Halysaah Page 45 By Khaleesat Haydar
Khaleesat na tafiya a hankali ta shiga parlon tana karanto addu’o’i a ranta don irin faduwar da gabanta yake yi isn’t normal, ga tsikar jikinta sai tashi yake, she was so uncomfortable and restless at the same time, Abdul ya kulle kofar parlon ya kalli mahaifiyarsa dake zaune cikin parlor ita da kanwarta Aunty karima da Meemah, ko wannensu da bowl cike da farfesun kayan ciki a hannu, Khaleesat ta sunkuyar da kanta ganin gaba dayansu zubo mata ido suka yi suna kallonta fuskarsu babu yabo babu fallasa, amma kana kallon kwayar idanuwansa babu abinda zaka gani sai tsantsan kiyayyarta, da kyar ta karasa tsakar parlon kamar zata harde ta fadi, ta duka kasa cikin sanyin murya ta gaishesu gaba daya, instead Momy sai ta dauke kai tana kallon Abdul tace “Flight din sai na dare ka samu kenan Babana, bayan tun sassafe Meemah tayi maka text” Aunty Karima ta hau kwalo ma mai aiki kira ta zo ta karo mata farfesu, Abdul bai ce ma Momy komai ba ganin babu wanda ya amsa gaisuwar Khaleesat cikinsu ya kalleta yace “Ta shi mu je” Khaleesat ta ɗaga kai ta kallesa amma bata tashi ba ga zuciyarta sai bugawa yake, Momy tace “Ta tashi ku je ina? Wacece ita din tukunna?” A takaice yace “Matata ce” Aunty Karima ta gyara zama da mamaki tace “Ikon Allah, ita ce er gidan barawon da yayi ma Alhaji sata har na miliyan dari kenan?” Meemah tace “Kwarai kuwa gashi kin gane ma idonki, ita ce dai er matsiyatan da Abdul ya makale ma saboda rashin sanin darajan mahaifinsa bai dubi rashin kirkin da aka yi ma Daddy a kotu akan hakkinsa ba ya koma ma yarinyar, dama yawon ta zube uwarta ta shigo yi Nigeria shi ne ta hadu da ubanta bayan sun yi watsewarsu ya aureta….” Katse ta Abdul yayi a fusace yace “Idan kika ci gaba da voicing gibberish zaki sha mamakin abinda zan maki a nan Amina, bridle ur tongue” Aunty Karima ta bude baki da mamaki tace “Amina kai tsaye? Ko ka fara shaye shaye ne Abdul? Akan shegiyar yarinyar nan kake nema kayi ma yayarka rashin kunya?” Abdul ya kalleta yace “Kar ki sake sako min baki tunda ba dake nake ba, stay out of anything that concerns me, Momy ce dolen ki ba ni ba” Momy tayi wani murmushi tace “Rabu da su Babana, take her inside ta huta, sannunku da zuwa” Tana fadin haka ta tashi ta taho kusa da Khaleesat ta dafa ta tace “Welcome my daughter, ku je sama kin ji” Da kyar Khaleesat ta mike tsaye duk jikinta a sanyaye ta bi bayan Abdul, Momy ta koma ta zauna ta bi ta da kallon gefen ido, har ta ga sun haura sama sannan ta kalli su Meemah tayi kasa da murya tace “Sam baku da hankali baku da tunani, haka muka yi da ku daxu?” Meemah da ke huci tace “Ni matsala ta kinsan ban iya pretending bane Momy, wallahi ban iya ba ko nace zan yi” A fusace Momy tace “To in kin san ruguza min plan za ki yi ki ja min asara to tun wuri ki tattara ki tafi gidan Suwaiba bana son hauka, duk ba ke kika ja mana wannan bala’i ba? da sa hannun ki fa abubuwan nan suka faru, ai wallahi sati daya yayi ma yarinyar nan yawa a gidan nan in dai ni na haifi Abdallah, don haka duk wanda bazai iya abinda nace yayi ba to ya bar gidan nan kawai kar ya ja min asara” Aunty Karima tace “Toh Momy kar kuma fa yace zai koma can gidansa da ita, kin san babu me sa shi babu me hanasa idan yayi niyyar yin abu” Momy tace “Ku dai ku zuba min ido kawai ku ga ikon Allah, ance maku ni mahaukaciya ce warce bata san abinda take yi ba irin ku? Ai ni ba yarinya bace nasan me nake yi” Mikewa Momy tayi tana tafiya gansan gansan ta nufi staircase, Meemah ta kyabe baki tace “Wallahi ji naki zuciyata bazata iya wani pretending ba akan shegiyar yarinyar nan me kamar sadaka yalla, ban taɓa jin tsanar mutum a duniya irin yanda na tsaneta ba, Abdul bai taɓa min kalan tijaran da yayi min akan ta ba, kuma fa a gabanta yayi min haka tana ji tana kallo” Aunty Karima ta sauke ajiyar zuciya tace “Nima ba gashi yayi min ba Meemah, fatan mu kawai komai ya zo karshe cikin gaggawa, mu yi yanda Momy tace kawai” Khaleesat ta dinga bin dakin da Abdul ya kawota da kallo wanda babu tantama dakinsa ne, a hankali ta zauna saman kujeran dakin tana kallonsa yana cire agogon wrist dinsa alamar zai shiga bandaki yayi alwala, abinda aka yi mata a parlor ne kawai ke yawo a kanta, tayi nisa tunanin da take yi sai gashi ya fito daga bandakin yana kallonta yace “Shiga kiyi alwala” Sosai gabanta ya fadi ta daga kai tana kallonsa, ta dake tace “Ai ban gama ba” Wani tsawan da ya gigitata ya daka mata, yana mata wani mugun kallo yace “Kar ki raina min hankali, is it going to take u forever to finish ur period? Karya kike yi kin gama” Tsabar yanda ta tsorata jikinta har bari yake ta ma rasa me zata ce masa, yace “Idan na dawo masallaci i will check for my self” Daga haka ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, hawaye ya fara zarya a idonta, wannan moment din take ta tsoro gashi ya zo kuma babu yanda ta iya, shesshekan kuka ta fara yi cikin tashin hankali, bayan ya fita da kamar minti biyu taji an bude kofar dakin, ta juya da sauri gabanta na faduwa, Momy ce ta shigo dakin ta sakar mata murmushi ta nufota tace “Ya sunanki daughter? Mu sai yace mana Khaleesat, ni dai nace Khaleesat ai ba sunan yanka bane” Khaleesat ta sauke idonta zuciyarta na bugawa a hankali tace “Sunana Hauwa” Momy tace “Maa sha Allah, ashe uwata ce, welcome to the family my dear, taso mu je kiyi sallah” Khaleesat felt a bit relieve da gesture din Momy toward her, ta mike tsaye Momy ta kama hannunta suka fita daga dakin, can bangarenta ta tafi da ita har cikin Bedroom dinta sannan ta nuna mata bandakin dake dakinta tace “Ki shiga ciki kiyi alwala, amma kafin nan let’s do a mother and daughter talk first my dear” Khaleesat ta daga kai tana kallon Momy, Momy ta nuna mata kan kujera tana mata murmushi tace “Get sitted Mamana” Khaleesat ta zauna kan 2 seater dake dakin Momy ta zauna gefenta tana facing dinta tace “Kar ki boye min komai mamata, ki daukeni tamkar mahaifiyarki, ki gaya min gaskiya wani abu ya shiga tsakaninku da Abdul ne tun bayan da ya dauke ki?” Sosai Khaleesat taji tambayar yayi mata nauyi a kai, hakan yasa ta kasa kallon Momy ta sunkuyar da kanta kawai, Momy ta kwantar da murya tace “Akwai dalilin da ya sa nake tambayarki haka ne Mamana, kar ki ji kunya ki boye min komai, open up to me” Girgiza mata kai kawai Khaleesat tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, Momy ta kamo hannunta tace “Kar fa ki ji kunyata ki boye min komai mamana, gaskiya zaki gaya min” a hankali Khaleesat tace “Gaskiya na gaya maki Momy” Momy ta dinga kallonta kamar dai bata yarda ba, can tace “To saboda me? Anya kuwa gaskiya kike gaya min Mamana?” Khaleesat bata dago kanta ba tace “Period nake yi ne” Momy tace “Toh kin gama yanxu?” A hankali Khaleesat tace “Daxu na gama” Momy ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “To naji dadin jin hakan mamana, don nasan irin daukan da Abdul ya tafi ya maki bayan dawowar ki daga makaranta, hakan bai ba iyayenki daman yi maki duk abubuwan da ya kamata su maki ba a matsayinki na budurwa kafin ki tare gidan mijinki, basu samu daman yi maki shirin xuwa gidan miji ba, amma tunda ya kawo ki nan in sha Allah zan maki duk abinda ya kamata diyata….” Ita dai Khaleesat tayi shiru har sannan bata dago kanta ba, Momy ta mike tace “Ta shi mu je bandaki ki ga….” Khaleesat ta mike tsaye ta bi bayan Momy har zuwa bandakinta, Momy ta nuna mata wani babban flask tace “Kin ga wannan flask din? To zaki dinga tsiyayan ruwan ciki ki sirka da ruwan zafi a pampo ki dinga tsarki da shi” Momy ta dauko wasu ɓakakken sabulai dake nannade a leda ta mika mata tace “Sabulan nan su ma tsarki zaki dinga yi da ko wannensu, in kin yi sai ki ajiyesa inda kika ga na dauko yanzu don naki ne” Momy ta nuna mata wani roba dake rufe a bandakin shi ma tace “Wannan ma diba zaki yi kiyi tsarki da shi, kin ji?” A hankali Khaleesat tace “Toh Momy” Momy ta dauko wani kwalba dake boye a cikin bandakin, Khaleesat dai bin ta kawai take da kallo ta bude flask din ta tuttule abinda ke cikin kwalban, sannan ta mike tace “Yauwa mamana, duk ki tabbatar kinyi amfani da su yanda nace, sai kiyi alwala ki fito” A hankali Khaleesat tace “Toh Momy” Daga haka Momy ta fito daga bandakinta ta shimfida ma Khaleesat darduma, sannan ta zaune kan kujera ta jirata har ta fito daga bandakin, Momy ta mike ta nuna mata darduman tace “In kin idar da sallan kar ki fito, kiyi zamanki zan kawo maki abinci” Khaleesat tace “To Momy” Daga haka Momy ta fita daga dakin ta kulle da key ta tafi da makullin tana ɗan murmushi, a corridor ta hadu da Abdul ya taho daga dakinsa bayan ya shiga bai ga Khaleesat a ciki ba, Momy tace “Har ka dawo masallacin Babana?” Yace “Na dawo, tana ina ne Momy?” Momy ta ja kunnensa tace “Yanxu abinda kayi ma yayarka ya kamata Babana? Kasan ta fa wani lokacin ba hankali ya ishi yayar taka ba, da sai kayi hakuri ka kyaleta da halinta kawai” Ya hade rai yace “Dukanta fa take kokarin yi Momy? A ina ta san ta ko kuma me tayi mata da zata zageta kuma ta nemi ta doketa??” Momy ta kama hannunsa suka shiga dakin baƙin dake kusa da su tana kallonsa tace “Ai na mata fada sosai Babana, yanxu ma haushin abinda kayi mata ne yasa tayi abinda tayi a parlor amma kayi hakuri kaji Babana” Yace “Naji, ina Khaleesat din take?” Momy tace “Bazan fa baka matar ka ba sai zuwa jibi in ma zaka cire ido a kanta ka cire, tun da baka bari iyayenta sun gyarata yanda ya kamata ba to ni zan gyarata” With confusion Abdul yace “Gyarata kamar yaya Momy?” Momy tace “Ka taɓa ganin inda aka dau mace budurwa aka kai ta gidan miji haka nan? To fin karfin iyayenta da kayi kuma suna shakkar ka shi yasa suka baka ita haka babu yanda suka iya maka, amma a al’adar mu ta Hausa babu inda ake yin haka, ni kuma kaga bazan baka ita ba sai nayi mata duk abinda ya kamata na gyarata, in kuma rashin kunya zaka yi min to yi Babana, Khaleesah dai bazan baka ita ba sai zuwa nan da jibi in sha Allah, zan mata duk abinda ya kamata a matsayin ta na ‘ya ta” Abdul ya kasa cewa komai yana kallon Momynsa, Momy tace “Mu je ka ci abinci” Bata jira cewarsa ba ta fita daga dakin, bin bayanta yayi ya fita amma duk tsaurin idonsa sai yaji nauyin ce ma uwar tasa komai, haka nan Momy ta dauko masa abincinsa da ta hada masa da kanta ta jera masa su a dinning sannan ta koma kitchen zata hada abincin Khaleesat, Abdul ya zauna kujeran dining amma ya kasa cin abincin, shi fa bai yi niyyar ma kwana gidan da Khaleesat ba don irin burin da ya ci a kanta yau ai sai Allah, nan da nan yaji ransa ya baci, ya mike ya shiga kitchen ya samu Momy ta sa mai aikinta ta jera ma Khaleesat abinci a tray, don irin abin da ta hada mata har ya fi na Abdul, Momy na kallon mai aikin tace “Tafi ki kai mata bangarena ki jirani ina zuwa” Mai aikin ta fita daga kitchen din da tray din, Abdul na kallon Momy a fusace yace “Toh wai menene yasa Meemah zata ce min Daddy ba shi da lafiya critically bayan ma ashe baya kasar?” Momy tace “To ai ganin likita yaje a Amurka, ko bai gaya maka bane? Karfe hudu na yamma jirginsu ya tashi, shi yasa kaji nake cewa baka taho da wuri ba don duk zatona zaka tarar da shi” Abdul yayi shiru yana kallon Momy, Momy tace “Ni dai bari in je wajen diyata, kar ka wani huce kan Meemah don ba ita ta hanaka matarka ba” Daga haka Momy ta bar sa tsaye a kitchen din, tsaye ta tarar da Mai aikinta a bangarenta tana jiranta don kofar a kulle yake, Momy ta bude mata suka shiga ciki, Mai aikin ta ajiye abincin gaban Khaleesat, Momy na kallon mai aikin wanda ranan ne ranan farkon da ta shigo mata daki tace “Toh fita ki ban waje….” Mai aikin ta fita da sauri ta kullo kofar, Momy tayi murmushi tana kallon Khaleesat tace “Ga abinci nan Mamata” Momy ta tafi ta dauko handbag dinta ciro wani kulli ta dawo kusa da Khaleesat ta bude kullin ta barbada mata abinda ke ciki a farfesun kayan cikin dake cike a bowl tace “Maza ki shanye har romon kin ji” Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Momy ta tafi ta zauna kan kujera tana murmushi ta dau remote ta kunna TV din dakin, a hankali Khaleesat ke shan farfesun tunani iri iri na yawo a kanta, to yanxu kenan hakuri kawai zata yi da auren Abdul, since gaba daya family dinta sun nuna sun yi accepting auren, sannan ga Mum dinsa ma ta ga tana sonta, kilan zaman aure da Abdul a kaddarar rayuwarta yake, she should just accept it with good faith, most important of all gashi mahaifiyarsa na sonta, his sister won’t be an issue tunda mamansa na sonta, kawai ta saka ma ranta salama ta amshi auren tunda haka Allah ya kaddara mata, Housemate dinta ne ya fado mata, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, da sauri ta sunkuyar da kai kar Momy ta gani cikin dubura ta dinga goge hawayen tana jin wasu masu zafi na sakkowa, sai da Momy ta tabbatar ta ci abincin sosai, sannan ta umarceta da taje tayi wanka ta tabbatar ta sake tsarki da duk abubuwan da ta nuna mata a bandaki, kafin Khaleesat ta fito Momy ta dauko mata kayan bacci da inner wears, Khaleesat ta shirya tayi sallan isha’i, Momy bata tashi barin dakin ba sai kusan karfe tara da rabi, bayan ta sa Khaleesat ta kwanta kan gadonta sannan ta kashe mata wutan dakin ta bata remote din Ac a kusa da ita, tayi mata sai da safe ta fita daga dakin, har ta kulle kofar ta sake budewa ta shiga tana kallon Khaleesat tace “Ko tashi kika yi zaki kama ruwa cikin dare kiyi tsarki da abubuwan nan fa Mamana kar ki manta” Khaleesat tace “Toh Momy” Momy ta kara mata sai da safe sannan ta fita ta kulle kofar da makulli ta sauka downstairs, Abdul kadai ne zaune parlor yana kallon kwallo amma kana ganinsa kasan ransa a bace yake, Momy tana kallonsa tace “Sai da safe Babana” Ciki ciki ya amsa mata, ta juya ta koma sama zuwa dakin da su Meemah suke, duk suka dinga kallon Momy bayan ta shigo, Aunty Karima tace “Ya dai Momy duk ta yi?” Momy tayi wani murmushi tace “Tun yaushe kuma” Meemah tace “Alhamdulillahi, shi Abdul din fa?” Momy tace “Shi ai dama a miyar shinkafa aka ce na zuba masa maganin, sai ruwan lipton, na kori mai aikin taje bakin pampo tayi wanke wanke shine na samu duk na zuba masa nasa” Meemah tayi murmushin mugunta tana gyara zama sanin Momy bata bin malaman banza, kai in malami yace zai amshi kasa da 1M a wajenta ma bata yarda da ingancin aikinsa ba, inda ake aikin da gaske take zuwa, ko da kuwa miliyan biyar zata kashe bata kyashi don tasan aiki na gaske ake mata.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via +234 803 810 3096_
