Hausa novels

Halysaah Page 56 By Khaleesat Haydar

Khaleesat har ta fara bacci wajen karfe goma da rabi Aunty Farida ta tasheta tana mika mata sabuwar wayarta dake vibrate, mikewa tayi zaune tana gyara hulan kanta ta amshi wayar taga Safiyyah ce ke kiranta, ɗagawa tayi ta kai kunne, daga daya bangaren Safiyyah tace “Ko har kin fara bacci ne” Khaleesat tace “Um, da wuri na kwanta ne” Safiyyah tace “Ayya sorry for waking you up, dama Housemate din ki ne yace in tambayeki wani account zai maki funding, cause nasan definitely Abdul ya amshi kudinsa dake account din ki ko?” Khaleesat tayi shiru ta kasa ce ma Safiyyah komai, har sai da Safiyyah tace “Hello” a hankali Khaleesat tace “Ina jin ki Sophie” Safiyyah tace “To naji kin yi shiru” Khaleesat ta daga kai ta kalli Aunty Farida dake kallonta, goge hawayen dake makale idonta tayi cikin sanyin murya tace “Daxu Mom dinsa suka zo za su amshi kudin, ni kuma bazan iya transfer ba kuma bani da Atm card, shi ne ta ajiye min account number wai in tura masu kudin yau, and today is Friday, mun je banki sun tashi, yanxu tace zata dawo gobe da safe idan ban tura mata kudin ba” Safiyyah dake ta sauraron Khaleesat cikin bacin rai tace “Allah ya sauwake, ke kiji wani tsiya don girman Allah, akan miliyan tara ne ko goma uwar ta kamo hanyar gidan ku da kanta? Can you imagine fa? A’a gaskiya sai yanxu nake sake tabbatar da su Abdul were once poor in this life, all of a sudden kawai Allah ya basu arziki sama ta ka, nobody can change this my perspective wallahi, banda tsiya meye kuma miliyan Goma a irin yanda suke show casing arzikinsu, what is 10M to them? wannan ai abun kunya ne a garesu, Ke kuma maimakon ki kirani tun daxu ki gaya min shi ne kika yi shiru? Yanxu ba don Housemate dinki yayi reason cewar dole sai da sufficient fund a account dinki za ki iya tafiya ba da shiru zaki yi kenan sai gobe da za mu tafi ki gaya min? Allah ya sauwake, ita kuma uwar Abdul wallahi matsiyaciya ce er wahala, har ta iya kamo hanyar Mariri akan kudin da ba ita ta bada ba, in kin bibiya ma ɗan nata bai sani ba ta kamo hanya, ki min sending shegen account din nata da ta bar maki” Daga haka Safiyyah ta kashe wayarta, Khaleesat ta jawo handbag dinta tana goge hawayen da ya taru idonta, ta bude jakar ta ciro takardan account details din da Mom din Abdul ta bar mata, tura ma Safiyyah account din tayi ta message sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta koma ta kwanta, ita dai Aunty Farida bata ce komai ba don duk ta fahimci conversation din nasu. Washegari Khaleesat na idar da sallan asuba kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tayi picking call din ta kai kunne, a hankali tace “Good morning Safiyyah” Safiyyah tace “How was ur night?” Khaleesat tace “Alhamdulillah” Safiyyah tace “Na tashi yanzu naga Housemate dinki ya tura min receipt din 10M da ya tura a account din da kika turo min jiya, he sent the receipt via my WhatsApp, ba ki yi activating WhatsApp dinki ba da sai in tura maki ki tura masu, sai su san su ne matsiyata” Kasa cewa komai Khaleesat tayi hawaye ya fara sauka idonta, Safiyyah tace “Ko kuma bari in tura ma Aunty Farida receipt din kawai since she is on WhatsApp” Khaleesat ta gyada mata kai da kyar tace “Nagode” Safiyyah tace “Kuka kike yi ko? Kina da aiki, ni dai sai anjima, make sure ki fito gida da wuri kin san Flight dinmu zuwa Abuja karfe daya ne” Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Umma na kallon Khaleesat tace “Wai me ya faru?” Khaleesat na share hawayen da yaki tsaya mata tace “Ta ce ya tura masu kudin ne, zata tura ma Aunty Farida receipt” Shiru Umma tayi ta rasa abun cewa, kana ganinta kasan jikinta yayi sanyi sosai, Aunty Farida dake zaune kan darduma tace “Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi ya kare sa sharrin masu sharri, Allah ya mayar masa da dubban abinda ya kashe maki, yanda ya rufa maki asiri Allah ya rufa masa shi ma” a hankali Umma tace “Ameen ya Allah” Mikewa Khaleesat tayi don dama ta gama azkar din da take yi, ta kwanta kan gadon Umma har sannan hawaye yaki dena sauka idonta. Da safe wajen karfe tara Aunty Farida na bude WhatsApp dinta taga Receipt din da Safiyyah ta tura mata, tana kallon Khaleesat tace “Yanxu ta ya za a tura masu receipt din su gani Khaleesat?” Umma tace “Ba kina da number Abdul din ba? Ki tura masa ta WhatsApp din kawai” Khaleesat dake cin wainar da Umma ta sa aka siyo mata ta daga kai ta kalli Umma, sai kuma ta girgiza kai a hankali tace “A’a Umma kar a tura masa, ba sun ce za su zo da safe ba, in sun zo sai a nuna masu receipt din” Umma tace “Saboda me? Ba kudinsa bane kuma shi ya aiko su karbar masa?” Aunty Farida ta kalli Umma tace “Suka aiko kansu dai Umma, don Abdul dai a yanda yake ji da kansa bazai ce a zo a amsar masa miliyan goma ba, dama sun san da kudin kuma kilan sun san bazai ce zai amsa ba shi yasa suka taho su amsa” Khaleesat tace “Shi yasa nace kar a tura masa receipt din, don nasan ba shi yace su zo ba” Umma tace “To ko ma dai yaya ne ai kudinsa ne, ni bana son su sake dawo mana nan su mana tijara makota na ji shi yasa nace a tura masa kawai, idan yaso sai yayi ma uwar tasa magana tunda zai ga a account dinta aka tura kudin ai, tonan asirin bai ishe mu bane da har za mu sake yarda su dawo gidan nan” a hankali Khaleesat tace “Umma ni bana son abinda zai sake hadamu magana da shi balle har yace zai dawo da wata magana kuma” Aunty Farida tace “Ya dawo da wani magana? Saboda ba shi da hankali zai dawo da wata maganar? Ai yanxu ba mu da abinda zai sake hadamu da shi da ya wuce kudin nan nasa, saki uku ya aiko maki balle ace zai dawo da wata magana” Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya tace “Aunty ba fa shi ya aiko da takardan sakin nan ba, ba rubutunsa bane, iya saki daya yayi min” Daga Aunty Farida har Umma kallonta suka dinga yi, a hankali tace “Shi yasa bana son a tura masa receipt din balle har hankalinsa ya dawo kan mu…” Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya tace “To Allah ya kyauta, yanxu su suka rubuto takardan suka aiko kenan? To su dai suka sani Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu da ke baki daya, idan sun kwaso kafa sun sake dawowa sai a nuna masu receipt din” Umma dai bata ce komai ba don bata ma san me zata ce ba. Meemah na bacci Momy ta shigo dakinta wajen karfe goma na safe ta tasheta tana mika mata wayar hannunta, Meemah ta amshi wayar tana kallon screen din, sai kuma ta kalli Momy tace “Kudin suka sako?” Momy ta tabe baki tace “Gashi kuwa kina gani, nima yanxu naga alert din ashe tun daren jiya aka sako” Meemah tace “To a gidan uban wa ta samu ta turo bayan tace bata yin transfer kuma bata da Atm card” Momy tace “Ke baki ga sunan wanda ya turo kudin ba? Ai ba ita bace ta turo” Meemah ta kara kallon wayar da kyau taga sunan namiji, taɓe baki tayi tace “To wai ke Momy da nake ce maki iskancinta ta dinga yi da maza a Amurka kin zata wasa nake? Ai ba abun mamaki bane don kin ga ta samu wanda ya turo miliyan goman, harkar iskancinta kawai ta dinga yi a Amurka da ‘ya yan masu kudi, kuma karya take babu miliyan goman nan a account dinta wallahi, to dai gashi nan daya daga farkanta ya turo kudin nan take” Momy tace “Oho dai koma wa ya turo kudin ta matse masu can, ni dai ba na amshi kudin ɗa na ba, da ban yi haka ba har a tashi duniya in dai Abdul ne wallahi bazai yi maganar kudin nan ba, kin ga da shikenan sun ci bulus, to ni da na haifesa ba asararriya bace da zan yarda ya bar masu makudan kudaden nan” Meemah tace “Wallahi Momy ni so nayi mu ce sai sun biya kudin sponsoring dinta da Abdul yayi, ke kinsan nawa Abdul ya kashe akan yarinyar nan kuwa? Wallahi idan na fara maki lissafi sai kin rike baki don mamaki, kudade ne ba na wasa ba da, duk kanta dukiyarsa ya dinga tafiya kamar kin masa baki, yaushe rabon kiji Abdul ya siya wani asset nasa ya ajiye? Tun da ya hadu da tsinanniyar yarinyar nan ya dena yi ma kansa komai sai dai yayi mata, ranan a gabana ya siya mata Abaya har biyu ko wanne dubu dari da hamsin, nayi masa magana ya nemi ya min rashin kunya cikin jama’a, handbag din nan shegiya sai Abdul ya siya mata na dubu kusan dari har fin haka, komai designer yake siya mata, suturu kam yayi mata ba iyaka, to wai ko monthly allowance da yake tura mata a kasar Amurka in kika ji sai hankalin ki ya tashi, uwa uba a zo kan kudin makarantar ta da House rent” Momy tayi mitsi mitsi da ido cikin bacin rai tace “Don Allah ki bar wannan maganar don raina baci yake Meemah, su je kawai Allah ya isa, ni da nake uwarsa ma sai ya ga dama yake siya min abu, to yanxu ko ce masu muka yi su biya a ina suka ga kudin biya Meemah? Ko gidan da suke ciki suka ce za su siyar wallahi karkari yayi dubu dari biyar, kai ni dubu dari biyar din ma bazan siya wannan kangon ba wallahi, kin ga kuwa gwara a bar zancen kawai, baki ji yanda raina ya baci ba wallahi, kawai Allah ya isa zan ta ja masu a kan uban kudin da Abdul ya kashe ma yarinyar kuma ba wai don bani da kudin maka su kotu ba….” Meemah tace “Ko kuma mu je duk mu kwaso kayan da ya dinga siya mata da jakunkuna masu tsada” Momy tace “Ki ci uwar me da su? Kema dai wallahi, shekara 38 ban san yaushe zaki yi hankali ba Meemah, Allah ya isan dai shi ne dai dai su, don babu abinda za mu ci da kayanta, tunda muka samu miliyan goman ma ai mun gode Allah” Meemah ta tabe baki ta koma ta kwanta tace “Kuma kin san wani abu Momy, da Abdul yana kasar nan har yanxu zai fa iya waiwayanta idan asirin ya sakesa, don wallahi masifaffen so yake ma shegiyar ke har yanxu baki gane ba, ji fa kafin su bar kasar yanda ko magana baya yi ma mutane a gidan nan, kullum zaka gansa babu walwala” Momy ta hade rai tace “Ni kuma ga er iska sai in sakankance har asiri ya sakesa ko? Ai da gangan na sa uban ya tafi da shi business trip din da za shi china, da biyu na takura uban su tafi tare don naga take takensa, ga sabon tijaran da na lura zai fara mana, kuma ko ba komai ai kinga za su dade a can kan su dawo, ni kuma kafin nan na sa anyi aiki sosai ya mance da wata shegiya wai ita Khaleesat a duniyar nan, sai kuma in tanadar masa mata er gidan mutunci, yana dawowa sai biki kawai” Meemah tace “Da dai yafi kam, yana dawowa yayi aure, ki sama masa yarinya dai dai class dinsa ba er talakawar da ya nace ma ba, ni wallahi ban zata talaucin iyayen yarinyar nan ya kai haka ba, har muka dawo gida na kasa cire view din gidan a idona, wannan ko karen gidanmu aka ajiye a gidan nan ai sai yayi rashin lafiya a bar mu da kashe makudan kudi zuwa veterinary balle ace mutum, to yanxu da bai rabu da ita ba haka wataran abu zai kama ki kwashi kawayenki da abokan business aje gidansu yarinyar? Misali ace ubanta ko uwarta wani ya mutu, haka za a kwasa aje masu gaisuwa wannan gidan?” Momy tace “Ai Abdul ya so ja min abun kunyan da bazai taɓa goguwa ba, ya so tona min asiri a idon duniya amma Allah ya rufa min asiri ya takaita abun, da irin rainin da Abdul zai ja min sai Allah wallahi, to ni dai tunda na samu aka rabu lafiya ai sai su bi wani sarkin kuma” Meemah tayi dariya tace “Kuma da bai saketa ba fa sai ya iya canza masu wani gidan don ba hankali garesa ba, tunda don yayi ta ma shegiyar yarinyar bauta Allah ya halitto sa” Wani shegen kallo Momy tayi mata sannan ta juya ta fita daga dakin. Khaleesat na durkushe gaban Umma dake mata addu’an Allah ya kai ta lafiya, ya bata sa’an karatun ta, ita dai Khaleesat kanta na kasa duk jikinta a sanyaye, a hankali Umma tace “Ki kula da kanki don Allah, duk da na yarda dake Jiddah amma ki kara taka tsantsan, kar ki mance tarbiyar da muka maki, kuma ki rike addu’a da azkar, Allah ya kare min ke ya tsare ki duk inda zaki shiga…” Nenne ce ta bude labulen dakin a fusace tace “Yau naga jaraba wajen Zahra’u, sai me motar yayi zuciya ya ja motarsa ya wuce ne ko yaya? Duk daren jiya da wayewar garin yau baki sakata gaba da duk wani zancen da zaki mata ba sai yanxu da motar da zai kai ta iyapot ya iso, haba Zahra’u ya ki ke haka ne? Ko dai maidata ciki za kiyi?” Aunty Farida ta wani kalle Nenne tace “To kyauta zai kai ta airport din da bazai jira ba, naga dai kudi zata basa Nenne” Nenne tace “Ai ba motar ubanta bane da zata shanya sa a rana don zata basa kudi, kuma shi ba boyi boyinta bane da zai ta tsayuwa yana jiranta a rana kamar ɗan iska, tunanin ku kenan ‘yan Adam, don zaka ba mutum kudi sai aka ce ka walakantasa? Ka ki darajasa?” Aunty Farida taki tanka Nenne, Umma na kallon Khaleesat tace “Tashi ki je Jiddah, Allah ya tsare ya kai ku lafiya” A hankali Khaleesat tace “Ameen Umma” Daga haka ta mike ta dau handbag dinta don duk an fitar da akwatunan ta kofar gida, Nenne na kallon Umma tace “In ji dai duk an saka mata doya da dankalin da na kawo mata a akwatin nata?” Da sauri Aunty Farida tace “An saka komai” Nenne tace “Wake da su albasa da garin masara da na alkama fa?” Aunty Farida tace “Har su an sa” Nenne tace “To mu je” Khaleesat ta bi bayan Nenne suka fita daga dakin, Aunty Farida ta kara tura doya da dankalin da Nenne ta kawo da su garin alkama da Masara a bayan kyaure ta boye yanda Nenne bazata gani ba ko ta dawo dakin, daga nan ta bi bayan su, kasa daurewa Umma tayi ta mike ita ma ta fita, su Mama Zubaida da Mama Shatu na tsaye tsakar gida duk suka bi Khaleesat da kallo, Kana ganin fuskokinsu kasan babu farin cikin komawa Amurka da Khaleesat zata yi, Yaron Mama Zubaida ya nufo Khaleesat da gudu yana mika mata kudin hannunsa yace “Wai gashi inji Ummanmu da Mama Shatu ki sha ruwa a hanya” Nenne ta karbe kudin a hannun yaron ta kirga taga dubu biyu ne, sokesa tayi jikin haɓar zaninta tace “Ta gode” Daga haka ta kalli Khaleesat tace “Mu je” Khaleesat tayi ma kishiyoyin ummanta sallama sannan ta bi bayan Nenne suka fita daga gidan Aunty Farida na biye da su, a kofar gidan Khaleesat ta kara sallama da Babanta don bai fita kasuwa ba ranan yana jiran tafiyarta, kasa hada ido tayi da shi yana mata addu’a da fatan alkhairi, Nenne ta bude mata bayan motar tace “Ni dai shiga don Allah, tun jiya basu san da addu’an su ba sai yau da kike sauri salon jirgi ya tafi ya bar ki” Khaleesat ta shiga motar Nenne ta kulle, haka kawai Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, ta daga masu hannu kawai sannan drivern ya ja motar suka bar kofar gidan. Ko da Khaleesat ta isa airport ta tarar Safiyyah na ta jiranta don tun daxu ta iso airport din, Khaleesat ta amshi boarding pass dinta suka nufi Departure Lounge, bayan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin Abuja, inda a nan za su hau jirgin da zai kai su kasar America.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button