Halysaah Page 87 By Khaleesat Haydar
Mami ce zaune parlon Aunty cikin bacin rai ta kare maganar da take yi da cewa “Don haka nake rokon ki alfarman duk yanda za kiyi convincing Mai martaba ya rushe zancen ya nuna masa bai isa ya maida mu yara ba to kiyi, Mai martaba ya nuna masa ba wani yace lallai sai ya yi accepting auren Hadiyah da farko ba, kawai ni so nake a sace masa gwiwa a nuna maganar bazai taɓa yiwuwa ba, kinsan dai yana jin maganar mai martaba…” Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ba idan ina kokarin nuna maki illar alakar Jawwad da Junaid baki daukata serious ba, babu yanda banyi akan kiyi kokarin datse alakarsu ba amma kika ki daukar maganata da muhimmanci don baki son ɓata ma Jawwad rai, ai ba shi ya haife ki ba yau in kika ce baki son yana mu’amala da Junaid kika yi masa jan ido dolensa yaji maganar ki, yanxu dai ga irinta nan, kuma kamar yanda kika fada babu me zugasa sai Junaid, ai bai son ci gabansa tun ba yau nake kokarin fahimtar dake haka, yanxu baki ga Walid ko ga maciji basa yi da shi ba” Mami ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ban sake tabbatar da Junaid ɗan iska bane sai yau Fulani, nayi da na sanin katse alakarsu da Jawwad da ban yi ba ta karfi da yaji” Aunty ta gyara zama tace “Bana mancewa shekarun baya har ce maki nayi ko addu’a ne ayi don farrakasu amma kika ki daukar hakan da muhimmanci” Mami tace “A’a ni duk wata sabgar shirka babu ni a cikinsa….” Aunty ta katse ta da sauri tace “Kai haba, meye kuma shirka ana zaune qlau Fulani, in aka ce addu’a ai bai wuce a ja carbi ba a roki Allah, ko kuma ka saka malaman zaure su saka ka cikin addu’ar su da bakunansu masu albarka, kai ma kuma kana yi ma kanka, amma nima ai kinsan babu ni a harkar saɓon Allah kwata kwata” Mami dai ko kallonta bata yi ba, shaff Aunty ta mance ta kawo ma Mami irin wannan maganar tsabar ƙin Junaid da take da kuma burin duk wani abu da zai tarwatsa sa, balle ko shirin kirki basa yi da Mami kamar yanda suke yi shekaru masu yawa da suka wuce a baya, Mami tace “To yanxu dai ke menene shawaran ki akan wannan mummunan lamarin Fulani? Kina ganin kuwa Mai martaba zai saurarari uzurin da zaki kai masa har ma ya dauka? Don Jawwad din fa har ce min yayi Mai martaba yasan da maganar tun ma a Amurka, kinga kuwa shi ma ya goyi bayansa kenan ai” Aunty tace “Ai ina ga mu ajiye batun yi ma Mai martaba magana tukunna, yanxu kamata yayi ma musan asalin ita yarinyar da yace maki yake so, Er wani gari ce ita, sannan waye ubanta a kasar nan, yaushe ma har ya hadu da ita ya fara son ta, informations dinta kawai ya kamata ace mun fara samu before anything else, ni ban so kin ma samu ɗan iskan Junaid din kin masa wata magana ba don kar ya koma ya gaya ma Jawwad, tunda kince baki nuna ma shi Jawwad din komai ba” Mami tace “Ae kuma kin san sa da shegen zurfin ciki da miskilanci, ba lallai ya ce ma Jawwad komai ba, kai bazai ma gaya masa ba” Aunty tace “Wannan gaskiya ne, a dai halinsa bazai gaya masa ba kam, yanxu kawai kara nuna ma Jawwad din zaki yi babu komai kawai yayi ta addu’a akan lamarin daga nan cikin siyasa ki bugi cikinsa mu san wacece yarinyar waye kuma ubanta a Nigeria” Mami tace “Ya ce min er Kano ce Tudun Yola” Aunty tace “Tudun Yola? To ai can cousin sister na Bara’atu take da zama, nan gidan mijinta yake” Mami tace “Kin ga ya zo mana gidan sauki kenan” Aunty tace “Ai kuwa dai ya zo mana gidan sauki, abinda yayi saura yanxu ki lallabasa cikin dubara a san a ina suke a cikin Tudun Yola” Mami tace “Kinsan sa da kaifin tunani fa Fulani, yana jin tambayoyin sun fara yawa zai ɗago wani abu” Aunty tace “In yasan wata ai bai san wata ba, number yarinyar kawai zaki nema a wayar sa bakin ki alekum” Mami ta sauke ajiyar zuciya tace “Shikenan, bari in je koma ya ake ciki dai zaki ji ni” Daga haka Mami ta mike ta nufi hanyar fita babban parlon, Aunty tayi murmushi tana girgiza kafa a hankali, ai ko tana ga yanxu ne dai dai lokacin ma da ya kamata ta farraka Jay da Ajay don da ta dau alwashin duk wani tsabgar Mami bazata sake shiga ba, duk da Jawwad din ma ba wai sonsa take ba, amma gwara dai shi sau dubu akan Junaid, farrakasu da zata yi shi ne zai sa rayuwar Junaid ya kara daidaicewa yanda take fata a kullum. Wajen karfe tara Jay ya bude kofar dakin Ajay, yana tsaye bakin kofar yake kallonsa ganin yana kulle tsadadden traveling box dinsa, Jay yace “What is the meaning of that?” Without looking at him Ajay yace “I am leaving for Abuja” Da mamaki Jay yace “Abuja? But you are not well Ajay” Ajay yace “I am” Jay yayi shiru still looking at him, after some seconds yace “Amma baka gaya ma Mai martaba ba tukun” Ajay yace “Na gaya masa” Jay yace “To ka bari zuwa gobe sai mu tafi tare mana” Ajay yace “Yau zan tafi” Jay yace “Amma bai fi kayi kwana biyu ba ai” Ajay yace “I can’t say” duk da kwana biyun ma Mai martaba yace yayi ya dawo tunda baya jin dadi, Juyawa Jay yayi ya bar bakin kofar ya tafi can ɓangaren Maminsa, Mami ta ajiye wayar da take bayan ya shigo tace “Kayi breakfast Jawwad?” Ya zauna saman kujera yace “Nayi” Mami ta ɗan yi shiru, sai kuma tace “Ya jikin ɗan uwan naka, ka shiga wajen nasa kuwa?” Jay yace “Daga can nake” Mami ta dinga kallonsa ta ji ko zai ce komai cause he look moody, har ta fara zargin ko Ajay ya gaya masa maganganun da taje ta masa daxu ne, Jay yayi breaking silence din yace “Abuja ma zai wuce yau” Mami tace “Wajen Amina?” Jay yace “Eh” Mami ta taɓe baki tace “Gwara ai yaje ya huta a can din” Jay ya kalleta yace “Duka kwanansa nawa a nan da zai je Abuja ya huta? Nan da Abuja ina ne asalin inda ya kamata ace ya samu hutu? The occupants of this palace ain’t being fair to him, they are just making the palace miserable for him to leave in, gida da mutum yake saka ran dawowa ya samu rest of mind and peace but in Ajay’s case it is totally different, he is always sad and restless in his father’s palace, walwalarsa iya America ne ko kuma wani state a nan Nigeria aside Bauchi, sau da yawa in ya dawo Nigeria sai Mai martaba ya dinga takurasa ya zo garin nan, till when za a bar shi ya zauna peacefully a gidan nan ya samu kwanciyar hankali? Shi ba shiga harkar kowa yake ba he is always on his own baya shiga sabgar da bata shafesa ba, sai ya ga dama zai tanka abu, step Siblings dinsa gaba daya an dora su kan hanyar maida sa bare a masarautan nan, what is his offense pls? Menene yayi triggering attitude din da ake ganin yake showcasing a gidan nan?” Mami dake ta kallonsa ta kwantar da murya tace “Ya ce maka an masa wani abu ne yanxu?” Jay ya mike yace “Sai yace Mami? Nafi kowa saninsa idan da abinda yake damunsa ko kuma yana cikin bakin ciki, Kullum ya dawo gidan nan ba shi da walwala, ba shi da farin ciki, nan din kamar ba comfort zone dinsa ba, banda Mai martaba dake son ganinsa a kusa ni na tabbatar Ajay bazai dinga shigowa garin nan ba balle ya zauna gidan nan” Mami ta taɓe baki tace “In zaka bar wahal da kanka ka bari Jawwad, yanda kaga halin sa din nan haka mahaifiyarsa take ba wai, ci kanka sai ta ga dama zata ce ma mutum a sanda take raye, bata fiye son shiga harkar abinda bai shafeta ba ita ma, she is always on her own, miskila ce ta ajin karshe, in ba saninta mutum yayi ba sai yayi zaton tana da damuwa ne amma tsabar miskilanci da nukurci ne, don haka ka bar Ajay gado yayi ba taka haye ba, Mai martaba kansa ai yana da miskilancin da izza, shi abun ne yayi masa yawa wai shege da hauka, in zaka yi harkar rayuwarka ka bar damun kanka akan Junaid da zai fi maka alkhairi, sannan ni da kake kawo ma korafi zama nake a gidan nan? Ba sai inyi wata ba a gan ni ba, na hanaka shiga sabgar da bata shafe ka ba amma baka ji Jawwad” Jay dai kallon Mami kawai yake, Mami tace “Allah dai ya kyauta kawai, shi ma in zai zauna ya saki ransa ya zauna lafiya da kowa ya bi su a yanda suke so da zai fi masa” Jay yace “Zan shirya za mu tafi Abujan tare yau….” Mami ta hade rai tace “Kanwar uwarka ko ta ubanka ce a Abujan Jawwad, ka kawo min magana mai muhimmanci ina jiran ka ka shigo mu iddasa magana kuma kace min zaka bi sa ku je Abuja?” Jay yayi shiru jin abinda Mami tace, after some seconds ya zauna a hankali yace “Yeah haka ne Mami, amma ai za mu iya gama maganar yau sai mu tafi, bai wuce yayi kwana biyu ba kawai” Mami tace “Kai ka sani, tun da ga Boss dinka zai tafi Abuja ai dole hankalinka ya tashi kace zaka masa rakiya” Shi dai Jay bai sake cewa komai ba, bayan wani ɗan lokaci Mami ta kwantar da murya tace “Amma Jawwad baka ganin maganar can da ka kawo min daxu da safe zai kawo tangarda a zumunci tunda kasan wacece Hadiyah a gidan nan?” Jay yace “Ai Mami ni ban yi deciding kwata kwata bazan aureta ba, na dai ce idan hakan zai zo da matsala ni na amince zan iya hadasu su biyu” Mami tace “Haka ne, a nan ma kayi tunani me kyau, kuma ana ta jiran ku dawo ne a tsaida rana fa, don a yanda aka tsara wannan lahadin ake son tsaida ranan in sha Allah, sai gashi ka dawo da wata magana kuma” Jay yayi shiru jin abinda Mami tace, a hankali yace “Mami in dai kun amince min don Allah a haɗa duk biyun a saka gaba daya” Mami ta ɗan yi murmushi, sai kuma tace “Ai kuma dole a ɗaga saka ranan Jawwad, don kaga wannan maganar da ka kawo dole sai an yi calling family meeting kowa yasan abinda ake ciki, yanxu ya sunan ita yarinyar?” Jay ya kalli Mami, sai kuma yace “Sunanta Jiddah” Mami tace “Ikon Allah, ba ka yi ma ɗan uwanka ƙara ba kenan dai, haka kake kiran nata?” Jay ya ɗan yi murmushi yace “A’a, Halysaah ake kiranta” Mami tace “Maa sha Allah, Allah Ubangiji yayi zabi mafi alkhairi” Yace “Ameen” Mami tace “To ba damuwa, zan fara samun Mai martaba da maganar sai mu ga yaya za ayi kafin ma a kira meeting din” Jay yace “To Mami” Mikewa yayi don hankalinsa na can wajen Ajay duk da bai san Flight din karfe nawa zai bi ba, in ma na yanxu ne yasan dai bazai tafi bai kirasa ba, Mami tace “Fita zaka yi ne” Jay yace “A’a ba da nisa zan je ba” Mami tace “Toh kira min Maman Hadiyah ta wayar ka naji an min warning ina waya kafin ka shigo” Jay na kallonta yace “Maganar zaki mata Mami?” Mami tace “Haba, sai kace wata yarinya, maganar mu daban, in ma maganar ne ai yayanta ne zai mata” Jay ya ciro wayarsa ya mika ma Mami, ta amsa tace “In ji dai babu password, naga ka miko min haka” Yace “Babu” Tace “Ohk” Juyawa yayi ya fita daga parlon, Mami ta shiga call logs dinsa, Miss call ta gani da number da yayi saving with Halysaah with love emoji a gefe, ko picking call din ma bai yi ba kuma tun karfe takwas ta kirasa, wayarta ta jawo ta kwashe number gaba daya ta adanasa a wayarta, sannan ta fita daga call log din, gallery dinsa ta shiga nan ta ci karo da recent pictures da suka yi da Halysaah a amurka wanda Safiyyah tayi masu, kallon hoton ta dinga yi babu ko kiftawa with shock, tayi zooming din Halysaah sosai tana kare mata kallo, ajiye wayar tayi tsabar yanda ta girgiza taji zuciyarta na bugawa, ita Jawwad zai jajibo ma wannan yarinya me kama da buzuwa ko halfcast, mutanen da aka san su da mugun mallake miji, sannan ko me miji ya mallaka to a kansu yake karewa su kadai ke mora don raba mijin suke da danginsa kaf, sosai hankalin Mami ya tashi ba kadan ba, ta dinga kallon duk hotunan, da irin kallon tsantsan kauna da Jay yake ma Halysaah a duk hotunan kamar zai cinyeta, Mami ta ajiye wayar ta dafe kanta da yayi mata nauyi ta dinga nanata Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, rabon da ta shiga irin wannan tashin hankalin da kidimewa har ta manta, wayarta ta jawo ta shiga WhatsApp dinsa tayi ma kanta sending hotunan guda biyu sannan tayi deleting yanda shi bazai gani ba ko yasan abinda tayi, daga nan ta fita daga WhatsApp din ta goge duk wata alamar da zai nuna wajajen da ta shiga a wayar nasa gaba daya, ta fi minti biyar a kidime sannan tayi dialing number Maman Hadiyah ta wayar sa don kar yaga bata kira ba, minti uku kawai suka yi suna magana da Maman Hadiyah sannan ta ajiye wayar tasa ta dau nata ta fita ta nufi bangaren Aunty cikin tashin hankali. Aunty dake zaune kan kujera ta dinga kallon hoton da Mami ta fiddo mata a wayarta, can ta kalli Mami baki bude tace “To ai na taɓa ganin yarinyar nan a Amurka da muka je kwanaki Fulani” Cikin tashin hankali Mami tace “Da gaske?” Aunty tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, wallahi a gidan nasu na Amurka take zaune sanda naje, don dakin da suke saukan baƙi a sama duk kayanta ne da akwatunan ta a ciki, har sai da na kira Mai martaba na kai masa kara” Mami tace “To ai a sanda ku ka je Jawwad na nan Nigeria Fulani” Aunty tace “Kwarai kuwa, daga ita sai Junaid da ma’aikata na tarar a gidan, Junaid ya min rashin kunya ya gaggaya min bakakken maganganu a kanta, daga karshe ya kuma dauketa ya bar gidan, Wato tunda watsattsiya ce kuma ba son ci gaban Jawwad din yake ba shine zai zugasa ya aureta, Shi idan ba mugu azzalumi ba me yasa bai ce zai aureta ba, don mugunta sai ya tusa ma Jawwad saboda shi ne dai dai er bariki, yo er bariki mana, in ba er bariki ba me take yi a cikin wannan gidan cikin maza har biyu sannan ga masu aiki? Wallahi a yanda Jawwad ke tsoron Junaid idan ya hanasa auren yarinyar nan tsaf zai hanu, duk mun fa san Junaid ke controlling dinsa kinga kuwa tabbas da goyon bayan Junaid dari bisa dari akan maganar yarinyar” Mami ta dafe kanta da yayi mata nauyi don gaba daya ta ma kasa cewa komai, cikin tashin hankali tace “Ba fa er Nigeria bace Fulani, bamu ma san ko er wace kasa bace suka dawo Nigeria da zama” Aunty tace “Ni tafi min kama da Buzuwa, kuma akwai su da mallake miji kuwa da rabasa da danginsa, Wallahi in zaki fito ma Jawwad a mutum ki yi masa fata fata ki ajiye wannan kulafucin nasa da kike yi a rai to zai fi maki, don wannan kamata yayi ki ci masa mutunci sosai ba kadan ba ki nuna masa bacin ranki” Mami tace “Bazan masa haka ba Fulani, amma nasan me zan yi…” Aunty tace “To ga shawara, kuma shi kadai ne mafita a yanxu dai….” Mami ta daga kai tana kallonta tana jiran jin me zata ce…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello* Ur evidence via 07087865788
