Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 45 Book 2 Complete Novel

  

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

_💋Boss Bature💋_

********AUNTY BABBA************

Zaune take agaban dressing mirror ranta a matuƙar 6ace fuskar nan tayi jawur saboda kukan da taci,ta zabga uban tagumi zuciyarta sai faman tafarfasa take yi,bakomai bane ya haddasa mata wannan 6acin ran ba face General ishaq daya hanata zuwa abuja,duk yarda ta kwallafa rai akan zuwa abujan ya hanata,sai da ya bari tasha wankanta ta kimtsa cikin leshi ta yafa mayafi ta ruƙo jakarta, tana fitowa ta same shi zaune a falo jikin shi sanye da gajeran wando baki,wani irin kallo yabi ta dashi tare da cewa”Ina zuwa,”

washe masa baki tayi tare da cewa”Abuja mana,kai fa kace zamuje duba jikin fawan,”

kai tsaye yace”ae nafasa wannan,ni kaɗai zanje inyaso ko a waya ne kun kira Abba kuyi masu Allah kyauta,”

Tur6une fuska tayi tare da cewa”dan Allah idan wasa kake mun ka daina,”

  Shima ya tamke fuskarshi yace”ba wasa nake ba,ni kaɗai zanje inyaso saina wakilce ku,”

  Hankali tashe tace”Haba Abban hafsat sai da na kammala shirina, tafiya kawai ta rage zaka ce wai an fasa gaskiya ni sai naje,” ta faɗi tare da ruƙe qugunta tamkar zata buge shi,

  Miƙewa ishaq yayi fuskarshi ba wasa yace”to ki sani muddin kikasa ƙafarki kika bar gidan nan without my permission hmmmmmm ke kinsan mai zai biyo baya, 

  Yana faɗin hakan ya fuce ma daga falon yabarta,

  da gudu ta koma bedroom ɗinta a ƙasa ma tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado ta faɗa tadinga shan kukan baƙin ciki har bacci ya kwashe ta,

Ta jima tana baccin kafin ta tashi cike da kunci ta koma gaban mirror ta zabga tagumi rai a6ace,

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

Ta jima tana tunanin meyasa general ishaq ya hanata zuwa gidansu don ta duba jikin fawan,abun ya ɗaure mata kai saboda shi da kansa yace zasu je dubiya atare amma ya canza ra’ayinsa yanzu,

   tsoki ta buga tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake agaban mirror ɗin,contact ɗinta ta shiga ta lalubo numbar wayar HAYAAM ta danna mata kira,ringing ta shiga yi kusan sau uku ba’a ɗaga ba,

tana a cikin toilet kiran ya shigo a lokacin wayar na hannun wani matashin saurayi dake zaune saman wani haɗaɗɗen gado, daga shi sai shorts ajikin shi ya baje abun shi, ganin sunan Aunty Layla ya bayyana akan screen ɗin wayar yasa shi ɗaga murya tare da cewa”babe!babe!ur phone is ringing,

  Daga cikin toilet ɗin tace”wanene ke kirana?in dae mommy ce ko Abi ka kashe wayar gaba ɗaya bana son takura,

  “No basu bane,wannan auntyn naki ne Layla,”

Jin sunan Aunty laila yasa ta yin wuff ta fito daga cikin toilet ɗin, doguwa ce sosai fara sol babu ko tabo ajikinta kai kana ganin fatar nan zakasan cewa ba ƙaramin kuɗi take kashe mata ba saboda yarda take ɗaukar ido,

ta ko’ina Allah ya bata ga dogon wuya,

Bin ta da kallo saurayin yayi sam yagaza janye idonshi akanta sai kace batare suke rayuwa acikin gidan ba,

Towel ne kawai ta ɗauro ajikinta cikin hanzari ta miƙa hannunta tare da kar6ar wayar tana cewa”nashiga ukuna Aunty laila kuma a awaya?yanzu zata rufe ni da faɗan ba gyara ba dalili mtswwwwww

  Ta ƙarasa maganar tare da ɗaga kiran ta kara a kunnanta tana faman zazzare manyan idanunta,

A ƙule aunty babba tace”ina kika je ne inata faman kira ba’a ɗagawa?

Cikin en ina tace”Nashiga toilet ne yanzu na fito na sami wayar tana ringing asaman gado,

aunty babba tace”hmmmm kina a gida ko kina awaurin yawon gantalin naki?

Cikin sauri tace”am….ina a gida……” bata bari ta ƙarasa ba a tsawace tace”Karki kuskura kiyimun karya Hayaam ina sane da duk wani yawon gantali da kikeyi ana sanar mun da komai,saboda tsabagen iya shege da fitsara idonki ya buɗe wuyanki ya isa yanka hada tattara kaya da komawa gidan saurayi da zama koba haka akai ba? Ta tambaya azafafe tamkar tana a gabanta,tuni ran Hayaam ya 6aci juyawa ta ɗanyi ta kalli Sofwan dake kallonta bai sauraron me suke cewa amma ya lura da yanayin fuskarta daya canza saboda hayaam bata iya 6oye 6acin ranta duk mun ƙanƙantarsa,

  sassauta muryarta tayi tare da cewa”Aunty layla mgnr da kika faɗa gaskiya ne,i can’t hide it 4 u ni bazan iya rayuwa a cikin gidan nan ba saboda baida marar raba da kwango a wurina,fentin gidan duk ya ƙoƙe kamar munfi kowa talauci a layinmu,bama wannan ba ɗakinmu bai da banbanci da kwankon ashana katifa ce kawai duk ta gwaigwaye sai akwatin kayan mu, ko na fidda kuɗi na siyi furnitures mommy bata barin komai sai dae kawai nadawo na taras ta siyar da komai ta hanani jin daɗin rayuwa kuma kinsan ni macace mai son rayuwar hutu rayuwar ƴanci wannan shine dalilin dayasa nabar masu gidan don wlh ko abincin da suke ci ynx 6ata mun ciki yake yi saboda wannan yarinyar ƙanwar Amani ita suke ba girkin gidan,yarinyar da bata wuci 14years duk wani aiki na gidan ita take yin shi har yanzu mommy bata haƙura ba akan ɗaukar fansar abunda mommynsu tayi mata” yadda take magana kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ba ƙaramar ƴar duniya bace magana take tana faman wurga ido tana kora jawabi 

Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa”ae ni tayimun dai dai,wato wayewa tasa kin manta da irin azabtarwar da matar nan tayi mana shine har kike ganin laifin mommynmu,kwara su kashe yarinyar ma kowa ya huta ae ni nafison su wulaƙantata,” ta fadi tana faman huci kamar tana agabanta,

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Ganin wayar tasu ba mai ƙarewa bace yasa Sofwan tasowa daga saman bed dinsa ya sauko, takawa yayi izuwa bayan Hayaam dake atsaye ya rumgumota tare da zagayo da hannayen shi ta waist ɗinta sannan ya kwantar da kanshi daga gefen wuyanta yana cewa”babe yaushe wayar zata ƙare?nifa a ƙagare nake,

ƙasa ƙasa da murya tayi tare da cewa”pls karkaja min bala’e,” 

Muryar aunty babba ce taci gaba cewa”Yanzu abunda nakeso dake kibar komai da kike yi ki tafi abuja gidan surukaina acan nakeso ki cigaba da zama,

  Ƙiris ya rage hayaam ta saki wayar dake a hannunta saboda jin sa6on da auntyn nata ke faɗi, cikin ruɗu tace”haba dae Auntyna amma dae wasa kike yi ko?if not ni mai zai kaini gidan in-lows din mu da zama abun ma babu daɗin ji……..,

Tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa”ke dalla yi mun shiru!duk ƙoƙarin da nakeyi akanki bakya gani!kina nan sake da baki ga wata can a gidan matsayin yar aiki Abbansu ya mayar da ita ɗiyarshi sun gatanta yarinyar har makaranta take zuwa,idan har kikayi gangancin rasa wannan damar ta komawa gidan da zama ina mai tabbatar maki da cewa Kin rasa cikar burinki na har abada,” shiru hayaaam ta ɗanyi gabanta na faɗuwa saboda ba abunda ta tsana fiye da ace zata Rasa SURGEON GENERAL RAFAYET saboda mutuwar son da take yi mashi ta kwallafa rai akanshi a lokacin baya tasa naci sosai akan shi sa’adda suke zuwa gidan sosai,amma tun da ta lura cewa kafin ya ma ɗaga idonshi ya kalli mace aiki ne don sai da ta share 2 weeks a gidan sau ɗaya suka ta6a hada ido shima ɗin by mistake ne ya ɗago a lokacin,abun ya tsaya mata arai, yadda take da kyawun surar nan babu namijin da zaiganta ya kawar da ido batare da ya neme ta ba sai akan SGR,tun a lokacin ta soma fidda rai akan shi amma yanzu aunty laila ta soma dawo da ita kan network,

lumshe idonta tayi tana tuna kyakkyawar fuskarshi har lokacin sofwan na manne da jikinta ya lafe mata kamar wani maye,

  ƙara kara wayar tayi akan kunnanta tace”Aunty laila komai zan iya yi akan na mallake shi,saboda shine namijin daya haɗa komai da nake kwaɗayi nake tsananin so a jikin ɗa namiji,amma abunda bansani ba aunty layla shin kina ganin zasu kar6e ni in naje gidan a matsayina na ƙanwar matar yayansu?

Wani irin shu’umin murmushi Aunty babba ta saki wato anzo dai dai wurin da tafi so, miƙewa tayi daga zaunen da take agaban mirror tashiga zagaye bedroom ɗin nata tana cewa”Hayaaam baki da Matsala indae a gidan nan ne! Kinsan yarda Abbansu ke da son ƴa’ƴa hannu biyu zai kar6eki abu daya kawai nasani shine dole sai da iznin Abi sannan zai kar6eki don haka kibarmun wannan a hannuna ni zanyi magana da mommynmu tunda ita ke juya shi da zarar tayi mashi magana zai amince!abunda kawai nakeso dake hayaam shine kiyi gaggawar komawa gidan da zama acikin watan nan!Ke bama sai kin je da komai ba tsurarki zaki tafi batare da trolly na kayanki ba,saboda inaso ki fara fakewa da cewa kinje duba Fawan ne da bashi da lafiya daga nan kawai saikiyi zaman ki dirshan babu mai tanka maki saboda duk matasan gidan miskilai ne babu ruwansu,da ace dae yana da ƴa’ƴa mata shine za’a samu matsala kinsan mu mata da bakin ciki da hassada muke….’

  Murmushi kawai hayaam ke saki tana faman lumshe ido tare da cizon pink lips dinta saboda shock ɗin da takeji na sofwan dake bin jikinta da hannun shi yana shafa ko’ina,

  “Auntyna indae ni ce just karki samu damuwa,ki ƙaddara cewa gani can ma acikin gidan ina watayawa ta,ita kuma wannan yarinyar da kika sanar mun cewa tana zaune a gidan tuni zansa su yi mata checking out badai ni bace ba hmmmmmm,

  Dariya aunty babba ta saki tare da cewa”har naji sanyi araina,burina na dab da cika,”

Download>>> Yar Harka Complete Document

  Sun jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama da junansu,

   Buge hannun sofwan tayi tare da cewa”duk kabi ka takuramin wai kai wani irin jarababben mutun ne mai nacin tsiya haba mtwww,”taja dogon tsoki

  Baki asake yabi ta da kallo tare da cewa”ni kike ma tsoki wai?wato wannan haɗamammar auntyn taki takira duk ta tunzuraki akan abunda bazai ta6a faruwa ba,duk naji mai kuka tattauna da ita,

  ya fadi yana faman sakin hucin 6acin rai,murmushi hayaam ta saki tare da cewa”Sofwan zamana dakai ya ƙare!!!!!!!

  Zaro ido waje yayi yana kallonta hankali atashe yace”saboda me hayaam?kada kiyimun haka don Allah!amma dae nasan wasa kike mun ko?

  ƴar dariya tayi kafin tace”na ta6a maka wasa irin wannan?zanje na nemi namijin duniya ne!cikakken namiji jarumin gaske wanda ya kasance burin kowace ƴa mace ne shi bazanyi gangancin rasa cikar burina ba sofwan…….

Bata ƙarasa ba ya dauke ta da mari ji kake faaaauuuu! 

  Rai a 6ace yace”Wlh baki isa ba hayaam ki katse mun jin daɗina ba!!saboda ke dakikiya ce sam bakisan meke maki ciwo ba wannan wani irin abun kunyane zaki kwasa kawai ki koma gidan surukanku da zama?Anya kuwa yayarki ba mahaukaciya bace…..

   bata bari ya ƙarasa maganar tashi ba ta zame hannunta data dafe kuncinta dashi ta daddage ta zabga mashi zafafan maruka har guda uku sannan tace”karka kuskura ka ƙara kiran auntyna da sunan mahaukaciya!!maganar tafiya kuma ba fashi sofwan inka ga ban tafi ba to wlh numfashi na ne ya tsaya don ko ba ƙafa saina je,😳

  Tuni sofwan ya rikice ganin yarda hayaam ta zabga masa mari batare da jin komai ba,duk irin yarda yake tarairayarta don karya rasa ta amma lokacin guda auntynta ta canza mata tunaninta,

  Kallonta ya shiga yi yana girgiza mata kai yayin da idonshi suka cicciko da kwalla muryarshi a kasalance yace”Hayaam kada kiyimun haka dan Allah!saboda ke na wulaƙanta iyayena na baro komai nawa don muyi irin rayuwar da kikeso,wannan gidan fa duk don saboda ke na gina shi hayaam,ki duba gidan da iyaye na suke ciki duk ya rakwakkwa6e amma saboda ke na gidan wannan katafaren gidan ko don saboda wannan pls hayamm kada kibarni komai kikeso zanyi maki shi,” yayi maganar tare da zubewa saman guiwowin shi a gabanta yana faman sharara hawaye,amma maimakon yaga alamun tausayi a idonta saima ta fashe mashi da dariya tashiga tafa hannaye tana cewa”sofwan kaifa dakanka kace ka wulaƙanta iyayenka saboda Ni?shin ni wacece a wurinka?mutumin da bai daraja iyayensa ba musamman uwarsa data tsugunna ta haifeshi taci baƙar wahala kanshi!ga kuma mahaifinsa daya fitar da gumi wurin nema masa kyakkyawar rayuwa duk bai duba wannan ba,burinka kawai ka farantama wasu can waɗanda basu son ciwonka ba,waɗanda ko yau ka faɗi ka mutu wlh shewa zasu yi suce Allah raka taki gona,shine har kake mun kwatance da ka wulaƙanta iyayenka don saboda wata banza can Ni?hanyar Aljanna nake sanya ka kota wuta?ko zan taimake ka ne ranar lahira?sofwan haƙƙin iyayenka ma kawai ya isa ya tarwatsa dukkan wani farin ciki na rayuwarka!!idan ma naci gaba da ra6arka nima zan shiga matsala ne don haka kawai muyi break up kawai kowa yayi rayuwarshi,”

  ta ƙarasa maganar tare da ruƙe waist dinta tana kallon shi a tsiyace,

  Miƙewa yayi daga kneel down din da yayi ya kalleta da fuskar tausayi yace”kada kiyi mun haka hayaam indae alaƙata da iyayena ne zan gyara komai…’

  girgiza mashi kai tayi tare da cewa”na yaushe sofwan?hmmm ba don Allah zama kayi masu ba sai don saboda ni abanza kam,shiyasa koda yaushe soyayyar SGR take ƙara ninkuwa araina duk da irin tarin dukiyar dake gare shi hakan baisa ya canza ma iyayenshi ba ko wani nashi,zokaga Namijin gaske mai tsananin biyayya ga iyayensa wanda yasan darajarsu yake binsu sau da ƙafa kaifa? Har yau mahaifinka bai daina siyar da kifi a gefen titi ba, ga Mahaifiyarka cen kullum safiyar Allah sai tafito da murhu kopar gida tana suyar ƙosar da kunu,taya ma zan cigaba da kasancewa dakai!!? Kana da arziƙin da zaka iya ciyar da karuwai ka gina ma iyayensu gida ka kuma gina masu su kansu Amma iyayenka fa!!!?

  shiru Sofwan yayi yana kallonta idanun shi sunyi jawur dasu ga wani ƙululun baƙin ciki daya tsaya masa a maƙoshinsa,

  Wuce wa hayaaam tayi wurin wardrobe dinshi saboda anan kayanta suke nasawa, hannu tasa ta buɗe wurin kayanta tana raira waƙar nan ta namej dayake cewa”ko babu mota ba abun hawa wlh saina jee,” 

  A wani irin fusace Sofwan ya cafki hannunta data ruko bra dinta dashi,dakatawa tayi da yin waƙarta ta tace”Malam sakarmin hannu na,”

  Yana wani irin huci yace”Hayaam baki isa kibar gidan nan ba, batare da kin mayar mun da duk wani abu dana kashe maki ba!!wlh bazaki ci bulus ba,duk kin taƙaitani duk ƙarshen wata saina kawo maki kayan abinci kwalin indomie kwalin taliya da sauran kayan abinci, sannan duk ƙarshen sati muna zuwan shopping mall dake nayi maki siyayya kuma mu fita restaurant cin abinci,ga kuma kuɗin mayukan da nake siya maki su kansu kudinsu yakai na dubu dari biyar,in kin ga kin bar gidan nan to ki tabbata kin haɗa mun kuɗaɗe na kin mayar mun dasu,” ya ƙarasa maganar yana jifanta da wani irin kallo,

  ta6e baki tayi tare da cewa”Naji duk zan biyaka ni kuma da me zaka biyani jikina da kayi amfani dashi?donni ma bazaka Ci bulus ba tunda ba uwar mutun ta haife ni ba,ka biyani budurcina nima saina biyaka kudinka”A shagale take maganar tana faman sakin murmushi,

  Shiru sofwan yayi yana faman mazurai aransa yana tunanin taya zai biyata virgin dinga da take magana akai?

  tsoki taja tare da buge hannunshi tabar shi tsaye a wurin ta koma daga gefe tana zura brazier dinta,

  Muryarshi ce ta kuma katse ta da cewa”naji wannan tabbas bazan iya biyanki budurcinki ba,amma inaso ki sani bazan bari ki ɗauki ɗaya daga cikin abunda nasiya maki ba da kudina,daga ciki kuma hada kayan sawa don dama a tsiyace kikazo gidan nan,

Download>>> Babban Yaya Complete Document

  harara ta wurga mashi tare da cewa”Matsalarka ce wannan!ae ni abun kunya gaba na bashi ba baya ba,in ka hanani sa sutura sai in tafi a zir abuna,”

ganin tana shirin ɗaura mashi hawan jini yasa shi buga jikin wardrobe din da hannunshi yana kallonta idonshi jawur rai a tsananin 6ace ya fuce yabar mata ɗakin gaba daya,

Murmushi tasaki tana cizon la66anta aranta tace”ƙaramin ɗan duniya har ni zakayi wa barazana,”

*******************

Tsare ta da ido hafsat tayi wadda shigowarta kenan  bedroom din ta,

Ta jima a la6e tana sauraron firar da mommyn nata keyi da Hayaam a waya, sai da tabari ta kammala sannan tashiga daga cikin ɗakin tana kallonta, tunkan tace wani abu aunty babba tayi saurin cewa”to ƴarsa ido uban me yakawo ki dakina?

murmushin takaici hafsat tayi kafin tace”narasa meke damunki mommy!gaba daya naji wayar da kikayi da aunty hayaam,saboda me zaki ce ta tattara kaya ta koma gidansu Abbana da zama?wannan wane irin abun kunya ne ace ƙanwar matar yayansu tana rayuwa acikin gidansu? menene alaƙarta dasu?gsky wannan tsarin sam baiyi ba mommy yakama ki dakatar da hayaam daga zuwan gidansu……..’

tunkan taƙarasa aunty babba ta kwatsa mata tsawa tare da cewa”munafuka!!ashe la6e kikeyi mun ni narasa gane meke damunki hafsat!!tunda waɗancan yaran da omar yakawo mun suka zo gaba ɗaya duk sun canzamin ke, yanzu bakya goyon bayana……’ Tana magana tana yin nuni da hannunta dake ruke da wayarta,

ta6e baki hafsat tayi tare da cewa”Mommy kenan,mgnr da kika faɗa gaskiya ce,Jahad da hossana ba ƙaramin sauyani su kayi ba saboda akansu na fara tausayin wani dan adam a duniya,sun goga mun kyawawan ɗabi’unsu da halayansu waɗanda ke baki ta6a gwadamun ba,haƙiƙa nayi rashinsu sosai kuma ina fata Allah ya ƙara hadani dasu wata rana…..’ murya asanyaye tayi maganar,

  Sakin baki Aunty babba tayi tana kallonta kamar me son gano wani abu can dae tace”Hafsat kodae kece kika sa Abbanki ya hanani zuwa abuja ganin jikin fawan?ina zargin hakan!!

kaitsaye tace”Nice mommy!ni nasame shi na roƙe shi akan cewa kada yabari ki tafi ke kaɗai sai tare dani saboda bana jin daɗi yanzu bazan iya zuwa ba,”

  a fusace tace”Meyasa”!

Murmushi hafsat tayi tare da cewa”Saboda ba don Allah zakije ba!bakuma don kije duba jikin fawan ba face donki je ganin yarinyar da Aunty Amani ta sanar dake, ni kuma gsky bana son ma ki ganta balle har kiyi yunƙurin cutar da ita, don kuwa bazan sake bari ki cutar da wani ba saboda wani buri can da kike dashi wanda bazai ta6a cika ba…….’

Da gudu hafsat ta fuce daga dakin ganin yarda Aunty babba ta zabura zata cafkota takai mata bugu,’

  bedroom ɗinta ta koma tana faman tiƙar dariya hadasu dafe ciki,

Ita kuwa aunty babba tuni idonta sunyi jawur saboda 6acin rai,tama rasa me zatayi ta huce,ashe hafsat ce ta hana ishaq barinta taje abuja yau lallaikam zata ci ubanta ne dani take magana,

Ta fadi tana faman huci,

*********AFTER 2WEEKS************

*Bayan Sati uku*

Tuni jikin fawan ya ɗan murmure yaji sauƙi sosai har yana iya miƙewa ya taka yaje inda yake so hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,a 6angaren su twins kuwa murna har ba’a magana saboda alert ɗin kuɗin da mommynsu ta turo ta wayar jahan a cikin dollar acct dinsa, a tsakar dare alert din yashigo a lokacin suna maƙale da juna kamar yadda aka saba,gaba ɗayansu suka buga shewa cikin jin daɗi ba don komai ba sai don zasu rabu da matsin Haroon su huta,a daren ranar har nafilar dare sukayi atare suka roƙi Allah akan ya yaye masu masifar dake damunsu, sun sha kuka kamar kamar me,sannan kuma sun shirya zuwa bank domin su kar6o masa kuɗinshi miliyan tamanin su damƙa mashi,😣 dama sai zarya yake yi masu kullum safiyar Allah yana musu barazana,ba don sun nuna mashi kuɗin ba dake cikin acct dinsu ba ya gani awayarsu, da bazai ƙyalesu ba,

DOWNLOAD: “HARIJI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT

A 6angaren Hossana da Jahad kuwa hmmmmm just speechless,wata irin rayuwar hutu da jin daɗi suke gudanarwa acikin hamshaqin gidansu,babu ruwansu da kowa su biyu abunsu sai Camillah dake yawan zuwa dubasu wani lokacin takan tsaya ta kwana ma acikin gidan,ba ƙaramin gyarasu tayi ba,domin kuwa sun canza fiye da tunanin mai tunani,fatarsu kanta abun kallo ce, ga wasu irin surorin kyau da suka bayyana ajikinsu,sun koma rainon Madara rainon bonvita 😂

Ƴancin da su hossana suka samu ko mutanen nigeria a 1960 basu samu makamancin shi ba,hossana fa har wasu kumatun jin daɗi tafara ajiyewa🤣 dama bata wasa da abinci gashi Omar ya cika masu store da kayan abinci kala kala, ga freezer dinsu dake shaƙe da kayan sha,kullum in jahad tayi mata maganar tadinga ci ahankali sai tace”ina ruwanki!In suka ƙare yaya Omar zai siya mana wasu,” 🥱

Marshal omar bai barsu hakanan ba, sai da ya ƙara masu security guards har mutun huɗu, Osman kuma shine a matsayin drivern da zai dunga kaisu School da wuraren shaƙatawa,tuni ya cike masu form na school koda akazo wurin sanya sunan uba ya tambayesu sunan mahaifinsu sai cewa suka yi “kasa mana sunanka kawai ya omar,mu bamu da uba,” wani irin kallo yayi masu tare da cewa”ban shirya haramta ma kaina ɗaya daga cikin ku ba,don haka zan sanya maku sunan Uncle ɗina ne a matsayin Mahaifinku amma banawa ba,’

Sam basu gane mai ya omar ɗinsu ke nufi ba da cewa bai shirya haramta ma kanshi ɗaya daga cikinsu ba,sun dai bar abun ne kawai azuciyarsu,

  Alhamdulillah Omar ya kammala cike masu form da sunan Uncle dinshi,JAHAD ABUSUFYAN da kuma HOSSANA ABUSUFYAN,ba ƙaramin daɗi suka ji ba saboda jin ya saka masu sunan mutumin nan da goggon katsina ta ƙaƙaba masu amatsayin Ubansu,

sunan makarantar da suka fara zuwa D.A International acadermy wato makarantar da Sehrish ke zuwa🤔

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Back to top button