Hausa novels

Zakuna Biyar Page 43 By Princess Teema

Sai da su V suka ga numfashinsa na shirin ɗaukewa ne Angelina ta yi zafan afkawa cikin wajen ta riko Arya tana tausanta, ba dan Angelina renon AZURE bace da ba shakka yau ba zata iya rike Arya ba, da kyar ta jata baya daga kan mutumin. Sai huci take yi tamkar zata kama da wuta.Kama matar V ta yi, ta miƙar da ita tana ƙoƙarin tambayarta me yake faruwa wannan mutumi yai mata duka haka?. Matar sai nishi take yi, hakan yasa V ta ce a bata ruwa, su kawo mata ruwa ta baiwa matar. Dik wajen babu wanda ya kula V, ga shi ita bata jin yarensu, su kuma basa jin turanci.Sake matar ta yi, ta nufi mutane tana masu ƴar kurma-kurma wajen nuna masu da hannu alamar zata sha ruwa. Darewa mutanen suka fara yi suna ja da baya alamar ba zasu basu ruwan ba, tsoron sojojin ma suke yi.Baya V ta koma tana mamakin mutanen, daga bayanta ta ji an taɓata, cikin zafa ta juya, tana juyawa taga wannan yarinya da suka haɗu a mission na gudanci Avaris, yarinyar tana rike da kwarya mai ɗauke da ruwa tana miƙawa V ɗin.Zazzare idanu a kan V ta yi, ta sha kuka sosai yarinyar, idanunta sun yi jajir sun kumbura, karɓar kwayar ruwan V ta yi, ta gagara zare kallonta daga kan yarinyar. Da sauri V ta nufi wajen matar, ta ɗan ɗagota ta fara bata ruwan. Sosai matar ta sha, sai da ta kusa shanye rabi, sannan ta ɗauke kai tana nishi…… Shiru wajen ya yi, after like 10 mins, kura ya ɗan lafa, wannan yarinya ta zo ya rungume wannan mata suka cigaba da kuka a tare.Ai Arya na ɗagowa ta kalli yarinyar bata san lokacin da ta baro jikin Angelina tana zazzarewa yarinyar idanu ba, ita ma yarinyar zare mata idanu ta yi ganin Arya, tabbas ta tunasu yanzu. Da gudu yarinyar ta miƙe ta ƙarisa wajen Arya.Rikota Arya ta yi, ta rage tsawonta wajen durkutsawa a kan gwiwowinta, ta rike kafaɗun yarinyar tana kallon fuskanta. Cikin harshen fillanci na bororin daji yarinyar ta ce da Arya. “Please ki taimaki addata, mijinta mugu ne, dan ta bani abinci shi ne ya ce zai daketa, ta bashi hakuri, shi ne da ta fita yawon neman itacen da zata yi girki ya zo ya cire mun kayana, ya kwantar dani a gadonsa ya hau kaina, da ta dawo ta gansa ta ture shi daga kaina tana ihu, shi ne ya fara dukanta wai zata zubar mashi da mutunci”. Tana kuka tamkar ranta zai fita tana magana, dik tana birkiceDik da Arya bata jin yarensu ta gane nufin yarinyar saboda kwatancen da take yi da hannunta, ta nuna ya cire mata kaya, ta nuna ya kwantar da ita, ta kuma nuna ya hau kanta, sannan ta nuna wancan matar ta ture shi, yanzu Arya ta fahimci fyaɗe kenan ya so yi wa yarinyar sai ALLAH ya dawo da matar tasa, dan ta dakatar da shi tana ihu ne ya hau dukanta, abin da ake cewa borin kunya, tabarmar kunya da hauka ake naɗeta.Ai wani irin tafarfasa Arya ta ji zuciyarta yana yi mata, a fusace ta saki yarinyar ta miƙe, gadan-gadan ta nufi mutumin, su dama ai aikinsu shi ne dakatar da ɓarna, kansa ta yi, ta zare ƙaramin wuƙarsu na sojoji dake da mazauni a jikin takalmarsu.Zare wuƙar ta yi, yana wani kyalli saboda kaifinsa, mutumin yana baje a ƙasa yana nishi sama-sama. Ai tana zuwa ta damki mazargin wandonsa, zata yi mashi kaciya part two tin da shi ɗan iska ne!. Nan fa mutanen dik suka watse suka fara ihu, wasu mata ƙalilan ne suka tsaya, basu wuce su 8 ba, suka tsaya suna kallon Arya cike da jarumta. Cikin harshen fillanci suke cewa Arya ta kashe shi, saboda dikkansu ya keta masu haddi, ya masu fyaɗe, ba mutumin kirki bane, ga shi kuma shi ne sarkinsu a wannan tafiya, haka yake amfani da matsayinsa na shugaban tafiyar yana keta haddin mata, dik kuma ƴan uwa tsoronsa suke ji, saboda zafinsa da mugunsa.Ya dakeka ya hanaka kuka haka yake yi. Arya bata jin me suke faɗe, ita dai ta nufi yin abin da ta yi niyya kawai. Ko kaɗan Arya bata razana ba, ta zare wandon mutumin nan, da wata abar tasa kamar karas saboda ƙanƙanta sai iskanci cike da kai, aikuwa Arya ta gille abar, tai mashi kaciya part two, tin daga ƙasanta ta yanke mashi ta jefar, sai ta yi jefa da wukar tata game da zare hand groves ɗinta ta zubar a wajen. Tana wani irin huci tamar zata kama da wuta, jinin mutumin ya fallatsa har kan hand gloves ɗinta ba iya wuƙar ba.Shi kuwa wani irin ihun azaba ya zunduma a lokacin da ta yanke, ihu ɗaya kuma ya kurma ya ɗauke wuta ɗiff alamar ya suma. Abin da Arya ta yi ya yi matuƙar gigita wannan yarinya, ihu ta kurma ita ma game da rikicewa ta rasa ina zata nufa, hakan yasa Angelina ta rikota game da rungumeta tana ɓoye mata fuskarta kan ta daina kallon mutumin ma.Ganin haka yasa wani matashi dake laɓe yana jiran ganin me Arya zata yi wa mutumin da ta zaro wuƙa ne ya dallah da gudu ya nufi cikin daji. A razane yarinyar ta fara nuna mutumin tana ihun tana faɗin har da shi ma yana cire mata kaya idan Addar tata ta tafi yin ita ce, yana cire mata kaya ya hau kanta, shi ma ƙanin wannan mutumi ne. Ai da gudu Arya ta bi bayansa shi ma, sai dai bai yi wani nisa ba ya ci karo da Zaynish da ya fito daga bakin ruwa, jin ihu a wajen yasa ya zo duba menene?. Karo matashin ya yi da Zaysh, ya bugi kirjin namiji, sai ga shi a kasa wanwar, daidai lokacin Arya ta iso gaban Zaysh da gudu tana nishi sama-sama. Kallo ɗaya Zaysh yai mata game da ɗauke kai kafin ya ce. “Lafiya?”. A daidai lokacin matashin ya miƙe zai cigaba da gudu kenan Zaysh yasa kafansa ɗaya ya kwashe kafafun matashin a in da ya zube ƙasa.Ƙamewa Arya ta yi tare da sarawa Zaysh kafin ta kora mashi jawabin abin dake faruwa. Ta faɗa game da nuna mashi ƴar yarinyar da ya yi wa fyaɗen. Kallo ɗaya Zaynish ya yi wa yarinyar, take ya ɗan rintse idanunsa, jikinsa har wani tsuma ya fara yi yana wani jijjiga saboda takaici, a yadda yaga yarinyar nan ha zata wuci 10 to 11 years ba, me ta sani da zasu yi mata fyaɗe?.Ai Zaysh bai san lokacin da ya damko matashin nan ba, wani irin jibga da ya fara yi mashi ko amaryar Aunty Ummi bai yi mata ba, ya dinga gwara kansa da jikin itatuwa. Sai da ya yi mashi lilis har matashin ya daina motsi, ya fashe mashi baki da hanci a in da ya haɗe mashi jini da majina.Jifa dashi ƙasa ya yi, ya kai hannunsa ya ware zariyar wandon matashin, ɗago idanu a kan Arya dake tsaye tamkar an sassaƙata ya yi, ta gane nufinsa, da sauri ta juya ta bar wajen, watau kada ta ga sirrinsu na maza, bai san Arya kam yanzu ya gama yi wa wani sabon kaciya ba.Tana barin wajen ya zaro wuƙarsu na sojoji dake jikin takalmansu ta jefe, shi ma babu tausayi ya datse mashi abar daga jijiyarta ya jefar. Wani irin azababben ihu da matashin nan ya kurma sai da gabaɗaya dajin ta amsa. Zaynish sai huci yake yi ya bar wajen ya bar matashin a baje a ƙasa.Ƙarisawa wajen da su Arya suke Zaysh ya yi, dan ya duba ko akwai wata matsala. Nan ya isko Arya ta tasa wannan matar mutumin a gaba tana yi mata bayanin ƴar kurma-kurma game da wannan yarinyar. Matar ta ce. “Wannan yarinyar dai a can yawonmu na fulanin tashi muka tsintota a cikin daji, dikka ƴan uwana sunki ɗaukarta, amma ni a matsayina na wacce na taso a gidanmu ina da ƙanwa kamarta, sai na ce zan ɗauketa, mijina ya ce ba zai ciyar da ita ba, haka na yarda na ɗauketa, muna rayuwa da ita a gida, mijina baya bata abinci, ni nake shiga daji in nemo mata abin da zata ci. (ALLAH sarki shiyasa ranar take kukan yunwa su Arya suka bata abinci a kudanci) Mijina baya sonta, ya sha korarta waje ta kwana a waje ita kaɗai, ga shi bamu san kowa nata ba, mun kasance tare da ita tsawon shekaru biyu muna yawo ƙasashe, tin bata iya yarenmu ba har ta koya, bamu san danginta ba, bamu san kowa nata ba”.Hakika basu fahimci maganar matar dikka ba, amma sun ɗan fahimci wasu, sun gane tsintar yarinyar suka yi, sannan sun gane cewa wannan mutumi mijin matar nan ne, sun gane yana ganawa yarinyar azaba.Da yake ba komai suka fahimtar ba sai Arya ta miƙe tana faɗin. “V muje”. Ta faɗa da nufin su tafi su barsu a wajen tin da sun hukunta mutumin…….. Zaynish da yakasance namu ne, ɗan mutan Niger girman Nigeria, tsab yana jin fillanci, sai dai baya jin na bororin daji sosai, shi ma bai gane komai yadda yakamata ba, amma ya fi su Arya fahimta.A dake cikin bada umarni ya ce da Arya. “Ki ɗauki yarinyar ku wuce da ita sansani, idan mun koma gida zamu miƙata ga gwamnati a nemi iyayenta, waɗan nan suma tsintarta suka yi”. Yana gama faɗar haka ya juya. Da sauri Arya ta kama hannun yarinyar, dan dama ta shiga ranta matuƙa, tin da ta fara kallon yarinyar a kudanci ta ji ta kwanta mata. Jan yarinyar suka yi, suka tafi suka bar matar da mijinta da sauran Fulani a wajen. Sansani suka koma, yarinyar ma ta ƙanƙame Arya sosai, da alama jininsu ya haɗu sosai, sai shasshafa hannun Arya yarinyar take yi kamar taga wani abin. Kai tsaye cikin tantinsu Arya ta shige da ita, ta zaunar da ita kafin ta ɗauko mata ragowat abincin safenta, da alama Arya na son yara, dan kuwa zama ta yi ta dinga baiwa yarinyar abinci a baki, bata ji kyamarta ba sam.Yarinyar tana cin abinci tamkar yadda dabbobi suke ci, babu wani control, turawa kawai take yi, hakan yasa Arya ta ɗaura ɗamara, ta dinga nuna mata yadda zata yi a natse. Su V dik sun zuba idanu suna kallonsu.Sai da ta tabbatar yarinyar ta ƙoshi, sannan ta bata ruwa kafin ta ce su je ta yi mata wanka, dan ta yi datti over, sai wari take yi, ga ƙananan kyawawan hakwaranta sun yi jajir saboda rashin yin brush, fuskanta dik a ƙoɗe. Su dai su V kallo ne kawai nasu, yau karon farko a rayuwansu sun ga Arya ta damu da wata, watan ma talaka, ƴar kauye, ƴar datti, kai wannan abu ya basu mamaki matuƙa, basu san so gamon jini bane, Arya irinsu ne mutanen da ake kira RESERVED PERSON, gaskiya irinsu basu da yawa a cikin al’umma, suna da tausayi amma a ɓoye, su komai nasu a ɓoye yake, basa bayyana kansu kai tsaye haka, sai dai jama’a su gane waye su ko su fassarasu yadda suke so, amma su kaɗai suka san ainahin waye su, zaku ganesu ne kawai ta aikinsu a aikace ba su fito fili su faɗa maka waye su ba, dik yaran GAT ita kaɗai ce wannan gifted ɗin.Wanka ta yi wa yarinyar a cikin tantin da suka kafa da sunan toilet, da kanta ta ɗebo ruwa a bakin teku, ta wanke mata wannan uban gashin kan nata dake da mugun yawa, tsantsi da tsawo, dan har ya ɗan zarce mazaunanta a tsawo, ga shi bakinkirin da shi har yana wani curlyn.Da shampoo na SB-LUSH (Stars body lush shi ne na taƙaita maku da SB-LUSH) sai kamshi shampoo ɗin gashinta yake yi, take ya ɗauki kyalli. Arya ta naɗeta da towel ɗinta suka fito suka koma cikin tantinsu, ta shafe yarinyar da mayukansu masu daɗin kamshi, sannan ta ɗauko doguwar rigar dake tsaya mata a cinyoyi ta sanyawa yarinyar, ya kai mata harƙasan gwiwa.Zaman gyara mata gashi Arya ta yi, tana tajewa yarinyar tana kuka saboda zafi, haka Arya ta dinga ce mata sorry har ta gama gyara mata, sannan ta shafa mata mai, ta ɗaure mata a tsakiyar kai game da kitse mata jelar, ta yi mata rolling na jelar jikin tibka. Take yarinta kyanta ya fara fitowa, ta ji gyara, kamanninta da Leo ya ƙara bayyana, bare ma idanun nan nasu. Wajen kwanciyarta Arya ta kwantar da yarinyar. Baiwar ALLAH, tata ci ta ƙoshi, ga wanka da aka wanke mata dauɗa, aka rabata da dattin gashinta, sai ta ji duniya sakayau, wani niimantaccen iska na shigarta, tuni ta ɓige da barci. Ita kuwa baiwar ALLAH Arya sai ta jawo laptop tana faɗin V ta zo ta faɗa mata kilomita nawa ne tsakanin daga nan zuwa in da aka harbe drone ɗinta. Jawo laptop dinta V ta yi, ta fara kora mata bayani.Nan Arya ta fahimci suna da mugun nisa daga in da suke da in da aka harbe drone ɗin, rucksack ɗinta ta jawo, ta fito da ɗan karamin drone mai kama da fly, irin ƙananan ƙidajen nan, ba zaka taɓa cewa camera bane, wlh zaka zaci ƙuda ne, na sirrinsu ne, sai abu ya yi tsamari suke tura irinsa. Shi ta saita ta yi connecting na camerar da laptop ɗinta, sannan ta sakesa game da fara controlling ɗinsa ya nufi in da aka harbe na V.While Leo yana zaune bakin ruwa shi da Noor, suna waya da Captain Onbish, kun san yi mugun sabo da Captain a lokacin training, shi ne ya kira Captain ɗin yana son latsa shi ya ji ko akwai wani ƙarin haske da zai samu kan manyansu na soja, dan yanzu ba sojojin ruwa kawai yake zargi ba, har da nasu sojojin.Sun jima suna waya da Captain, sai kara kwarara masu gwiwa Captain yake yi, daga karshe Captain ya ce. “Ban taɓa son wasu sojoji da na horar irinku ba, ba zan so mu rasa haziƙan sojojin irinku ba, Nirash ka kula sosai, arewaci ya sha banban da kudanci, sannan shawarar da zan baka ta ƙarshe, wannan daga zuciyata ce a matsayin aboki ba shugaba ba, lallai ba umarnin kowa zaka karɓa ba a lokacin da kake tsakanin mutuwa ko rayuwa, a wannan lokaci ka ɗauki umarni mai kyau ka watsar da mara amfani, sannan kada ka yarda da kowa a bakin aiki, kowa yana iya cin amanarka a bakin aiki, dayawan mutane abin duniya na canzasu a lokacin da baka tsammata ba, dayawan manyan sojojinmu masu gaskiya an kaisu ƙasa ne tare da sa hannu da haɗin bakin na jikinsu, gaskiya ta yi ƙaranci, dan haka team 1 ku kula matuƙa, ku riƙe amanar junanku, kada ku yarda da kowa”. Tin da ya fara magana Leo ya yi shiru yana saurarensa, da ya kammala okey thank you sir kawai ya ce mashi, suka yi sallama. Shiru Leo ya ɗan yi yana tinanin kalaman Captain bayan ya katse kiran, lallai ya samu ƙarin haske bana wasa ba. Captain bai fito ya faɗa mashi me a karkashin ƙasa ba, amma waɗan nan maganganun sun fi wa Leo komai, watau dik wani soja da za’a kashe da haɗin bakin sojoji na kusa da shi.Kuma haka ne, ya za’ayi a kashe soja ba tare da haɗin bakin na kusa da shi ba? Impossible ai, ya samu karin haske a nan, sannan Captain ya ce ba kowani umarni kai tsaye zai yi amfani da shi ba, which’s mean akwai umarnin zalunci kenan. Kun san wani abu ne jama’a, a lokacin horar da soja ana basu tsastsaurar wahala a kan bin umarni, ana sanya masu tsananin tsoron rashin bin umarni, ana nuna masu rashin bin umarni azabar tafi ta mutuwa, zaka ce gara mutuwa, shiyasa zaku ga soja idan manyan su suka bashi umarni, ko kuma zai yi zai tsaya a kan wannan umarni.Kun san azaban da akewa soja idan yaki bin umarni? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, hakika soja zai gwammaci mutuwa da hukuncin taka umarnin manyansa, ya rabb, azaba sai ta zautar da shi, tsoron wannan hukunci yasa yake binsu a kan komai, yana mantawa azaban lahira ta zarce ta duniya. Idan mutum yana da hankali hakika ba zai taɓa zagin ƙananan sojojin dake karɓar umarni daga sama ba, su tamkar juyasu ake yi, komai ba su suke yi ba, gangan jikinsu yake yi da kuma bin umarni! Laifin yana sama.Bayan sun gama waya ne ya dubi Noor dake faman kallon ruwa. A natse sosai ya ce. “Brother ina son Captain sosai”. Ba tare da Noor ya juyo ba ya amsa da. “Sosaima, yana da kirki matuƙa, da alama kuma yana da gaskiya”……. Kai Leo ya jinjin alamar haka ne.Shiru ya ɗan biyo baya kafin can kuma Leo ya ce. “Zan zama mutum na farko da zai kawo abubuwa dayawa a hukumar soja, zan canza tarihi, zan zama silar canzawar doka ta duniyar hukumar soja”……. Noor dake da buri irin nasa ne ya amsa da. “Zamu zama tare! Amma yanzu ya zamu yi da sojojin can da muka kama?”. Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. “Da farko na so faɗawa Captain sai na manta, amma bari in faɗawa yayana ya bani shawara, ni ina tinanin in sakesu dan basu da amfani a garemu”. Ya kai karshen maganar game da ciro wayansa, ya laluɓo number da aka yi saving da my champion, ya dannawa Aryan kira, dan yasan shi ne kawai a cikin IRON FIST zai sauraresa a gaggauce ya bashi amsa, Lion ai sai ya mashi kira 10 bai ɗauki ɗaya ba, daga karshe in ya tashi saƙo zai ajiye mashi a Whatsapp, shi kuwa guru da waya ma bata wani damesa ba, zaka kira sau uku baka jisa ba, Vir ya fi su dikka rashin damuwa da waya, dik kuma ba zasu faɗa mashi yadda zai yi ba, zasu ce ya girma da kansa, ya yanke hukuncin da ta dace, dan suna son gobensa ta yi kyau ta yadda ko babu su zai tsayawa kansa. Shi kuwa Arya komai yaya sai ya taimaka mashi, ko da shawari ne…… Bugu ɗaya Aryan dake kwance saman gado ya tada kai da cinyar Lion ne ya ɗauka game da cewa. “Hello boy”. Kara natsuwa Leo ya yi kafin ya ce. “Bro dama shawara nike son ka bani”…… Satar kallon Lion Aryan ya yi, saboda yasan Lion ɗin ya hanasu tsoma baki kan Mission ɗin. “I’m listening”. Aryan ya faɗa. Nan Leo ya kwashi dik abin dake faruwa ya faɗa mashi. Nisawa Aryan ya ɗan yi, su IRON FIST wannan ai a wajensu ba abin mamaki bane, su da suke tare da ainahin manya masu ɓarnar, Leo ne bako yake ganin cin amanar ta yi zafi dayawa har da sa hannun hukuma, dan haka sai ya ce. “Ku ɗaukesu zuwa tsakiyar teku, dik ku harbesu su faɗa cikin ruwa, kada ku barsu da rai, dan cigaba da ɓarna zasu yi, kuma kun kyauta da baku taɓa kayan ko kuce zaku ƙonasu ba, da duk abin da kuka yi wa kayan a kan ƴan ƙasan za’a fanshe”.Cike da rashin fahimta ya ce. “Brother a kan ƴan ƙasan za’a fanshe shi kuma?”. Miƙewa zaune Aryan ya yi. “Yeah, a kansu za’a fanshe, ai dik wani asarar da ka yi wa gwamnati ko ka yi wa manyan sanannu a duniya fa to a kan al’umma zasu fanshe, su basu san asara ba, dan zasu ninka cutar da suke yi wa ƴan ƙasa ne, su tsananta kidnapping, su ninka farashin kaya, su kwashi mutane fiye da kima a makarantu su ce sai an biya miliyoyi, dole al’umma su fitar da kuɗi su biya, idan suka biya kunga ai sun fanshe a kansu, ka lura dik lokacin da gwamnati ta yi wani asara to a cikin wannan ɗan tsakanin zaka ga an ninka satar mutane, an ninka fashi da makami, an ɗaga farashi abubuwa”.Ya ɗan nisa game da cigaba da cewa. “Gara da baku taɓa kayan ba, dan bashi da wani amfani ma ku kona, dakatar da mai laifi ya fi dakatar da kayan laifi! Lallai ka zaƙulo dik masu hannu a cikin lalacewar kasar, ka fiddosu ka hukuntasu, ka gwada masu jininmu ne kai, ka jagoranci tawagar da zasu tsabtace garin tas daga ɗauɗar miyagu”. Ya ALLAH muma ka turo mana waɗan da zasu jagoranci tawagar kawo mana gyara da canji yanayi, ko a cikin sojojinmu, ka a cikin ƴan siyasarmu, ko a cikin malamai, ko a cikin matasa, koma a ina ne ALLAH ka turo mana su!.Sosai Leo ya ji kwarin gwiwa da kalaman Aryan, ya yi mashi godiya, Aryan yai mashi fatan alkhairi kafin su yi sallama da juna. Dik zancen da suke yi Noor yana jinsu, dan a h-free Leo ya sanya wayar. Ɗago ido ya yi ya kalli Noor, sai ya ce. “Mu ajiye batun aiki a jefe, less talk about Islam, yakamata ka fara koyan wasu abubuwa”.Kai ya jinjina game da cewa. “Ina son hakan, kuma ina son my Juliet ta musulunta ita ma”…….. Lion ya ce. “Yakamata ku yi aure yadda addinin musulunci ya tanada”…….. Ɗan zarowa Leo idanunsa ya yi, sai kuma ya ce. “Kamar ya kenan?”. Bayani Leo ya hau yi mashi dallah-dallah. Ya gamsu matuƙa, sai ya ce to zai bata sadaki a nan, Leo yai mashi alƙawarin zama waliyinta idan ta amince, shi kuma zai kira daddynsa a waya ya shaida, ga shedu Vash da Zaynish, dama shedu biyu ma a musulunci sun wadatar, dan haka a daren yau za’a ɗaura masu ainahin aure. Sosai Leo ya ji daɗin amincewa da Noor ya yi, ALLAH sarki, kome aka faɗa mashi kan addini hannu bibbiyu yake runguma. Dan haka Leo ya zage wajen koya mashi addini, basu bar wannan waje ba sai lokacin sallar azahar, nan ne suka koma sansaninsu. Bayan sun yi sallah Leo ya shiga ya duba wannan aiki na Arya.Hayakin dai yana nan yana fita yadda yake, babu wani abin da ya canza a wannan waje, ita kuma Arya a lokacin tana ƙoƙarin samo mashi bayanai kan wajen da aka harbe drone na V, bata faɗa mashi an harbe ba, dan ita bata dogon bayani sai dai ta bada result a aikace, tana son in ta gama bincike ta tattara komai, sai ta bashi good result da ba sai ya sha wahalar tambaye-tambaye ba.Bayan ya duba ya fito ne suka haɗu da Zaynish, nan suka wuce bakin ruwa a tare da Noor and V. Da suka zauna saman duwatsun bakin ruwa ne Zaynish ya sanar da Leo batu kan yarinyar can, jinjina mashi Leo ya yi kafin ya ce. “Ku ajiyeta, idan muka gama mission muka koma sai a miƙata wa gwamnati ita a nemo iyayenta a hukumance”…… Na’am suka yi da wannan batu. Daga nan suka cigaba da tattaunawa kan aikinsu, kowannensu yana kawo hasashensa da zurfin tinaninsa kan menene a wajen wannan hayaki. Suna tsaka da hirar ne sai ga team 2 sun zo wajen, su Unays kenan. Da ido Leo ya cewa ƴan room ɗinsu su yi shiru kan wannan case ɗin, yanzu Leo ya ƙara hankalta da mutane tin da suka kama sojojin ruwan nan, da Captain ya daka mashi warning kan aminta da mutane ma sai ya kara kame kansa, dama can su basa yarda da mutane ai kun sai.Da su Unays suka zauna sai Noor ya ɗauko masu wani hira daban kan aiki, ya fara neman jin hasashensu kan wannan mission ɗin……. A haka suka cigaba da hira har dare, lokacin sallah ne kawai yake tada su. After some hours. Gari ya yi sanyi, sojojin dake sansanin gabaɗaya suna wajen wuta suna shan ɗimi, matan ma suna tare da su except Arya dake cikin ɗaki tare da wannan yarinyar nan, ta baiwa yarinyar abincin darenta sun ci tare, ta ƙara yi mata wanka, yanzu haka tana zaune a tsakiyar tantinsu rike da laptop tana ta ƙoƙarin tabbatar da abin da take zargi a kan wannan waje da aka harbe drone na V.Yarinyar kuma ta kwanta a ƙasa kusa da ita, sai Arya ta ɗago kanta ta ɗaura a kan cinyarta, ta rasa meyasa take son yarinyar sosai take kuma tausayinta. Yarinya har ta fara murmurewa kyanta na kara bayyana.A wannan lokacin ne sojojin team 1 suka fita da waɗan nan Navy ɗin ta bayan tantunansu ba tare da kowa ya sani ba, dikkansu suka ɗauki mutum ɗaiɗai suka wuce. Kai tsaye bakin ruwa suka nufa. Suna tafiya cike da jarumta, dik sauran sojojin ba wanda yasan meke wakana, suka isa cikin ruwa ta baki kaɗan. Leo yasa pistol ɗinsa ya harbesu ba tare da sun farfaɗo daga alluran barcin da aka yi masu ba, suka jefa gawarwakinsu a cikin ruwa, suka tsaya sai da suka tabbatar gawarwakin sun bi ruwa, sannan suka juya suka koma sansani.Cikin tantunansu suka shiga, suka canza kaya zuwa marasa nauyi na barci, sannan Vash, Zaynish and Noor suka fito zuwa wajen wutar nan. Leo kuma sai can ya fito game da zuwa bakin wutar.Dik suka mimmiƙe suka sara mashi, bai yi magana ba ya kira V ta hanyar yi mata alama da hannu, da sauri ta nufesa. A gefe ya tsaya ta bisa, cikin wannan natsuwa tasu ya faɗa mata abin da suka shirya da Noor. A daidai lokacin Noor ya iso wajen. Leo baya son Noor ya fara aikata ba daidai ba daga shigansa musulunci shiyasa yake son ɗaura wannan aure, dan yasan Noor ba zai hakura da daina taɓa V ba tin da sun saba.Noor na zuwa wajen ta rungumo shi game da faɗa mashi ita dik hukuncin da ya yanke ta yarda da shi. Ya ji daɗin hakan, ya ɗauko sadakin diamond chain ɗinsa ya bata, ya kira daddynsa a waya ya haɗa shi da Leo. Kun san daddy farincikin yaransa kawai yake so, dan haka ya aminta da wannan haɗi, sai dai fa ya ɗan tirge da farko, ya ce meyasa Noor zai shiga wata addinin ba tare da ya nemi shawarinsa ba?.Hakuri Noor ya dinga bashi, daga nan komai ya wuce. In taƙaice maku a wannan dare aka ɗaura masu aure irin na addinin musulunci ba tare da sanin GAT ba, sai dai sanin Aunty Lisa da ita dama kun san ai tana bayan Noor koma me zai je ya zo, tana nan dai tana cin amarcinta abinta, ta ƙara kyau, yanzu da GAT yaga su Arya sun yi dogon zango ya fito da batun auren nasa, yanzu haka ana ta shirye-shiryen dinner partyn da za’ayi a cikin barikin.V bata musulunta ba, Noor bai ce ta musulunta ba, Leo ya ce ya kyaleta da kanta zata ce zata musulunta, kuma wannan musulunci shi ne daidai, ba wanda za’a cewa mutum ya yi ba, a cewar Leo in dai tana zaune da musulmai tana ganin kyawawan halayensu tsab zata musulunta.Bayan sun ɗaura auren ne, Noor da V suka koma wajen wutar, Vash and Zaynish suka rufa masu baya, shi kuma Leo ya koma cikin tantinsa dan aikin dake gabansa, bashi da lokacin zama a bakin wuta dan jin ɗimi shi, yasan me yake gabansu. Arya ma dai irinsa ce, bata da wannan lokacin, aiki ya fi mata komai muhimmanci.A wannan lokaci Manassa ta ɗauko rucksack ɗinta, ta zo ta da nufin ta gyarawa Zaynish hannunsa ta sake wanke mashi. Da sauri Angelina ta bita, a kusa da shi suka zauna, ya ware masu tafin hannun nasa, ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon farin yashin dake wajen. Kwance bandejin dake hannunsa Manassa ta yi, ta wanke mashi hannun game da zuba mashi magani, ta sanya sabon cotton kafin ta mayar da bandeji ta rufe mashi. Sai sorry Angelina take ce mashi, shi kuma ko kaɗan bai ɗago ya kalleta ba. Bayan sun kammala Manassa ta miƙe ta nufi tantinsu ta mayar da rucksack ɗinta, sannan ta dawo ya zauna a kusa da Vash tana satar kallonsa ta ƙasan ido, while tana chatting da shi matsayin aljana, ya ce mashi taga ya kula mace yau, kuma sai ta hukunta yarinyar.Shi kuwa ya ce mata. “Wannan yarinyar rayuwata ce, in kika kasheta ni kika kashe, dan haka kin rasani kema”. Wani irin musulmin daɗi ta ji, yadda ya ce wannan yarinyar rayuwansa ne, ya rabb, sai ta ji tamkar ta miƙe ta je ta rungumesa, sai murmushi take yi, tama gagara amsar da zata bashi.Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna. —————————-🔥CRYSTAL PALACE.Ko da aka fita breakfast Seraphina ta yi rarrashin duniyar nan Rimsha taki kulata, daga karshe ma miƙewa Rimsha ta yi ya fice waje, zuciyanta baya jin rarrashi ko kaɗan, ita kaɗai tasan waye Aryan.Tana fita Uncle ya dawo kusa da Seraphina ya zauna, yana kallon kyakkyawan face ɗinta ya ce. “Baki yi kewata bane?”. Ɗan turo baki ta yi. “Na yi amma kaɗan”. Haɗaɗɗen murmushi ya sakar mata kafin ya ajiye mata chocolate ɗin hannunsa a saman table ɗinta, chocolate mai heart design, ya yi mugun burgeta chocolate ɗin, ta ɗan zaro idanu a kan face ɗinsa kafin ta ce. “Is so nice, thank you”. Ta faɗa game da miƙa hannu ta ɗauki chocolate ɗin. Zuba mata idanu ya yi, yana binta da wani irin kallon ƙauna mai narka zuciya, yana jinsa a wani irin duniya na musamman. Ita kuwa ɓare chocolate ɗin ta yi, sai taga mai zalar madara ce a tsakiya, ɗan turo baki ta yi. “Daddy ya hanani sha milk”. A dame ta ya maganar tamkar zata yi kuka. Kai wannan shagwaɓar tata yana mugun tafiya da imaninsa fa, ɗan nisawa ya yi game da cewa. “Meyasa ya hanaki shan milk?”……… Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. “There was a time da na yi ciwon ciki a school, sai muka je hospital, a nan ne aka ce in daina shan milk”.Hannu ya kai kan eyes ɗinta, ya ɗan janye fatar ƙasa na idanun kafin ya ce. “E kam dole daddy ya hanaki shan milk, anyway ki sha wannan ba dayawa bane ai, ba zai maki wani illah ba”. Ya faɗa game da cire hannun nasa daga kan fuskarta. Ai tana jin hakan ta ɗauki chocolate ɗin ta fara ci, sanyawa a bakinta ta yi zata gutsira ta cire saura kenan uncle ya yi saurin ɗago haɓarta, sai yasa bakinsa ya ɗan gutsira yana kallon cikin kwayar idanunta. Ai bata san lokacin da ta saki chocolate ɗin ya faɗi ƙasa ba, ta fasa sha, ta kuma zazzare violet eyes ɗinta a kansa sosai. Ganin ta jefar da chocolate ɗin ne yasa uncle ya ɗan miƙe yana ƙoƙarin haɗe bakinsu ya tura mata na bakinsa da ya gutsira. A zabure ta miƙe tana ja da baya. Cike da mamaki ya fara binta da kallo, dan su wannan ai ba wani abin bane a wajensu, meyasa take gudu to?. “Beb, are you okey?”. Ya faɗa yana miƙewa tsaye da kyau. Tana ƙara zazzare mashi idanu ta ce. “Dad ya hana in bar wani namiji ya taɓani, and i promised him that ba zan yi hakan ba, then mom also, ta mun warning a kan irin haka, please sir kada ka sake gigi yi mun irin wannan abin, kada ka sake gigin haɗa bakinmu, i can’t tolerate this”. Da iya gaskiyarta take magana, babu wasa a kan fuskanta.Ganin hakan ne yasa ya ja da baya yana ce mata sorry, ya ce ba zai kara ba ta yi hakuri…….. “Just go kawai!”. Ta faɗa cikin tsiwa tana nuna mashi hanyar wajen chair ɗinsa, bata son dik wani abun da zai ɓatawa daddy Champion namu rai.Uncle na juyawa zai koma wajensa ta yi gaggawar wucewa ta fito, ta nufi wajen Rimsha, ta yi ta ƙoƙarin dannarta har aka dawo class, yau ko abinci basu ci ba. Haka suka wuni a school babu daɗi, Rimsha taki sakewa su yi hira, har aka tashi school. Farya ya riga Aryan zuwa, sai ya ce da Seraphina ta zo su mai da ita gida. Tana ɗan murmushi ta ce. “No uncle, ka bari daddy zai zo, ya hanani hawa motar kowa”……….. Faryan bai matsa mata ba, ya ɗauki Rimsha kawai, da yake Rimsha jikin babu daɗi ba wani sallamar kirki suka yi da Seraphina ba, baiwar ALLAH jikinta ya yi mugun zafin zazzaɓi sosai, wani irin azababben ciwo kanta ke yi mata, duk ta fita hayyacinta, ta shiga fron seat kawai ta zauna shiru, ƙara bata hakuri Seraphina ta yi game da yi masu bye-bye. Daga nan Faryan ya tada mota suka wuce suka barta tsaye. After 10 mins da tafiyarsu sai ga daddy ya faka a gabanta, a daidai lokacin kuma Aisha ta ƙariso wajen……. Gidan baya ta buɗe ta shiga tana ɗagawa Aryan gaisuwa. Bai amsa mata ba, hankalinsa gabaɗaya yana a kan Seraphina da taki shigowa, ta yi folding hands ɗinta a kirji tana kallonsa cike da tsantsar so. Sauke glass na motar ya yi game da cewa. “Kema yau sarautar ce ta motsa irin uncle…………”. Sai kuma ya yi shiru tunawa da ya yi yanzu kowani magana ya yi rikewa take bata mantawa, dama zai ce irin Uncle ɗinta Zayra’an dake can gida yana zuba masu sarauta ne, sai kuma ya tina tsab zata ce sai ya nuna mata shi, ko ma ta tuhumesa da wani abin.Dik da bai ƙarisa maganar ba sai da ta titseye shi da cewa. “Daddy wani uncle kuma?”…… Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. “Wanda na haɗaki da shi a waya ranar”……. “Daddy yaushe zaka zo da shi?”. Shiru ya ɗan sake yi, sai kuma ya ce. “Ranar aurenmu zai zo, yanzu dai shigo mu je”.Tana ɗan tura baki ta buɗe ta shigo, ta ɗaura rucksack ɗinta a kan laps ɗinta tana kallonsa. Tada motar ya yi suka nufi gida. Yana parking ta fito tana turo baki, fitowa ya yi shi ma game da karɓar rucksack ɗinta, Aisha ma ta fito suka nufi cikin elevator. A parlo suka isko Madam da su Aunty Safiyya suna hira, suna ganinsu suka hau yi masu welcome, kai tsaye ɗakin Seraphina ya nufa ba tare da ya yi masu magana ba, ko kallon in da suke ma bai yi ba. Yana shiga ya ɗaura rucksack ɗinta a saman table, ya wuce ya hau saman bed. “Zan yi barci kada ki tasheni”.Tana turo baki, ta kai hannu ta rike waist ɗinta, tana kallon kyakkyawan face ɗinsa kafin ta ce. “My gentle chaos, waye zai yi feeding ɗina lunch?”…… Wani irin kallo ya bita da shi da idanunsa dake rikiɗewa zuwa na mai jin barci sosai, can ƙasan maƙoshi ya ce. “Aikinki nike yi ne? Maza je ki yi wanka ki je ki yi feeding kanki da kanki, dan kin samu da safe na baki ko?”.Turo baki ta ƙara yi, take ta hau hura numfashi sama-sama tamkar zata fashe da kuka. Zazzaro idanunsa ya yi. “Awwa my cherry, jeki yi wanka sai ki dawo in yi feeding ɗinki, barcin banza, ni ai naki ne, komai nike saboda ke ce”….. Wani irin murmushi ta saki wanda ya sanya shi lumshe idanu saboda kyan da ta ƙara, da sauri ta nufi closet ɗinta.Nisawa ya yi, a cikin zuciyansa ya ce. “My first love Seraphina, my rigima, my shagwaɓa, my drama, my everything, ALLAH ka mallaka mun ita, kasa tawace”. Ya faɗa tare da waro idanunsa kai tsaye sai cikin violet eyes ɗinta a dab da shi.Wlh ta yi mugun bashi tsoro, unexpected haka, dole ya razana, ga violet ɗin ya ciza sosai, ta zazzaro mashi a dab face ɗinsa, ya lumshe idanu yana tinani bai san lokacin da ta fito har ta iso in da yake ba. Ɗan ja da baya ya yi yana kallonta, a zahiri ko kaɗan ba zaka zaci ya tsorata ba, dan bai nuna alama ba. Murmushi ta ɗan sakar mashi kafin ta ce. “Daddy ina dubawa ne in ga kayi barci ne ko baka yi ba”…… Harara ya dallah mata kafin ya ce. “To ban yi ba, jeki yi wanka ki zo”……. Dama ta rankwafo kansa ne, sai ta ɗan miƙe tana murmushi.Unexpected idanunsa suka sauƙa a kan tudun kirjinta da suka bayyana ta wuyan bathrobe ɗin jikinta. Ai ji ya yi barcin nasa ma ya watse, ɗan lumshe idanu ya yi ya sake warowa a kansu, sai kuma slowly ya ɗago da kallonsa a kan face ɗinta dan yaga shi take kallo ne ko yaya. Da sauri ta ɗauke idanunta daga kansa, sarai ta ga in da yake kallo, amma ta yi kamar bata gani ba. A bayyane ya sauke ajiyar zuciya ganin cewa bata kallonsa, slowly ya dawo da kallon nasa a kan kirjin nata, ya rabb, watau matasan tula-tulan nan nata sun yi matuƙar tafiya da dik wani tinaninsa na yau. Wani irin nyawu ya haɗiya har sai da ƙashin maƙogwaronsa ta harba sama ta sake yin ƙasa. Ita kuma ja da baya-baya ta fara yi tana faɗin. “Daddy ko zaka zo ka mun wankan ne?”. Da sauri ya lumshe idanu game da warowa a kan face ɗinta, ta ɗan tsaya a tsakiyar ɗakin tana kallonsa. “Jeki yi wankanki, akwai lokacin da zan dinga yi maki ɗin yana zuwa”. Da kyar ya faɗa saboda nauyi da tongue ɗinsa ya yi mashi. Slowly ya ɗan yi ƙasa da eyes ɗinsa izuwa kan tsala-tsalan cinyoyinta da suke jajir tamkar ka taɓa jini ya fita, suna wani sheƙi, ga shi kunsan gaban bathrobe ɗin a buɗe yake, sai wannan igiya tasa da ta ɗaure tsakiya, so sama wajen wuyan a buɗe, haka ƙasa daga wajen igiyar cikinta a buɗe yake. A iya tsakiyan cinyoyinta rigar ya tsaya mata, ga shi a buɗe, har farin pant ɗinta na ciki yana iya hangowa. Da kyar ya danni zuciyansa ya ɗauke kallonsa daga kanta, muryansa tamkar wanda yake a cikin maye ya ce. “Cheery kina buƙatar shopping, waɗan nan riguna din sun maki gajarta, kin cika tsawo dayawa, kina saurin girma sosai”.Tana ɗan murmushi na ganin ta rikita shi ta amsa da. “Daddy ni su nike so, sun fi daɗin sakawa, so ba sai an mun shopping ba”. A shagwaɓe sosai ta faɗa, in baku manta ba ai ta cewa Rimsha zata yi maganin daddy very soon, shi ne ta fara tin yanzu, tana goge mashi hadda.Baya son sake juyowa ya kalleta, sai ya ɗaga mata hannu kawai yai mata alamar taje. Tsabar rashin ji irin na yarinyar nan a maimakon ta je ɗin, sai ta nufosa, tana turo baki game da shagwaɓa ta ce. “Daddy nice baka son gani?”.Yana ƙoƙarin ce mata a’a sai ji ya yi ta haye gadon, ta dawo ta in da face ɗinsa yake facing tana saka mashi kukan shagwaɓa. Ai kawai zuba mata idanu ya yi, ya gagara motsa ko da ɗan yatsansa ne. Ita kuwa kuka take sosai na shagwaɓa game da rike hannunsa da yatsunsa suke ɗan rawa saboda yanayin da jikinsa yake. Ai bai san time ɗin da cikin zafa ya fisgota ta faɗo jikinsa gabaɗaya ba, da yake bai saba ba, bai taɓa jin irin wannan yanayi ba, sai gabaɗaya jikinsa ya hau kerma, musamman yatsun kafafunsa dana hannayensa. Juyawa da ita ya yi, ya mata runfa da lion chest ɗinsa, hannunsa na rawa ya kai saman wuyar rigar jikinta, ya yi ƙasa da wuyar yana ƙoƙarin taɓa mata tula-tulanta.Ƴar ƙaniya gabaɗaya ta rikice, wani irin tsoro ne ya dira mata a rai, take jikinta ya fara kerma, turesa ta fara ƙoƙarin yi tana ambatar sunansa game da bashi hakuri, hakan ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa. A zabure ya dakatar da kai hannunsa kirjinta, a zabure ya miƙe daga kanta, ya saketa da sauri. Cikin zafa ya diro kasan bed ɗin.Door ya nufa, ko sau ɗaya bai waiwayota ba har ya fice cikin zafin jini. Yana fita ya nufi benensu yana furta auzubillahi minasshaiɗanin rajin, yana koran shaiɗanin da ya kusa galaba a kansa, ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi da hannu ɗaya, har wani irin jiri yake gani. Ita kuwa yana fita ta diro ƙasa, jikinta na kerma ta afka toilet da gudu, ƴar ƙaniya ta tsorata.Zaune ya isko Vir and guru a saman sofas dake balcony suna hira, Lion yana wanka. Jikinsa sam babu kwari ya wuce ya kwanta saman sofa, ya tada kai da cinyar guru yana mayar da numfashi a hankali-hankali.Duka Vir ya kai mashi a damtsen hannunsa yana faɗin. “Yana ganka a wannan yanayi?”…….. Shiru bai amsa masu ba, ya lumshe idanu kawai. Gashin kansa guru ya fara shafawa yana faɗin. “Kai Vir ka kyale champion, yanzu ya wuci yadda kake tinani”. Vir zai yi magana Lion da ya fito wajen yanzu ne ya ce. “Aryan come”. Ya faɗa tare da juyawa yana hararar Vir ya koma ciki. Da kyar Aryan ya iya miƙewa ya rufa mashi baya, Vir ya dawo da kallonsa a kan guru kafin ya ce. “Kamar wani abin na damun ɗan uwanmu”……… “Ba komai”. Guru ya bashi amsa, watau idan kuna neman mutum mai mugun zurfin ciki na wuce misali to ku samu guru, kunga dai ba laifi bane ya nunawa Vir cewa Aryan ya faɗa soyayya ne tin da basa ɓoyewa juna komai, amma ba zai iya faɗa ba tin da Aryan ɗin bai faɗa masu ba. Shi in kun fahimcesa ko a tsakaninsu ne ba zaku taɓa jin maganar waninsu yana faɗawa wani ba, zai nuna kamar bai san komai ba, idan Aryan ya faɗa masu to fine, in bai faɗa masu ba shi dai ba za’a ji daga bakinsa ba.Sosai Vir ya damu yana ganin kamar Arya bashi da lafiya ne. Amma guru ya hakikance lafiyansa lou. Dole Vir ya rufe zancen suka ɗauko wani chapter. A can kuwa Lion ne zaune a gefen bed suna fuskantar juna da Aryan, cikin tsantsar natsuwa Lion ya ce. “Na nemi zaɓin ALLAH kan komawa gidan daddy da bayyana manufarmu ga duniya, na samu natsuwa a kan hakan, sai dai ina jin zuciyata babu daɗi sosai”. Ya yi shiru yana yin ƙasa da idanunsa.Babu mai fahimtar Lion biyun yadda Aryan yake fahimtarsa a duniya. Shiyasa magana irin wannan yake fara yi da Aryan ɗin kafin su Vir, kuma a irin wannan gaɓa ya fi son jin ra’ayinsu one by one ba tare da sun ji ra’ayin da ɗan uwansu yake badawa ba, shiyasa sai ya yi zama da su one by one. Nisawa Aryan ya ɗan yi, tuni ya wastsake daga komar da ya shiga na love, ya dawo daidai ɗan duniya, ai Lion ba’a kawo mashi wargi da shirme…………… “Tin da har kayi addu’a, kuma ka samu natsuwar zuciya kan can ɗin, to ina ga is better ne can ɗin shiyasa”.Kai ya ɗan jinjina alamar haka ne, shiru ya biyo baya for like 2 mins, Aryan ne ya katse masu shirun da cewa. “Our Lion ina neman wata alfamar”……. Zazzaro jade eyes ɗinsa Lion ya yi, bai taɓa jin Aryan ya nemi alfarma a wajensa ba, abin da yasani shi dai komai nasu na juna ne, komai nasu ɗaya ne, amma yau Aryan yake batun alfarma? Menene wannan da girma haka?.Shiru Lion bai tankar mashi ba, da yake suna fahimtar shirunsa sai Aryan ya gane yana saurarensa kenan, wlh shi kansa Aryan ɗin zuciyansa a razane yake da kalaman dake shirin fitowa daga bakinsa, amma bashi da wata mafita ne, sai ya daure da cewa. “Alfarmar da nike nema shi ne ina son ɗauko sister ɗinta in kawota nan ta ɗan zauna for some days”. Tamkar fuska tamau Lion ya yi har sai da Aryan ya ji kishi ta kama shi….. “Reason?”. Lion ya faɗa a dake….. “Kada ka tambayi reason please, zan faɗa maka gaba, yanzu dai please bro, ba zata jima sosai ba”…… Shiru Lion bai sake yin magana ba, sai ma miƙewa da ya yi zai bar wajen, saboda baya son abin da zai ɓatawa Aryan rai, kuma shima baya son ransa ta ɓaci a wannan lokaci.Binsa da kallo Aryan ya yi yana tinanin yadda zai ɗauko Rimsha, har Lion zai fita Aryan ya ce. “Our Lion yarinya ce ƙarama, zata……..”. Maganar tasa ta dakata ne sakamakon juyowa cikin zafa da Lion ya yi, wani irin kallo ya wurga mashi kafin ya ce. “Mace ko jaririya ce zafin cizonta ya fi dafin kunama! Ko yau aka haifeta kada ka kuskura ka jawota cikin rayuwarka!!”. Ai Lion an shaka ka warke, kome zaka ce mu mata ba zamu ga laifinka ba, sister Lazy ai sai shiru.Maganar da ya yi ne yasa su Vir shigowa cikin room ɗin da saurin dan ganin menene yake faruwa, a fusace Lion ya juya ya fice da sauri. Miƙewa Aryan ya yi, ya kwanta a gado cike da tinanin yadda zai yi ya dawo da Rimsha gidan, ya yi rantsuwa da ALLAH sai ya dawo da ita.Saman bed ɗin su Vir suka hau suna tambayansa menene yakefaruwa tsakaninsa da Lion? Banza da su ya yi, suka tambaya har suka gaji bai yi magana ba, daga karshe ma rufe idanunsa ya yi tamkar mai barci. Dole suka kyalesa suma. ————————🔥KHAIZA’AN’S HOUSE.Su Abba sun ɗauko Aunty Luna lafiya sun dawo da ita gidan, a lokacin da Rimsha ta dawo daga school sai ya isko Aunty Luna a gidan, ɗan baya-baya da ita ta fara yi tana rakuɓewa.Aunty Luna watayyar mace, kuma da kallo ɗaya ta ji Rimsha ta shiga ranta, sai ta jata a jikinta, tin bata cire uniform ba ta rikota game da cewa su je ta cire mata uniform ta yi wanka. A lokacin su Abba dik basa nan, ya ce Harleen ya kashi shopping dake saman nan da kansa ya sayawa surukarsa kyauta ta ban girma na maraba da shigowa Khaiza’ans family. To shi ne suka tafi, Ammie na ɗakinta, Faryan yana shigo da Rimsha suka gaisa da Aunty Luna ya wuce room ɗinsu. Kama hannun Rimsha Aunty Luna ta yi suka nufi ɗakin Rimshar tana tambayarta meyafaru idanunta suka kumbura sosai har haka. Ai tamkar Rimsha jira take a tambayeta, fashewa da kuka mai tsuma zuciya ta yi, sai kawai ta juya ta rungumi Aunty Luna tana cigaba da kuka, anki a fahimta, anki a gane damuwarta, kowa yana ganin kamar zasu yi zaman lafiya da Aryan, ina zaman lafiya tsakanin wuta da audiga fisabillillahi?.Rungumeta Aunty Luna ta yi suka karisa cikin ɗakinta, a gefen gado ya zaunar da ita game da ɗago haɓarta tana goge mata hawaye tana faɗin. “Sorry my sister, yo shiru ki faɗa mun menene yake damunki? Waye ya taɓaki?”. Ai gagara yin shiru Rimsha ta yi, tana wani irin shessheƙa tamkar zata shiɗe, gwanin ban tausayi.*Jama’ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba’ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*

Back to top button