Page 62
“Na shiga uku, mama, dan Allah a taimakeni, ƙonewa nake yi fa”
“Ai da ni ki ka yi niyyar ƙonawa, sai dai mu ƙone tare” ya haɗa hannayenta ya riƙe da hannu ɗaya, ya cigaba da zuba mata ruwan har a fuskarta.
Ta dinga mutsu-mutsu ta tashi, amma abu ya gagara, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa, sai ta hau kuka, tana yi masa magiya, a kan ya ƙyaleta.
“Har da sha mini toothpaste ko, saboda ke ƙazama ce”.
“Ni ban sha ba”.
“Ai ina jin duk abun da ki ke cewa, idan mu ka gama ƙonewar, sai mu yi jinya tare ”
Cikin kuka ta ce “Dan girman Allah ka yi haƙuri, fata ta zata kwashe, dan Allah ka yi haƙuri”.
“Ai baki isa ba, ni zaki ƙona da ruwan zafi ki huta ko?”.
“A’a ba haka nake nufi ba, dan Allah ka yi haƙuri “.
“Ni sharifi ne, ba abun da ruwan zai yi mini, ke da ki ka shirya ramin muguntarki, gashi kin faɗa”.
Ganin ta na kuka wiwi, ya sanya ya cikata, ta tashi da sauri, ta fice daga bath ɗin, jikinta na tsuma ta tafi ɗakinta, ta tuɓe kayan a tsakar ɗakin, ta zura da gudu toilet, ta sakarwa kan ta shower, jikinta yayi ja, ta zauna a toilet ta cigaba da kuka tana faɗin “Wallahi ba zan yafe ba, wuta balbalin bala’i”
Sai da ta daina jin zafi, sannan ta fito ta ɗaura towel.
Duba jikinta take yi, tana duba wa ta ga, ko fatarta za ta kwashe, cikin ikon Allah ba abun da ta yi.
“Wato shi ba ma ya jin zafin ruwan, amma ni ya ƙona ni, zai gane ni ya taɓa, sai na rama, har da wani rungumeni saboda tsabar rashin sanin abun da ya dace, Innalillahi Allah ya sa kar a gane idan na fita, ya kuma riƙe mini hannu na kasa guduwa”. Ta saka hannu ta toshe bakinta ta ce “Astagfirullah, Allah ka yafe mini”.
Sai kuma ta tuna abun da ya yi mata na cewa, ba ta da nono.
Ta kalli jikinta a mudubi, ta ɗan bankaɗa towel ɗin ta kalli ƙirjinta, ta ce “Saboda tsabar saka ido, wai nonona ne bai fi wake ba, mutumin nan ya cuceni, wato kallona ma yake yi haka? To saboda ba ni da su ake cewa ni ba mace ba ce? To na ga ma ba sai mutum ya haihu ba suke da amfani? Amma bakomai, Allah ya sa su fito mini, na huta da gori. Kai Astagfirullah, in rasa mai zan roƙi Allah sai wannan abun, Allah na tuba ka yafe mini. Amma wallahi sai na faɗi abun da mutumin nan yake yi mini, tun wuri ayi mini tsakani da shi, a taka masa burki, kar ya sake rungume ni”.
Sai da ta gama surutanta ita da mudubi, sannan ta tashi ta shafa mai ta saka kaya.
Ta daɗe a ɗakinta, sannan ta fita, ta tarar shi tuni ya fice, ta kwaso kayan gyaran ɗakin, ta ce yayi wa kansa dan ba za ta gyara ba.
Ba uwani ce zaune a ɗakin su, tana waya, ita da Samha.
“Wai haryanzu babu sani muhimmin bayani a kan in da zamansu ya dosa, ba kya bani wani update”.
“Ranki ya daɗe, su suna saman bene, mu muna ƙasa, bana iya sanin me yake faruwa”.
“Dole ki din ga bibiya ki sani, bamu saka kin yi faɗi tashi, ta amince ki je gidan ki zauna ba domin ki je ki miƙe ƙafa ba, biyanki zamu din ga yi, dole ki yi mana aiki yadda ya dace, ba kuma iya leƙen asiri ba, ki yi iya ƙoƙarin ki, wurin haɗa husuma a cikin gidan nan, ki nuna mata kin fita daɗewa a duniya, dole ta fito ta bar gidan nan”.
“In sha Allah uwa ɗakina, za ayi yadda ki ka ce, kar ki damu”.
“Ina saurarenki” Samha ta katse wayarta.
Rumaisa kuwa kitchen ɗin ƙasan ta shiga, Aisya da barira suna ta wanke-wanke.
Rumaisa ta ce “Ina kwananku”
Cikin sauri suka risuna suna gaisheta.
Rumaisa ta ce “Dan Allah ku daina gaisheni, wai ba ku ga ni ƙarama ba ce?”.
Asiya ta ce “Ranki ya daɗe, ai Allah ya riga ya baki girma dole a biki, kuma ke matar basarake ce, dole a girmamaki”.
Rumaisa ta yi murmushi ta ce “Kunya ku ke bani ne”
“Ba wani abu, ko wani abun za ayi mikk?”
Ruma ta ce “A’a, girkin rana zan yi, kar ku dafa abinci da mu, ku yi daga naku, sai na sauran masu aikin”.
Barira ta ce “To, amma ba abun da zamu tayaki?”.
Rumaisa ta ce “Bakomai, Anty Asiya, dan Allah ɗauko mini mai, ki tayani na kai sama, bari na tafi da wannan kayan”.
Asiya ta ce to.
Rumaisa na shirin fita, baba Uwani ta shigo tana tsuma, ta ce wa rumaisa “Amarya ba kya laifi, har mai gidan ya fita ne?”.
“Eh, ya fita”.
“Ina fatan dai ba wata matsala ko? Idan da wata matsalar zaki iya gaya mini, ni uwa ce a wurinki, kuma kin bar shi ya saukko shikaɗai, ai kamata ya yi ace ki na raka shi har mota”
Murmushin gefen baki rumaisa ta yi, ta wuce ta bar baba uwani.
A kitchen ɗin ta, Asiya ta sameta, ta ajiye mata man, har za ta tafi rumaisa ta ce “Anty Asiya, bari na baki hijjabi, da ke da Barira, a cikin kayan lefena suke, sun yi mini tsawo sosai”.
Asiya ta buɗe baki ta ce “Wane mu ranki ya daɗe, kayan lefenki fa”.
Ruma ta ce “menene a ciki, kyauta zan baku, sun yi mini tsawo”. Ta tafi ɗakinta, ta ɗaukko hijjabai a akwati ta kawowa Asiya.
Asiya ta din ga godiya, ruma ta ce “Dan Allah ki daina yi mini godiya, har kin saka na ji kunya, ba fa ni na saya ba, nima bani aka yi”.
Asiya ta ce “Haka ne, duk da haka dole na yi godiya, sannan dan Allah ranki ya daɗe, ki din ga ɗabi’ar matan sarakuna, girmanki ne dole a biki, kuma duk hukuncin da ki ka yanke a gidan nan dole a bi shi, amma wani abu nake son gaya miki, ban san ya zaki ji ba”.
Rumaisa ta ce “Gaya mini bakomai”.
“Ki yi hankali da taka tsantsan da baba uwani, amma kar ki ce na gaya miki dan Allah”.
Ruma ta ce “Ai ni dama ba ruwana da ita, bana son dariyar da take yi mini, bakomai in sha Allah na gode” Asiya ta juya ta sauka tana murna, yarinya ƙarama mai halin manya, ta san ta yi kyauta.
***
“Amma Jabir kana ganin abun da Adam ya yi ya kyauta, idan Fulani matarsa ce, mu kuma ƴan uwanta ne, shi jami’in tsaro ne nima haka? Dan meyasa bai ɗauki wani mataki a kan ɓatanta ba, meyasa bai gaya ba? Daga yin garkuwa da ita ya aka yi ya ɓoye wa duniya? Ya yi wa kansa adalci kenan, idan yana da gaskiya, ai tuntuni yakamata ya bayyana Yarinyar nan, ayi bincike a kanta, ko za a samu wani information ɗin”.
Jabir ya ce “Easy mana, haba Jamil, ina ga mun fi kowa sanin Adam, a ɓangaren taurin kai da zurfin ciki, duk familyn nan albarka, kowa ya san shi a kan haka, kai waye ya ce maka a zaune yake tun da ta ɓata? Adam ya shiga cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, tun bayan ɓatanta, kuma ba wai yana zaune ne kawai ba, da shi da gayen nan Bashir, da wasu daga ƴan sandan garin katsina, suka yi ta ƙoƙari a kan lamarin”.
“Amma ya aka yi kai ka sani, ni ban sani ba? Ina yayanta kuma jami’in tsaro kamar shi?”
“Saboda na fi ka kusanci da shi, na san halinsa tsaf, dan haka na fika iya zama da shi, shiyasa nake sanin abun da ba ka sani ba, yanzu abun da ya kamata shi ne, kamar yadda ya ce ka tamabyai mai girma turaki, ka yi masa zancen ka ji mai zai ce?”.
Jamil ya ce “Ai gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne ma, amma zan zurafafa bincike a kan lamarin nima”.
Jabir ya ce “Better”.
***
Ta window rumaisa ta leƙa, ta hango motar Adam, kusan biyar da rabi lokacin, Murmushin mugunta ta yi, ta koma ɗakinta ta yi zamanta, a sababbin litattafan da ya saya mata, na makaranta da za ta fara zuwa, ta ɗauki ɗaya da fensir, tana zane-zanenta.
A gajiye yake sosai, ya tarar da abincinsa a ɗakinsa, yanayin yadda aka ajiye abincin ya bashi mamaki, har da jug, jikinsa gaba ɗaya babu daɗi, dan haka ya yanke shawarar fara yin wanka, sannan ya ci Abincin.
Yayi wanka, ya sauya kaya, ya zo ya zauna, ya fara buɗe jug ɗin, yayi arba da ruwan famfo a ciki, shi da yake ajiye cartons na ruwa, da lemuka, ya buɗe abinci ya ga shinkafa fara ƙal, ga man ƙuli ga dunƙule da yaji.
Wani irin ƙululun takaici, ya ƙule masa wuya, ba ƙaramar yunwa yake ji ba, kuma ba ya cin abinci da mai da yaji. A fusace ya tashi ya fita, ya sauka ƙasa yana kiran baba uwani.
Ta fito a rikice tana tambayar ko lafiya?.
“Meyasa za a dafa mini abinci mai da yaji a gida? Idan akwai abun da babu, ba na ce a din ga gaya mini ba, dan me za a dafa mini mai da yaji?”.
Ta shiga tafa hannu ta ce “Wallahi ranka ya daɗe laifin matarka ne, babu yadda ban yi da ita ba, ta ce ita za ta yi maka girki, na ce mata ba ka cin abinci da mai da yaji, amma yarinyar nan ta ƙi yarda”.
Asiya ta kalli baba uwani, suna ƙasa basu san ma me ruma ta girka ba, balle baba uwani ta hanata, amma ta ce ta hanata ba ta hanu ba.
A fusace ya koma saman benen, baba uwani ta lallaɓa ta bi bayansa, tana cigaba da salallami.
A falo ya tarar da rumaisa ta fito, cikin fushi ya kalleta ya ce “Muzuru ne ni da zaki dafa abinci da mai da yaji ki ajiye mini?”.
“Papa meye a ciki, abinci ne fa?”.
“Shut up! Na yi kama da wanda zai ci abinci da mai da yaji ne?”.
Baba uwani ta ce “Ayi haƙuri mai gida, ba za ta sake ba, rashin sani ne, in sha Allah zan nunnuna mata abubuwan da yakamata ta sani, duk laifina ne, yarinta ce take damunta”
“Ba wani yarinta baba uwani, ai na ce girki ba huruminta bane ba, ta bari a din ga yi amma kasancewar, kunnen ƙashi ne da ita, ba za ta ji ba”.
Kuka rumaisa ta saka ta ce “Kuma sai na gaya wa ammi kana yi mini faɗa, idan na yi abu gwaleni ka ke yi”.
Taski ya yi ya , tafi ɗakinsa, yana barin falon rumaisa ta yi wa bayansa gwalo.
Ya fito da mukullin motarsa, ruma ta ce “Papa ina zaka?” Banza yayi mata ya sauka, baba uwani sai bashi haƙuri take yi.
Bayan ya sauka baba Uwani ta kalli rumaisa ta ce “Ranki ya daɗe, ai ba a….”
Rumaisa ta kasteta ta hanyar cewa “Idan mun yi faɗa, ba sai kin nema mini afuwa ba, yarinya ce ni ba mahaukaciya ba, kuma ina sane na yi hakan, na san ba ya cin abinci da mai, an gaya mini” galala baba uwani ta bi rumaisa da kallo, dama baki ne da ita haka? Kamar ba daga bakinta maganganun suka fito ba.
“Amma ƴar nan idan ki ka fusata shi, yana da larura fa”.
Rumaisa ta kalleta ta ce “Wace larurar?” Sai kuma ta tuna katoɓarar da ta yi ta ce “A’a bakomai”.
“Shikenan tun da ba zaki gaya mini ba , idan ya dawo sai na tambaye shi wace larurar ce da shi?”.
Baba uwani ta ce “Na shiga uku, da wasa nake yi miki, ba ya son ɓacin rai ne dai, dan Allah kar ki gaya masa”.
Rumaisa ta ce “Aini duk abun da aka gaya mini sai na bi diddigi, bana mantuwa” ta wuce ta bar baba uwani tana gumi da dana sanin maganar da ta yi.
***
Ƙishirwar son ganin Umar faruk, ta din ga damun zuciyar iman, hotunan biki din ga shiga, tana kallon hotunan duk da ya fito a ciki. Cikakken namiji mai cikar zati kamala, duk da ba fara’a yake yi ba, son kowa ne ƙin wanda ya rasa, namiji mai matuƙar jan ajinsa da tsare gida.
‘Na shigesu, me yake damuna ne?’
‘son wanda bai san kina yi ba, wanda ba ki da damar ki nuna masa hakan, wands tsantseninss da kamewarsa, da matsanancin kwarjininsa ba za su bari ma ya gane hakan ba’ wata zuciyar ta bata amsa.
Tashi zaune ta yi ta ajiye wayar, tare da furta ‘Allah ka iya mini” ga gefe guda Jabir yana ta hura wuta, wanda har Ammi ta fara ganewa.
Ta sake ɗaukar wayar, ta shiga what’s app ɗin ta, da ta yi saving number sa, da Yaya Omar, ta shiga chat, sai dai ta rasa mai za ta rubuta, ta buɗe hoton ka dp ɗin sa, hotonsa ne shi da hassan ɗin sa, wato yaya Abubakar.
Ta sake ajiye wayar, tana ajiyar zuciya.
***
Baba uwani addu’a ta din ga yi, Allah ya sa kar rumaisa, ta tambayi Adam, dan sai yanzu ta fara lura, yarinyar a tsaye take, gata dai yarinya amma alamu sun nuna ba ta ji.
Sai da aka yi sallar isha’i, Adam ya dawo, sai dai abun mamaki, ya tarar da abincin a ɗakinsa, amma a wannan karon har da miya, da salad da komai aka shirya masa.
Bai kula abincin ba, dan ya ciko cikinsa a gidan ammi.
Ya zauna babu jimawa, sai ga rumaisa ta shigo da sallama.
Ya shareta, ya fara ƙoƙarin buɗe laptop.
“Sannu da zuwa”
“Zo ki kwashe abincin nan, ki fita da shi”.
“Da miya ce fa yanzu”.
“Ba na ci”
Ta yi dariya ta ce “Na sha gaya maka, ka daina yanke hukunci da zuciyarka, ka din ga yi da ƙwaƙwalwarka, na san ba ka cin abinci da mai da yaji, Iman ta gaya mini, to in gaya maka na yi miya, ina sane na baka da mai da yaji, na san faɗa za ka yi, ka yi zuciya, na san halinka ai tas, to ranawa na yi, soyanin da ka yi da ruwan zafi da safe” ta yi maganar tana haƙiƙancewa.
Yayi mata shiru, bai ce uffan ba.
“Kuma saura abubuwan da ka ke yi mini, duk sai na rama”.
“To, idan kin gama, ki kwashe abincin ki je ki san yadda za ki yi da shi”
Ba ban haƙuri, ta kwashe ta fice abun ta
Ya dafe kansa, rumaisa gaba ɗayanta danger ce, yana duba nasihar ammi ne a kan yayi haƙuri da ita, duk abun da za ta yi masa, y din ga duba girman sadaukarwar, da ta yi masa. Gefe ga shawarar da bashir ya bashi kan Ya aure ta, a kan ya bi ta a hankali su saba, dan ya samu bayanan da yake son samu a wurinta, idan ya tsananta ba zai samu ba.
“Allah ka shiga lamarina” ya furta a hankali ya tashi ya bi bayanta.
Ya ganta tana hawowa sama, bai san me ta je yi ƙasa ba, ya ce “Ki shirya, gobe in Allah ya kaimu da safe, zan kai ki makaranta”
Ɓata fuska ta yi, dan sam ko zancen makaranta ba ta so. Ya juya ya koma ɗakinsa.
Da asuba ta yi wanka, ta yi salla, tana tantama dai-dai ma ta yi wankan, ko ba daidai ba, dan ba za ta iya tunawa complete yadda mama ta koya mata ba, kuma ita ba za ta tambayi takawa ba.
Haryanzu rumaisa tana ɗokin sababbin kayan kitchen, dan haka haryanzu ba ta gaji da shiga kitchen ta yi girki ba.
Ta dafa tea, ta fito da biscuit, ta nufo falo, takawa ta gani a kan dining, ga kayan karyawarsa a kan dining, baba uwani kuma durƙushe a gabansa, ba ta san me take ce masa ba.
Kai tsaye ta nufi dining ɗin, ba ta kula su ba, ta je ta hau saman dining table abun ta, ta fara ƙoƙarin haɗa tea.
Baba uwani ta yi shiru, ta daina maganar da take yi.
“Barka da safiya ranki ya daɗe”.
Rumaisa ta ce “Yauwwa sannu”.
“Meye haka, zaki hau saman dining?”.
“Idan na zauna a kan kujera, bana jin daɗin zama a kan tebur ɗin, gara na hau sama, ya fi daɗi, ka san babu a house”.
Ya girgiza kai ya ce wa baba uwani, “Je ki kawai, ma ƙarasa maganar”.
Tunani rumaisa take yi, me baba uwani take gaya masa, da ba za a faɗa a gabanta ba.
“Haɗa mini tea zan karya, ki je ki ɗauki jakarki mu tafi”
“Ni na kawo maka da zan haɗa maka, ita wadda ta kawo makan ta haɗa maka mana”
Hannu ya saka ya janyo ta ta baya, ya jawota ta ƙeya tana kallo fuskarsa.
Ya ce “Da ni ki ke?”.
“A’a da kaina nake” ya hankaɗata ta tashi zaune, tana ƙiƙƙifta id.
Ta janyo kayan tean, ta fara haɗa masa, tana yi tana tura baki ta miƙa masa.
Ita kuma ta yi ƙerere a kan table, tana karyawa.
Ba ta gama na ta ciye-ciyen ba, ta ji ta ƙoshi, ta tashi ta kwashe kayan.
Sai wurin ƙarfe tara da rabi, sannan suka fita, ya tafi kaita makaranta.
Tsari da ginin makarantar, ba ƙaramin burge rumaisa ya yi ba, ta tabattar wa da kanta, akwai banbanci a tsakanin makarantarsu, da wannan, hatta ajinsu, basu da yawa, ga kujeru masu kyau, ga fankoki ko ina ga kayan wasa, ajinsu har da projector, da ake haska musu komai, duk wani abu na koyo da koyarwa akwai makarantar nan, makarantar ta burge rumaisa.
Kan takawa ya tafi, sai da aka kai shi har ajin su rumaisa, ya kalli ruma ya ce “Yau ga ki a makarantar ƴaƴan ɓarayi da suke sace muku kuɗi suna karatu. Sannan ba zan lamunci ina biyan kuɗin makaranta in tarar ba kya karatu ba, kullum zan din ga tambayarki me aka koya muku. Ban da surutun banza, da ciye-ciye. Na bayar da ordern abinci a wani restaurant, za su kawo miki abincin break, tun da kin ce ke ba za a dafa a gida ki ci ba”.
“To, kai zaka zo ka ɗaukeni, ko gida zan tafi?”.
“Dama ke ki ka kawo kanki?”
“Ahh na san hali ne, kar ka tafi ka barni, ka ga kayan wasa a makarantar nan, zan sha lilo, idan na din ga hawa ina sufa….”
“Ba shi na kawo ki yi ba, karatu zaki yi, wuce ki shiga aji”
Rumaisa ta shiga ajin, tana ƙarewa ajin na su kallo.
***
Takawa kuwa da ya tafi hanya, Bashir ya kira a waya, ya ce masa zai shiga bamfai su haɗu su yi magana.
Haka kuwa aka yi, ya haɗu da Bashir, sai dai bai shiga ciki ba, a shiya fito haraba, suka haɗu.
“Allah ya taimake ka, ya amarya yaushe za a gayyaceni cin abincin amarya ne?” Yayi maganar cikin zolaya.
Adam ya ce “Idan ma da wasa ka ke yi, to ta iya girki”.
“Ahha haba dai?”
“Ka bari kawai bashir, yarinyar nan caza mini kai kawai take yi, Ammi ta bata masu aiki, amma ta ce kar su kuma dafa abinci su kai mata, wai kar ayi mata asiri. Jiya fa horon yunwa ta yi mini, mun samu saɓani da safe, na fita aiki ta hana ayi girki, wai ta dafa mai da yaji ta bani, na yi magana, wai ramawa ta yi. Wallahi haƙurina na daf da ƙarewa, duk maganar da ta zo bakinta, idan zan mutu haka za ta faɗa mini”
“Adam, sai ka yi haƙuri, ka san yadda yarinyar nan take tun farko, kuma ka san ba shiri ku ke yi ba, dole ka yi haƙuri da ita, idan ka nuna mata halin muzurai, ba zaka samu abun da ka ke so ba”.
Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce “Na gaji ne, gashi familynmu, sun fara yar mata da maganganu, ka san ba ta da kunya ba za ta yi shiru ba. Ga matar da take tare da ita tana yi mana aiki, baba Uwani na san zaka santa, ita ma sun fara faɗa, ita duk abun da yake dama to ita hagu za ta yi”.
Bashir ya yi dariya ya ce “A dai ƙara haƙuri, zai wuce in sha Allah”.
“To, Allah ya sa, gata can dai na kaita makaranta. Jabir ya gaya wa Jamil rumaisa ce yarinyar da ta tsinci sabir, ya kuma tayar da jijiyoyin wuya a kan, dan me na ɓoye masa yana jami’in tsaro kuma yayanta. Abun da nake so da kai shi ne, ko da zance zai zo, ya san tare da kai mu ke bincike, kar ka gaya masa komai”.
Bashir ya ce “In sha Allah, ba zan bayar da wata ƙofa na kowane bayani ba, sai mun yi nasara in sha Allah”.
“Allah ya amince, na gode sosai ” suka yi sallama Adam ya tafi.
Da daddare bayan ta dawo, tana ta murna, ta sha lilo har ta gaji, sai dai ba ta gane turancin da ake yi, dan malamansu har da turawa.
Tana ɗakinta, ta baje textbooks ɗin aka bata tana kallon hotuna, Adam ya shigo hannunsa riƙe da wayarsa, rumaisa na ɗaga kai ta kalli takawa, ta yi sauri ta rufe idonta, da hannunta, saboda daga shi sai dogon wando babu ko riga a jikinsa.
“Gaskiya ka daina shigo mini ɗaki tsirara”
“Dalla karɓi” yayi maganar a kausashe, ta ɗan zame hannunta ɗaya ta karɓi wayar, ta duba ta ga kira ne, ta saka a kunnenta.
“Ƙanwar maza, ƙanwar maza”.
“Yaya Aliyu, ashe baku manta da ni ba, tun ina kuka har na daina”.
“Saboda kin samu duniya ko?”.
Ruma ta ce “Ba wata duniya, ina mama? Ba za ta zo ba ko?”.
“Mijinki sun yi waya da mama, ta ce kar a kawo ki”
“To Meyasa, bani ita”.
Mama ta karɓi wayar ta yi sallama ta ce “Ƴar auta”.
“Mama shi ne ki ka ƙi zuwa, kuma ki ka ce kar a kawoni”.
Mama ta ce “Ke tafi can, ba gaki nan ba abun da ya same ki ba”.
“Ni dai dan Allah ki zo, ko in ta yi masa kuka, tun da kin fi son sa”
Mama ta ce “Shi wa?”.
“Mijina” ta bata amsa kai tsaye.
“Sannu mara kunya, ai dama ban ce nawa ba ne naki ne”.
Ruma ta ce “Mama albishirinki”.
“Goro”
“Kin ga haɗaɗiyar makarantar da ya kaini, kamar a turai, kin ga liluka kuwa? Ga fankoki har da malamai turawa, baki gani ba, baki taɓa zuwa gidana ba ma, gidana haɗaɗɗe, duk ya sai kayan daɗi ya zuba mini”
Mama ta ce “Sai ki je ki same shi, ki yi masa godiya, dan na san baki yi ba”
“Taɓ, mama yaushe zaki zo to?”
“A’a ni ba zan zo gidanki ba, amma dai idan ya kawo ki shikenan”. Za ta yi wa mama taɓara, mama ta kashe wayar.
Rumasai ta share hawayenta, ta bishi ɗakinsa, ta tarar yana banɗakin, ta ajiye masa wayarsa ta fice.
Kwanci tashi asarar mai rai, yau juma’a rumaisa kwana biyar da fara zuwanta makaranta, kuma wata guda cif, da ɗaura mata aure.
Takawa ya ɗaukota daga makaranta, ta ga ya canza hanya, maimakon su tafi gida.
“Ina kuma zamu je?”.
“Sayar da ke, na yi tsafi da ke, kamar yadda aka ce na yi da aisha” ya bata amsa.
“To ai dai bani na faɗa ba ko?”
Tana gane gidansu zai kaita ta ce “Yeee zan ga Ammi zan ga Sabir da Anty Iman”.
Da haka suka ƙarasa, cikin murna ta riga shi shiga sashin Ammi.
“Oyoyo ga ruma”
“Ammi, kin ga na fara zuwa makaranta, kin ga jakata”
Ammi ta yi murmushi, ta ce “Masha Allah, Allah Ya sanya albarka”
Iman ta ce “Congratulations Anty rumaisa”.
“Thank you anty iman”
Takawa ya shigo, ya tarar da rumaisa a kusa da ammi tana nuna mata litattafanta.
Wato rumaisa ko kumyar nan ta sirka ba ta da ita.
“Ammi ina Sabir?”.
Ammi ta ce “Yayi bacci”
“To bari in gama nuna miki litattafaina, sai na je na ganshi”.
Ammi ta dubi Adam ta ga yanayinsa, kamar mara lafiya, ta ce “Takawarka lafiya, ya aka yi ne? Na ga yanayin ka kamar akwai damuwa”
Ya ce “Bakomai” tare da kashingiɗa.
Ta kalli rumaisa ta ce “Rumaisa, ko akwai matsala ne?”.
Ruma ta gyara zamanta ta ce “Eh, dama ƙararsa zan kawo miki tun rannan, dan dai bamu zo ba ne, na ce sai na gaya miki, kin ce duk abun da yayi mini na gaya miki”.
Ammi ta ce “Subhanallah, meyafaru?”
Ya kalli rumaisa yana jiran ya ji me za ta ce “Wai cewa yayi zai ƙara aure, saboda ba ni da nono!!!”
Tirƙashi!.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.