Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 14 Hausa Novel

Shigowar saƙo wayanshi ne ya sa da wani irin hanzari ya miƙe daga jikin motar yana duba wa.”Ba ni da lafiya”Abin da kawai ta iya rubutawa kenan, sai ya ji hankalinshi ya fi na baya tashi don bai san wa zai kira ya taimaka mata ba, idan ma ya ƙira su Samha ya san abin ba zai yi kyau ba mommy kuma za ta iya ɗaga hankali a kan ya aka yi ya san bata da lafiya yana Maiduguri tana Kaduna? Wani tunani ne ya faɗo mishi, nan ya shiga neman Layin wani friend dinshi da yake nan capital hospital Kaduna ɗin a kan ya taimake shi da Layin Dr. Sulaiman, cikin mintuna biyu sai ga Layin a take ya shiga ƙiran Layin ringing uku aka ɗaga “Dr Cap. Saleem ne don Allah wani taimako ne nake nema daga gareka please in ba damuwa” Ya faɗa bayan sallama da gaisuwa, Nan ya yi ta mishi godiya bayan sun gama disussing, ko gida bai iya ya je ba yana zaune ne kawai cikin motar shi cike da tsumayin sake ganin ƙiran Sulaiman.A chan Kaduna kuwa sallamar da ake ta doka wa ne ya sa sameera Miƙewa ta nufi ƙofan, Sadiqa suna dining da Ƙawayenta ana cin abinci ana hira, mommy ke karyawa a tsakiyar parlorn, Samha na wani research a system ɗinta hakan shine ma ya tilastawa sameera da ke danna waya Miƙewa tana mitar irin uban Sallamar da ake tayi, tana bude kofan ta yi niyyar masifa ne sai idanunta suka sauƙa kan Dr. Sulaiman da ke jingine ɗan nesa kaɗan da jikin motar shi, daga ganinshi ka san responsible matashi ne da yake kan ganiyar samartakarsa daga yanayi shiga da kuma tsarin motar shi zaka san ko shi ba mai kuɗi bane daga gidan kuɗin ya fito, Baaba jummai ce dake doka Sallamar ta katse ta “Har na fara tunanin babu mutane ne gidan ‘yan nan ashe kuna ciki”Ta ɗan harareta a fakaice “eh muna nan, lafiya kam?”Ta ƙarasa tana sake kallon Dr. Sulaiman da har yanzu hankalinshi ke kan wayanshi.”Wanchan likitan Afeefah ne mun zo duba ta da jiki”Ta haɗe fuska kan tace “Ina zuwa”Ciki ta koma kafin mommy ta tambayi waye ta shiga ce mata”Mommy wai sun zo duba wanchan Mayyar da yaya salim ya kawo wai likitan ta”Ɗan shiru mommy tayi tana tunanin Allah ya sa ba salim bane ya aiko su, sai kuma ta tuna ai bai ma san halin da take ciki ba, kila ma ya zuwa yanzu ya mance da ita ko ma bai mance da ita ba ta san ba zai taɓa saɓawa umarnin ta ba itama kuma hankalinta ya fi kwanciya a yadda yayi uwar watsi da rayuwar yarinyar yake kuma mu’amala da ita da ƙannenshi lafiya ƙalau.”Tura Talatuwa ta kai su, su suka sani”Ta ɗan zauna kaɗan kan ta miƙe ta nufi ɗakin Talatuwa ta tura ta, Baaba jummai har ta gaji da tsayuwa sai ga Talatuwa, suka gaisa kan tace su tafi ɗakin Afeefar don yadda ta gantan nan ta tabbatar ba za ta iya fitowa ba, Dr. Sulaiman Baaba ta yiwa magana ya bi bayansu har ɗakin da Afeefar take su biyu ya bari suka fara shiga, Baaba jummai na ta sallalamin yadda ta gantan kan ta fito ta kira Sulaiman cikin sauri “Alhaji ƙarami zo ka ga yarinyar nan jiki babu daaɗi sam”Ita kaman uwa take wurinsu don gabanta aka haife shi har ya girma tana gidan su, kuma shine babba a yadda ya ɗauke ta kaman uwa haka ƙannenshi suka tashi suka gani su ma kuma suka yi following footsteps ɗin shi a girmama ta, shiga dakin yayi ya isa gabanta ya duƙa.”Afeefah”Ta amsa da “uhmm” ba tare da ta buɗe idanunta ba.”Menene yake miki ciwo?”Ta Nuna mishi kanta da kaman zai tsage.”Akwai amai?”Ta girgiza kai.”Jiri fa?”Ta gyaɗa kai.”Mura fa da tari?”Nan ma ta gyaɗa kai, plate na abincinta na safen da ke rufe a gefe ya buɗe ko spoon ɗaya bata yi ba.Ledojin da ya shigo dasu a hannunshi ya shiga buɗewa babu bukatar zuwa asibiti drip ya haɗa ya ɗaura mata ya haɗa allurai yayi wasu a jikin canular wasu kuma jikin ruwan, ya dubi Talatuwa “Kin san magungunan da suka shafi na mura da zazzabi da sa bacci, bare ma jininta ya yi ƙasa sossai tana ɗan buƙatar hutu na kwana biyu ba tare da ta yi hulda da ruwa ko abu mai sanyi ba””Toh fa, ranka ya daɗe ni ma ‘yar aiki ce kamar ta ba ni da ikon bata hutu da dai Hajiya da kanta ka yi wa bayanin da sai ya fi”Ita dai Baaba jummai ta zabga tagumi tana kallon Afeefah dake bacci ji take kaman ta yi mata kuka ashe itama aikatau take yi gidan su Saleem ɗin? Muryar Sulaiman ne ya katse ta yana cewa Talatuwa “ko za ki kai ni wurin hajiyar?”Duk da basu yi haka da Saleem ba amma ba zai iya kau da ido a kan yarinyar ba she’s too young and fragile kaman she’s having a lot a cikin zuciyarta.Fitowa suka yi Baaba dai kaman ta tsaya haka take ji Don Allah ya saka mata ƙauna da tausayin Afeefah kaman jikar ta.Talatuwa ta duƙa gaban mommy bayan ta bar su a waje “Hajiya da ma wai likitan ne yake son gani ki”.Kan mommy ta yi magana ma sameera tayi saurin cewa”Ki ce ya shigo, mommy bari na ba ki mayafi”Samha ta ɗago ta kalleta, mommyn bata ce komai ba har sameerah ta kawo mata mayafin daidai Sulaiman ya yi sallama ya shigo.Kamshinshi ne ya cika parlorn duk yadda mommy ta so ta kame nagartarshi da kwarjininshi ya sa ta shiga mishi sannu da zuwa a dole, gaisheta ya shiga yi cikin girmamawa bayan sun gama Sameerah ta shiga gaishe shi, ya amsa da murmushi saman fuskanshi dole Samha itama ta gaishe shi itama ya amsa mata kan ya dubi mommy “Da ma akan patient ɗi ta Afeefah na nemi ganin ki Hajiya, na zo duba jikinta don ganin lokacin komawarta checkup ya yi ban ganta ba sai na samu ashe tana kwance rip da zazzabi mura da kuma low BP da ya addabe ta”Mommyn ta yi kaman bata san bata da lafiya ba tace “Asshaa ka ga aikin rashin wayaun Afeefar ko? Babu fa wanda ta sanar wa bata da lafiya, mutum kullum a maƙale a ɗaki ya ba za’a yi zazzabi ya dame shi ba? Allah dai ya kyauta”Sulaiman ya ɗan murmusa don wannan ba hujja bace a gareshi idan kai ka kula da mutum ba lafiya ba sai ka jira ya gaya maka ba, haka kuma idan baka ji mutum ba ana dai zaune tare kai ke da alhakin leƙa wa ka ji shin yana lafiya?”Ai duk alamun rashin lafiyar ne Hajiya, a likitance duk wadda ba ya son interracting da kowa ya fi gane kaɗaici da rashin magana yana shiga ƙuncin ko damuwa duk akwai alamar tambaya kanshi, Don Allah a taya mu kula da ita idan tana samun kulawa in No time za ta ji sauƙi ta komawa aikinta in Shaa Allah”Sameera ta riga mommy magana “In shaa Allahu Dr. Za mu yi duk yadda ka ce Allah ya bata lafiya”Yayi mata murmushi kan ya amsa da Ameen itama dai fuskar nan cike da fara’a take ta kallonshi.Mommy ta ce “Ba na son ka faɗawa Salim, ka ga yana wurin aiki kar ya zaci ba ma saka ido ne a kanta duk hankalinshi ya tashi, bills ɗin ka dinga turomin zan ke covering”Ya gyaɗa kai kawai yana kokarin Miƙewa Sameera tace “Ko ruwa baka tsaya ka sha ba?”Ya ce”No na gode, ai daga gida na fito”Daga an suka fice suka bar su.Wayanshi ya zare bayan ya yiwa motar tashi key ya ɗan zubawa Layin salim ido yana nazarin abin da ke faruwa, Salim ya ce kar mamanshi ta san shi ya turo su, mamansu ta ce kar salim ya san Afeefah bata da lafiya to me kenan? Ɗan shrugging Kafada yayi kan ya danna ƙiran salim yana ficewa daga harabar gidan, kaman jira ko ringing na farko bai yi ba salim ya ɗaga “Ya ya jikin nata Dr.? Is it worst? Sai an tafi hoapital ko?””Calm down Captain jikin da sauƙi”Nan ya shiga koro mishi bayanin yadda suka yi da mommyn. Numfashi ya sauƙe bai wani ji damuwarshi ya ragu ba don ya san da matuƙar wuya su bi ta kanta, roƙon Sulaiman yayi da akan ya dinga zuwa yana duba masa ita kaman yadda yayi alkawari.Yana dan murmushi yace”ba ka da matsala in shaa Allahu””Thank you so very much Doctor””Ɗo not mention”Daga nan suka ajiye wayar.”Oh ashe wannan baiwar Allahn aiki take gidan su salim ɗin?”Baaba tayi maganan da alama dai har yanzu tana jimamin yadda suka tafi suka bar Afeefah ɗin.”Ni ma sai yau nake fahimtar hakan Baaba, kaman kuma mutanen gidan ba su ɗauki ma’aikatan su da muhimmanci ba”Ta ɗan juya kai cikin manyanta tace”ko kuma ita Afeefar ce ba su ɗauke ta mutum ba ba”Ajiyar zuciya ya sauƙe daga nan bai sake magana ba itama haka har suka isa gida, ta sauka kenan yana shirin ƙarasar da motan parking space ta juyo ta kira shi “Alhj ƙarami Don Allah idan za ka koma da dare ko ban bi ka ba zan baka kunun gyaɗa ka kai mata kila ta iya shan shi”Ya amsa da”Toh Baaba Allah ya kaimu dare ɗin”Ya ƙarasa da motan yayi parking kan ya nufi cikin gidan shi ma don bashi da aiki da safen sai dare za shi asibitin ya kwana, Salim ne ya fitar dashi dole.Da misalin ƙarfe bakwai na dare ya fito a shirye tsaf cikin kananun kaya da suka amshi kalarshi na baƙi, skin ɗin shi da yake kalkalewa tamkar mace sai shining yake don shi mutum ne mai tsananin tsafta, hannun shi rike da ninkakken labcoat ɗin shi, mahaifiyarshi Hajiya Amina da ke zaune cikin kujera ta ɗaga kai ta kalleshi “An fito kenan bokan Turai?”Yayi murmushi yana furta “Eh umma zan fara bi gidan su saleem akwai patient da zan duba kan na wuce asibitin””A’ah ko dai wacce Baaba jummai ke ta jajenta tun safe?””Ita fa Umma da safe mun fita kina bacci, ko da na dawo ban leƙo ba ashe Baaba kam tayi ta baki labarin Afeefah”Tana murmushi tace “Ai ina ga zuwa yanzu kowa ya san labarinta a gidan nan, Allah ubangiji ya bata lafiya. Sai ka leƙa kitchen ta yi mata kunu da ferfesu ka karɓa ka tafi mata dashi”Yayi murmushi kan ya amsa yana nufan kitchen ɗin baabar tana side ɗin su bai neme ta bane saboda ba gida zai dawo ba daga chan asibiti zai wuce shiyasa ma bai ba kanshi wahalar neman ta ba don sai yayi mata dogon bayani da kyar ta fahimce shi, kwando ne mai kyau da tsari ta shirya mata komai ciki, ya dauka kawai ya fito yana yi wa Ummarshi sallama take sanar mishi Abban su yace ta sanar mishi lallai lallai yana son ganinshi da safe saboda kullum a saɓani suke.Ko da ya isa gidan su saleem a mota ya cigaba da zama yana tunanin yadda zai nemi iso don bai ga gilmawan kowa ba, sai time yake dubawa ganin zai iya makara ya sa ya sauka ya nufi mudi dake zaune bakin gate da iliya.”Assalamu Alaikum warahmatullah” Yayi musu sallamar yana sake miƙa mishi hannu duk da sun gaisa Shigowar shi “Don Allah ku dan yi haƙuri zan shiga lokacin aikin ku, Afeefah nake son gani ko za ka min iso?”Shiru suka yi cikin tunanin wacece ma Afeefah a gidan, a tare suka tuna ta sai suka kalli juna suna zazzaro ido, mudi ya ce “A’a malam sai dai ko in nema maka Talatuwa ta maka iso amma mu kam magana ma da wacce ka ambata ya haramta tsakanin mu har Abada”Ya ƙarasa cikin yanayin jimami da tabbatarwa iliya ma na gyaɗa kai tabbacin hakan ne.”Magana ya taɓa haramtuwa tsakanin musulmi da musulmi kuwa Malam mai gadi?”Yayi maganan yana ɗan dariyar yadda suke reacting.”Kai dai in ana sallah ba’a magana”Iliya ya faɗa, tuni mudi ya nufi ciki ta baya ya bi ya tsaya daga kofan mashigan kitchen ɗin “Talatuwa akwai wadda ke neman iso wurin yarinyar nan mai wanke-wanke zo ki ji da shi”Sameera da ke shigowa kitchen ɗin ta ɗan yi jimmm kan tace”Talatuwa ci gaba da aikin bari na je”Da kallo Talatuwa ta bi ta har ta ɓace, sai da ta koma ɗaki ta dubi kanta ta kuma ƙara turare kan ta fito ta nufi waje, Sulaiman na ta bugar cikinsu don ya ji dalilin rashin mata magana kuma wai na har abada dole ya sa suka shiga bashi labarin abin da saleem yayi musu, Sossai Sulaiman ke dariya… Tahowar Sameera ta wani zuba mishi idanu tana tsintar kanta da murmushi.Kallon farko da ta mishi ya tafi da imaninta, ya shiga ranta fiye da yadda tarin samarin da suke bibiyar ta, a yanzu da ta ci karo da shi yana dariyar nan kuma sai taji tana narkewa, zuciyarta na wani irin macewa a kanshi, ganinta ya sa ya tsagaita dariyar shi, ta shiga gaishe shi ya amsa yana murmushi “Whats so funny haka Dr.?””Ki bari kawai ni da su mudi ne, zan iya shiga?”Ta ɗan yi farrr “Sauri kake haka?”Ya ɗan duba time a agogon dake ɗaure bisa tsintsiyar hannun shi”Kusan hakan don kaman na shiga lokacin aikina”Ya ƙarasa yana nufar mota, ta bishi suka jera.”Ai ma kuna ƙoƙari SLT nake karantawa amma ji nake kaman na gudu bare likitance da aikinshi”Ya ɗan yi dariya bai ce komai ba, ta tsaya tana kallonshi har ya buɗe booth ya ɗauki kyakyawar basjet da Baaba jummai ta shirya mata kunu da ferfesu ɗin kayan ciki da suka nuna suka yi tuɓus cike da kayan kamshi, ganin basket ɗin sai da ya ba Sameera haushi amma ta danne, ta sake ganin ƙatuwar leda sai zuciyarta ya shiga tambayarta Anya alaƙar nan na likita da marar lafiya ne ko akwai abin da bata sani ba? Amma me Afeefah take dashi da guy irin Sulaiman zai so ta? Dukda haka zuciyarta bai huta da bugun tara-tara ba, kar dai ta faɗa soyayyar abin da ba za ta samu ba, ji tayi bata da ƙwarin gwiwar bin shi don tabbas matukar ta bishi ta fahimci akwai alaqa tsakaninsu zuciyarta zai iya bugawa ko ta shaƙe yarinyar har lahira, ba za ta iya bin shi ba sam bata da ƙwarin gwiwar. Ta manta cewa kwata-kwata ma yau ne ta fara ganinshi har da zaƙewa haka, wayar ƙarya ta ƙirƙira ya ɗan kalleta”Ka je Dr zan sameka”Tana kai nan ta juya tana cigaba da magana a ƙarya, shi kam bai damu ba ya nufi ɗakin Afeefah ɗin a kan varender ya tsaya yayi knocking, a jiran da ya ɗan yi ya fahimci maza ne cikin ainihin Boys quaters ɗin don ga wani murya na waya, kuma shine aka ajiye mace tare da su? Sam tsarin bai mishi ba… Anan ne kuma ya shiga tuna hirar su iliya sai ya fahimci saleem yayi hakan ne don ya bata kariya Dukda haka shi abin bai burge shi ba, ya juya ya kalli main building na gidan, yanzu duk girman gidan nan a ce babu inda za’a ajiye Afeefah sai cikin maza?Kimtatar lokaci yayi daga knocking da sallamar shi zuwa yanzu kan ya tura kofan ya shiga da wani sallama again, ta lallaɓa ta tashi zaune ta sanya hijabi tana jingine da gini ƙafafunta na cikin bargo “Sannu da zuwa Dr”Ta faɗa cikin sassanyar muryarta da ya ƙara ƙasa sossai.”Sannu Afeefah ya jikin dai?”Ya faɗa yana ajiye abubuwan hannunshi”Da sauƙi”Plate na safen nan ya ƙara gani a yadda aka ajiye da safe, wani tunani ne ya darsu a ranshi hakan ya sa ya miƙa hannu ya buɗe ga mamakin shi abincin nan na safe ne still zaune cikin plate ɗin, bata ci ba don ko da Talatuwa ta shigo ta duba ta ta ɗauka ta tafi da shi don ta kawo mata wani mommy ta koro ta akan ba za su yi almubazzaranci ba sai dai ta cinye shi kan a saka mata wani.”Afeefah tun safe baki ci komai ba?”Da ɗan tausayi haɗe da zafi yayi maganan ranshi na sosuwa kwarai.Ta Yi shiru “Ina za ki samu ƙarfin jiki idan ba kya cin komai? Ai ko mai azumi zuwa yanzu dai ya sha ruwa”Tsam ya miƙe ya nufi bayin ta, ta lumshe ido bayan ya shige chan sai gashi ya fito da bowl haɗe da brush ya bata, ruwan goran da ya shigo dasu ya buɗe bakin ɗaya ya dinga zuba mata tana wanke bakin sai da ta gama tsaf ya mayar yaje ya zubar, ya dawo ya tsuguna ya saka mata peppersoup ɗin da kunun ya ajiye mata a kan kafafunta ɗayar hannunta na hagu ya miƙa mata kofin kunun ta karɓa ta riƙe idanunta na kallon cikin bowl na psoup ɗin, sai turiri da kamshi yake fitarwa.”Oya ci yanzun nan, ko in baki da kaina?”Ta girgiza kai ta sanya hannu ta dauki spoon ɗin ta shiga sha, da kaɗan da kaɗan yana matsa mata har ta sha dayawa ta sha kunun kuwa sossai, fruits da ya sayo mata ya kara mata da shi. Ta marairaice”Zan yi amai fa idan na ci, cikina ya cika””kin manta kina tare da likita? Ai aman ma tsorona yake ji Harara ɗaya tak zan mishi ya koma”Ta saki murmushi karo na farko da har hakwaranta suka bayyana, ta sanya hannu ta karɓi ayaban da ya bare mata.Magungunan ta ya duba ya haɗa Allura yayi mata a canular tana ta wash wash ya ce “Wato ɗazu ma saboda bakya hayyacinki ne kika manta da raki ko?”Ta duƙar da kai, wayanta ne yayi haske ya ɗauko ya duba “Saleemullah ne yayi miki saƙo in karanta miki?”Ta girgiza kai alamun A’a. “Zan duba anjima”Ya gyaɗa kai ya shiga Phone ya sanya Layin shi yayi flashing kan yayi saving da “Dr. Sulaiman””karɓi, zan zo gobe da safe duk abin da kika ji kina so ko sha’awa just give me a call za ki samu kin ji?””Toh Dr na gode”Yayi saurin cewa “Yanzu kam na wuce wannan matsayin tunda har jinyarki kika saka ni a bati”Tayi dariya kuma da gaskiyar shi don ta mugun samun ƙwarin jiki, da Allah bai turo mata shi ba haka za ta kwana don ba zata iya cin abincin safen ba.Sallama yayi mata ya fice don ya makara yau kam ainun.Sameera da ke tsaye jikin Window tun ɗazu ta ƙura mishi ido tana jin zafi a ranta, idan ta kimtata daidai mintunanshi Arba’in da biyar a ɗakin yarinyar me ya ajiye shi haka? Har zafi zafi take ji a idanunta shi kam da bai san ma tana yi ba tuni ya shiga motar shi ya bar gidan.

Back to top button