Hausa novels

Halysaah Page 23 By Khaleesat Haydar

Washegari Wednesday da yamma Jay na zaune parlon dake sama tare da AJ da ya maida parlon wajen kwanansa, don tun da Khaleesat ta kwana dakinsa tsakaninsa da dakin kawai ya shiga ya dau kaya, ko bandakin dake dakin baya shiga, Jay dake kallonsa yace “Yanzu dai zan iya dawowa dakinka kenan tunda ka tashi a dakin?” AJ yayi banza da shi yana ci gaba da hada few kayansa da yake yi a tsadadden box dinsa da zai yi tafiya gobe, Jay yace “To wai kayi booking flight din ne da naga kana hada akwati?” AJ yace “Bana son Airline din da na gani jiya, anjima zan siya Ticket din Turkish Airlines” Jay yace “How many hours connection time for the layover?” AJ yace “Baya wuce 2 to 3 hours, ko ma bazai kai haka ba” Jay yace “Will you mind travelling same plane with my Housemate? I just remembered I will be meeting my Mami at the UK, tare za mu koma Nigeria da ita daga can” AJ yace “Of course I will mind Jawwad, because my OCD will never allow me board the same plane with her, ga Airline kala-kala ka nemi wani ka siya mata ticket mana, what is my business with her da zaka hadani da ita sai kace ni na kawota America, there is this Airline na mance sunansa Economy class ticket dinsu naga is just 600 dollars, you can get her the ticket as the Good Samaritan that you are” Mikewa Jay yayi bai ce masa komai ba ya bar parlon. Wajen karfe biyar da rabi Jay ya kwankwasa ma Khaleesat kofa, bayan ta bude yace “Ba abinda zaki dauka a can apartment din da zaki koma da shi Nigeria Housemate?” Khaleesat tace “Ohk, zan dau wasu kayan” Yace “To ki shirya sai in kai ki can ki dauka” Khaleesat na kallonsa a hankali tace “Pls kar kace zaka siya min ticket ina da kudi a account dina, i will get the ticket” Yayi murmushi yana kallonta yace “To Hajiya me kudi, kudin zai isa ki mana booking har ni da AJ?” Tana murmushi ta fara wasa da gefen gyalenta tace “Sae dai kai kadai, ni ai ban san wani AJ ba” Akan kunnen AJ da ya taho daga parlor zai sauka downstairs, ya tsaya yana kallonta babu fara’a, Jay ya juya ya kallesa yana murmushi yace “Je ki shirya ina jiranki downstairs Halysaah” Juyawa tayi ta tura kofar dakin a hankali, ko da Khaleesat ta sauko downstairs ta tarar da Jay yana jiranta, and it’s almost 6pm, ya mike suka fita daga parlon, bayan sun bar compound din a motarsa ya ɗan kalleta yace “Kinga kin kara tsokanar AJ ko?” Ta marairaice tace “To ni ai ban san yana wajen ba, why is he always eavesdropping?” Jay yayi dariya yace “Ni dai ba ruwana” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, she can’t even wait ta dena ganin AJ she is already exhausted with him and his problem, she can’t wait to stop seeing him, suna isa apartment dinta abinda ya faru ya dawo mata fresh, kawai sai take ganin kamar trauma din ya dawo mata sabo a kwakwalwarta, lkci daya duk jikinta ya mutu, haka dai jikinta ba kwari ta tafi dakinta ta fara hada kayan da zata hada shi kuma Jay ta bar sa parlor yana jiranta, sau uku Safiyya na zuwa gidan debo mata kayanta kwanaki kuma duk Housemate dinta ne ke kawota, after a while Khaleesat ta gama daukan abubuwan da zata dauka a akwatinta, sauran kayan dakin duk ta haɗa su waje daya, ko zata dawo kasar ko bazata dawo ba ita dai bata sani ba, ta kuma bar ma Allah komai, ta gama tidying ko ina a dakin sannan ta fito wajen karfe shidda tana jan akwatinta a hankali zuwa parlor, kwance taga Housemate dinta kan doguwar kujera ya fara bacci, ta tsaya tana kallonsa, sai kuma ta tafi kusa da kujeran still looking at him ta ɗan tapping din jikin kujeran gently, a hankali ya bude ido sai kuma ya mike zaune yace “Kin gama ne?” Tace “Are you sleeping?” Yace “A’a, kawai na kwanta ne ina wani tunani, it’s even time for magrib bari inyi sallah, kema kije kiyi” Bandakin dake parlor ya shiga ita kuma ta koma dakinta, sai bayan wani minti sha biyar din suka bar gidan, tunda suka fito gidan Khaleesat tayi shiru, shi ma kuma bai ce komai ba, amma ya lura mood dinta ya canza, kawai ya sa a rai bazai tafi da ita gida a haka ba, after a while ya ɗan kalleta yace “Would you mind watching a movie in Cinema tonight?” Khaleesat ta juya ta kallesa, sai kuma ta sauke idonta bata ce komai ba, yace “Ko baki kallo?” Tace “Ina yi, amma ba sosai ba” Yace “To yau za ki yi” Waje ya samu yayi parking, ya dau wayarsa ya shiga website din Cinema din dake Maryland to check their schedules for that day, yayi selecting movie din da za su kalla, da lokacin da za su kalla sannan ya siya masu ticket aka turo masa ta online, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa, without looking at her yace “I hope you will enjoy the movie” Ita dai bata ce komai ba har suka isa Cinema din, ya siya masu popcorn and lemonade, sannan suka nufi cikin Auditorium din da za a haska film din da ya siya masu ticket, in some minutes kuma za a fara haska film din, wannan ne zuwan Khaleesat Cinema na farko a rayuwarta duk da a baya babu irin takuratan da Safiyyah bata yi akan su je tare da frnds din Safiyyar amma ita dai bata yarda taje, suna shiga Jay ya fara cin popcorn dinsa kamar abinda ya kawosa kenan, ita dai Khaleesat dama bata wani damu da popcorn ba hakan yasa take ɗan ci jifa jifa tana kallon film da ake, she is beginning to like the film hakan ya sa ta tattara gaba daya hankalinta kan film din, after almost 35 mins da fara film din ta juya ta kalli Jay taga bacci yake, ta dade abu bai bata dariya haka ba, she couldn’t believe he is seriously sleeping abun sa, ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya a hankali, she don’t know why she feel relieve a duk sanda take tare da shi, there is never a boring moment with him, gently ta kai hannu kusa da shi ta dauki popcorn dinsa daya, he was still sleeping ta dinga kallonsa maimakon film din da ya kawota ta kalla, idan yana bacci komawa yake so gentle and calm, a nan ne kuma ainahin handsomeness dinsa ke fitowa, if there is the sleeping princess then he will be the sleeping prince, har awa daya da fara film din Jay baccinsa yake kuma ta kyalesa bata tashesa ba, she watched the movie har sai da ya kusa karewa and she really enjoyed every bit of it, ta juya ta kallesa sai kuma ta dau popcorn daya ta matsa dai dai kusa da shi a hankali ta saka masa a baki, da sauri ta gyara zamanta ta maida hankalinta kan movie, ya bude ido, taji yace “What a nice movie” Sai a sannan dariya ya taho mata ta juya ta kallesa tace “Ain’t you ashame of saying this?” Yana gyara zama yace “You don’t like the movie? But it’s nice, i like it” Tana murmushi tace “To in ka gama baccin ka tashi mu tafi, ni na gama kallona” Ya ɗan shafa kai trying not to smile yace “Wa yace maki bacci nake, i was only meditating duk nasan abinda ake yi ai, ba gashi an kusa gamawa ba” Ita dai murmushi kawai take tace “Naji, tashi mu tafi, a hanya sai ka bani labarin film din don akwai inda ban gane ba” Yayi shiru yaki cewa komai, tana danne dariyarta ta tashi ta dau sauran popcorn dinta da nasa, tashi yayi ya bi bayanta suka fita daga Auditorium din, lokaci lokaci take juyawa ta kallesa don ta tabbatar he is not walking and sleeping at the same time, da sauri ya jawota ta fado jikinsa bayan tayi missing step saboda waige waigen sa da take sai kuma yayi saurin saketa, within few seconds aka yi hakan, ta rufe bakinta da hannu don ba karamin tsorata tayi ba, yace “Yanzu da kin fadi kika fara min kuka kilan har mu kai gida” Ta marairaice tana kallonsa, Softly yace “Alright Sorry Halysaah” Ta juya ta fara tafiya a hankali, a haka suka fita daga cinema din bata sake waigen bayanta ba, yana biye da ita yana kallonta har suka isa gun da yayi parking. Wajen karfe goma suka isa gida bayan yayi parking ta juya ta kallesa a hankali tace “Thank you so much” Ya mata murmushi yace “You are welcome House mate” A haka suka sauka daga motar tana biye da shi suka shiga gidan, kafin ta shiga daki yace “Get me ur travelling documents” Ta kallesa zata yi magana ya daura fingers dinsa biyu a lips dinsa, ta sauke idonta sannan ta juya a hankali ta shiga cikin dakin, after some minutes ta fito ta mika masa, ya amsa yace “Good job, zan tura maki ticket din ta Email dina, sai da safe” A hankali tace “Allah ya tashe mu lafiya” Juyawa tayi ta koma cikin dakin ta kulle kofar, Jay ya tafi parlon sama yaga AJ kwance kan Couch yayi bacci, shi dariya ma yake basa, kawai mutum ya dora ma kansa wahala, juyawa yayi ya wuce dakinsa, wajen karfe sha biyun dare Khaleesat na ta juye juye ta kasa bacci ita kanta ta rasa dalili, message taji ya shigowa wayar Jay dake wajenta ta mike zaune ta jawo wayar tana duba message din taga Email ne ya shigo, tana bude Email din taga ticket din ya turo mata na Turkish Airline, kuma Business class seat, bata san me yasa taji hawaye ya cika idonta ba, ta ajiye wayar a hankali ta koma ta kwanta.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button