Halysaah Page 85 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 85…Khaleesat bata yi zaton gidan da Jay ya siya ma iyayenta yafi yanda ta tsammacesa a hoto ba, she was totally speechless don gida ne lafiyayye kuma a unguwa me kyau sosai, babu abinda ba a zuba a cikin gidan ba, ga wuta da ruwa 24/7 don Solar ne a gidan, maimakon tayi farin ciki sai ta zamto so emotional tana kara jin Jay a ranta, tasan a yanxu dai bata da enough words da zata yi amfani da su wajen fara yi masa godiya tayi expressing how grateful she is, balle ko zata yi hakan ma bazai saurareta ba, Nenne kam baki yaki rufuwa don farin ciki tasa masa albarka tare da iyayensa yafi cikin Kwando, Chalet din da ta mayar nata tsabar murna bata kwana ciki ba, a main building din gidan ta kwana a parlor kan lallausan bargo da sabon Pillow ga AC da ta sa aka kure mata, ai ko da asuba ta tashi hanci duk sun toshe, sai ta ɓige da cewa yawace yawacen da suka yi jiya cikin gari da Farida ne ƙuran garin Kano ya saka mata mura, gari na wayewa Nenne aka dinga goge goge da share share a parlon duk da babu ko digon datti, Aunty Farida da Khaleesat kuma na kitchen suna girka breakfast don sun taho da few food stuffs dinsu na can gidan, Umma ta fito parlor zata amshi wayar Aunty Farida ta kira Malam Ali don nata babu kati, Nenne ta matse tsumman hannunta da take goge tsadaddun kujerun parlorn da shi tace “Kinga dai Ali da ya dawo nan ya kwana cikin ni’imar Ubangiji gwara ya kwana a takure cikin zafi da sauron Mariri, ko da yake ban ga laifin sa ba kinga dole zai yi ma su Zubaida rakiya zuwa tasha kuma zai ɗan hada masu hatsin da za su tafi da shi tunda su ma suna da hakki gwara ya sallamesu cikin mutumci su tafi” Ita dai Umma bata ce komai ba, Nenne tayi kwafa tana ci gaba da goge gogenta tace “Dama ai ance mahakurci mawadaci, yanxu da kika yi hakuri Zahra’u baki ga ribar hakuri ba? Ni nasan Allah bazai bar ki haka ba don hakurin ki abun dubawa ne, gashi yau dai kin ga riban hakurin ki, ni dai kullum addu’ata shine Allah Ubangiji ya albarkaci ‘ya yan da kika haifa ya tsare maki gabansu da bayansu, gashi wai tun Khaleesah bata fara aiki ba mun fara cin moriyarta saboda kyawawan halayyan uwarta da irin tarbiyyar da aka mata, cikin ruwan sanyi kuma Allah ya rabaki da matsiyatan kishiyoyin ki lafiya duk tuggun da suka maki ya kare kansu, ke kika ci riba” Umma dai ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba, amma da Nenne tasan action dinta na ƙin amincewa a taho da su Mama Zubaida jiya har baccin kirki sai da ya hanata da bata ce haka ba, gaba daya rasa sukuni tayi tana jin bata kyauta ma kanta ba tunda ita ma bata san Allah zai bada gidan nan ba, sannan ba dubaranta ko wayonta bane yasa Allah yayi mata hakan, yanxun ma wayar Aunty Farida da zata amsa Malam Ali take son kira tayi masa magana ko zai samu ya lallaba Nenne tayi hakuri su dawo gidan kawai, gudun tsine mata da Nenne zata yi yasa bata gaya mata abinda ke ranta ba kawai ta nufi kitchen ta tambayi Aunty Farida inda wayarta yake, bayan Aunty Farida ta gaya mata ta juya ta bar kitchen din, Aunty Farida na kallon Khaleesat dake juya miyan kan wuta don shinkafa da miya suke dafawa for breakfast, tace “Ina jin ki Khaleesah” Khaleesat dai bata kalleta ba tana ci gaba da juya miyan a hankali tace “Haka muka yi da shi Aunty, ni dai ban ce masa komai ba har yanxu” Aunty Farida dake ta kallonta cikin sanyin murya tace “Amma kina ganin iyayensa za su amince masa cikin sauki duba da status dinki ga kuma irin gidan da ya fito Khaleesat? Bana son ki saka ranki da yawa cause anything can happen, kin ga dai ai baza a boye ma iyayensa status dinki ba a yanxu, in ma aka boye magana irin wannan baya buya Khaleesah” Khaleesat ta kasa kallon Aunty Farida amma sosai taji jikinta yayi sanyi, taji ƙafafuwanta sun kasa ci gaba da ɗaukan ta, all this while ita bata taɓa kawo wannan tunanin a rai ba ko don tasan babu abinda ya shiga tsakaninta da Abdul ne yasa hakan, to amma bayan ita da Abdul din wa ya san ba abinda ya shiga tsakanin su? Aunty Farida ta jingina jikin cabinet ita ma dai duk jikinta a sanyaye, she wish everything will be easy as it seems now, amma gidan sarauta abun su sai su, babu abinda ya kara kashe mata jiki sai zancen Hadiyah da kuma alakarsa da Hadiyar da Khaleesat ta gaya mata, amma don ta kwantar mata da hankali ta sauke ajiyar zuciya tace “Ki ci gaba da addu’a Khaleesat, Nima zan taya ki, Umma ma zan yi mata magana duk za mu taya ki da addu’a, Allah Ubangiji ya kawo komai da sauki, kuma Allah ya tabbatar da alkhairi” Har sannan Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta nufi kofa ta fita daga kitchen din, sai a sannan Khaleesat taji hawaye masu zafi sun zubo idonta, ta juya tana kallon windown kitchen din babu ko kiftawa, da Aunty Farida bata ankarar da ita ba da bazata taɓa hango kalubalen dake tattare da aurenta da Jay yace zai yi ba, she never saw all this coming, kasa controlling kanta tayi ta duka a hankali kitchen din hawaye na zubo mata, sai yanxu ta kara tabbatar da masifaffen son da take ma Jay a ranta, she can’t imagine loosing him, hade kanta tayi da gwiwa hawaye masu zafi na zubo mata tana shesshekan kuka…. Aunty Farida na shiga dakin Umma ta sameta tana waya da Malam Ali, hakan yasa ta juya ta bar dakin, sosai wannan maganar da Khaleesat tayi mata ya tsaya mata a rai, she don’t want her to go through another heartbreak, kuma ta lura tayi zurfi a son nasa ita ma with the way she reacted, tana shigowa parlor Nenne tace “Zuwa nan da anjima kadan fa za mu fara ganin yan uwa sun zo mana Allah ya sanya alkhairi Parida, er shinkafar nan zata isa a girka a ɗan tarfa ma kowa a kwano kuwa?” Aunty Farida tace “Idan mun karya za mu fita kasuwa da Khaleesat, da kudi a hannuna sai a siyo duk abubuwan da ya kamata….” Nenne tace “Allah Ubangiji dai ya baki miji nagari kema kiyi auren ki Parida, bauta kam kin bauta ma yayarki, abun ki bai rufe maki ido ba sam, kin rike zumunci gaskiya” Ita dai Aunty Farida kawai tayi murmushi bata ce komai ba, Nenne tace “Dama mun taho da tabarmin mu, su za a shimfida a tsakar gida babu shegen da zai shigo mana nan a lalata mana sabon waje, kowa yayi Allah ya sanya alkhairinsa daga tsakar gida ya kama gabansa” Wajen karfe goma da rabi Aunty Farida da Khaleesat suka bar gidan za su je kasuwa siyayya, Khaleesat har ta mance rabon ta shiga damuwa irin wannan da take ciki yanxu, sau biyu ta kira Jay daxu taga bai dauka ba shine damuwar nata ya linku akan wanda take ciki tun bayan maganganun Aunty Farida daxu a kitchen, Aunty Farida na kula da yanda tayi sanyi gaba daya bata da kuzari tun daxu, bayan sun shiga adaidaita Sahu da zai kai su kasuwan Aunty Farida tayi kasa da murya tace “Damuwa kike son sa ma kanki Khaleesat?” Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace “A’a Aunty” Da sauri ta kauda zancen tace “Safiyyah ce ma daxu ta min voice tana kuka wai kilan shirgata yayanta yayi, gashi ta saka ran dawowa, ni dama a raina nasan ba lallai ya barta ta dawo ba” Tana dariyar karfin hali ta kare maganar, Aunty Farida tace “Ai ko bai kyauta mata ba, Allah sarki baiwar Allah” Har suka isa kasuwan Khaleesat was trying to act alright, amma Aunty Farida tasan deceiving kanta kawai take, Aunty Farida bata zo kasuwa da Khaleesat with the expectation of her buying anything ba don bata san tana da kudi ba ma, ita dama Aunty Farida da dubu ɗari biyu ta shigo kasuwan domin ta ɗan tsintsintar masu abubuwan da za su bukata na gida, har da su Bucket da sabulu da omo da su tsintsiya da mop, duk dai wani abun amfanin gidan, sauran kudin kuma tayi maneji ta ɗan hada masu kayan abinci da cefane ko babu yawa, amma nan take Khaleesat tayi withdrawing 1M a kasuwan, don kudi ne sosai a account dinta wanda Jay ke tura mata a kai a kai na Uber da kuma wasu abubuwa idan tana bukata barin sanda ya dade a Nigeria bai dawo ba, sanda yake Nigeria kuma Ajay ma ya amshi account dinta during that period ya tura mata kudi multiple times for her transportation to school and in case she needs to get anything for herself, duk da abubuwa da yawa shi yake siya mata a lokacin, kuma in ya tashi tura mata kudin shi ma ba kudi kadan yake saka mata ba, sannan ga 5000 dollars da Mai martaba ya bata, dama Safiyyah taki amsan wanda ta bata a ciki, Jay kuma ya amshi kudin yayi mata transfer dinsa gaba daya a account dinta, ganin uban kudin da Khaleesat ta cire Aunty Farida ta fara fada tace “Baki da hankali ne? Ke da ba gama karatun kika yi ba zaki ciro wannan kudi haka” Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace “Aunty in babu ai bazan cire ba, akwai kudi a account din ne” Sai wajen karfe daya suka koma gida da siyayya maƙil, a compound suka tarar da yan zuwa sanya alkhairi Nenne ta shimfida masu tabarma ta hada kowa da pure water, tana zaune kan kujerar plastic ta ɗora kafa daya kan daya, ita ma Umma na zaune tsakar gidan don ta rasa yanda zata yi da Nenne, ko kadan bata ji dadin barin jama’a da tayi a tsakar gida ba taki bari su shiga cikin gidan. Nenne tayi kicin kicin da fuska don bata so su Aunty Farida sun shigo da kayan da suka siyo kan idon mutanen dake tsakar gidan ba, a haka dai su Islam da Noor suka dinga diban kayan da za su iya dauka suna kai wa cikin gidan, Khaleesat ta dau iya wanda zata iya dauka sannan ta wuce ciki ta tafi daki tayi wanka ta dauro alwala tayi sallah sannan ta kwanta, sosai hankalinta ke a tashe ganin Jay bai biyo kiranta ba har lkcn, Umma ta shigo daki tana kallonta tace “Khaleesah ke da ke karatu har yanzu menene na kashe kudi har haka?” Khaleesat ta kalli Umma tace “Na fa ce ma Aunty Farida akwai kudi a account din ne Umma” Umma tace “Toh Allah yayi albarka, ki tashi ki zubo abinci ki ci” Khaleesat tace “Anjima zan ci Umma” Umma tace “Allah ya kai mu” Daga haka ta fita daga dakin, Khaleesat ta koma a sanyaye ta kwanta, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a ranta, hawaye taji ya cika idonta ta rufe fuskarta da Pillow ta fara shesshekan kuka a hankali…. Nenne ta fita ta zagaye unguwan tana neman almajirai da za su kama buhunhunan shinkafar da su Aunty Farida suka siyo a shiga da shi kitchen, da kyar ta samo almajiran biyu ta dawo tana mitan su Mariri yaushe za a nemi almajirai a rasa, daya daga mutanen dake zaune tsakar gida tace “Ai da kin mana magana mu kama mu shiga da shi ciki Nenne” Nenne tayi banza da ita tana tafe almajiran na biye da ita a baya har aka shiga da buhunhunan kitchen, naira hamsin ta basu suka tsaya suna kallon ta, tace “Lafiya ku ke kallona haka?” Wata er cousin din Malam Ali tayi dariya tace “Ya masu kadan Nenne, ke baki ga unguwan ta masu kudi bace, ai hansin ta masu kadan” Nenne ta juya ta kalli almajiran baki bude, kafin tace komai Umma ta mika masu dari biyu su hada da Naira hamsin din, suka amsa suka fita daga gidan, Nenne ta kalli Umma tace “Kin ji almajirai kamar barayi, mu Mariri yaushe almajirai za su yi haka? Kudin ne ya maki yawa kika basu dari biyu, ai niyyar ce masu su shiga su fito da buhunhunan shinkafar nake da shi” Nenne bata rufe baki ba aka rafka sallama bakin gate, duk aka juya ana kallon gate din gidan sai ga Sha’awa da yan Mariri su hudu sun shigo cikin compound din kafafuwansu butu butu da ƙura, Nenne da ta girgiza sosai ganinsu tace “Su waye nake gani haka, daga ina?” Sha’awa na washe baki tace “Su mu ne Nenne, Sha’awa ce da su Maman Sagir da Maman Balki da Maman Shehu, sai sabuwa” Nenne da zufa ya keto mata ta ja kujera ta zauna da kyar tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, wa ya nuna maku gidan?” Ita kanta Umma was so shock amma hakan bai hanata dinga ce masu sannu da zuwa ba da murmushinta duk da gaba daya hankalinsu na kan Nenne da ta tsare su da tambayoyi cikin kidimewa, Sha’awa tace “Almajirin ki ne wai an taɓa zuwa da shi yayi share share da goge goge sanda aka siya gidan, ai ko ranan yayi ma Salisun Tabawa kwatancen gidan ashe Salisu sun taɓa zuwa aikin pilamba a wani gida a Tudun Yola, shi ne muka sa yayi mana kwatance, tun karfe sha dayan safe muke neman gidan sai da muka zaga kaf Tudun Yola muna cewa sabon gidan da aka tare jiya da daddare muke nema, da kyar wallahi aka gano gidan da taimakon wasu yara, ga uban kudin mota duk bamu san haka unguwan ke da nisa ba, ko sallan azahar bamu yi ba ga la’asar ta gabato” Nenne ta rike kai tace “Hu….huhu, ashe dama ƊanLami munafiki ne ɗan iska ban sani ba nake alaka da shi jama’a? Wa iyazubillahi” Ita dai Umma ta shimfida masu wani tabarma tana welcoming dinsu da fara’a kafin Nenne tayi recovering daga shock din da ta shiga ta fatattake su daga gidan don tsaf next action dinta kenan. Wajen karfe takwas na dare Jay ya shigo parlon Maminsa ta dalilin kiransa da tayi har sau biyu a waya, tun da ya shigo parlon take kallonsa har ya zauna, tace “Ina ka shiga ne tun daxu Jawwad?” Ya ajiye wayarsa ba tare da ya kalleta ba yace “Ina gidan ai” Mami tace “Duk na bi na damu kace zaka min magana me muhimmanci saboda kai ban je inda zan je ba yau amma don rashin sanin ciwon kai da ka tashi shigowa bangaren nan sai ka shigo min da Junaid, to da a gaban Junaid din kayi niyyar min magana saboda baka da sirrin kanka Jawwad? Ko har ka fesa masa ne shi” Ya daga kai ya kalleta, can yace “Ni ban san me Junaid yayi maki da yayi deserving wannan ill treatment din ba Mami, Billah bana jin dadin wannan abun da kike masa, beside ni na shigo da shi kinsan baya taɓa saka kansa a abinda bai shafesa ba ai, he is even sick but still followed me and you treated him that way, I wasn’t happy at all Mami, Ni Ajay na daukesa ne kamar brother dina da kika haifa bayan ni, kuma shi ma haka ya daukeni, then why all this Mami?” Mami ta katse sa tace “Toh ubana, dama ai ka saba zuba ma idonka toka ka gaya min son ran ka akan Junaid, I have no issue with Junaid coming to my part, my issue in here is u bringing him to my part when you know we have an important issue to discuss, kai abubuwa nawa ka sani a kansa? Ina ce kawai sai dai kaga yayi abun sa, Duk ya maida kai wani wanda bai san ciwon kansa ba yayi ta controlling dinka yanda ya ga dama, ya maida kai wawa, baka da kwakkwaran say din kanka sai abinda yace maka kayi, haba Jawwad, yaushe zaka yi hankali ne wai?” Jay bai sake ce mata komai ba a parlon yana kallon direction daban, tace “Me ya samesa da yake rashin lafiya? Shi kullum yana dawowa gidan nan sai yace rashin lafiya, meye ma’anar hakan?” Still Jay bai ce mata komai ba, Mami tace “To Allah ya basa lafiya, amma ya kamata ka gaya masa yaje kakarsa ta basa maganin baki, daga ya tsallaka kafa ya shigo gidan nan sai yace rashin lafiya, in kuma da wata manufar da yasa yake hakan it’s left to him” Jay was still silent, da ace akan wani abu daban ne ya bata rai haka da yanxu ta fara lallabasa tana kokarin ganin ya sake fuskarsa don babban damuwarta Jay ya ɓata rai, amma akan Ajay duk fushin da zai yi yayi zai sakko da kansa ba lallabasan da take yi, abun na bakanta mata rai yanda ya maida kansa kamar wawa wajen Ajay yana juyasa yanda ya ga dama, in Ajay yace kar yayi abu to fa abun nan komin kyansa bazai yi ba, in ko yace yayi to zai yi, ko kuma in tace yayi abu sai yace Ajay ya basa shawaran kar yayi saboda abu kaza, to ina dalili ita da ɗan ta, in kuma tace yayi sai yace ai Ajay yace kar yayi ya kuma zayyano mata reasons dinsa, Mami tace “To ka ci abinci kuwa? Ga abinci na ajiye maka tun daxu shiru shiru baka shigo ba” Jay yace “Na ci” Mami har ranta ta tsani abinda zai ɓata ma ɗan nata rai ko ya yake, ta kwantar da murya tace “To ina jin ka Son, maganar meye za mu yi, speak to me dear” Mikewa yayi ya dau wayarsa yace “I don’t want to talk about it now Mami” Yana fadin haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, wato yayi fushi ta taɓo kanin ubansa Ajay, Mami tace “Toh ga dai abincin idan kana bukata, ko kuma ka tafi maku da shi ku ci da Ajayn a can ɓangaren nasa” Tuni har ya fice daga parlon, Mami ta kyabe baki don ta san zai ma huce, anjima zata dau abincin ta kai masu can shi da Ajayn su karata. Jay na komawa bangaren Ajay ya tarar da Mai martaba zaune a parlon, zaunawa yayi gefen Ajay da ya ajiye PS Controller din hannunsa bayan mahaifin nasa ya shigo, Mai martaba na kallon Jay yace “Ashe jikin nasa ma yayi sauki” Jay ya sauke kansa yace “He is much better now ranka shi dade” Mai martaba ya jinjina kai yace “To maa sha Allah, ina jin Hajiya ma gobe zata shigo in sha Allah” Jay yace “Allah ya kawo ta lafiya” Mai martaba yace “Ya ku ka yi akan maganar yarinyar nan da Fulani?” Jay ya sauke kansa cikin ladabi yace “Anjima nake son zan mata magana ranka shi dade” Mai martaba yace “Alright then, sai ka gaya min duk yanda ku ka yi” Jay yace “In sha Allah ranka shi dade” Mai martaba ya kalli Ajay da kansa ke kasa, ya mike yace “Allah ya tashe mu lafiya” Duk suka amsa masa da “Ameen” Ya nufi kofa, Ajay ya dau fruit da yake sha kafin Abban nasa ya shigo ya ci gaba da sha, Jay ya duba wayarsa dake vibrate yaga Khaleesat ce ke kiransa, kallon screen din ya dinga yi don yana ta son zai kirata tun daxu but he was together with Ajay tun safe don in bashi da lafiya ya dinga yi ma mutane surutu kenan, kuma baya son Jay na nisa da shi, katse kiran nata yayi ya mike ya tafi kan kujera ya zauna sannan ya kira ta, tana picking yayi kasa da murya yanda ita kadai zata ji sa yace “Halysaah, I am sorry I didn’t call all through, ya kike ya gida?” Khaleesat dake sauraronsa tana jiran jin excuse dinsa tace “Lafiya lau” From her intonation he knows she is not happy, ya sake yin kasa da murya yace “I am so sorry Halysaah, Ajay ne ba shi da lafiya but he is better now, shi yasa kika ji ni shiru all through, hope you will forgive me?” Khaleesat tayi shiru jin abinda yace, can a hankali tace “To Allah ya basa lafiya, tun yaushe ne bashi da lafiya?” Jay yace “Da safe, amma yaji sauki ma” Tace “Ku na tare ne?” Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ɗan kalli Ajay yace “Nop” Tace “Toh Allah ya basa lafiya” Yace “Ameen, so ya su Umma and everyone back home, kaka tace gobe za ku koma Tudun Yolan ko?” Cikin sanyin murya Khaleesat tace “Ai mun ma koma jiya” Ya ɗan bude ido yace “Haba dai?” Ta gyada masa kai tace “Uhm” Mikewa yayi ya fita daga parlorn Ajay ya bi sa da ido, bayan Jay ya kulle kofar parlorn yana tafiya down the long hallway yace “So now tell me the truth gidan yayi maki Halysaah?” Kasa ce masa komai tayi, yace “Are you there Halysaah?” A sanyaye tace “Ban san me zan ce maka bane, i don’t even know where to start thanking you from….” katse ta yayi yace “Come off it pls Halysaah….” Hawaye taji ya taru idonta, yayi kasa da murya yace “I miss you soo much Halysaah” Tayi murmushi don bai san ta fi sa missing din da yake cewa ba, sun kusa minti ashirin suna waya daga karshe yace “Zan kira ki zuwa karfe goma da rabi in sha Allah Halysaah” Tace “Toh Allah ya kai mu” Yace “Ameen Dear” Bangaren Ajay ya koma suka ci gaba da game din da suke, wajen karfe goma saura Mami ta shigo parlorn Ajay tare da daya daga worker din palace din dake biye da ita da abinci, bayan worker din ta ajiye abincin ta gaida Ajay da Jay cikin ladabi sannan ta juya ta fita, a kujeran da Mai martaba ya zauna Mami ta zauna, Ajay ya gaisheta bayan ya ajiye Controller din hannunsa, Mami na kallonsa tace “Kai baza kaje kakarka ta nema maka maganin baki ba, ko baka gaji da ciwace ciwacen da kake a gidan nan ba, kowa ya bude baki yace Junaid, ko da yake maganinka kenan gwara kayi ta yin abin da za a dinga saka ka a bakin duniya, in zaka sauke wannan shegen girman kan naka ka bi mutane a yanda suke so ka zauna lafiya da su then you will be doing justice to ur self, in kuma kace baza ka bi su ba to ya rage naka” Shi dai Ajay bai kalli inda take ba, Jay kuwa sai kallon Mami yake cikin bacin rai, ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon, Ajay ya dau strawberry dinsa ya ƙishingiɗa ya ci gaba da sha… Karfe goma da minti sha biyar Jay ya bar bangaren Ajay bayan ya tuna yace ma Khaleesat zai kirata karfe goma da rabi sannan yana son discussing issue dinta da Mami a daren yau, yana barin parlon ko minti biyar ba ayi ba wayar Ajay ya fara ringing, ya kalli screen din wayar har kiran ya katse bai yi picking ba, ita din ce ke kiransa, sake kira tayi sai da ya kusa katsewa sannan ya dau wayar ya daga ya sa handsfree ya ajiye yana jiran jin me zata ce, daga daya bangaren tace “Good evening” Babu yabo babu fallasa yace “Wacece wannan?” Khaleesat ta hade rai kamar yana ganinta, can ta tura baki tace “To ai dai Housemate dina ne yace min baka da lafiya that is why I called to check on you” Ajay yace “I see… Sai dai in shi ne bashi da lafiya, ni kin ji alamar bani da lafiya?” Khaleesat ta ɗan taɓe baki tace “Toh ai shikenan, bye….” Zata katse wayar, Calmly taji yace “Kar ki kashe min waya Malama”*Halysaah is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa bello Jiddah* Ur evidence via 07087865788
