yi parking mai kyau ba ya fito yayi cikin asibitin zuwa office d’in Doctor don watakila a nan zai samu Laila. Bai kwankwasa ba ya bud’e k’ofar ya shiga ya tsaya a gurin yana kallon abunda yake faruwa. Laila ce kwance akan gado yayin da Doctor da Nurse d’aya mace suke kanta suna mata wani abu tana hawaye. “Shikenan kin zubar kin huta Laila.” Shine abunda ya fad’a suka juyo suna kallonshi idanunshi sun kad’a sun yi ja. Cikin sauri ya fita daga office d’in ya koma bakin motarsa yana jin duniyar gaba d’aya ma ta fita a kanshi. Hawaye masu zafi ne suka sauk’a kan k’uncinsa yayi saurin gogewa amma bai hana wasu zubowa ba. Minti d’aya da haka Mas’ud yayi parking a gefenshi ya fito daga motarshi yana cewa, “Ina Lailan?” “Ban zo da wuri ba, sun cire mata cikin.” Amsar da Haydar ya bashi kenan yana share hawayen fuskarsa. “Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un.” Mas’ud kasa cewa komai yayi saboda yasan wannan karon Yayarshi ta kai mak’ura, kuma ta cancanci duk hukuncin da za’a mata. “Kayi hak’uri Haydar.” “Idan kaine hakan ya faru da kai ya zaka yi? Shiru Mas’ud yayi domin yasan zai iya dukan mace idan ta mishi haka, sai dai bazai furtawa Haydar hakan ba saboda yayarshi ce ta aikata. “Kayi hak’uri.” Kawai ya k’ara nanata mishi yana dafa kafad’arshi ba don hak’urin da yake bashi zai sa yaji sassauci a zuciyarsa ba. Wayar Mas’ud ce ta fara k’ara ya duba yaga sunan yayansu Madu, da kamar bazai d’auka ba amma yayi tunanin ko jikin Ummii ne ya tashi. Yana d’aukan yaji muryar Madu na cewa, “Kaje gidan Laila ku zo gida yanzu.” “Ummii ce bata da lafiya?” Mas’ud yayi tambayar cikin tashin hankali domin ko Ummii bata da lafiya ba’a ce mishi yazo gida sai dai a fad’a mishi nan take. Ko dai wani abun ne ya sameta? “Tana lafiya, ita ke nemanku.”Bai jira me Mas’ud zai ce ba ya kashe wayarsa. Mas’ud da hankalinshi bai kwanta da wannan kiran ba yace, “Haydar zamu je gida Ummii tana nemanmu ni da Laila, Inaga gidan ba lafiya ne.” Haydar na jin hakan ya tuno ya bar Amminshi a can yace, “To.” Kana ya kunna motarshi ya fita daga asibitin domin d’auko Ammi saboda babu amfanin zamanta a can. Mas’ud kuma shiga cikin asibitin yayi ya duba in zubar da cikin da Laila tayi bai fara galabaitar da ita ba su tafi gida.
Mum Fateey 👌



