Ruwan Zuma Page 29 Hausa Novel
(29) Bacci sosai Haydar da Laila suka bayan nan wanda sai bayan la’asar ta tasheshi yayi wanka yayi sallah, kana ya zauna a gefenta yana tsokanarta tana basarwa. “Idan kaci gaba da mini haka bazan sake maka ba.” Ta fad’i hakan tana harararsa. “Wallahi na daina. Kin ga ma fita zan yi, zan je gidan Ammi yau ban ganta ba.” Ya fad’i hakan yana kissing kumatunta. Bayan fitarshi Laila ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana jin wani mugun kunya, wai ita ce ta yiwa Haydar wannan abun? Haydar d’in k’anin bayanta? Sai dai ta sani age is just a number, saboda ko a ina ne Haydar shine babba a kanta a yanzu. Motarta ya d’auka ya tafi gidan Ammi, tare da bak’i ya sameta wasu ‘yan unguwarsu suka mishi fatan alkhairi a aurensa ya amsa kana ya shiga d’akinsa wanda yake jin yayi kewarsa. Sauran kayayyakinsa masu kyau ya tsinta kana ya had’a tsoffin guri d’aya da sauran tarkacen da baya so zai bawa Ammi ta kyautar ga masu buk’ata. Sai da mutanen suka tafi sannan ya fito ya samu Ammi ya zauna a gefenta sai washe baki yake yi. “Ali yau me ka samu kake ta murna haka?” Dariya yayi kana ya gaisheta ta amsa tana tambayar lafiyar Laila. “Lafiyanta kalau Ammi.�? “Yau dai fara’arka ta daban ce, Allah yasa ka dauwama a cikinta.” Ta k’ara fad’i tana jin dad’i a zuciyarta ganinshi cikin farin ciki da tayi. “Baza ki gane bane Ammi. Ameen Ameen.” “Aikin banza.” Tace dashi tana tashi zata d’aura tuwo tana murmushi. Yau aka haifeta ne da zai ce baza ta gane ba? “Ammi ki bar dafa abincin bari in fita in sayo miki.” “Kaima kasan abincin waje ba burgeni yake yi ba, nafi son inyi tuwo da miyana gobe in samu na d’umame.” “Dama ke ba’a miki gwaninta. Amma akwai wani abu da kike buk’ata ne?” Ya tambayeta yana kishingid’a a jikin gini. “Babu komai Ali. Ina da kayan abinci Alhamdulillah sai fatan Allah ya k’ara maka bud’i.” “Ameen. Irin abun girkin baturen nan nake son saya miki ki daina hura murhu.” “Gas cooker?” Ta tambayeshi. “Ammi a ina kika san gas cooker? Ni cylinder mai irin tray a saman nan nake nufi.” Tsaki Ammi ta ja kana ta fara had’a itace tace, “Ka manta inda muka taso ne? Wani lokacin in bani da aiki ina shiga kitchen gurin Maman Iyabo kuma dashi suke girki.” “Ohh haka dai. Gobe kema zan saya miki ki fara amfani dashi. Idan kuma aka yi salary next month zan nema miki wata mata wacce zata dinga kwana dake tana miki aiki.” “A’a bana son mai aiki. Zama zanyi haka kurum Ina kallonta tana mini aiki? Ni me zan yi kenan? Ai zama guri d’aya ciwon jiki zai saka mini.” Dafe kai Haydar yana jinta tana ta surutai wai bata isa ta zauna bata motsa jiki ba. Sai da tayi ta gama sannan tace, “Muna zuwa gidanka fa ranar jumma’a.” “Ku nawa zaku zo?” “Mu goma dai haka zuwa sha uku.” “Ammi duk mutanen unguwan zaki kwaso? Haba mana don Allah.” Yayi maganar yana tashi zaune don bai ji zai amince da hakan ba. Bata ce komai ba taci gaba da aikin gabanta yana binta da ido. Can ta shiga d’akinta ta fito da kud’i tace, “Ka sayo mini attarugu da albasa na ashirin, daddawan ashirin, sai cittan goma da kuma kafi zabuwa na goma.” “Ammi bazan saya miki kafi zabuwa ba. Wallahi cewa ake yi yana saka cancer da ciwon k’oda.” “Kai Ali yaushe kaji hakan?” Ta dafe k’irjinta tana kallonsa. Dariya yayi cikin ranshi ya fara mata k’arya. “Jiya a office muna zaune wasu mutane suka zo irin masu wayar da kan al’umma d’in nan. Su suka fad’a mana cewa da kitsen alade ake had’awa kuma kinsan cinsa haramun ne a musulunci.” “Kai Ali!” Ta k’ara zaro ido wanda ya bashi dariya sosai. “Da gaske Ammi. Yanzu haka ma na hana Laila sakawa a abincinmu.” “Yanzu hanata abu kake yi kai tsaye ko dai shawara kake bata in taga dama ta d’auka?” Girgiza kai yayi yana murmusawa yace, “Ammi kenan. Kina son kiga d’anki bashi da iko da iyalinshi ne? Bai isa yaga abun gyara ya gyara musu ba?” “A’a. Allah ya k’ara had’e kanku.” Kawai ta fad’a kana ya fita zuwa aikanta tana murmushi. Bai jima ba ya dawo ya kawo mata abunda ta aikeshi. “Ya ka sayo mini albasa da daddawan da yawa?” “Saboda sayan gutsil-gutsil d’in bashi da riba. Tunda su suna dad’ewa a ajiye sai ki dinga sayan attarugun kad’ai.” Albarka ta saka masa kana ya mata sallama ya tafi gurin abokinsa Nasir. “Ya kamata yau kazo mu je gidana. Ko har yanzu tsoro kake ji?” Dariya kawai Nasir yaya yace, “Yau kam nine da aiki babu dama in fita, amma ranar jumma’a da zan zo in ga Amarya.” Suka kwashe da dariya suka tafa. Bai jima ba a gurin ya koma gida ana kiran sallan magrib, sai da yayi sallah a waje sannan ya shigo gidan ya bud’e k’ofar falon. K’amshin turaren wuta ne ya fara dukan hancinsa ya lumshe idanunsa kana ya bud’e ya k’arisa shiga ciki. A kitchen ya sameta tana tuk’a tuwo tayi wanka ta canja kayan jikinta ta saka wata farar doguwar riga mai laushi mai guntun hannu. “Ka dawo?” Ta fad’i hakan bayan ta amsa sallamarshi. “Eh.” Ya isa gurinta ya rungumeta ta baya ya kwantar da kanshi a kafad’unta. “Haydar ka mini nauyi kuma tuk’a tuwo nake yi.” “Kiyi a haka.” Bata k’ara kulashi ba har ta gama tuk’awa duk inda tabi yana bayanta yana binta. “Wallahi ban san haka kake da son jiki ba.” Ta isa bakin dinning table ta ajiye kulolin hannunta shima ya ajiye plates d’in da ta bashi. “Da baki aureni ba ko?” “Ban ce ba. Ka zauna kaci abinci.” “Ke fa?” “Bana jin yunwa sai anjima.” “Nima sai anjima. Amma wannan abun zuman nake so a k’ara mini.” Ya d’aga kanshi yana lek’en fuskarta. Murmusawa tayi suka nufi falo ta zauna ya fara mata massage a kafad’unta. “Wallahi kamar kasan shi nake buk’ata. Yauwa ta nan.” Ta lumshe idanunta yaci gaba da mata yana kallon fuskarta yanda ya zama so calm. “Nima a biyani.” Ya fad’i hakan bayan ya gama mata. “Ban iya ba.” “Ki koya a kaina.” Dariya tayi ta koma saman kujeran tana jin kanta cikin nishad’i ta fara masa yana lumshe idanunsa. “Bamu yi maganan kayan aure ba har yanzu Laila.” A bazata taji maganan domin ita koda wasa hakan bai zo ranta ba. Wanda Alhaji Abdul ma ya mata ta da duk kud’in da ya bata na aurensu ta mayar mishi da kayanshi. Ko da yace ya yafe itama tace bata buk’ata ya rik’e kayanshi. “Na yafe maka Haydar, dama kuma budurwa ake yiwa ba bazawara ba.” “Kema budurwa ce a gurina.” Dariya kawai tayi ta kad’a kai taci gaba mishi da matsan idanunshi a rufe. “I’m serious Laila.” “About what?” “About maganan budurwan.” “Sai ka jira kaji tukunna kafin ka yanke hukunci.” Bud’e idanunsa yayi ya juyo da jikinshi kana ya jawota kan cinyarshi yace, “Yaushe?” Buge k’irjinshi tayi tana neman tashi ya rik’e kunkuminta da kyau ya had’e goshinsu guri guda. “Don Allah yaushe?” Shiru tayi idanunta a rufe amma a ranta mamakin yanda Haydar ya canjata take yi, tun tana jin kanta babbar mata har ta daina ta bashi girman yana yin yanda yaga dama da ita. “Sai na gama.” “Wayyo Allah.” Yayi ihu ya fara rawa daga zaune. “Wallahi baka da kunya ko kad’an Haydar.” Ta tashi ta bashi guri yana mata signa yana kashe ido. Dariya tayi ta shige d’akinta ta barshi a gurin yana ta murna. Ranar friday su Ammi suka zo kamar yanda suka fad’a, Laila ta tar6esu hannu bibbiyu kana ta kawo musu abun sha da abinci. Shi kuma Haydar bayan ya gaishesu ya fita zuwa waje inda Nasir yake suka tsaya a nan suna hira. Sai da su Ammi suka tafi sannan Haydar ya shigo da Nasir bayan yasa Laila ta saka hijabi. Yanda Nasir ya gaishe da Laila yana sunkuyar da kai ya bawa Haydar dariya amma bai ce komai ba. Daga nan kan dinning suka nufa suna cin abinci ita dai Laila ta shige d’akinta ta barsu a nan. “Kai mutumina kana hutawa fa. Ga k’aton gida ga hutu sannan ga sam6aleliyar mata kyakkyawa.” Tsuke fuska Haydar yayi kana yace, “Watch your mouth Nasir. Matata kake magana a kai, bana son haka.” Dariya Nasir yayi nervously kana yaci gaba da cin abincinsa bayan ya canja zancen. Bayan Nasir ya gama cin abinci Haydar ya rakashi bakin titi ya hau achaba ya tafi. Yana dawowa cikin gida kafin ya shiga cikin falo wayarshi tayi ringing ya d’auka ganin sunan Mas’ud ne. Suka gaisa sama-sama, Haydar yaga kamar akwai matsala yace, “Lafiya kam?” “Abul ya gudu bayan ya kwashi kud’i a shago.” “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ina zan sameka yanzu? Ina son mu je mu nemoshi kafin Laila taji hankalinta ya tashi.” “Gani a mota gidan naku nake son zuwa yanzu. Bana son in k’ara 6oye mata wani abu game dashi saboda a baya da nayi bata ji dad’i ba. Sannan bazamu ta6a sanin ina ya shiga ba.” “Gani a cikin gidan nima, sai ka iso.” Bayan Mas’ud ya shigo ya samu Haydar har lokacin bai shiga ciki ba yana jiranshi. “Yanzu ya za’a yi? Zaka fad’a mata ne?” “Babu amfanin 6oye mata.” Shiru Haydar yayi yana jin d’aci a zuciyarsa yana kuma tunanin wace hanya zasu bi Haydar ya shiryu. Yana son Laila kuma yana son ‘yayanta tunda ba zai so uwa ya k’i ‘yayanta ba. Duk da cewa sun girma sun mallaki hankalin kansu bai k’i ace akwai ranar da zasu bud’i ido su d’aukeshi a matsayin uba a garesu ba duk da k’ank’antar shekarunsa. Tare suka shiga cikin gidan suka samu Laila na rubutu a cikin wani Memo da take yawan rubutu a ciki. Ganin Mas’ud yasa ta fad’ad’a fara’arta suka gaisa. Bata tambayeshi ya Abul ba kamar yanda kullum take yi sai ma ta d’auko wani hira daban tana mishi. Haydar bai ce komai ba yayi shiru yana kallonta amma ya lura tana cikin damuwa. “Kalti magana nazo muyi.” “A kan guduwan Abul?” Ta tambayeshi cikin basarwa. “Waya fad’a miki? Haydar kai ka fad’a mata?” “Ban shiga gida ba tunda muka yi magana.” “Abul ya kirani a waya da wata sabuwar number yake fad’a mini ya bar Kano, sannan duk ranar da na kashe aurena zai dawo gida.” Shiru kawai suka yi suna kallonta, dukkansu sun san cewa tana nuna brave face ne a waje amma a zahirin gaskiya she is crumbling inside. Kallonsu tayi taga duk sun zuba mata ido cikin tausayawa, haushin hakan taji ba kad’an ba ta dubesu rai a 6ace ta fara magana. “Meyasa zaku tasani a gaba kuna kallona kamar nice abun tausayawa? Shine abun tausayawa shi da ya gudu ya bar gidansu akan wata banzar magana tashi. Babu abunda zai sake damuna in dai akan Abul ne, ya je duniya kad’ai zata koya mishi hankali.�? “Karki masa baki Laila.�? Haydar ya kwa6eta ta harareshi kana ta tashi ta shige d’akinta. Mas’ud ya mik’e tsaye ya isa gurin Haydar ya dafa kad’arshi ya fita daga gidan. Ajiyar zuciya ya sauk’e kana ya tashi yabi Laila d’aki ya sameta a bakin gado, shigowarshi yasa ta kawar da kanta gefe tana share hawayen fuskarta. Zama yayi a kusa da ita ba tare daya matso jikinta ba yace, “I’m sorry.�? “Kayi hak’uri na muku tsawa.�? Itama da bashi hak’uri. “Zai dawo gida kuma zai gyara halayensa Insha Allah.�? “Allah yasa. Amma dolena na rage damuwa a kanshi tunda na lura yana hakan ne don ya bak’anta mini ya tayar mini da hankali. Zanyi ta mishi addu’a bazan fasa ba, amma abun yana cina a zuciyata Haydar, ina jin bak’in cikin abunda yake yi. Wallahi kullum halin Abul yana raina bana mantawa dashi.�? Ta fashe da kuka tana rufe fuskarta. Matsawa yayi kad’an ya kwantar da kanta akan k’irjinshi yana shiru ba tare daya k’ara cewa komai ba. Sai data fitar da abunda take ji sannan ta goge hawayenta ta tashi daga kanshi. “Na jik’a maka riga.�? “Ba komai.�? Yace da ita kana ya kalleta kad’an yace, “Ina kike tunanin zai je?�? “Babu wanda zai nemeshi saboda ba samunshi za’a yi ba. Duk ranar daya ga dama zai dawo gida babu wanda ya sani. Bashi kad’ai na haifa ba balle bak’in cikinshi ya kasheni.�? “Zai dawo.�? “I hope so Haydar, I hope so.�? Ta share hawayenta. Text message ne ya shigo wayan wani mutum ya karanta kamar haka. ‘Ina yaron?�? ‘Ya shiga mota zuwa Abuja, yanzu haka ina seat d’in bayanshi.’Ya mayar da martani shima ta text. ‘Karka bari ya 6ace maka, duk inda ya shiga ya fita ka bishi sannan ka tabbatar ka jefa kwaya a cikin jakarshi.�? ‘An gama yalla6ai.�? Washe gari da yake saturday ne har k’arfe taran safe Laila da Haydar basu tashi ba suna bacci. Bugun k’ofar falonsu da ake yi yasa Haydar ya farka yana mutsike idanu. Barin jikinta da Haydar yayi yasa itama ta farka ta tashi ta shiga band’aki shi kuma ya zura jallabiyarsa ya fita yana goge fuskarsa. “Ana zuwa.�? Ya fad’a da k’arfi sai dai hakan bai hana duk wanda yake buga k’ofar cigaba da bugawa ba. A fusace ya bud’e amma yana ganin wata dattijuwar mata sai ya sake fuskarsa yana cewa, “Sannu da zuwa. Ki iso.�? “Munafuki algungumi dole kace mini sannu da zuwa mana tunda kayi ikonka ka kori jikana daga gidan. Ina Lamlar take? Wallahi kin ji kunya mai auren d’an cikinta. Kin ajiye yaro a matsayin mijinki yana yanda yaso dake, tirr da wannan hali da bak’ar k’addarar. Ina take?�? “Ohh tana fitowa.�? Ya shige d’aki ya barta a gurin tana masifa. “Wacece waccar matar Laila? Me dangantakarku?�? Laila da fitowanta kenan daga bandak’i ta fara goge fuskarta data watsawa ruwa tace, “Umma ce, Kakarsu Sabrin.�? Tana fad’in hakan ta fita shi kuma ya zauna yana sauraron hayaniyar Umma. A tsakiyar falon Laila ta sameta tana ta fad’a ita kad’ai. “Umma ina kwana? Ki zauna mana.�? “Ba zan zauna ba kuma ba amsa gaisuwarki nazo yi ba. Ina jikana Abul?�? Laila ta samu guri ta zauna ta dubeta tace, “Nima ban sani ba.�? “Ban gane baki sani ba!Dolenki ki sani tunda a gurinki yake kin k’i barin kowa ya ra6eshi.�? Shiru tayi kanta a k’asa tana jiran Umma ta gama abunda zata yi ta tafi domin ta saba mata hakan musamman in Abul ya dad’e bai je ya gaisheta ba. Dama kuwa Umma bata saka Sabrin a layin jikokinta tunda Aliyu ya saka mata sunan Maman Laila. “Kin cuceni Laila, kin 6oye mini shaye-shayen da Abul yake yi gashi har ya gudu ya shiga duniya saboda son zuciya da rashin kamun kai irin naki. Wallahi nayi dana sanin ranar da Aliyu ya ganki yace yana so, daa ya san zaki yi sanadiyyar lalacewar d’ansa da ko kallonki ba zai yi munafuka mai kyawun d’an maciji.�? Haydar da yake d’aki yaji d’acin wannan batu ya taso ya fito ya samu Laila tayi k’asa da kanta bata ko motsi. “Hajiya inaga hakan ya isa tunda ba ita ta kaishi bakin duniyan tace ya shiga ba. Sannan duk damuwar da kike ciki baki kaita ba ita da take mahaifiyarsa. Idan baza ki tausaya mata ba ba kuma zaki zo ki tayar mata da hankali a cikin gidanta ba.�? “Haydar don Allah kar kayi magana.�? Laila ta fad’i hakan hawaye na taruwa a idanunta. “Ni zaka yiwa fitsara? Yaro k’arami da kai sa’an jikana? Dama daga ganinka na gane kalar kwad’ayi ne kai, kuma da wannan munafurcin naka ka kori Abul a gidan nan. Kar ka sake shiga maganata domin da Lamla nake ba da kai ba mijin tace mijin Hajiya, mai jira a samu a bashi shi da uwarshi.�? Runtse ido yayi domin yaji zafin maganarta kana ya bud’esu ya sauk’e a kanta. Cikin nitsuwa yace, “Na san Laila tana girmamaki kasancewarki uwa ga mijinta na daa, so zan bari wannan karon duk abunda kika yi ya wuce amma gaba bazan bari ko da wasa ki zageta ki d’aga mata hankali ba tare dana saka hukuma ta shiga tsakaninku ba. Laila matata ce kuma nine mai kareta idan har buk’atar hakan ta taso. Ki fita daga gidan nan sannan karki k’ara zuwa idan har kinsan ba abun arziki ne ya kawoki ba.�? Sake baki Umma tayi tana kallonshi shima yana kallonta domin bazai ta6a juran aci mutuncin Laila a gabanshi ya share ba, she is his wife and he promised to protect her. “Haydar da baka tanka mata ba, ta saba yin hakan idan ta gama zata tafi.�? “Wannan karon ba sai an jira ta gama ba, ni zan dakatar da ita.�? Daga bakin k’ofa aka yi sallama sai ga Nazifi tare da Muna sun shigo. “Laila kije ki saka hijabi.�? Fad’in Haydar. Ba musu ta tashi ta shiga d’aki Nazifi yabi bayanta da ido. Gyaran murya Haydar yayi wanda yasa hankalinsa ya dawo kanshi, Haydar ya d’aure fuskarsa tamau yana masa magana ta ido ‘karka kuskura ka k’ara kallon bayan matata.�? Nazifi yayi kasak’e yana kallon ikon Allah, yaro d’an cikinshi ke mishi haka? Ko da ya lura babu wasa a fuskarsa sai ya maida dubanshi ga Umma wacce ta fara kuka tana buga k’irji tana cewa, “Ya zageni yaci mutuncina don nazo jin ba’asin inda jikana ya shiga.�? “Umma kiyi hak’uri kiyi shiru, wai meya kawoki gidan ne tun farko?�? “Na fad’a maka taji labarin shaye-shayen da Abul ya keyi ne, sannan da cewa ya gudu ya bar gida.�? “Bake na tambaya ba kuma ki rufe mini baki, kar in sake jin kin tanka.�? Ya gwatsaleta kana ya isa gurin Haydar ya mik’a mishi hannu suka gaisa yana tambayarshi meya faru tunda ya lura Umma kuka hani’an take yi bazata iya magana ba. “Ta shigo ta fara zage-zage shine nace ta daina d’agawa Laila hankali tunda ba ita tace ya gudu ba. Idan bazata kwantar mata da hankali ba bai kamata ta k’ara d’aga mata shi ba. Sannan nace bazan lamunci hakan ba domin Laila matata ce, ko da wasa bazan bari a shigo har cikin gidanta a zageta ba.�? “Kuma kayi gaskiya. Umma ki tashi mu tafi gida, idan kin nitsu sai ki dawo kuyi magana kan yanda zaku shawo kan al’amarin.�? “Bazan tafi ba sai ta dawo mini da jikana yanzun nan.�? “Hakan zai yi wuya Umma. Muna d’auka mata ledan goronta mu tafi.�? Muna ta sunkuya ta d’auki ledan wanda garin masifa Umma ta jefar a k’asa. Shi da kanshi ya jata har bakin k’ofa Haydar yabi bayansu yana cewa, “Sai anjima.�? Ya kulle k’ofar bayan sun fita. Komawa d’aki yayi ya samu Laila ta shiga wanka ya fita zuwa kitchen ya d’aura musu abinci yana jin tausayin wannan rayuwar tasu da ba’a kwana biyu sai sun had’u da tashin hankali.
Mum Fateey 👌




